Advertisements
Chapter 8 Reading ALHINI by Zee Mmn khadye BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALHINI by Zee Mmn khadye

Author :  Zee Mmn khadye Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 10

21K to 24K   out of 27.3K words

kece dangina, nasan Hajiya zaki iya
tsayamin akan kome, dan Allah kiyimin kome ba sainaje 'kauyeba, idan lokaci yayi
zanje...

Cike da tausayi Hajiya tace "to shikenan Allah shige mana gaba, suduka suka amsa
da Ameen, jidda hada yin wani gajeren murmushi dan jin Hajiya ta Amince da bu'katar
Fatima, dan ita a duniya tana masifar son abinda Fatima keso.



*_BAYAN SATI BIYU_*

Ansaka ranar Auren Laraba da mukhtar, lokaci d'aya aka sanya dana jidda, hakan yayi
dai-dai da saura wata d'aya da sati daya ayi bikin.

Wai kada kaga farin ciki tsakanin masoyan, jidda kuwa tafi kowa murna, dan tana
masifar son kasancewar fatima amatsayin matar yayanta.
Tun daga ranar da'aka saka biki hankali ya kwanta hidima ta kankama,

Bayan sati biyu mukhtar yasa akayo ma amaren odar kayan d'aki kome da kome yasa
sukayi Mashi list,

Ankawo kaya abin gwanin ban burgewa, mukhtar kuwa angama 'kera mashi gidanshi a
unguwar dutsin safe malali quaters, gidane nagani na fad'a dan ba 'karamin 'kerashi
akayiba.

Ana saura sati biyu biki aka kawo lefen jidda daga gidansu sahibinta Usman, akwati
shidda nar'ke da kaya nagani na fad'a.

Washe gari kuma mukhtar ya dam'kama Fatima nata lefen akwatina takwas, nar'ke da
kayan arzi'ki, ranar saida Fatima ta zubar da hawaye na abu biyu, wani 6angaren
farin ciki wani 6angaen kuma tana _*ALHININ*_ rashin mahaifiyarta lokacin dazatayi
aure, tasan datana raye datafi kowa farin cikin kasancewar zuwan ranar.

A 6angaren Hajiya kuwa hidima takeyi sosai dan duk wani Abu daya dace uwa tayima
'yarta lokacin aurenta Hajiya tayima jidda da Fatima, babu wani banbanci take had'e
kome tanayimasu tare.

Maman Ummi itace 'Kanwar Hajiya wacce sukafi sha'kuwa, saboda haka ita Hajiya
tabarma 'kwangilar kome na gyaran amare.

Ana saura sati d'aya bikin Maman Ummi tazo har gida tatafi da amare dan gyaresu.

Gyara kuwa sosai amare sukasha, cikin kwana biyar, idan kagansu dole ka 'kara
kallonsu dan wani masifaffen 'kyau dasukayi, jikinnan nasu har wani she'ki yakeyi,
dan dilkar da Maman Ummi kemasu irin wacce ake yiwa larabawace daga 'kasar
saudiyya, tataho da ita musamman saboda gyaran amaren,

Dan Maman Ummi saudiyya take zaune saboda bikin kawai tazo, dan sune *Amara 'Kirjin
biki*_{Littafin badi'at lbrahim}_ dan batada biki kamar na jidda *Autar
Hajiya*_{Littafina daya gabata}_
Aiko sunsha gyara gurin Maman Ummi dan wani abun idan tashafe masu jikinsu dashi
jin fatarsu suke kamar ta jarirai saboda laushi, 'kamshi kuwa ajikinsu kamar anyi
6arin turare.

