Author : Zee Mmn khadye Category : Complete Novels
tace mata, yakamata ki bada address d'in baffa
Lawal saboda za'a tura magabatan mukhatar suje neman aure.
Laraba cike da damuwa da far gaba tace "Hajiya kibari da safe zan bada yanzu kaina
yana min ciwo, Hajiya ta tausaya mata tace "eyyah Allah sauwa'ke to kisha magani
kafin ki kwanta kinji, tace "to, sannan tanufi d'akinsu zuciyarta cike da tunani
kala-kala, *gaskiya bekamata ta sakama mutanen nan da sharri ba, yanda suka
d'auketa amatsayin 'ya suka ri'keta suka nema mata gata wanda ko a mafarki batayi
tunanin samun irinsaba, gaskiya dole tasamoma kanta mafita*
Haka ta isa d'akin ta iske jidda tana chat da Usman d'inta tana dariya ita kad'ai
kamar mahaukaciya, laraba ta kalleta batayimata magana ba ta haye gadon tayi
kwanciyarta.
Jidda ta kaimata duka, "ke yau baki chat da yayana, nasan yana online yana jiran
zuwanki, Fatima tayi wani d'an guntun tsaki ta 'kara gyara kwanciyarta tace "kaina
ne yakemin ciwo nasha magani bacci zanyi, cike da tausayawa jidda ta dafa kanta
tace "Allah sauwa'ke, itama sai taji chat d'in yafita ranta haka sukayi sallama da
Usman yanata magiyar kada ta tafi ta barshi, tace "kayi ha'kuri sister d'inace ba
lafiya bazanji dad'in yin chat d'ina, yace "Allah sauwake sukayi sallama.
Itama jidda kwanciya tayi bayan tayi addu'a tashafe jikinta, sannan tayima Fatima
addu'ar dan ta lura da lokacin data kwanta batayi addu'ar ba.
Duk abinnan Laraba na jinta dan ba bacci tayiba, tunanine kala-kala cikin
zuciyarta.
Jidda bata dad'e da kwanciyaba bacci yayi awon gaba da ita, haka laraba tayita juyi
kan gado bacci ya gagari idanunta, wayarta ta d'auko ta duba 'karfe 1:58 am na
dare, a zuciyarta tace yanzu ne yakamata in samoma kaina mafita, dan muddin nasan
idan nabari mutanen nan sukaje 'kauyenmu sunan dana 6oye masu nawa na *mayya* zai
bayyana.
Saboda haka ahnakali ta tashi cikin sand'a ta d'auko site bag d'inta ta bud'e
wadrope ta d'auki kaya kala 2 sannan ta cire rigar baccin jikinta ta Sanya wata
doguwar riga ta atamfa sannan tasa wando legis daga ciki, sannan ta Sanya wata 'yar
'karamar hijab, ta d'au takalminta a hannu, ta lalla6a tayi sa'ar barin gidan
batare da Kowa ya gantaba kokuma yaji motsinta.
Bakin titi ta tsaya ta 'karema unguwar kallo bakajin kome sai kukan maguna da
karnuka, da tsintsaye, haka ta yanki hanya tacigaba ta tafiya, zuciyarta cike da
tsoro.......
4⃣1⃣to4⃣2⃣ Very 4⃣1⃣4⃣2⃣
4⃣1⃣4⃣2⃣
🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:11 PM] www.gidannovels.blogspot.com [31/08 8:21 am] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 *_ALHINI_* 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_written by_
*_Zee Mmn khady_*😘
4⃣1⃣4⃣2⃣
4⃣1⃣to4⃣2⃣
4⃣1⃣4⃣2⃣
🖊 Tafiya take batare da tasan inda zata dosa ba, ta d'anyi nisa kad'an da gidan
zuciyarta cike da tsoro, sai tajiyo Alamar tafiyar mutane bayanta suna tafiya suna
magan-ganu wanda bata iya jiyo abinda suke cewa, saboda suna d'an nesa kad'an da
ita, hakan yasa zuciyarta kara tsorata, tayi maza ta 'kara sauri cikin sa'a tayi
karo da wani gida da aka fara ginawa amma ba'a karasaba, aiko tayi saurin shigewa
ciki dan ta 6uya, da sauri ta shige wani guri a cikin gidan wanda da Alama d'aki ne
amma ba'a karasaba dan ko rufi ba'ayiba, gidan dai kamar kango ne dan duk illahirin
gidan ba 'kofar da aka sanyama 'kyaure, sai uwayen karikitai da Shara a cikinsa.
