Advertisements
Chapter 7 Reading ALHINI by Zee Mmn khadye BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALHINI by Zee Mmn khadye

Author :  Zee Mmn khadye Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 10

18K to 21K   out of 27.3K words

6atan fatima jidda ke kuka, idanunta sun
kumbura ga matsanancin ciwon kai dake damunta sakamakon kukan datake ba
'ka'k'kautawa.

Mukhtar ma kukan yake kamar mace, kokuma 'karamin yaro, sun tasa hajiya gaba, wacce
itama duk illahirin jikinta mace yake, dan ta d'auki fatima kamar 'yar data Haifa
da cikinta saboda haka dole taji 6atanta har cikin ranta, amma ganin yanda yaranta
suka d'aga hankalinsu yasata daurewa tari'ka rarrashinsu.

Suna cikin wannan zaman ne megadi yashigo da sallama, bayan Hajiya ta masa sallamar
yace Hajiya sallama ake a waje, cikin damuwa Hajiya ke tambayarshi "wanene me
sallamar, yace "eh to Hajiya gaskiya ban shedashiba amma yace maganace me mahimmaci
ke tafe dashi idan da hali yanaso ayimashi iso yashigo,
Hajiya tace "OK shigo dashi.

Bayan fitar me gadi da kamar minti biyar saigashi yashigo, cikin shigar manyan kaya
shaddace jikinsa, light blue, sai hularsa light blue, sai takalmi ba'ki, kallo
d'aya zakayimashi ka gane mutum ne wanda naira ta zauna mawa...

Bayan yasamu gu ya zauna yafara magana "ni sunana sadiq kuma ni d'an cikin garinnan
ne, idan bazaku damuba inaso insan yara nawane a gidannan, ma'ana 'ya'ya nawa kuke
dasu.....

Wani 'kululun ba'kin ciki ya tsayama mukhtar a wuya, a fusace ya kalli mutumin yace
"wannan wane irin rainin wayone zakazo kana mana tamabayar da bata shafekaba,
Sadiq yabud'e baki zeyi magana kenan sukaji tafiyar mutum ana shigowa gidan, da
sauri suka kai dubansu gurin....

Da gudu jidda ta tashi taje ta rungumeta tana kuka, tana cewa "sister ina kika
shige kika barmu cikin tashin hankali, fatima kasa furta kome tayi sai hawaye
datake zubarwa, cike da murna da fargaba Hajiya tazo takama hannun Laraba tashigo
da ita falon, mukhtar kuwa kasa furta kome yayi, illah bin fatima da yayi da ido.

Maganar Sadiq ce tadawo da hankalinsu gareshi, yayinda yake sanar dasu abinda
yafaru tsakaninshi da Fatima, be 6oye masu kome ba ya sanar dasu gaskiyarshi, dan
yariga ya tuba daga mummunar d'abi'ar dayake ta 6ata yaran mutane.

Wani irin takaici da ba'kin ciki da kishi suka taru suke rufe Mukhtar dan jin
labarin da Sadiq yafad'a saboda haka ido rufe ya tunkareshi kamar wani tsohon
mayunwacin zakin daya kwana beciba.......




4⃣9⃣to5⃣0⃣ Very 4⃣9⃣5⃣0⃣
4⃣9⃣5⃣0⃣




🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:12 PM] www.gidannovels.blogspot.com [04/09 10:48 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 _*ALHINI*_ 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘


4⃣9⃣5⃣0⃣
4⃣9⃣to5⃣0⃣
4⃣9⃣5⃣0⃣


🖊 A zuciye mukhtar yakaima Sadiq wani wawan naushi a fuska, take gancinsa yafara
zubar da jini, cikin 'kankanin lokaci jini ya 6ata mashi tsadaddiyar shaddarsa
wacce tasha d'inkin computer, ganin jinin dake zuba daga hancin Sadiq besa Mukhtar
ya saurara mashi daga dukan dayake mashi ba, cigaba yayi da dukanshi ta ko'ina,
sannan yacimashi kwala ya tadashi tsaye ya angizashi, cikin fushi da d'aga murya
yace "kafita daga gidannan tun kafin inzama ajalinka, mugu azzalumi barin irinka
cikin Al'umma had'arine.