Gurin 6angaren kayan tsumi kuwa, ba'a magana, dan suma Maman Ummi tazo dasu daga
'kasar saudi, _*(Hmm ni su Maman Ummi mutanen saudia, kome na larabawa)*_๐Ÿ˜œ




๐Ÿ–ŠZee Elkaseem
Mmn khady๐Ÿ’‹
[10/16, 8:12 PM] www.gidannovels.blogspot.com [08/09 9:37 am] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ _*ALHINI*_ ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ ๐Ÿ˜˜


5โƒฃ7โƒฃ5โƒฃ8โƒฃ
5โƒฃ7โƒฃto5โƒฃ8โƒฃ
5โƒฃ7โƒฃ5โƒฃ8โƒฃ


*_RANA BATA 'KARYA SAI DAI UWAR 'DIYA TAJI KUNYA_*

๐Ÿ–Š Ni zee da inada dogon hanci dana rangad'a guda, amma ko yanzuma bata 6aciba dole
ince ๐Ÿ‘ƒ๐Ÿป Ayuuririri........ ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป

Yau nahango dandazon dubban jama'a 'kofar gidan su jidda da mukhtar wad'anda suka
halacci d'aurin auren Mukhtar da amaryarsa fatima (laraba) sai jidda da angonta
Usman, kowanensu akan sadaki dubu sittin-sittin.

Wai kada kaso kaga farin ciki gurin masoya aranar, mukhtar na hango ansha shadda
hada uwar babbar riga, ga hula an d'ora, takalminnan nasa designer massaraci abin
dai yabadada kala, kallo d'aya zakayima angwayen kagane suna cikin farin ciki, dan
kowannensu bakin ya'ki rufuwa.

Amare kuwa acikin gida Mmn Ummi tagama shiryasu cikin wani rantsatstsen material,
kalar purple sai takalmin 'kafafunsu fari kowace da Jakarta fara, sai manyan
mayafinsu fari da aka yafa musu, sunyi wani masifaffen 'kyau kamar yayan sarakuna,
kome iri d'aya akayimasu musamman Hajiya tayi masu kaya kala shidda-shidda domin
yin hidimar biki, dan suduka ba wacce tayi amfani da kayan lefenta.

Da misalin 'karfe biyar na yamma Hajiya ta tara amaren a bedroom d'inta tana yimasu
nasiha, ba abinda sukeyi sai kuka, jidda na kukan rabuwa da hajiyarta da kuma farin
cikin kasancewa da masoyinta, yayinda Fatima kukanta ya kasu kashi ukku, wani
6angaren farin ciki wani 6angaren kukan rabuwa da Hajiya matar data zama tamkar
uwa uba dangi agareta, sannan babban jigon yin kukanta shine *_ALHININ_* rabuwa da
innarta, taso ace inna na raye a dai-dai wannan likacin itama taga Auren 'yarta
tayi farin ciki, amma ina ba haka Allah ya 'kaddaraba...

Ana cikin haka motar Alh mansir tayi parking a harabar gidansu jidda, Alh Mansir
'kani ne ga mahifinsu Mukhtar kuma shine ke shige masu gaba akan kome idan bu'katar
hakan ta taso.

Ganin shigowarsa yasa Ameeno saurin tashi daga zaman datayi kusa da Maman Ummi
wacce keta bata labarin saudiyya, dama Ameenoo da Mmn Ummi 'kawayene, tun kafin
Maman ummin tayi aure sukoma saudiyya itada me gidanta, Ameeno kuwa a gombe take
aure amma duk da haka suna waya da Maman ummin.

'Dakin Hajiya tanufa ta iske ta tasa maren gaba tanayimasu nasiha, guri tasamu ta
zauna itama ta d'ora da nata nasihar, dama Amino badai nasihaba, dan kan nan nata
cike yake da wa'azi da nasihohi.

Ahaka mutanen dake falon suka fara magana afito da amaren, jidda najin haka tafad'a
jikin hajiyarta tana kuka, da 'kyar aka 6am6areta jikin Hajiya aka fita dasu kowace
na sharar hawaye.

Alh Mansir da kanshi yakai kowace gidanta, sauran mutane kuwa sai dai sukabi daga
baya dan ganin gidajen amaren.