Tana cikin kangon gidan data 6uya 'kirjinta na dukan tara², sai ji tayi wad'annan
mutanen data 6uya dominsu sun iso gurin, jitayi sun tsaya bakin 'kofar kangon gidan
data 6uya suna magana, muryar guda taji yace "gaskiya nifa na gaji da abinda
mutuminnan yake samu muna aykatawa, kawai hakanan yasa muri'ka kawo mashi 'ya'yan
mutane yana 6ata Masu rayuwa.
Gudan yayi dariya, cikin wata muguwar murya marar dad'in sauraro yace "nikam bazan
ta6a barin wannan sana'ar danikeba, dan in baccin ita ina zamu ri'ka samun 'kudin
da muma zamuji dad'in rayuwarmu, haba baba, kazo muje kawai mucigaba da neman
abinda ya fiddo mu, gudan yace to yanzu ina zamu nufa? Kasan dai yanzu duk wata
d'iya mace indai tanada mutunci to tana gidan iyayenta, gudan ya gagga6e da wata
irin dariya yace "yo dama duk wacce muka kama yanzu ay bata mutunci bace, dama mu
irin 'yan iskan nan muke nema masu yawon dare, idan sunsha sun bugu mukuma sai muyi
awon gaba dasu, suduka sukasa dariya marar dad'in sauraoro.
Duk abinda suke Fatima na La6e cikin wannan gidan tana jinsu in banda kyarma ba
abinda take, lokaci guda ta had'a wani uban gumi, dan tariga ta fahimci inda
zancensu ya dosa,
A gida kuwa da misalin 'karfe ukku da minti sha shidda na dare jidda ta farka zata
shiga toilet sai taga bataga Fatima ba, hakan yasa tayi tunanain ko tana toilet
d'in ta dad'e tana jiran fitowarta amma kusan minti goma shiru saboda haka saukowa
tayi daga kan gadon da niyyar ta duba toilet d'in.
Abinda idanunta yafara karo dashi shine ya d'aga mata hankali, kayan baccin Fatima
yadde a 'kasa, bata tsaya d'auka ba ta tura 'kofar kewayen, nan ma ba Laraba, cikin
tashin hankali tayo baya sai tayi karo da wadrop bud'e tayi sauri dubawa cikin
wadrop d'in saitaga kaya yamutse da Alama an d'auki wani abu aciki, nan tashiga
matsanancin tashin hankali lokacin data ta6a kofar fita daga d'akin tajita bud'e.
Cikin tsananin tashin hankali tanufi d'akin hajiyarta ta sanar da'ita abinda ke
faruwa,
Mukhtar ma an tasoshi an fad'a mashi halin da ake ciki, cikin tashin hankali
yafito, haka suka shiga duba ko'ina na gidan Amma ba Alamar Fatima, an tambayi me
gadi yace shikam bega fitar Kowa a gidan ba.
Lokacin idan hankalinsu yayi dubu tashe yake, mukhtar d'akinsa yanufa ya d'auko
key d'in motarsa yacema Hajiya "Zan fita in duba ko Allah zesa in ganta.
Lokacin itakuma jidda ta d'auko wayarta dan ta lura duk inda Fatima take ta tafi da
waya dan ta duba bata gantaba, lokacin ta lalubo sunan sister Fatima, sunan data
sanyama Laraba kenan ta danna mata kira.
Dadai lokacin da wad'annan mutanen guda biyu suka tashi daga 'kofar kangon gidan da
Fatima ke la6e a ciki guda na cewa "baba yakamata fa mu'kara gaba ko mun samu, ya
duba agogon hannunshi yace 'karfe ukku da rabi kada gari ya waye mamu anan, kasan
oga mayen mata ne duk ranar dabamu samo mashiba bamuda jin dad'i, d'ayan wanda tun
farko yace yagaji da sana'ar yace "waallahi ni abin na oga yana bani mamaki, ga yan
mata nan karuwai masu Neman mazan da kansu meyasa baya ri'ka d'aukosu yabiya
bukatarsa yabiyasu 'kud'insu hankalinshi kwance suma hankalinsu kwance, gudan yace
"kai dai banzane baka ta6a ganewa, ai a cewar oga duk macen data kai kanta ga
naminiji batada wani fa'ida yafison wacce za'a d'auko Mashi ya mata fyad'e, yafi
jin dad'in hakan dan duk wacce aka kawo tana tirjewa yasan ba 'yar iska bace, ko ka
manta lokacin damuka kawo mashi wata yarinya tanata ihu tana zillewa, ta d'auka
yankata za'ayi koda tagane ba yankata za'ayiba, tagane manufarsa kawai sai tace
"dakasan wannan ne da baka sa nayi wahalar hawayena ba, kawai mallam bissmillah,
yana ganin haka yace afita da ita, wallahi beyi amfani da itaba, dan ya lura
sana'arta ce.