Duk abinnan da Mukhtar yayima Sadiq beyi 'ko'karin hanashiba, kuma be kare kanshi
daga dukan dayayi mashiba, badan beda 'karfin daze ramaba, dan a girme sadiq yakai
d'aya da rabin mukhtar, dan acewarshi duk abinda Mukhtar yayimashi ya can-canci
hakan.

Jidda ce taga abin na yayanta yayi yawa dan dukan sad'iq yake kamar baze barshi da
rai ba, ta kalli Hajiya tace "dan Allah kihanashi kada ya kasheshi,
Bata jira hajiyaba tanufi gurin tari'ke hannun mukhtar tana cewa "dan Allah yaya
kayi ha'kuri ka 'kyaleshi tunda Allah be bashi ikon aiwatar da kome kan Fatimar ba.

Ganin beda niyyar sauronta yasa ta kama hannunshi tari'ke tana bashi ha'kuri a
zuciye ya hankad'ar da ita tafad'i zaune tafashe da wani irin kuka.
Ganin abin na Mukhtar bana hankali bane yasa Hajiya tazo ta kamashi, tace "kai
mukhatar ka daina dukanshi nace, be saurari hajiyaba sai 'ko'karin tura Sadiq waje
yake, yana cewa "kafita kabar gidannan ban 'kaunar ganinka, wallahi idan ina
ganinka zan iya illataka dan ban had'a fatimana da kowaba.

A fusace Hajiya ta fincikoshi, cikin fushi take magana "wai kai Mukhtar wane irin
mutum ne, yaushe kafara rainani da inama magana baka saurarena.

Wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonshi, baya yayi yasamu guri ya zauna kan
d'aya daga kujerun falon yana cika yana batsewa, jiyake dama Hajiya tabarshi da sai
yakusa halaka sadiq.

Fatima kuwa tunda suka shigo gidan taga halin data iskesu hankalinta yatashi, bata
'kara shiga wani tashin hankalinba saida taga yanda Mukhtar ke dukan Sadiq gashi
harya fitar mai da jini amma be daina dukansaba.

*_Innalillahi'wa,inna'ilaihirraji'un_* tashiga furtawa, tana kuka kamar zata cire
ranta, jidda ce takamata tace "ki daina kuka fatima ki godema Allah daya tseratar
dake da mutuncin ki,
Cikin dusashshiyar murya Alamar tayi kuka tagaji tace "jidda dole inyi kuka, duk
halin damuwar da kuka shiga nice na jefaku, sannan abinda mukhtar yayi yanzu duk
saboda ni yakeyi, wayyo Allah na ina zani da Alhaki, nazama butulu, na guji mutanen
dasukayimin hallaci a rayuwa, mutanen dasuka sharemin hawayen da 'kanin mahaifina
yakasa sharemin,

Zuwa tayi gaban Hajiya ta dur'kusa gwiwa biyu, tana kuka tace "dan Allah Hajiya Ku
yafemin nasan nashiga rayuwarku na jefaku cikin damuwa.

Cike da damuwa da tausayi Hajiya takama hannun fatima ta zaunar da ita kan kujera
tana gogemata hawayen dake zuba Daga idonta.

.
Hajiya takai dubanta ga Mukhtar Wanda keta cika yana batsewa, tace "ba haka
akeyiba kawai ka kama mutum kayita duka har ka jimasa ciwo, duk da abinda yafad'i
yana aikatawa ai bekai ga aikatashi ga ita fatimar ba,
Kuma tunda kaga yakawota har gida ina tunanin akwai dalilin sayasa yakawota.