Alhmdulillahi jidda ma gidanta ya had'u a unguwar layout aka kaita, fatima kuwa
malali quaters mukhtar ya 'kyan'kyara masu 'kerarren gidansu.


Bayan mutane sunje anga gidajen amaren anyimasu duk abinda yadace bayan sallar
isha'i kowace takama gabanta, anbar amare su kad'ai a gidajensu.

Fatima zaune tsakiyar gadonta ta had'e kai da gwiwa tana sharar hawaye wanda ita
kanta ta kasa tantance na minene, farin ciki ko *_ALHINI_* A haka angon nata ya
risketa, tanajin shigowarshi amma bata d'ago ta kalleshiba.

Hawowa yayi kan gadon ya zauna gab da ita har jikinsu na gugar na juna, hannu yasa
ya yaye lullu6in dake kanta, yasa hannu ya d'ago da 'kya'kyawar fuskarta wacce duk
ta 6aci da hawaye, yace fatimana miye yasaki kuka, Baku far in ciki da kasancewa
mallakina ne,? Shiru tayi mashi tacigaba da zubar da hawayenta wani na bin wani.

Farin handkerchief ya fiddo daga Aljihunsa yasa yana goge mata hawayen dake zuba
daga idonta, wani daddad'an 'kamshi dake jikin handkerchief ya doki hancinta
batasan lokacin data saki wata ajiyar zuciyaba,
"Plz fatimana ki dainamin asarar hawayenki, baniso, idan kuma kinaso nima kiga nawa
hawayen to kicigaba da zubar danaki, kinriga kinsan damuwarki damuwatace, farin
cikinki shine nawa, ki taimakeni ki daina kukannan.

Haka yayita rarrashinta harya samu tayi shiru, sannan ya tashi ya nufi kitchen da
kansa ya d'auko plate da duk wani abu dayasan zasu bu'kata.

Dan'karaยฒ kajine guda 2 ya baje musu da kanshi yari'ka yaga yana samata abaki, da
tana d'an nonno'kewa tanajin kunya har dai tasaki jikinta taci, shima yaci sosai
sannan yazuba musu lemu cikin glass cup suka sha sannan sukabi da ruwan roba, bayan
sun kammala ne ya kalleta yace "kinyi sallah isha'i kuwa kai kawai ta iya d'aga
mashi alamar eh dan duk illahirin jikinta 'kyarma yake sakamakon wani mayen kallo
dataga mukhtar namata, yace "to sai ki tashi mu d'auro Alwala mu gabatar da sallar
nafila domin nuna godiyarmu ga Allah daya cika mana burinmu,
Nan fa ta daburce tarasa wacce amsa zata bashi dan tasan tana fashin sallah ne kuma
bazata iya fad'a mashi ba.

Tashi tayi tafad'a toilet tashe'ka wanka ta gyara jikinta, sannan tafito shima
wankan yashiga, kafin yafito ta shafe jikinta da mayukan masu dad'in 'kamshi tare
dayima jikinta 6arin turarruka masu 'kamshin gaske, sannan tanufi wadrope ta d'auko
rigar baccinta tasaka tabi lafiyar gado.

Mukhtar kuwa daya gama wanka sai ya d'auro alwala, yana fitowa yaganta kwance,
beyimata magana ba saida ya d'auko wata jallabiya milk me gajeren hannu ya Sanya
sannan yace "ki taso muyi sallar, shiru tayimashi tare da lumshe idanunta kamar
bata jinsa, ganin tayimashi shiru yasa ya hawo kan gadon ya tallafo ta yace my fati
kitashi muyi sallah, ahankali ta baud'e idonta tace nayifa sallah yace "eh
kinfad'amin sallah nafila nake nufi, cike da jin kunya tace "uhm ina fashi ne, wani
irin fad'uwar gaba yaji dan jin tace tana fashin sallah dan yau yayi niyyar suci
amarcinsu, amma ba hali, haka ya kwantar da ita yaje ya kabbara sallah nafila
raka'a biyu yayi sanan yayi addu'a yashafa, kafin yagama bacci me dad'i yayi awon
gaba da ita.

