Advertisements
Chapter 2 Reading ALHINI by Zee Mmn khadye BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALHINI by Zee Mmn khadye

Author :  Zee Mmn khadye Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 10

3K to 6K   out of 27.3K words

'kawayensu
da dama wad'anda mafi yawansu sunada aure, marassa auren basuda yawa, wasu ma harda
'ya'yansu.

A gajiye suka dawo, gidansu indo suka sauka, lnnar indo tayi masu sannu,
Sannnan suka wuce d'aki suka cire mayafansu suka fito suka d'aura alwala suka
gabatar da sallar la'asar sannan lndo ta d'auko masu abinci suka fara ci, dambun
masara ne yaji zogale, sai 'kamshin man gyad'a ke tashi,
Sun kammala indo ta d'ebo masu ruwa me sanyi a tulu suka sha, sannan suka cigaba da
tattauna yanda shirin bikin ze kasance, sun shirya taron 'kawayen amarya ana gobe
d'aurin Aure.

Sai gab da magrib suka fito indo zatayima Laraba rakiya ta tafi gida, suka gamu da
ilu saurayin lndo,

Laraba ce tafara gaidashi, ya amsa cike da fara'a,
Sannan lndo ta gaidashi cike da jin kunyarsa, ya amsa sannan ya maida dubansa ga
Laraba cikin tsokana yake magana "Amarya baki laifi,.... Laraba tayi saurin
tarbarsa "kada dai ka ida wannan magana dan ba yanda za'ayi mutum yakashe d'an masu
gida ace beyi laifi ba, kai ko kazar masu gida marya takashe sai tayi laifi
barantana d'a.

Suduka sukasa dariya, ilu yace yanzufa nan da kwana hud'u kinzama marya, tayi
dariya tace kai kuma nan da wata d'aya kazama ango, yace "inshaAllah ga kuma
amaryata, ya nuna indo ya wani kashe mata ido, cike da jin kunya indo taja hannun
Laraba tace zomuje dan Allah yamma na'karayi, haka suka wuce suka barshi cike daso
da 'kaunar indon sa.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Yau Yakama Alhamis, kuma daren d'aurin auren indo,
Yau ne kuma suke taro da 'kawayenta, sun taru gidan wata mata nan makwabciyarsu,
anata shewa, Kowa kagani cikin farin ciki, abin Alhamdulillah.
Indo ce tafito cikin shigar sabuwar atamfa riga da zani d'inkin yayimata kyau,
duk da simple ne d'inkin amma ya'kara fito da kyawunta,
Kafarta tasha 'kunshin Jan lalli, tayi kyau tafito amarya sak _(amma a 'kauyensu)_😜

Sun zauna Kowa na yaba kyawu irinna Laraba, wata daga cikin 'kawayensu me suna
hansai tace "gaskiya Laraba kinada kyau, inama ace yayana ne ze aureki ki ri'ka
haifo masa kyawawan 'ya'ya masu Kama dake.

Murmushi kawai Laraba tayi mata dan tasaba jin haka 'kawayenta da dama sunaso ta
auri yayyensu.

Hansai ta matso kusa da Laraba ta rad'a mata a kunne, wallahi yaya habu ya d'ad'e
yana sonki, abinda yasa be furta maki ba dan yaga lokacin bashida 'kud'i, tun bayan
rasuwar masoyinki na farko, yanzu kuma yadawo daga birni yayi kud'i, amma sai
yadawo da rashin sa'a ya iske saura sati d'aurin aurenki.

Wani mummunan fad'uwar gaba Laraba taji lokacin da hansai ta tuna mata da rasuwar
saurayinta, sai lokacin ta tuna da samari biyu nefa aka saka masu rana sai ana gab
da d'aura masu aure suka mutu.

Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta tasa gefen mayafinta ta goge, cikin ranta
tace _(Ya Allah kada ka kashe Hashim Allah sa muna da rabon kasancewa inuwa d'aya
nida shi)_
Ganin Laraba na hawaye yasa hansai tayi shiru da maganar datake tace "dan Allah
kiyi ha'kuri idan maganata ta 6ata maki rai, bata jira jin abinda Laraba zatace ba
ta tashi ta koma cikin 'kawaye aka cigaba da labari, amma tana yawan satar kallon
Laraba dan ganin yanda lokaci d'aya hankalinta ya tashi.