Sannan ta maida dubanta ga Sadiq tace ina jinka yaro, cike da nadama Sadiq yafara
magana,cikin muryar tausayi da nadamar abubuwan daya aikata a baya.
_ ```na kasance ni 'kadai iyayena suka haifa, kuma iyayen nawa sun kasance masu
tarin dukiya, tun ina 'karami suke nunamin tsantsar so da 'kauna, hakan yasa
natashi banajin magana ko kad'an kuma duk abinda naga dama shi nakeyi, tun ina
secondary school nake 6ata yaran mutane, ta hanyar yimasu fyade idan sun'ki
amincewa, a lokacin nama fi so inyi fyaden dan nafi jin dad'in hakan, kuma idan aka
ganeni aka kawo 'karata babana sai yakama fad'a yace anjamin sharri dan ana ba'kin
ciki da dukiyar da Allah yayi Mashi, kuma yabani shi amatsayin d'a d'aya tilo haka
yake fatattakar mutane, wasu su fita suna kuka wasu kuma suje suna Allah ya isa,
ana cikin wannan halinne mamana da babana sukayi tafiya, kan hanyarsu ta dawowa
suakayi had'ari suduka suka mutu, nayi kukan rashin iyayena sosai, bayan kome ya
lafa aka raba gado aka bani, kasancewar bani ganin Kowa da gashin arzi'ki yasa ba
wanda yayi gigin cewa ze ri'kemin dukiyata, cikin dangin mamana, kona baba na, haka
nacigaba da bushasha, har basamu yarana wad'anda sune ke d'aukomin 'yan mata ina
keta masu haddi ta 'karfin tsiya```

Wasu hawaye masu zafi suka zubo daga idanunshi, yace amma sanadin zuwan fatima
gareni yasa natuba na daina wannan mummunar d'abi'ar danikeyi, kuma inaso dan Allah
fatima ki yafemin, yafad'a yana kallonta.

Mukhtar be tausayama sadiq ba ko kad'an illah wani irin haushi daya 'kara bashi
yace "dallah Malam kafita kabar gidannan munji duk bayaninka Allah shiryeka, bani
son ganinka cikin gidannan kuma bani bu'katar jin muryar ka.

Cikin fad'a Hajiya ke magana, dan mukhtar yafara 6ata mata rai tace "wai kai wane
irin mutum ne, mutum yazo har gida yaro'ki yafiya amma kakama cimasa mutunci, ay
inajin koda kafirine yazo neman gafara gareka zaka gafarta mashi kodan yasan
musulunci akwai Alfarma acikinsa, barantana d'an uwanka musulmi, Allah yana son
masu yafiya ga junansu, wai Mukhtar ina iliminka yake,?
Kuma kafin wannan ma ay komiye fatima itace babbar mai laifi, da bata fitaba da duk
haka be faruba.

Sadiq yace "ni najin dad'in fitar tata dan tazama sanadin shiriyata, fatana shine
tace ta yafemin, yafad'a yana zubar da hawaye...


Cikin muryar kuka fatima take magana "tabbas kome yafaru nice na jawo, dan daban
fitaba da hakan bata faruba,
Ta kalli sadiq tace nayafema, Allah 'kara shiryaka, kuma naji dad'i dana zama
sanadin shiriyarka.

Tana gama fad'in haka Sadiq yami'ke yace nagode Hajiya sai anjimanku, yafice daga
gidan.

Fatima kuwa durkusawa tayi tsakiyar falon tana kuka, tana ro'kon Hajiya da jidda da
mukhtar su yafemata,
Mukhtar har cikin ranshi yakejin kukanta, baze iya juraba saboda haka barin d'akin
yayi zuciyarshi na tafarfasa.




5⃣1⃣to5⃣2⃣ Very 5⃣1⃣5⃣2⃣
5⃣1⃣5⃣2⃣




*_'kya'k'kyawar gaisuwa ga 'kanwata, NASIBAT ELKASEEM_*
_Love u my sister_😘




🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:12 PM] www.gidannovels.blogspot.com [06/09 3:22 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 _*ALHINI*_ 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘


5⃣1⃣5⃣2⃣
5⃣1⃣to5⃣2⃣
5⃣1⃣5⃣2⃣
🖊 washe gari bayan kome ya lafa, da misalin 'karfe tara da rabi na safe,
Zaune suke a general falo, bayan sun kammala kalacin safe, Kowa yayi shiru, amma
akwai abinda yake sa'kawa cikin zuciyarshi, yayinda Fatima takan goge guntayen
hawayen dakan zubo mata daga idanunta akai-akai.

Mukhtar yana lura da halin datake ciki saboda haka hankalinshi duk yana gurinta,
fatanshi Hajiya ta wuce d'akinta ya rarrashi fatimarsa ya kwantar mata da hankali,
dan idan akwai abinda yafi tsana a duniya shine 6acin ran hajiyarsa sannan kuma
yaga fatimarsa cikin damuwa.