Yana kan prayer mat yajuyo ya kalleta baccinta take cikin kwanciyar hankali, ya
'kurama 'kya'k'kyawar fuskarta ido yayi wani 'kyawataccen murmushi, addu'a yayi ya
shafe jikinsa sannan itama yayi addu'ar yashafe mata jiki, sannan ya kashe fitilar
d'akin ya kunna masu ta gefen gado, sannan ya haye gadon ya rungumota jikinshi
zuciyarshi cike da farinciki, a haka har bacci me nauyi yayi awon gaba dashi.

A 6angaren jidda kuwa a ranar Usman ya more kud'in sadakinsa dan be d'aga mata
'kafaba, ba 'karamar hawala tasha ba, haka ya rin'ka raraahinta yana shimata
Albarka, wani irin sonta ya'karaji cikin zuciyarshi dan yanda yasameta yaji dad'i
sosai.
๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn Khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:12 PM] www.gidannovels.blogspot.com [08/09 9:40 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ _*ALHINI*_ ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ ๐Ÿ˜˜


5โƒฃ9โƒฃ6โƒฃ0โƒฃ
5โƒฃ9โƒฃto6โƒฃ0โƒฃ
5โƒฃ9โƒฃ6โƒฃ0โƒฃ



*_BAYAN SATI BIYU_*

๐Ÿ–Š da misalin 'karfe biyu na rana fatima na hango kitchen tanata ha'kilon had'ama me
gidanta abinci.

Cikin awar da bata wuce d'aya da rabi ba tagama shirya kome kan dining, sannan
tanufi d'akinta bayan tagyara kitchen d'in tsaf ta goge ko'ina kamar ba yanzu
tagama girki ciki ba.

Kai tsaye toilet tafad'a ta she'ka wanka, sannan ta d'auro Al'wala tafito ta
kabbara sallar azahar, bayan ta kammala sallar gaban dressing mirror ta zauna
tafara d'and'asa kwalliya, bayan tagama wadrope tanufa ta d'auko wasu riga da siket
na atamfa ta Sanya, kayan kuwa sun zauna da6as jikinta kamar a jikin nata aka
d'inkasu, sannan takashe d'aurin d'an kwali, turarruka ta feshe jikinta take
'kamshin jikinta ya gauraye da 'kamshin preshner dake d'akin da 'kamshin girkin
datayi, yabada wani kalar 'kamshi me dad'in sha'ka.

'Karar tsayuwar motar angonta taji, da sauri tafito ta zauna falo tana jiran
shigowarshi, dan yahanta zuwa tarboshi harabar gidan saboda me gadi na kallonta
shikuma yana masifar kishinta.

Da sallama yashigo falon, da sauri ta tashi ta tako zuwa gurinshi tana wani yanga
tana karairaiya kamar wacce batasan taka 'kasa, rungumeshi tayi tare dayimashi
'kya'k'kyawan Sumba a kumatu tace "welcome my husband, yace welcome fatimana,
nasameki lafiya, cikin zazza'kar muryarta tace "lafiya lao, kadawo lafiya yace
"lafiya.

Tace kafin kome muje ka watsa ruwa tukun, ba musu yabita zuwa toilet dinshi tahad'a
mashi ruwan wanka sannan yashiga itakuma ta jawo mashi 'kyauren toilet d'in, sannan
tazauna bakin gado tana jiran fitowarsa.

Bayan ya fito ya sanya kaya marar nauyi sannan tayimashi jagora suka nufi dinning.