Indo tafito da biskit da cingam wanda suka kulla cikin ba'kar leda tashiga
rarrabawa, saida ta tabbatar da Kowa ya samu sannan takoma kusa da Laraba ta zauna,
tin tana cikin rabon kaya ta lura da 'yanda 'kawar tata take cikin wani irin
yanayi.

Sai gab da magrib 'kawayen amarya Kowa ya watse, lokacin lndo da Laraba suka wuce
gidan su Laraba.

Gidan cike yake da 'yan'uwa da abokan arzi'ki, anata hidima, nan suka gaisheda
mutanen dake tsakar gidan sannan, suka wuce d'aki.

Suna shiga Laraba ta cire mayafinta ta zauna da6as kan tabarmar dake shimfid'e
tsakar d'akin jikinta ba 'karfi ko kad'an,
Indo ta kalleta tace "Laraba na lura dake tun d'azu baki cikin nutsuwarki, wai me
ke damunki?

Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta tace, "lndo jikina duk ya mutu,
hankalina yakai 'kololuwa gurin tashi, gani nake Hashim mutuwa zeyi kamar yanda,
lro da sabi'u suka mutu... ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi.

Indo tace ki daina wannan tinanin acikin ranki, dan Allah ki daina kuka inshaAllah
Hashim baze mutuba, ay mutum baya mutuwa sai kwananshi sun 'kare, suma da suka mutu
dama Allah ya 'kaddaro hakan ne garesu.

Nan lndo tarin'ka rarrashinta, sai bayan isha'i sannan tabar gidan cike da tausayin
halin da 'kawarta take ciki.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Rana bata 'karya sai dai uwar d'iya taji kunya```

'Daruruwan mutane sun taru 'kofar gidansu Laraba domin halartar d'aurin Aurenta.

Yayinda itakuma a ranar ta tashi sukuku, jikinta ba 'karfi ko kad'an, matar 'kanin
babanta ce mal Lawal ta matsa mata tayi wanka ta shirya cikin wata koriyar atamfa,
riga da zani sannan tayi mayafi da kalar zanin atamfar,

A 'kofar gida kuma yan'daurin aure sungama taruwa dangin ango kawai ake jira a
d'aura aure, amma shuru basu ba labarinsu,

Mal Lawal yagama 'kulewa shiru kawai yayi, jira yake dangin angon suzo sai ya sauke
masu ta cikinsa snnan a d'aura auren.

Bayan kamar minti talatin mal Lawal yanata cika yana batsewa, sai ya hango ml bala
tare da wasu mutane guda biyu suna tinkaro su.

Cike da bala'i mal Lawal ya mi'ke dan ya saukema mal bala ta cikinsa, sai mal bala
yafad'a mashi wata magana wacce ni kaina bansan meya fad'a ba, sai ji nayi ya rafka
uban salati, nan mutane suka taso suna tambayarsa "meya faru?.

Cikin gida kuwa mata sunata tsegumin an'ki d'aura aure an shanyasu, jira suke a
d'aura atafi da amarya gidan mal Lawal daga can za'a d'auketa akaita gidan miji.

Baba salame ce wata makwabciyarsu tashigo gidan hankali tashe, bako sallama, da
sauri mutane sukayo kanta ana tambayarta "meya faru? Sai ta fashe da wani irin
kuka, wata magana tafad'a masu bansan me tafad'aba saboda cikin muryar kuka tayi
maganar sai jinayi suduka sun d'auki salati.



*To fah 🤔 nifa ansani aduhu😱 miye ake fad'a wanda yake tada hankalin mutane 😭🙆🏻*



_ku biyo zee mmn khady dan jin cigaban labari_

_08166169254_




🖊Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [21/08 12:15 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*😘


1⃣1⃣1⃣2⃣
1⃣1⃣to1⃣2⃣



🖊 zaune take d'aki tasha lulli6in zanin atamfa, wani mummunan fad'uwar gaba taji,
kawai sai jitayi hawaye suna gangarowa daga idonta, suna diga bisa jikinta.

