Advertisements
Chapter 3 Reading ALHINI by Zee Mmn khadye BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALHINI by Zee Mmn khadye

Author :  Zee Mmn khadye Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 10

6K to 9K   out of 27.3K words

yaji,
jin an ambaci sunan Laraba, mal Lawal be jira abinda Haruna ze fad'aba yaci gaba
da magana, "tace kaine wanda ta tsaida shine nace ka turo magabatanka bamu bukatar
kome daga gareka sadaki kawai zaka kawo nan da sati d'aya a d'aura maku aure.

Haruna Wanda tinda mal Lawal yafara maganar jikinsa ke rawa kamar mazari yace "a'a
ni maganar soyayayya bata ta6a had'ani da Laraba ba, kuma bani sonta, inaji ba dai
ni harunan take nufiba

A fusace mal Lawal yabar gurin da niyyar yaje gida yaci mutuncin Laraba da
mahaifiyarta.

Tinda mal Lawal yabar gurin jikin Haruna ke 'kyarma, ya kalli abokinshi yace kanafa
jin wannan mutumin, abokin nashi yayi dariya yace "watako yarinyar nan tasaka a
zuciyarta tagama kwad'aituwa da kai walh saika tashi tsaye,
Kazo muje gidan kakata 'yar me ganye tana bada maganin mayu, Malam abaka kasha kayi
wanka.

Ba musu Haruna yace mutafi,
Sun isa gidan 'yar me ganye anba Haruna maganin daze ri'ka ji'kawa yana wanka dashi
sannan aka bashi tazargade yari'ka haya'ki, matar tace indai yana amfani da wannan
badai maye ba, ko sarkin mayu sai dai yaganshi ya 'kyale.
๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [22/08 6:41 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


1โƒฃ7โƒฃ1โƒฃ8โƒฃ
1โƒฃ7โƒฃto1โƒฃ8โƒฃ
1โƒฃ7โƒฃ1โƒฃ8โƒฃ



๐Ÿ–Š "lna 'yar iskar yarinyar nan take, dan ubanki kinsan babu soyayya tsakaninki da
Haruna kika turani gurinshi, naje naji kunya, to bari kiji in gaya maki tunda dai
kinzamar ma mutane bala'i kin zamar masu 'karfen 'kafa to zan aurar dake ga duk
wanda naga dama,sannan ya juya gurin inna wacce tunda yafara fad'anshi ta kauda
kanta gefe tana zubar da hawayen takaici, shin wai dame zasuji da tsana da
tsangwama da tsoro da 'kazafin da 'yan garin kemasu koda masifa da bala'in mal
Lawal.

Yaci gaba da magana, cikin d'aga murya "Kara Ku yanke shawara tun kafin nan da
kwana biyu idan kuma ba hakaba zan yanke duk hukuncin da naga dama, yasa kai yafice
yanata kumfar baki.

Yana Fita Laraba ta taso tafad'a jikin innarta ta fashe da wani irin kuka me ban
tausayi, itama lnnar kuka take amma duk da haka rarrashin 'yar tata takeyi.

*```Bayan kwana Hud'u```*

Inna ce ke rarrashin 'yarta wacce duk yinin yau kuka take, ko ruwa takasa sama
cikinta saboda tsananin damuwa, tariga tagama sanin sunan da ake kiranta dashi a
'kauyen na *Mayya*
"Kiyi ha'kuri Laraba duk tsanani yana tare da sau'ki, in Allah ya yarda duk
masu gudunki sai sun dawo suna binki, kedai kiri'ka addu'a Allah yayi maki maganin
matsakarki.

Suna cikin wannan ne sukaji an bankad'o 'kyauren gidan, suduka suka maida
hankalinsu ga 'kofar ganin 'kyauren sukayi 'kasa ya karye, kasancewar dama na
langa-langa ne bayada wani 'kwari.

Mal Lawal ne yabi ta kan 'kyauren yashigo gidan a sukwane,
Laraba na jikin inna ta 'kan-'kameta duk tsoro yakamata gani take yau baffa Lawal
dukan ta zeyi.

Kudi ya watso jikinta yace "ga sadaki nan na d'aura aurenki da habu, yayan hansai,
idan kin cika ke mayyace yau kada ya kwana da rai, tinda sauran kafin a d'aura kike
kashesu, to wannan karan an d'aura kuma 'kurwarsa kur kuci kanku, *Mayu*.