Cike da jin dad'i da farin ciki suke cin abincin, har suka kammala, sukayima Allah
godiya,
Mukhtar ne yafara tashi daga dinning d'in yakoma kan kujera three seater ya kwanta,
itakuma fatima tsayawa tayi tana tattare kayan dasukaci abinci.
Bayan takai kuloli kitchen tadawo zata d'auki jug da cup's, sai taga wani
had'ad'en zobe kan table d'in, dariya tayi sannan ta d'auki zoben tace nayi
tsintuwa, mukhtar najin haka yatuno da zobenshi daya ajiye kan table din, da sauri
yataso yace kibani ring dina, ๐Ÿ’ nasan dai shine kika gani, cike da tsokana tace
bazan bayar ba, saika fad'amin wacece tabaka, cike da tsokana yace budurwata
tabanishi kuma zoben Al'kawarine, bekamata ta ganni babu shi a hanuna ba, fatima ta
yamutsa fuska tace "idan taganka babu shi ta tambayeka kace mata wacce tafita power
a gurinka tarabaka dashi, matsowa yayi gab da table d'in yace "kibani abuna tun
muna wasa da juna, cike da nishad'i ta 'kyal'kyale da dariya tace "bazan bayarba,
yana kallo ta zirashi a yatsanta, aiko da sauri yanufota yana dariya yace "kkkkk
kada ki Sanya........

Kafin yazo harta Sanya aiko ya nufota ze kar6a da gudu ta ruga tana dariya yabita
haka suka rin'ka zagayen falon amma besamu ya dam'keta ba, bedroom tanufa dagudu
yabita tana 'ko'karin turo 'kofar yayi saurin turawa yashiga, dariya takamayi
tafad'a kan gado tana maida numfashi, shima kan gadon yafad'a kusa da ita yana
maida numfashi, rungumota yayi jikinsa yace "waye nakama, dariya tayi tace baka
kama kowaba, dariya yayimata yace zakiyi bayani zaki san ban kama kowaba,
Nan fa wasa ya canja salo, a lokacin saida suka samu ladar aure,
Saida sukaji amfara kiran sallar la'asar sannan suka dawo hayyacinsu, toilet suka
nufa suka she'ka wanka sannan suka d'auro alwala, mukhtar yawuce masallaci, itakuma
fatima Bakin gado ta zauna zuciyarta cike da farin cikin yanda mukhtar d'inta ke
nuna mata tsantsar so da 'kauna.

Wayarta ta lalubo ta 'kira jidda, ringing biyu ta d'auka "hellow sister ya kike,
"lafiya lao sister ya amarci, to Alhmdlh zamuce, haka sukasha firarsu, kusan kullum
dama sai sunyi waya akalla sau hud'u ko sau shidda.

Bayan sunyi sallamane fatima ta tashi domin gabatar da sallar la'asar.


Rayuwa me dad'i da so da 'kauna tsakanin masoyan abin gwanin birgewa,

6angaren jidda ma tana samun kulawa sosai daga gurin Usman d'inta.

Fatima da jidda sukam sunyi dacen mazaje saidai suyima 'yan baya fatan samun mazaje
kamar nasu.

Sai dai lokaci zuwa lokaci fatima na kukan *_ALHININ_* Innarta, kuma tanason zuwa
'kauyensu amma lokacin data tsarama kanta na zuwa 'kauyen beyiba.




๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:12 PM] www.gidannovels.blogspot.com [11/09 9:00 pm] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ _*ALHINI*_ ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ ๐Ÿ˜˜


6โƒฃ1โƒฃ6โƒฃ2โƒฃ
6โƒฃ1โƒฃto6โƒฃ2โƒฃ
6โƒฃ1โƒฃ6โƒฃ2โƒฃ



*_BAYAN SHEKARA 'DAYA_*

๐Ÿ–Š Fatimana......Fatimana.....tun daga falo yake kwalamata kira, amma yaji shiru,
cike da mamaki ya nufi d'akinta dan yasan muddin tana lafiya to dataji tsayuwar
motarshi take zowa bakin 'kofar falo tajira shigowarshi ta tarbeshi, amma yau sai
yaga akasin haka, cike da fargaba yanufi d'akinta dan yimata Albishir Wanda yasan
idan tajishi har 'kyauta sai tayimasa, dan kuwa so yake ya gayamata haihuwar jidda,
dan kullum batada magana saita haihuwar jiddar, duk da itama tana fama da tsohon
cikinta haihuwa ko yau ko gobe koma yanzu.