Hayaniya tajiyo a tsakar gidan, a tunaninta an d'aura auren ne amma koda ta 'kara
saurarawa sai taji sa6anin haka *_Dukkan me rai mamacine, Allah ji'kan hashim_*

Wata uwar 'kara ta saki tare da fashewa da wani irin kuka, wanda yajawo hankalin
mutane zuwa gareta,

Lokaci guda tanemi numfashinta ta rasa, ta fad'i 'kasa sumammiya, nan fa aka shiga
tsananin tashin hankali, inna tayi saurin tallafota tana kuka, tana kiran sunanta,
da sauri aka d'ebo ruwa aka yayyafa mata sannan numfashinta ya dawo, amma duk da
haka batasan inda kanta yakeba.

A ranar dai anga tashin hankali, mutanen dasuka taru d'aurin Auren Hashim sune
sukayi jana'izarsa,

Bayan an kaishi makwancinsa aka dawo aka cigaba da zaman makoki, mutane kowa na
Al'ajabin yanda mutuwar Hashim ta kasance, dan kuwa ranar saida abokaninsa duka
suka taru, yashiga wanka bayan yafito ya shirya cikin farar shaddarsa, har sun fito
zasu tafi, yace masu kanshi na ciwo zeje chemist ya siyo magani.

Har wani cikin abokanin yace bari yaje ya siyo mashi, amma sai yace ya barshi kawai
zeje da kanshi, haka yatafi yabar abokaninsa suna jiran dawowarsa su wuce gurin
d'aurin auren,

Sun kai kimanin minti arba'in suna jiransa amma shiru,saboda haka suka Yanke
shaawarar binsa.

Innalillahi'wa,inna,ilaihirraji'un suka furta, lokacin da suka hango Hashim kwace
cikin ciyayi, ga jini duk ya 6ata farar shaddar dake jikinsa, amma ba Alamar rauni
jikin sa.

"To ta ina ya samu wannna jinin? Tambayar dasuka rika yima Kansu kenan wacce basuda
amsarta.

Nan suka d'aukeshi suka nufi gida hankali tashe,
Kafin kace miye labari yagama baje gari, abunka da 'karamin gari duk inda kanufa
maganar akeyi, dan wasu har sun fara yima abun wata mummunar fassara,

*_°Bayan sati biyu_*°

6angaren Laraba kuwa tun rasuwar Hashim batasan inda kanta yakeba sai yau tadawo
hayyacinta, abin mamaki batayi maganr mutuwar Hashim ba, kawai tacigaba da
hidimominta,

Wanka tayi ta shirya cikin, sabuwar atamfarta d'aya daga cikin wacce aka kawomata
na lefen aurenta, da aka maida gidansu Hashim suka 'ki kar6a,

Kwalliya tayi sosai, tayi gwanin kyau abunka ga 'kya'kyawa duk yanda tayi kwalliya
yimata kyau take, duk da tana tashin 'kauye, gyale ta dauko ta rataya kafad'arta
tazo gaban inna tace inna zanje gidansu lndo, inna ta d'ago idanunta ta kalleta
cike da damuwa, da mamakin yanda halayyar Laraba ta canja bayan rasuwar Hashim,
tace "haka zaki fita Laraba yakamata ki sanya hijab d'inki, ta turo baki tace ni
gaskiya inna bazansa hijab ba kamar wata me takaba, lnna ta girgiza kai cike da
takaici da kuma mamakin abinda ke damun 'yarta wanda har zatayimata magana tace ba
hakaba, wanda da ba halinta bane.

Koda taga Inna batada niyyar mata magana kawai sai tasa kai tafice, tace "saina
dawo, cike da takaici inna ta matse kwallan dasuka taru idonta tace "Allah maidoki
lafiya.

Tafiya take hankalinta kwance abinta, ga gyalenta rataye a kafad'a gashi ta wani
kashe d'aurin d'an kwali,
Kan hanya kuwa duk wanda yagamu da ita cikin wannan yanayin sai yayi mamaki, kafin
kice me mutane sun fara tsorata da Al'amarinta.

A zaure ta iske indo da saurayita ilu suna zance, Wanda yau yarage saura sati d'aya
bikinsu, dama suna cikin tattaunawa ne akan maganar Larabar ne, inda ilu ke
garagad'in indo a kan ta rabu da laraba indai har tanason su shirya, sai gata
tashigo, ta kalli ilu cikin sakin fuska tace ango kasha 'kamshi,...