Wani irin kuka Laraba ta 'kara fashewa dashi, ta 'kara shigewa jikin innarta Wanda
shi kad'aine yanzu take ra6a taji sanyi tace.

"Shikenan inna bamuda Kowa bamuda Wanda zamu ra6a muji dad'i, abin takaici da
ba'kin ciki wai hada baffa Lawal ake kirana *Mayya* to waye ma baze kirani da
*mayya* ba tinda 'kanin mahaifina ma yakirani haka.

Bayan magrib mal Lawal da kansa yazo ya tafi da Laraba tana kuka tana kome ya
kaita gidan miji, basu iske kowa gidan ba amma duk wani Abu na Al'ada na tarbar
amarya an kawo an aje masu,

Haka baffa lawal ya ajeta yabar gidan, tunda Allah ya halicceta bata ta6a ganin
irin wannan auren da akayimata ba, gashi dai ankawota gidan miji amma ba kowa sai
ita kad'ai cikin gida kamar *Mayya* _(sunan da mutanen 'kauyen ke kiranta dashi)_

Ta fad'a kan soson katifar da aka kawota dashi wanda ko zanin kirki bayadashi, ta
fashe da wani irin kuka, baiwar Allah Laraba tana cikin tashin hankali, duk tabi ta
rame, ta kod'e idanun nan nata sunyi zuru-zuru, hancin ya 'kara tsawo sai wani uban
'kashin wuya daya fito yayi mata 'kwaro-'kwaro.

A 6angaren habu kuwa yariga yasan an kawo amarya, yaje gun 'yan uwanshi yaro'kesu
akan suje gidan ayi d'an shagalin bikin da akeyi bayan an kawo Amarya amma sukace
"ina ay basu gaji da rayuwaba tukun, waye ze kai kanshi ga halaka.

Indo kuwa taso zuwa bikin 'kawarta kuma aminiyarta, amma ilu ya bad'e ido toka yace
bazataba, 'karshe data isheshi da magiya sai cewa yayi idan ta'kara maganar zuwa
bikin Laraba to bakin aurenta, hakan yasa ta ha'kura badan ranta yaso ba.

Bayan habu yagama fama da 'yan uwanshi akan suje gidanshi sun'ki sai yatafi gidan
'kanwarsa hansai, da sallama yashiga gidan, ta amsa sannan ta gaisheshi ya amsa,
nan yake tambayarta

"Hansai ya ban ganki gurin bikin ba, lafiya kuwa? Hansai ta yamutsa fuska tace
lafiya lau, kaina ne yake d'an yimani ciwo, cike da tausayi yace eyyah Allah
sauwa'ke tace Ameen.

Yace Amma naga kamar kin d'anji sauki, kozaki daure ki le'ka gidan kai amaryar,
Cikin firgici Hansai ta kalli yayanta tace "wah ni Yaya habu, idan ka ganni lahira
kaini akayi, wallahi bazani gidan *mayya* ba.

Cikin 6acin rai habu ya d'auke hansai da mari yace "idan bazakiba ki zauna, amma
kada ki kuma kiran matata da *Mayya* yasa kai yafice ranshi a 6ace.

Me zai faru yana fita daga gidan Laraba yagani tanayimashi murmushi, ta 'karso
gurinshi tace masoyina nagaji da jira ne gida ni 'kad'ai shine na biyoka...

cike Da mamaki yace "ya akayi kikasan ina nan, murmushi kawai tayi Mashi ta kama
hannunshi suka nufi gida.




๐Ÿ–ŠZee Elkaseem
Mmn Khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [23/08 5:48 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜




1โƒฃ9โƒฃ2โƒฃ0โƒฃ
1โƒฃ9โƒฃ2โƒฃ0โƒฃ
1โƒฃ9โƒฃto2โƒฃ0โƒฃ



๐Ÿ–Š Tafiya suke Laraba na ri'ke da hannun angonta Habu, sai da sukayi nisa da gari
sun shiga gonaki, baka ganin kome sai duhun daji da kukan tsuntsaye,

kasancewar akwai 'yar tazara tsakanin gidan Hansai da gidan Laraba, sun shiga
cikin duhun ciyayi, Habu ya waigo ya kalli Laraba yace "Amma Laraba nayi mamakin
yanda kika san ina gidan Hansai, kodai wani ya gaya maki ina nan?