Zasu tafi kenan wayar fatima tashiga ruri lokacin, kiran jidda ya shigo, cikin
tsananin tsoro da kad'uwa ta sa hannu ta danne wayar, harta tsinke bata d'aukaba
sai kuma aka 'kara kira karo na biyu, tayi ko'karin takashe wayar baki d'aya amma
sai ta kasa saboda tsananin rud'ewa.
Da sauri wad'annan mazan suka shigo cikin kangon gida suna dubawa dan jin waya nata
ringing, lokacin kuwa Fatima tagama sadaukar da rayuwarta, cikin sa'a kuwa suka
ganta basuyi wata-wata ba suka sungumeta, guda ya d'orata kan kafad'arsa tanata ihu
tana dukansa tana yagunsa, hadama cizo amma ko a jikinsa, ganin zata tona masu
asiri yasa gudan ya fiddo wani salatif ya toshe mata baki.
Tafiya marar nisa ta sadasu da inda suka ajiye motarsu wata bakar Hummer jeef mai
ba'kin glass suka jefata ciki, sannan sukaja motar, tafiya mai nisa sukayi wacce
fatimar batasan inda sukeba, bata iya ganin kome, saboda duhun dare ga kuma ba'kin
glass d'in motar.
Bakin wani 'katon gida wanda zamu iya kira aljannar duniya saboda 'kyawunsa, sukayi
horn me gadi ya bud'e masu get suka shiga, wani had'adden bedroom suka jefata kan
gado sannna suka kware salatif d'inda ke bakinta, saboda tsananin azaba saida
tafasa 'kara.
Haka suka fita suka barta sukaja 'kofar, itakuma banda kuka ba abinda takeyi.
'Karar bud'e d'akin yasa ta d'ago kanta wani 'katon mutum tagani, dogo ne fari me
dogon hanci da manyan idanuwa, ga bakinshi ma barakallahu babbane, ga 'kiba dake
gareshi kamar basamude.
Tsayawa yayi ya 'karema Fatima kallo, sannan ya matso yana lasar baki kamar tsohon
maye, yace "kai amma yau nayi dace tunda ake kawomin 'yan mata ba'a ta6a kawomin
'kya'kyawa kamarkiba, yasa hannu ya cire hijabin dake jikinta, ganin surar jikinta
yasashi 'kara rikicewa dan rigar datasa tad'an kameta, ga kanta ba d'an kwali, yayi
dariya yace amma kinada ala'ka da india ko? Wannan 'kya'kyawan gashi haka, yakai
hannu yana shafa kanta, itakuma kuka kawai take takasa ta6uka kome, a zuciyarta sai
addu'a take Allah kada yaba wannan mutumin ikon aikata abinda yake nufi akanta.
Haka yacigaba da shafata yana latsata, inbanda kuka ba abinda take, nan yashiga
'kokarin rabata da 'kayan jikinta, tasa hannu ta rirri'ke koda yaga zata kawo mashi
gardama sai ya nunamata 'karfi lokaci guda ya rabata da rigarta, jikinta yarage
daga ita sai bes, sai wando lagis data Sanya lokacin dazata fito, ganinta haka da
bayyanar 'kya'ky'kawar surarta ya'kara rikitashi, ya fita hayyacinshi gaba d'aya ya
rungomota jikinshi....
_*Ina barar addu'arku masoyana a duk inda kuke, shekaran jiya anyima babana theatre
Emergency, amma yaji sauki, kutayani addu'a Allah 'kara Mashi lafiya da duk musulmi
baki d'aya*_ 👏🏻😭
🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:12 PM] www.gidannovels.blogspot.com [03/09 4:10 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 _*ALHINI*_ 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘
4⃣3⃣4⃣4⃣
4⃣3⃣to4⃣4⃣
4⃣3⃣4⃣4⃣
🖊 kuka Fatima tashiga yi ganin yana neman keta mata haddi, tana cewa "dan Allah
kayi ha'kuri kada ka cuceni kada ka 6ata min rayuwa, tana fad'ar haka tana wani
irin kuka me tsuma zuciyar me sauraro, amma mutuminnan ko ajikinsa, dan ko kad'an
bata bashi tausayiba illah 'kara kwad'aituwa dayayi da ita.