Wani irin fad'uwar gaba ilu yaji lokacin daya jad'a ido da Laraba , saboda haka
jiki na kyarma yayima lndo sallama yabar gidan.

Cike da mamaki lndo ta kalli Laraba, tace "kawata yau kece da wannan shigar abinda
ban ta6a gani kinyi ba,
Laraba tayi dariya tace "lndo kenan yo kuma kullum haka zanta yawo da hijabi kamar
me takaba, ay nan gaba ma ko gyalen barin sawa zanyi.

Cike da mamaki indo tace "to Allah ya 'kyauta, sannan suka wuce cikin gidan.

Innar indo na zaune tana shan iska taji shihowarsu,
Laraba ta gaisheta, wani mummunan fad'uwar gaba taji da ganin Laraba, dan taji
rad'e-rad'in da akeyi agari, *aiko dole tasan yanda zatayi taraba 'yarta da Laraba
tun kafin suma ta kashesu.

Indo ce ta lura da yanda mahaifiyarta tashiga dogon tunani tace "inna Laraba na
gaisheki ko bakijiba ne? Firgigit tadawo daga dogon tinanin datake ta washe baki
tana ya'ke tace lafiya lao.




🖊Zee Elkaseem
Mmn khady💋
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [21/08 4:53 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*😘