Shuru yaji tayi batada niyyar amsa mashi tambayar da yayi mata, hakan yasa ya juyo
ya kalleta, suna had'a ido da ita gabanshi yayi mummunan fad'uwa dan ganin ta yayi
ta d'ad'd'aure fuska yanda kasan tunda Allah ya halicceta bata ta6a dariya ba, ga
fuskar tata tayi duhu, ba alamar haske tattare da ita, kamar ba larabar da
yasaniba, kya'kyawar yarinya fara tas fatar ta kamar ka ta6a jini yafito, amma
lokaci guda ta sauya takoma ba'ka, ga fuskar ba Alamun fara'a tattare da ita.

Lokaci guda jikinsa yafara 'kyarma kamar mazari, yakasa matsawa daga inda yake, sai
da 'kyar yasamu ya iya daga baki yace La....la....Lara...ba, miya sa kika biyoni,
miyasa zaki tsoratar dani......

Kafin ya rufe bakinsa yaji ta gagga6e da wata irin mahaukaciyar dariya tace,

"Tambaya kake yanda akayi nasan inda kake, to ayni ba sai na tambaya ba, tunvdaga
ranar daka furta kalmar so gareni nake biye dakai, kuma kasani sai nazama
ajalinka..... Hhhhhhhhhhhhhhhhh, ta 'kara gagga6ewa da wata nahaukaciyar dariya
karo na biyu.

Habu kuwa banda 'kyarma ba abinda yake, yariga yagama sad'aukar da rayuwarsa, dan
yasan 'karshen rayuwarsa ne yazo, kwata-kwata kasa yin wata addu'a yayi dan
tsananin tsoro, sun kai kimanin minti ashirin tsaye gurin Laraba, tana tsoratar da
Habu.

Sai zuwa can Allah yabashi ikon furta kalmar *lnnalillahiwa,inna'ilaihirraji'un*
sannan yasamu 'kafar guduwa daga gurin,

Gudu yake iyakar 'karfinsa, domin yau ya tabbatar ma kanshi maganar da mutane ke
fad'a suna cewa Laraba *mayya* ce, a zuciyarshi yana cewa koma miye Nina jawoma
kaina, dama ance _(Wanda beji bari ba yaji hoho)_.๐Ÿ˜ฑ

Lokaci guda yahad'a wani uban gumi, ga tsabar tsoro ga kuma uban gudun dayasha, da
kyar yashiga gida ya maida 'kyaure yarufe, yana maida numfashi.
'Daki yanufa yana nishi yana goge uwar zufar data rufeshi kamar wanda aka watsama
ruwa,

Mutuwar tsaye yayi dan wani babban tashin hankalin daya tarar a gidan, yasan dai
yabaro Laraba a daji, amma kuma yanzu gata ya tarar da ita kwance kan 'yar
katifarta tana kuka.

Jin alamun shigowar mutum yasa Laraba tashi daga kwancen datake, ta d'ago da manyan
idanunta wanda suka kad'a sukayi jawur saboda tsabar kukan data sha.

Cike da mamaki Habu ke kallonta, a zuciyarshi yace "to wai miye ke shirin faruwa
dani ne, kodai ba Laraba bace wacce nabaro a daji.

Ganin bashida niyyar ida 'karasowa cikin d'akin yasa Laraba tayi magana "Sannu da
zuwa, tafad'a cikin zazza'kar muryarta mai sanyin sauraro.

"Yauwa yafad'a zuciyarsa na dukan ukku-ukku, "bari inje in dawo nayi mantuwa a
gida, cike da tsoro Laraba tace "miye kuma ka manta, nifa wallahi tsoro nakeji ni
d'aya gida, a zuciyarsa yace _"Ai kece abin tsoron laraba, ke yakamata aji tsoro
bake zakiji tsoron wani abu ba_

"Tinanin me kakeyine, ta tambayeshi dan ganin ya tsaya a gun bayada niyyar tafiya,

Yayi saurin dai-daita nutsuwarsa yace "a'a zanje bari intafi bazan dad'eba zan
dawo, sannan yasa kai yafice, cike da tsoro yafita daga gidan, zuciyarshi cike da
tunani kala-kala.

Tafiya yake bekoyi nisa da gidan ba amma wani mugun abun tsoro daya gani shine
yakusa sanya numfashinshi ya d'auke, dan Laraba yagani gabanshi, ta kashe d'an
kwali ta ri'ke 'kugu tana jijjiga jiki, suna had'a ido ta gagga6e da wata
mahaukaciyar dariya, sannan kuma ta d'aure fuska kamar bata ta6a dariyaba.

Tace "Habu kana gan-ganci da rayuwarka, inaso kafin nan da safiya ka gaggauta
yankema kanka hukuncin daze fitar dakai.