'Ko'karin rabata da sauran kayan dasuka rage jikinta yakeyi, itakuma banda addu'a
ba abinda takeyi, dan batada wani sauran kuzari tattare da ita.
A 6angaren Mukhtar kuwa yasha yawo har kusan 'karfe biyar na asuba amma bega Alamar
zega laraba ba, be 'kara shiga tsananin tashin hankaliba saida yafara jiyo kiraye-
kirayen sallar asuba,
haka yakoma gida zuciyarshi cike da takaici da ba'kin cikin rabuwa da
masoyiyarshi.
Yana shiga gidan a falo ya iske Hajiya da jidda sun buga uban tagumi, suna tunanin
ko yaga fatimar,.....
Ganin shigowarshi shi d'aya batare da laraba ba yasa jidda saurin tashi cikin
muryar kuka tace "yaya baka gantaba? Innalillahi munshiga ukku, ta fashe da wani
sabon kuka.
Jiki sanyaye mukhatar yasamu guri ya zauna.
Sai lokacin Hajiya ta kalleshi jiki a sanyaye tace "Mukhtar Yaya ba'a gantaba ko?
Wata nannauyar ajiyar zuciya yayi sannan ya d'ago da idanunshi wad'anda suka kad'a
sukayi ja saboda tsabar damuwa, yace "Hajiya Fatima ta su6ucemin shikenan Hajiya
narasa Fatima, lokacin wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanunshi, yace "Hajiya
me mukayima Fatima ta gujemu? Me tanema a gidannan tarasa?.
Lokacin wani irin tausayin Mukhtar tashige hajiya, a zuciyarta tace tabbas mukhtar
yana cikin halin damuwa, dan na lura da yanda ya gama dam'ka duk illahirin
soyayyarshi ga Fatima, a Zahiri kuwa cewa tayi "inshaAllah duk inda Fatima take
zata dawo garemu, kudai kucigaba da Addu'a Allah tsareta a duk inda take,
Lokacin jidda ta fashe da wani sabon kuka tana cewa "ya Allah ka bayyanamin
'yar'uwata a duk inda take, Allah kareta da duk wani mugun abu.
Sai da sukaji an kabbara sallah a masallacin kusa dasu sannan kowanensu yatashi
yanufi sashensa dan gabatar da sallah, mukhtar kuwa koda yayi Alwala masallaci ya
wuce zuciyarshi cunkushe da ba'kin ciki da takaicin halin daze tsinci kanshi inhar
yarasa Fatima.
A 6angaren laraba kuwa haka mutumin yari'ka jagulata amma har yanzu Allah be bashi
ikon cimma burinshiba na keta mata haddi,
Amma duk illahirin jikinta yagama jagulata, hannu yakai yana kokarin ida rabata da
bes d'in jikinta wacce ita kad'ai tarage sai lagis d'inda tasa hannu ta rirri'ke
lokacin dataji yana Neman rabata dashi,
Wani irin 'karfi yazo mata a lokacin hannuwanta tasa duka biyun ta d'ora kan
'kirjin mutumin Wanda gaba d'aya yayimata rumfa dashi, ta turashi iya 'karfinta.
Jiyayi kamar wasu 'katti goma sun angizashi, yayi baya,yafad'i 'kasa, lokacin kuma
Fatima ta taso mashi hai'kan kamar wata tsohuwar damisa, lokaci guda duk wani haske
na fuskarta ya dishe, idanunta suka canja launi zuwa ja, tayo kan mutumin hai'kan,
a tsorace yatashi yafara ja da baya, dan ya masifar tsorata dan yanda take
tunkaroshi.