1⃣3⃣1⃣4⃣
1⃣3⃣1⃣4⃣
1⃣3⃣to1⃣4⃣


```Bayan kwana sha ukku```

Yau ake taron 'kawaye na lndo, gobe kuma d'aurin aurenta, 'kawayenta ne cike ma'kil
da gida anata shewa, Kowa kagani cikin farin ciki, hansai ta kalli lndo tace "waini
indo ina Laraba naga tunda nazo ban gantaba, lndo tayi murmushi tace "tun d'azu
muna tare ta koma gidane ta shirya, amma nasan tana gab da dawowa, hansai tace
Allah sarki, sai ta tashi ta goya d'anta tace "to amarya ni zan wuce sai kuma gobe
idan Allah ya kaimu, lndo tace "kai hansai tun yanzu bazaki bari Laraba ta dawo
tabaki biskit d'in ba? Hansai tayi dariya tace a'a ba kome wlh ay zan dawo gobe,
kafin tarufe Baki suka jiyo sallamar Laraba, aiko ko kallon inda take Hansai
batayiba tasa kai tafice daga gidan,
Can sai wasu gun-gun 'kawayensu suka taso suma sun kai su goma suka ce "muma dai
mun wuce, cike da mamaki lndo ta kallesu "tun yanzu baku bari ajima, tare suka
had'a baki suka ce "a'a akwai inda zamu ne, suka sa kai suka fice,

in takaita maku labari shigowar Laraba gidan saida yasa duk mutanen dake gidan
suka tafi.
Indo tasan dalilin tafiyarsu, har ga Allah bataji dad'iba amma ba yanda zatayi, ta
dad'e da sanin mummunan zaton da mutanen 'kauyen keyima Laraba, wasu guntayen
hawaye suka zubo daga idonta tasa hannu ta goge batare da Laraba ta kula da halin
datake ciki ba.

Ranar dai haka suka gama yinin, abin ba dad'i.
Laraba kanta ta fahimci yanda mutanen garin ke gudunta, a zuciyarta tace
_"me nayima mutane suke guduna_ *_Innalillahiwainnailaihirraji'un_*
Tafad'a tare da goge wasu zafafan hawaye.

Washe gari aka d'aura auren lndo da ilu, da dare aka kai amarya,
Ranar Laraba taga tashin hankali, dan 'kiri-'kiri mutane suke nuna tsana da
tsangwama da 'kyama gami da tsoro agareta.

Hakan yasata barin gidan bikin batare da ta shirya ba, lndo ta tausayama 'kawarta,
cike da tausayi take mata addu'a Allah ka yayemata abinda ke faruwa da ita.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Kiyi ha'kuri kinji Laraba, inshaAllah kome ze wuce, kiri'ka addu'a kinji Allah yaye
maki matsalar dake tattare dake, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunta tasa
hannu ta goge "yanzu shikenan inna babu ni babu maganar Aure duk namijin dayace ze
aureni da lokaci ya gabato sai a wayi gari ya mutu, gashi nazama abin tsoro cikin
mutane duk inda naje sai afara barin gurin, ta'kara fashewa da wani sabon kuka.

Inna har cikin ranata take tausayama d'iyarta, itama hawayen take, tace "kiyi
ha'kuri Laraba ki d'auki wannan matsayin kaddara, inshaAllah wata rana kome ze zama
labari.

Nan lnna tayita rarrashinta tana kwantar mata da hankali,
Harta samu tayi shiru tace "tashi ki d'au tukunya ki d'ebo ruwa kiyi wanka, ba musu
ta tashi ta dauki 'yar 'karamar tukunya tanufi rafi, bako gyale jikinta barantana
hijab wanda har ta manta yanda ake sanyashi, inna tayi fad'an harta gaji ta
'kyaleta

Haruna ta hango zaune cikin gonarshi shida wani abokinshi suna cin gyad'a me 6awo,
suna fira, abokin nashi ne yafara hangota ta doso inda suke, cikin dabara ya tashi
yacema Haruna "ina zuwa bari in d'an zagaya can wlh jiya naci wata tafasa tad'an
6atamin ciki.

Haruna yace "Allah sauwa'ke, ya mi'ka mashi ruwa, ya amsa yawuce, yayi nesa kad'an
ya hango Laraba ta iso inda Haruna yake zaune tanayimashi magana, a fili yace
"Allah nagodema da Laraba bata riskeni gurin can ba, da sauri ya 'kara gaba yayi
cikin gari yana tinanin yanda abokinshi ze rabu da Laraba *Mayya* la'kanin da
mutanen 'kauyen suka fara kiranta dashi kenan dan su acewarsu mayya ce shiyasa duk
wanda yace yana sonta take cinye kurwarshi ya mutu.

Da fara'a take magana "Haruna dama ina nemanka, cike da tsoro ya kalleta, duk
illahirin jikinsa kyarma yake amma bakinsa yakasa furta kome,

Bata kula da halin dayake cikiba tacigaba da magana, "waini Haruna ya maganar
soyayyarmu, tunda Allah besa anyi da Hashim ba mizai hana ka dawo a d'aura mana
aure.
Sai lokacin yasamu yayi magana cike da tsoro bakinsa na 'kyarma yace "Laraba dan
Allah kiyi ha'kuri ni wallahi tuni nafasa yin Aure, bazanyi Aureba kwata-kwata.....

Cike da mamaki Laraba ta 'kara matsowa inda yake tace bazakayi aureba fa kace
Haruna, nice fa Laraba ka manta irin soyayyar da kace kanayi mani, a da,

Yace "a da ba amma yanzu na daina soyayya kiyi ha'kuri, Laraba ta'kara matsowa kusa
dashi yana matsawa "Haruna nice Laraba baka ganeni ba ne?