๐Ÿƒ๐ŸปDa gudu yayi baya yakama hanyar gidanshi, tashin hankali wanda ba'a samashi
rana ๐Ÿ˜ณ Laraba ya iske a tsakar gida tafito daga kewaye hannuta ri'ke da buta.

Wata irin gigitattar 'kara yasaki nan take yafad'i 'kasa kanshi yabugu da wani
dutsi dake tsakar gidan, aiko kan yafashe jini yafara zuba.

_Innalillahiwa'inna,ilaihirraji'un_ Laraba tashiga furtawa, tanufi inda Habu yake
kwance tana jijjigashi tana kiran sunanshi amma ba alamar numfashi tattare dashi.




๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [24/08 2:03 pm] Zee Elkaseem: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


2โƒฃ1โƒฃ2โƒฃ2โƒฃ
2โƒฃ1โƒฃto2โƒฃ2โƒฃ
2โƒฃ1โƒฃ2โƒฃ2โƒฃ


๐Ÿ–Š "wayyo nashiga ukku dan Allah habu katashi kada ka mutu, idan kamutu nasan bazan
'kara shan ruwa garinnan ba, dan Allah ka taimakeni, Laraba ce ke fad'in haka cikin
muryar kuka,
Yayinda habu yake kwance har yanzu besan inda kanshi yakeba, ga kuma inda kanshi
yabugu har yanzu zubar da jini yake,
"Ya salam laraba tafad'a "Lallai rayuwata tana cikin had'ari ya Allah ka fitar
dani, wasu sabbin hawaye suka gangaro kan kumatunta.

Lokaci guda jikinta ya mutu li'kis kamar wacce akayima duka
Ta tashi da sauri tanufi d'aki ta dauko wani tsohon zani cikin zannuwanta ta yaga
ta d'aurema Habu kanshi inda jini ke zuba, cikin ikon Allah kuwa sai jinin ya
tsaya, amma har yanzu ba Alamar numfashi tattare dashi,

Sai lokacin dabarar ta yayyafa mashi ruwa ya fad'o mata a arai, da sauri tanufi
randa ta d'ebo ruwa me sanyi ta yayyafa mashi, a firgice ya tashi yana "cewa "dan
Allah kiyi ha'kuri Laraba kada ki kasheni, Laraba ni me 'kaunarki ne bekamata ki
sakamin da sharri ba.

Wata irin 'kara Laraba tayi, cikin wata gur6atacciyar magana take cewa, Habu bazan
ta6a raga makaba, babu ragi ba ragowa tsakanina dakai, nariga na gaya maka kafin
gari ya waye ka nemama kanka mafita,

Cike da tsoro da firgici habu ya kalli Laraba, yaga fuskarnan tata ba Alamar
sassuci, tabbass idan yaci gaba da zama da ita ze iya rasa rayuwarsa, hakan yasa ya
yanke shwarar rabuwa da ita.

"Laraba"yakira sunanta,
Jiki a sanyaye ta juyo ta kalleshi, yace "kije na sakeki *Saki ukku*
Daga yau babu ni babu ke,

"Hhhhhhhhhhhhhh, wata irin mahaukaciyar dariya sukaji ta gauraye gidan, har tsawon
minti biyar sannan dariyar ta lafa, wata irin murya sukaji wacce basu San daga inda
take fitowaba ana cewa,

"Yaro kayi ta barka, ashe kana son rayuwarka, aka sake bushewa da wata dariya,
sannan sukaji d'if kamar anyi ruwa an d'auke.

Wani matsanauncin tsoro Yakama Laraba dan jin wani sabon Al'amari, da gudu tanufi
habu wanda shima jikinsa mazari kawai yake saboda tsananin tsoro tafd'a jikinsa ta
'kan'kameshi.

Cike da tsoro habu ya finciketa daga jikinsa, yajata kiiiiii, ya turata waje yace
"kije nace nasakeki *Saki ukku* ya maida 'Kofa ya rufe.