Ringing d'in wayarta yajiyo bedroom d'inta hakan ya tabbatar mashi da tana ciki,
dan haka da sauri yanufi d'akin.

Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un ya furta tare da saurin 'karasawa ya tallafota ya
had'ata da jikinshi yana fad'in "lafiya fatimana meya sameki, meya faru, cikin
tsananin azabar rad'ad'in ciwon dake addabarta ta nuna mashi mararta, sannan ta
dafe bayanta tana wash....
Can ciwon ya'kara tsinkulota tafara salati cikin wata wahalalliyar murya "wayyo
yayana zan mutu ka taimakamin bayana ze 6alle 'kuguna, tana fad'i tana 'kara
shigewa jikinsa tana kuka, cikin tsananin rud'ewa Mukhtar ke rarrashinta ga kuma
wayarta gefe tanata ringing amma bebi kantaba, lalla6ata yayi ya kwantar da ita
tare da fita domin yakira wata makwabciyarsu malamar asibiti, da sauri yashiga
gidan sister safiyya ya sheda mata halin da Fatima take ciki, ba'afi minti gomaba
suka shigo gidan tare,tana zowa tasa safa ta dubata taga ta kusa haihuwa, nan ta
rubutama Mukhtar duk abubuwan da ake bu'kata.

Da sauri yaje chemist d'in kusa dasu ya siyo, yana dawowa yabata kayan ba'afi
mintuna 5 da dawowarsaba laraba tayi wani 'kwa'k'kwaran nishi me 'karfi tare da
santalo sankad'ed'en yaronta.

Sister safiyya tayi hamdala sannan ta gyara yaro tayima Fatima duk abinda ya dace,
mukhtar kuwa dan tsananin murna bakinshi ya'ki rufewa nan ya fiddo yawa yakira
Hajiya ya sanar da ita haihuwar Fatima, sannan yacigaba da 'kiran 'yan'uwa da
abokan arzi'ki yana sanar dasu.



Bayan sister safiyya ta taimakama Fatima tayi wanka ta gyarata itada baby.
Fatima ta fito shar da ita kamar ba itabace wacce ta haihu sai buga uaban 'kamshi
take itada baby, sister safiyya da kanta ta shiga kitchen tahad'oma Fatima tea me
kauri Wanda yaji milo sosai takawomata tana zaune bakin gado, saida ta tabbatar
data shanye duka sannan tabata magungunanta tasha sannan tafito da niyyar tafiya
gida.

A harabar gidan tagamu da mukhtar yana niyyar fitowa daga mota, da Alama wani wuri
yaje amma bame nisaba saboda be dad'e da fitaba, ganinta yasashi saurin ida fitowa
daga motar yace "ah sister har kin fito?
Cikin fara'a da sakin fuska tace "harna fito Baban baby, zanje gidane kafin in
'kara zagayowa inga lafiyar baby da momynsa.
Cike da jin dad'i mukhatar yayimata godiya sannan ta wuce, shikuma yashiga cikin
gidan kai tsaye bedroom d'in fatima ya nufa da sallama yashiga.

Zaune take gefen gado ta rungume babynta tanata murmushi abinta, da murmushin shima
ya 'karaso yasa hannu ya 'kar6i baby yayimashi addu'a sannan yayimashi hud'uba
kamar yanda addinin musulunci ya tanada,ya dad'e yana kallon babyn sannan ya maida
dubanshi gareta yace "ammafa babyn nan dani yake kama,cikin shagwa6a tare da
marairaice murya tace "Ba wani dani yake kama, cikin tsokana mukhtar yace "Ba wani
ki duba kiga hancinsa irin nawane da manyan idanunsa, yafad'a yana kallonta cikin
tsokana dan yasan kallo d'aya zakayima idanun yaron kasan irin na Fatima ne,
bandasu amma duka face d'in mahaifinshi ya d'auko,
Cikin murya kamar zatayi kuka tace "ka tambayi sister safiyya kaji tun tana mashi
wanka tace dani yake kama......