Hajiyace ta maido da kowanensu daga duniyar tunanin daya Lula, yayinda ta kalli
Fatima tace "Fatima inaso ki nutsu ki kwantar da hankalinki ki fad'amin gaskiyar
dalilin dayasa kikayi 'ko'karin guduwa daga hannunmu wanda hakan yajefamu cikin
matsanancin tashin hankali.

Shuru tayi na d'an wasu mintoci bakajin kome sai sheshshekar kukanta, sannan tafara
magana cikin sarkewar murya tace "da farko inaso in ro'keku yafiya akan halin
damuwar dana jefaku na 'ko'korin guduwa danayi,
Bawai nayi hakan bane dan kun gaza da ri'kon da kukemaniba, ba kuma dan na raina
hallacin da kukayimani bane, a'a nayi hakane saboda baniso in sakamaku da sharri
akan Alkhairin da kukayimani.

Sannan inaso Ku gafarceni akan 6oye maku wasu abubuwa da dama danayi dangane da
labarina, yau inaso zan sanar daku kome bakin gaskiyata, dan baniso nazama sanadin
rushewar farin cikinku.

*_HAKA LARABA TA KWASHE LABARINTA KAF TA FA'DA MASU BATARE DATA 6OYE MASU KOME BA_*

Bayan tagama basu labarinta ne tacigaba da cewa "muddin na yarda da auren mukhtar
nasan shima 'karshen rayuwarsa yazo, nasan shima ze mutune kamar yanda maza ukku
suka mutu sanadiyyar aurena, a 'kauyenmu' yayinda na hud'unsu yasha ba'kar azaba
har yarabu dani ranar dana tare gidanshi, shima na tabbata kwanasa ne be 'kareba da
yanzu shima sai labari.

Jidda wacce tunda Fatima tafara bada labarinta take kuka tace "Fatima duk wanda
yamutu kwanansa ne suka 'kare kuma inshaAllah yayana ze aureki kuma ze zauna dake
ba abinda ze faru daku.

Hajiyama saida ta goge guntayen hawaye dan tausayin da Fatima ta bata, tace ki
kwantar da hankalinki Fatima ni nayi Al'kawarin zama dake kuma inshaAllah ko miye
ze rabu dake, kuma aurenki da Mukhtar ba fashi muddin kuna son junanku.

Wani sanyi Fatima taji har cikin ranta, dan son mukhtar ya dad'e da d'arsuwa a
zuciyarta.

Shima mukhtar haka yaji,
Cike da farin ciki yace "Hajiya inaga Al'amarin Fatima kamar hada iska cikinsa,
saboda haka inaso zan kaita gurin wani friend d'ina wanda shida babanshi sun 'kware
gurin magance irin wannan matsalar ta hanyar amfani da ayoyin Allah da kuma
magungunan musulunci wanda babu shirka a cikinsa.

Cike da jin dad'in yanda d'anta keson taimako Hajiya tace "to Allah taimaka Allah
sa a dace.
Su duka suka amsa da Ameen.

Sannan jidda takama hannun Fatima suka nufi d'akinsu, kai tsaye toilet suka shiga
suka d'auro alwala suka kabbara sallar nafila da niyyar Allah yayema Fatima lalurar
dake tattare da ita.


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Washe gari da musalin 'karfe goma na safe sun fito cikin shiri, jidda da faima suna
sanye da riga da wando na fakistan sannan suka d'ora hijabansu, sunyi kyau abinsu,
Mukhtar kuma cikin shigar manyan kaya shadda ash colour sai ba'kin takalmi sai
'kamshin turarensa daya buge ko'ina,

Har mota Hajiya tayi masu rakiya, suka shiga me gadi ya bud'e masu get suka d'au
hanya.

Mintuna talatin suka sadasu da gidan mal bature, shine mutumin daya 'kware gurin
magance matsalar jinnu ko asiri ko sihiri, ta hanyar amfani da ayar Allah batare da
an kauce hanya ba.