Laraba ta shiga bugun 'kyauren gidan, tana cewa "Dan Allah habu ka taimakeni ka
barni in kwana gobe sai intafi, haka ta rin'ka magiya amma bataji Habu yayi
maganaba, hakan yasa ta kalli gabas ta kalli yamma kudu da arewa, ba Alamar haske,
garin yayi duhu dind'um bakajin kome sai kukan tsintsaye, take wani mugun tsoro ya
dira a zuciyarta.
[24/08 2:38 pm] Zee Elkaseem: Wani irin haske ta hango daga nesa yana nufo inda
take, tin tana kallonsa nesa da ita har yazo gab da ita,
Wani irin matsanancin tsoro ya'kara kamata,
Wata irin 'kara ta fasa sannan ta ranta a na kare๐Ÿƒ๐Ÿป

ยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐยฐ

Inna na kwance d'aki, kan guntuwar tabarmarta sai juyi take bacci ya gagari idonta,
ba abinda take sai tinanin kowane hali 'yarta take ciki,
Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta, tasa hannu ta goge,
Lokacin kuma taji Uciyarta tayimata nauyi kamar an d'ora mata wani katon dutse,
lokaci guda taji yun'kurin amai, aiko tatashi zaune tafara amai, babban tashin
hankalin da inna tagani duk yun'kurin datayi maimakon taga aman abida taci, jini ne
take amayowa hadda gundarinsa,

Cikin 'kan-kanin lokaci ta galaibaita tafita hayyacinta,

Da gudu Laraba tashigo gidan, wata irin 'kara tasaki dan ganin halin da inna take
ciki, sauri ta 'karaso gareta, takamata tana kuka tana kiran sunanata,
inna....inna...inna... Da 'kyar inna ta iya d'aga ido ta kalleta tace "Laraba nasan
tawa ta 'kare amma bazan gusheba inamaki addu'ar Allah fiddaki daga mawuyacin halin
da kike ciki.

Fad'uwa tayi rai yayi halinsa, ```Allahu akbar inna tarigamu gidan gaskiya```

Wata uwar 'kara Laraba tasaki, dan ganin inna ba Alamar numfashi tattare da ita,

Wani irin duhu taga ya gufta mata, kokacin kuma kanta yayi wata irin sarawa, jiri
ya ibeta ta fad'i kasa sumammiya,....




๐Ÿ–ŠZee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:10 PM] www.gidannovels.blogspot.com [24/08 7:45 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


2โƒฃ3โƒฃ2โƒฃ4โƒฃ
2โƒฃ3โƒฃto2โƒฃ4โƒฃ
2โƒฃ3โƒฃ2โƒฃ4โƒฃ


๐Ÿ–Šwashe gari tunda asuba Habu yanufi gidan iyayenshi, yana isa innarshi taganshi da
uban rauni a kai, ga jikinshi jage-jage da jini, dan be canja kayaba haka ya kwana,
wani uban salati ta buga tace "Habu lafiya meya faru dakai, ina Larabar,? Lokaci
d'aya ta jero mashi wad'annan tambayoyin, Habu bayaso ya fad'i gaskiyar Al'amarin
abinda yafaru dashi saboda besan wani halin fad'in ze jefa laraba ba, saboda haka
shiru yayima innar tashi.

Innar taga bayada niyyar bata amsar tambayoyin datayi mashi, kawai saita d'ora
hannu a kai tafashe da kuka, wanda yin hakan ya jawo da hankalin mutanen gidan
garesu, duk akayo d'akinta ana tambayarta lafiya meya faru, dayake gidan irin
gidan yawa ne,
Ganin habu dasukayi zaune ga jini duk ya 6ata jikinsa yasa suka ba kansu amsa,
tabbass koba tambaya sun san larabace ta tasarma kasheshi Allah beyiba dayake
yanada sauran shan ruwa.

Wata mata cikin mutanen dake tsai-tsaye Bakin 'kofar d'akin tace "ina kabaro
amaryar angon Laraba?
cike da takaici habu ya kallesu yace "Laraba na gidansu na saketa,

Wani uban salati matan suka d'auka lokaci guda, sukace "yo habu ya akayi haka
tafaru?
Be basu amsaba illah fita dayayi yabar gidan dan bayaso ana can-cana maganar.

Wata tsohuwar mata ta kalli innar Habu tace "Wallahi atika kinyi ta barka, dan
wannan maganin da 'yar me ganye tabada tace ki binne a gidan, amma da badan haka ba
da yanzu habu sai dai wani bashiba.

Innar habu tayi murmushin takaici tace "Hmmm Wanda beji bari ba ay yaji hoho, cikin
gidanan waye be ba Habu shawarar kada ya auri Laraba ba amma yakafe, ay dama me
rabon shan duka bayajin kwa6a, bata jiran me sauran matan zasu fad'aba tashige
d'aki tana matsar kwalla.