Mukhatar ya 'kyal'kyale da dariya dan ganin yanda Fatima ta ha'kikance akan yaro
yana kama da ita...

Cikin nishad'i yacigaba da magana ammafa gaskiya sister safiyya tanada kirki,
kiduba kiga yanda take hidima dake, fatima tace "hmm kaidai bari wallahi ni har
kunyartama nakeji, yanzu abinda tayimin ko asibiti naje baza'a kula dani kamar
hakaba........

Wayartace ta katse masu firar dasukeyi tahanyar yin ringing Alamar ana kira, da
sauri ta tashi ta d'auko amma kafin ta danna OK har kiran ya tsinke, 18missed call
tagani...

Fiddo idan tayi waje tare da kallon Mukhtar tace "18 missed call, yace ki duba
kigani nasan dai bewuce jidda, kinsan itama ta haihu....

Cikin zumud'i tace "dan Allah fa banda tsokana, yace "kirata kiji d'azu da Albishir
d'in nazomaki saina taras kina labour shiyasa hankalina ya d'auke ban gaya makiba.

Wayarta ta Shiga dubawa aiko 15missed call tagani na jidda sai 3 na Hajiya, Hajiya
tafara Kira ta gaisheta, nan hajiyar ke nunamata cikin tsananin farin cikin datake
na samun jikoki biyu Lokaci guda....

Nan Fatima ta ida tabbatar da maganar haihuwar jidda, saboda haka sunayin sallama
da hajiya number jidda takira, lokacin itakuma jidda tanada labarin haihuwar
larabar haka suka dad'e suna waya sunama juna barka sannan sukayi sallama.

Itakuma jidda da asubane ta haihu tasamu baby girl, fatima kuma bayan azahar.




_````ZEE```_ *Wishes u*
```HAPPY SALLAH```
*IN*
_*ADVANCE*_

๐Ÿ’ž```EID MUBARAK```๐Ÿ’ž




๐Ÿ“note
Inaba masu bin wannan Littafin ha'kuri akan jina da kukayi shuru kwana biyu, hakan
yafarune saboda wasu 'yan hidimomi dasukasha kaina, gakuma hidimar sallah saboda
haka kucigaba da ha'kuri zan ri'katurowa duk lokacin dana samu lokaci kafin agama
hidimar sallah.
Love u all ๐Ÿ’ƒ๐Ÿป




๐Ÿ–Š Zee Elkaseem
Mmn khady ๐Ÿ’‹
[10/16, 8:13 PM] www.gidannovels.blogspot.com [17/09 8:34 am] .: ๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ญ *_ALHINI_* ๐Ÿ˜ญ
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ยฎ```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ ๐Ÿ˜˜


6โƒฃ3โƒฃ6โƒฃ4โƒฃ
6โƒฃ3โƒฃto6โƒฃ4โƒฃ
6โƒฃ3โƒฃ6โƒฃ4โƒฃ


Haka 'yan uwa da abokan arziki sukayita zuwa gidan mukhatar da gidan jidda suna
ganin baby, barakallahu.
jidda Usman yayimata kaya nagani nafad'a, akwati ukku yacikama baby da kaya,
jidda kuma akwati biyu sha'ke da kayanta,

6angaren mukhtar kuwa akwati set yacikama fatima da babynta, abin dai gwanin
sha'awa anyi kome cikin tsari.

Ranar kwana bakwai akayi suna, d'iyar wurin jidda aka samata suna Rahama, d'an
gurin fatima kuwa sunan Mahaifin mukhtar aka sanyamashi, amma suna kiranshi sultan.

Ba 'karamin abin arzi'ki fatima ta

8 / 10