Suna Isa Mukhtar yayima abokinshi waya me suna Usman ya sanar dashi isowarsu,

Da far'a ya fito ya tarbesu, sannan yayimasu iso,
Bayan sun shiga sun gaggaisa Mukhtar ya sanar dashi abinda ke tafe dasu, duk da dai
kamar 'karin bayanine yake mashi dan sun riga sun gama maganar kome ta waya, har
Usman d'in ya Sanar da babanshi zuwansu.

Nan ya nunamashi Fatima matsayin wacce za'ayima maganin, Fatima wacce tunda sukazo
kanta ke sadde 'kasa Usman yakira sunanta "Fatima, sai lokacin tad'ago ta kalleshi,
suna had'a ido gabanta yayi mummnar fad'uwa wanda ita kanta batasan dalilin hakan
ba.

Cewa yayi su biyoshi zuwa gurin babnshi, haka suka bishi Fatima jikinta sai 6ari
yake kamar wacce ake girgizawa....




5⃣3⃣to5⃣4⃣ very 5⃣3⃣5⃣4⃣
5⃣3⃣5⃣4⃣




🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:12 PM] www.gidannovels.blogspot.com [06/09 7:00 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 _*ALHINI*_ 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```


_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘


5⃣3⃣5⃣4⃣
5⃣3⃣to5⃣4⃣
5⃣3⃣5⃣4⃣
🖊 Bakin 'kofar d'akin Fatima ta toge ta'ki shiga, mukhtar ya kalleta yace "muje
mana Fatima ko wani abu kk jira, banza tayi ta 'kyaleshi ta tsaya gurin batada
niyyar matsawa ciki, saima 'kokarin komawa da baya take.

Jidda da tayi gaba harta shiga inda malam yake saida ta waigo taga Fatima da
mukhtar basu shigoba, dawowa tayi dan ganin ko lafiya, nan ta iske mukhatar na fama
da ita akan ta shiga d'akin ta 'kiya.

"Haba Fatima ki shigo mana' gurinfa maganinne mukazo nasan kinfi kowa son rabuwa da
lalurar dake tattare dake, jidda tafad'a cikin rarrashi.

Ganin Fatima batada niyyar tanka mata kuma batada niyyar shigowa yasa jidda kama
hannunta da niyyar tashigo da ita.

Saukar wani lafiyayyen mari jidda tayi a kumatunta, Wanda saida ta gigice saboda
tsananin zafin marin, takai dubanta ga Fatima wacce ke cika tana batsewa tace "me
nayimaki zaki mareni.

Cikin wata gur6atacciyar murya Fatima tafara magana, wacce ko alama ba muryarta
bace dan muryar tafi kama data maza, "an mareki d'in tafad'a tana wani irin huci,
"ke har kin isa ki shigar dani gurin dabanyi niyyaba.

Mukhtar naganin haka yasan ba Fatima bace, saboda haka ya kalli jidda yace "maza
kiramin Usman ya taimakamin dan wannan abin nayine.

Jiki na 'kyarma jidda tatafi kiran Usman, abin kamar jira tana fita kokowa ta kaure
tsakanin Fatima da Mukhtar, dan niyyar guduwa tayi shikuma ya ri'keta.

Saida Usman yazo da taimakonshi aka shiga da ita inda malam yake.

Suna shiga tafasa wata uwar 'kara wacce duk illahirin mutanen dake gurin saida suka
firgita, banda Malam wanda dama yasaba ganin irin haka.

Fad'uwa tayi 'kasa bakinta na fitar da wani irin kumfa, Malam yataso ya tsaya
gabanta yace "waye kai, ko wacece? Shiru Fatima tayi sai wani gurnani takeyi, Malam
ya'kara magana karo na biyu nan ma shuru tayi, wani ruwa ya d'auko ya karanta wasu
addu'oi yatofa aciki ya watsa mata, wata irin 'kara tasaki firgigi tatashi zata
gudu kamar wacce aka watsama garwashin wuta, mallam ya daka mata tsawa yace "koma
ki zauna, ba musu ta zauna tanata wani layi kamar wacce tasha ta bugu.