Saida ya dangane da bangon d'akin lokacin yashiga laluben 'kofa dan tsira da
rayuwarshi, amma kafin yayi yun'kurin bud'e dakin yafita ta kaimashi wani wawan
bugu da hannunta d'aya, wani irin duhu yaga ya gifta mashi, kanshi ya bugu da
bangon d'akin, take yafashe jini yafara ambaliya, yana wanke mashi jiki, a tsorace
yafasa wata uwar 'kara yana Neman taimako,
da gudu yaranshi suka nufo d'akin dan jin ogansu yana neman taimako, suka shiga
tura 'kofar amma ko kad'an ta'ki bud'ewa, da sauri guda yanufi wani d'aki ya d'auko
wani makullin ya bud'e, da sauri suka nufi inda ogan nasu yake kwance yana maida
numfashi sama-sama ga jini duk ya gama wanke mashi jikinshi, suka d'agoshi suna
fad'in "oga lafiya meke faruwa? cikin dusashshiyar murya ya nuna Laraba, yace
"ita....itac...itace... Nan kafin yagama fad'a masu yafad'i sumamme.
A harzuke suka nufi Fatima wacce hankalinta yayi masifar tashi da ganin halin da
mutumin dayayi niyyar yimata fyad'e yake ciki, dan ita bata San meya faru da
itaba, tun lokacin da mutumin yanemi ida rabata da kayan jikinta.
Amma me kafin su 'karaso gareta sai ji sukayi an d'aukesu da wasu mahaukatan
marurruka, kowanensu ya dafe kunci yana duba d'an uwansa, kafin suyi wata magana
aka rufesu da duka ta ko'ina, nan suka shiga ihu suna neman taimako, amma ba wanda
ke jinsu, dan dama haka gidan yake ihunka banza ne, dan da haka ogansu ke samun
damar keta haddin 'ya'yan mutane batare da anji koda ihunsuba.
Saida suka daku sukayi li'kis sannan aka 'kyalesu,
Fatima kuwa banda kuka ba abinda takeyi, dan ita kanta abin ya tsoratata yabata
mamaki dan ganin yanda mutanen keshan jibga batare da su duka sunga me dukan nasu
ba,
Lokacin jikinta yashiga 'kyarma takama kuka tana 'yarfa hannuwa tana kiran
innalillahi,
Hanyar guduwa tashiga nema dan tsira da rayuwarta, lokacin idonta yakai kan 'kofa
dake bud'e tun lokacinda yaran oga suka shigo dasukaji yana neman taimako.
Bata tsaya d'aukar kayan taba tanufi 'kofar tashiga falon d'akin tari'ka shiga
'kofofi na gidan, tashiga nan tafita nan amma har yanzu Allah besa taga 'kofar da
zata sadata da wajen gidan ba, 'karshe ma idan tashiga wata 'kofar sai taga ta
'kara maidota cikin gidan.
Haka tayita zagayen gidan, har 'karfe bakwai da kimanin minti sha shidda na safe,
lokacinne kuma oga ya farfad'o daga doguwar sumar dayayi, yayi saurin kai dubanshi
gurin da laraba take amma be gantaba, cikin tsananin rud'ewa ya kai dubanshi ga
yaranshi dake kwance suma basu san inda kansu yakeba, lokacin ya ta'kar'kara
yatashi yakai masu duka, "kutashi kai dan uwarku ku tashi ina yarinyar nan take, a
firgice suka kai dubansu ga ko'ina na d'akin basu gantaba.
Cikin d'aga murya oga yake magana, kuyi sauri ku nemomin ita, kada ku kuskura tabar
gidannan, da sauri suka tashi suka shiga zagaya gidan suna nemanta, dan sun tambayi
me gadi yakuma tabbatar masu da bata fitaba, aiko suna cikin dubawa sukayi kici6is
da ita a cikin wani korido, wata 'kara ta fasa tayi baya, kafin tayi wani yun'kuri
har sun cafkota.
Cikin gidan suka koma da ita, wannan karon wani d'akin suka kaita ba wanda suka
fara ajiyeta da farko ba.
Wata igiya suka sa suka d'ad'd'aureta, sannan sukaja 'kofar d'akin sukasa key suka
kulle.
Banda kuka ba abinda Fatima keyi, wannan karon tariga ta gama sadau'kar da
rayuwarta,
Bayan kamar awa d'aya da d'auretane, taji ana murd'a kofar, takai dubanta ga 'kofar
dan ganin me shigowa.
Oga ne yashigo cikin shigar ba'ka'ken jacket da wando sai wani ba'kin 'katon glass
dake fuskarshi me suna no respect 😎.
sai yaranshi guda biyu suma cikin 'kananan kaya suna take mashi baya.