Cike da tsoro yace "na...na..ganeki mana, haba sai lokacin yasamu ya ranta a na
kare 🏃🏻
Mamakine tare da takaici da ba'kin ciki suka rufe Laraba ta dur'kusa nan tana kuka.
_Allah sarki laraba na tausaya maki_




🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [22/08 7:26 am] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*😘



1⃣5⃣1⃣6⃣
1⃣5⃣to1⃣6⃣
1⃣5⃣1⃣6⃣




🖊Zaune suke sun buga uban tagumi, Laraba na zubar da hawaye itama lnna hawayen take
zubarwa dan taji yanda ake maganar Laraba a 'kauyen mutane suna kiranta *mayya*
tasa hannu ta goge hawayen dake idonta, abinda yafaru da ita jiyane yashiga dawo
mata a kwalwa,

shikenan yanzu abin Laraba har inna yake shafa, dan jiya akayi bikin wani d'an
Aminiyarta, wacce a da matar taso ace d'anta Laraba ya aura amma Allah be nufaba,
lnnar Laraba batada aminiya wacce ta wuceta, amma har aka fara biki ba'a
gayyacetaba, saboda haka tace bari taje tayi mata Allah sanya Alkhairi,

Haka ta shirya ta nufi gidan, tana isa zauren gida, magan-ganun dataji anayi
gidanne yasa hantar cikinta juyawa,

Muryar mata taji daban-daban suna magana "wah ay Laraba ta fiddo maitar ta fili,
yanzu fa mutum ukku ta kashe 'kauyennan kinsan kuwa maitarta takai inda takai, can
wata mata ta kar6e zancen "ay ance gado tayi gurin mahaifiyarta, dan ance ita ta
kashe mahaifin Larabar, muryar wata matar taji tana cewa "to mudai uwar biki Allah
sa baki gayyato mamu suba, dan nasan bakida Aminiya kamarta, can sai tajiyo muryar
amiyar tata tana cewa "a da ba, amma banda yanzu dan ban gaji da rayuwaba inaso
inga auren auta ta har inga jikokina, suduka sukasa shewa "heyyyyyy, wata tsagerar
mata takama hanci ta rangad'a guda "ayyuririiii,.........

Innar Laraba najin haka wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, zuciyarta
tayimata nauyi, kanta yayi wata irin Sarawa, take ciwon kai me tsanani ya saukar
mata jitake kamar kanta ze rabe, haka ta dafe kanta tanufi gida cike da takaici da
ba'kin cikin magan-ganun data ji, dan gidan bikin da bata shiga ba kenan,

Kan hanya ma duk wanda tayima magana sai taga ya matsa da Alamar tsoro tattare
dashi baze ko amsa maganar ba,
Wasu kau dasun hangota suke rugawa, abin ya matu'kar d'aure mata kai.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Yanzu kai habu larabar kake so, kana ganin yanda mutane ke gudunta, amma kai karasa
wacce zaka za6a sai ita, kuma kariga ka gama sanin *mayya* ce,
habu ya kalli abokinsa cike da takicin kalmar mayya daya furta ga Laraba yace "eh
ni ina sonta koda zata ri'ka yankan naman jikina tana ci d'anye 'karewar maita zan
aureta, abokin nashi yace to "Allah raka taki gona, nidai kaga tafiyata, kuma
muddin kasani idan kana tare da Laraba to abotarmu ta 'Kare, habu yayi wani guntun
murmushi mai d'auke da takaici yace, Allah had'a kowa da rabonsa, rabuwar habu
kenan da abokinsa.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Zaune suke sunyi tagumi duniya tayi masu zafi itada innarta, dan fitama wahala take
masu kullum suna gida basuda aiki sai tinani sai kuka,
Rabon kau da wani mutum yashigo gidansu har sun manta,
Itako Laraba da gidan lndo kad'ai take zuwa taji d'an dad'i-dad'i shima yanzu
yaushe rabon dataje, tun ranar dataje ilu yayimata wula'kanci yace kada ta 'kara
zuwar mashi gida idan kuma bata dainaba hukuma zata rabashi da ita,

Suna cikin wannan yanayin sukaji an bankad'o kyauren gidan kad'an yarage a
karyashi, mal Lawal ne yafara magana cikin bala'i da masifa, watau kin koyama d'iya
maita tana kashe mutanen gari, to wallahi ba maitaba ko uban maita ke gareki dole
Laraba ta fito da miji inyimata aure, dan bazan yarda tana yawo agari ana zagina a
matsayin mahaifinta na gaza aurar da itaba.

Tunda yafara magana basu cemashi 'kala ba, saida yagama bala'i sannan ya kalli
Laraba yace "waye kuma yanzu kike so wanda tsautsayi ke shirin afka mawa,

Cikin kuka da bakin ciki tace "dama Haruna ne tin kafin rasuwar Hashim yake sona,
mal Lawal yace "to bari yanzu inje in samu Haruna idan da gaske yake ya turo
iyayenshi dan bazaki 'kara sati biyu a gidannan ba, sadaki kawai ze kawo a d'aura
aure, haka yafita gidan yanata bal-balin bala'i, inna dai bata cemashi ci kanka ba
illah kuka datakeyi.

Haruna Zaune shida abokinsa suna fira, mal Lawal ya iso gurinsu, suka gaidashi ya
amsa, sannan yace Haruna gurinka nazo kan maganar Laraba, wani irin fad'uwar gaba
Haruna

2 / 10