Ganin haka yasa kowace takama gabanta, suna fad'in albarkacin bakinsu,
Abinka ga matan 'kauye kad'an suke jira su 'kara, kafin kace me labari ya bud'e
gari.

Mutanen gari anata yayatawa, Laraba takusa kashe Habu Allah ya taimakeshi ya
saketa.

Aiko labari yakaima mal Lawal, a fusace yanufi gidansu Laraba da niyyar yaci masu
mutunci itada uwarta wacce ke d'aure mata gindi tana kashe mutane.

Bako sallama ya bankad'a 'kyauren gidan yashiga,
Laraba yagani ta had'a kai da gwiwa tana kuka, gefe kuma ga innarta kwance cikin
jini.

"Ke.....ya daka mata tsawa, da sauri ta d'ago da fuskarta ta kalleshi, saitaji wata
dama-dama a ranta, tunda tariga tasan inna tamutu, kuma batasan wa zata gaya
mawaba, tunda mutane yanzu da sun ganta guduwa suke.

Da sauri ta taso tazo gabanshi ta dur'kusa, yanzu kam idonta ba hawaye ko kad'an
dan tayi kuka har hawayenta sun 'kafe, tace "dan Allah baffa Lawal ka taimakeni
inna ta mutu, tun jiya da dare, ban san yazanyiba, shiyasa ban fitaba dan nasan duk
inda na nufa ba wanda ze saurareni,

Wata irin dariya mal Lawal yayi sannan ya kalli Laraba yace, "watako maitar taki
har takai ga uwar data haifeki, to wallahi ki shiga hankalinki, danni idan kikace
zaki cinyeni sai inci ubanki, 'yar iska kawai, yakai mata wani hauri har saida ta
fad'i, sannan yafita yabar gidan.

Zuwa yayi yasanar da mutane, innar Laraba ta mutu, amma kowa sai yace Allah
ji'kanta, da ance suzo ayimata sutura akaita makwancinta sai kaga mutum yafara
zame-zame Alamar dai baya zuwa.

Haka akayita fama da muatanen Gari, karshe dai saida me gari yasa Baki, yasa liman
da wasu tsirarun mutane akaje akayima innar
Laraba wanka akayimata sutura aka kaita makwancinta,
Kuka kau Laraba yanzu ta daina na hawaye, sai dai na zuci, dan zuciyarta tariga
tagama soyewa, tasaba da ba'kin ciki da takaici.

*_BAYAN KWANA BAKWAI_*

Yanzu Laraba ita kad'ai ke kwana gidansu babu me ra6arta, ga yunwa dan ba wanda
kebata koda sauran abinci, idan kuma tafita dan tasiyo abinda zataci dataje shago
sai muatane sukama gudu, haka zata dawo gida takama kuka, abin dai gwanin ban
tausayi, duk ta rame ta kod'e idanun nan sun kara fitowa sunyi zuru-zuru, ga wani
ciwon ciki datake fama dashi sakamakon yunwar datake fama da ita,

Ruwa kawai take banka ma cikinta koda yaushe, to yanzu ma idan tasha ruwan sai ya
'kulle mata ciki tayita amai,

Yau dai tagaji da bala'in datake ciki, saboda haka tayi niyyar zuwa gidan baffa
Lawal dan ya taimaka mata.




๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [25/08 7:08 am] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*๐Ÿ˜˜


2โƒฃ5โƒฃ2โƒฃ6โƒฃ
2โƒฃ5โƒฃto2โƒฃ6โƒฃ
2โƒฃ5โƒฃ2โƒฃ6โƒฃ



๐Ÿ–Š Baffa Lawal ne cikin gonarshi yanata noma, yanayi yana 'yar wa'ka irin ta mutanen
'kauye, abin yayi masa dad'i har gyad'a kai yakeyi, zuwa can kuma sai yatashi
yanufi inda ya ajiye kayansa ya fiddo da wata 'yar madai-daiciyar radio, yasanya
sabbin batura ya 'kunna, ya kuwa yi sa'a gidan redio an sanyo wa'kar d'an kwairo,
aiko sai ya rataye redion jikin bedi yana ji yana aikinsa,

Befi minti shidda da kunna red'ion ba sai yaji d'if redion ta d'auke, ya d'ago
kansa ya duba bega kowaba, yaje ya ta6a redion sai yaji kashe take, nan ya sake
kunnawa ya maida yarataye ya juya ze cigaba da aykinsa sai yaji an 'kara kashewa,
yana juyowa wa ze gani,

Laraba

3 / 10