Bakin 'kofa yaran suka tsaya, kowane gefe guda yayinda sukasa 'kofar tsakiya,
Shikum oga ya ida shigowa d'akin inda fatima take d'aure yanufa yashiga zagayata
yana tafa hannuwa, itakuma sai binshi take da ido duk illahirin jikinta 'kyarma
yake,
Wani shu'umin murmushi yayi yace.......
4⃣5⃣to4⃣6⃣ Very 4⃣5⃣4⃣6⃣
4⃣5⃣4⃣6⃣
🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:12 PM] www.gidannovels.blogspot.com [04/09 3:57 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 _*ALHINI*_ 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
®```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘
4⃣7⃣4⃣8⃣
4⃣7⃣to4⃣8⃣
4⃣7⃣4⃣8⃣
🖊 Cigaba yayi da kallonta, sannan yace "A gaskiya na kwad'aitu da kyakkyawar surar
da Allah yayimaki, kuma iya tsawon rayuwata ban ta6a d'ora idona kan wata mace ba
tabani sha'awa in kyaleta batare dana biya bu'katataba, amma ke sai gashi na kasa
aiwatar da kome a kanki.
"Ianso zan miki wasu 'yan tamaboyoyi yanzu, ki tabbatar da kin bani amsarsu iyakar
gaskiyarki, hakan zesa in fiddaki daga gidannan da kaina batare da wani abu yafaru
dakeba.
Binshi kawai takeyi da ido, dan ita ahalin yanzu tariga ta sadaukar da rayuwarta,
kuma yanzu take danasanin gudowa datayi daga hannun mutanen dasukayi mata halacci,
yanzu batasan halin da guduwarta ya jefasu cikiba, tabbas ko ba'a fad'aba tasan
idan hankalinsu yayi dubu yatashi, ba kamar masoyinta Mukhtar Wanda ya d'auki son
duniya ya d'ora mata, a zuciyarta tace _(ya Allah ka fitar dani daga hannun wannan
mugun mutumin, Allah ka maidani gurin masoyina abin 'kaunata Mukhtar)_.
Wata uwar tsawa ya daka mata, wacce tayi saurin maidota daga duniyar tunanin data
afka, yace "miye sunanki?
Jiki na 'kyarma ta kalleshi idanunta na zubar da hawayen nadama tace
"Sunana Fatima...
Murmushi yayi sannan ya maiamaita sunan fatima koh? Ya'kara tambayarta, ta d'aga
Mashi kai alamar eh.
Yayi shuru na kimanin mintuna biyu sannan ya'kara jeho mata wata tambayar,
"Fatima ke mutum ce ko Aljan?
Tace "ni mutum ce.
"Amma ke matsafiyace,
Jiki na 'kyarma ta girgiza kai tace
"Ni ba matsafiya bace ban ta6a tsafiba.
Shuru yayi na wani d'an lokaci sannan yace "to fatima abinda yafaru jiya miye
kikayi idan kince keba Aljana bace, cikin muryar kuka tace "minayi,? Wallahi banyi
kome ba.
Cikin takaici ya kalleta yatuno da irin 'karfin data nuna mashi jiya lokacin dayake
'ko'karin yimata fyade, da ciwon data jimashi, yashafa kanshi inda ta dokeshi gurin
ya fashe, take wani irin mugun tsoronta ya dirar mashi a zuciya, ya maida kallonshi
gareta yace "yanzu zaki iya gane gida?
Kai kawai ta d'aga mashi alamar "eh badan tasa ran ze maidata gidan ba.
Hannu yasa ya kwanceta daga d'aurin da sukayimata, sannan yace "zaki iya shiga
toilet ki watsa ruwa ki canja kaya ni zan maidaki gidanku da kaina, dan barin
irinki suna zuwa hannun masu irin halinmu babban had'arine.
Be jira abunda zata fad'aba yafita daga d'akin yaranshi suka take mashi baya.
Tana ganin yafita jiki na 'kyarma taje ta kulle d'akin hada sa key da sakata,
sannan tafad'a toilet tahad'a ruwan d'umi tayi wanka, tad'an gasa jikinta dan duk
illahirin jikin ciwo yake mata, sannan ta d'auro Alwala tafito tasa kayanta sannan
ta d'ora hijab ta kabbara sallah, dan bata manta da batayi sallar asuba ba.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Zaune suke jugum-jugum kowanensu yabuga uban tagumi bakajin kome sai sheshekar
kukan jidda, dan tunda aka tabbatar da