Sannan yace ina jinka waye? Cikin muryar daba ta Fatima ba take magana tace "nine,
hakan yasa Malam yagane namijine yace "Kaine wah?
Yace "nine masoyinta.
"Masoyinta kamar ya?
"Me shirin aurenta
"Me shirin aurenta kome shirin cutar da ita.
"Niba cutarta zanyiba, dan na dad'e ina dakon soyayarta tun tana cikin tsumma nake
tare da ita ina rainonta da niyyar idan ta girma in aureta.
"Kasan dai babu aure tsakanin mutum da aljan saboda haka kayi gaggawar barin
jikinta.
"Bazan iyaba ina sonta.
"Kafita da arzi'ki kokuma in fidda kai da tsiya.
"Bazan fitaba ko zaka kasheni.

Haka akayita daga tsakanin aljani da Malam, 'karshe dai mallam yayita karanto ayoyi
yana tofa mata, tashiga birgima tana ihu, hakan besa mallam ya daina karanto ayoyin
Allah yana tofa mata ba.
.
Kusan awa d'aya da rabi ana abu guda, sannan daga 'karshe Fatima ta fasa wata uwar
'kara tafad'i 'kasa war-was,

Wani abin al'ajbi dai-dai wannan lokacin kuma wannan 'katon ramin wanda laraba tayi
niyyar fad'awa a 'kauyensu lokacin da mukhtar ya tsinceta, yakama da wuta,
Ashe dama nan ne mazaunin wannan Aljanin da yake jikin Fatima.

Mallam ya kalkesu yace Alhmdulillahi kome ya wuce, babu sauran wani jinnu a jikinta
zaku iya tafiya gida, cike da tsoro jidda ta kalli malam tace "mallam a haka zamu
tafi da ita bata fa farfad'o ba, mallam yace "kada ku damu zata tashi wannan
nannauyan baccin dole tayishi, ga wannan garin habbatussauda ne tar'ika amfani
dashi tana zubawa a abinci ko cikin abinsha, kamar kunu ko koko, ko tea, sannan ya
mi'ko wani maganin yace wannan 'kuma haya'kin shaid'anune, tarika turarashi kullum
kafin ta kwanta, sannan ta ri'ke addu'oi da azkar da salatin annabi, Allah
sauwa'ke, suduka suka amsa da "Ameen.

Sun kar6i maganin sukayi godiya,mukhtar ya ajiyema mallam kud'i me tarin yawa yace
"mallam ga sadaka, mallam yace Allah ya kar6a.

Haka mukhtar da jidda suka kama Fatima wacce batasan inda kanta yakeba, suka
sakata mota,
Har gurin mota Usman yazo sukayi bankwana yaimasu Allah kiyaye tare dayima Fatima
fatan samun lafiya me d'orewa.


Tunda suka tafi a mota jidda ke faman kuka dan fatima ta masifar bata tausayi,
Mukhtar kanshi 'karfin hali yake gurin driving dan duk illahirin jikinshi kyarma
yake, haka suka iso gida bakin get sukayi horn megadi yabud'e masu get suka shige.

Suna shiga jidda tabud'e motar tafita, cikin gida tayi tana kuka, Hajiya dake zaune
falo tayi uban tagumi tana tunaninsu, tajiyo sallamar jidda, kafin tayi magana
jidda tafad'a jikinta tana kuka,
Cikin tashin hankali Hajiya ke tambayar jidda "ina fatimar meya faru da ita?

Sallamar Mukhtar tajiyo, yashigo falon d'auke da fatima kamar wata jaririya,
Shimfid'ar da ita yayi tsakiyar falon sannan yasamu guri ya zauna suka zubama
sarautar Allah ido.....




5⃣5⃣to5⃣6⃣ Very 5⃣5⃣5⃣6⃣
5⃣5⃣5⃣6⃣




🖊 Zee Elkaseem
Mmn khady 💋
[10/16, 8:12 PM] www.gidannovels.blogspot.com [07/09 9:30 pm] .: 🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇
😭 _*ALHINI*_ 😭
🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇🐇


®```NWA```
_Written by_
_*Zee Mmn khady*_ 😘


5⃣5⃣5⃣6⃣
5⃣5⃣to5⃣6⃣
5⃣5⃣5⃣6⃣



🖊 *_BAYAN WATA BIYU_*

Fatima ta samu lafiya, kuma acikin 'yan kwanakinne soyayyarta da mukhtar tayi
'karfi wanda sukayi tsananin shakuwa, da so da 'kaunar juna.

Wata rana suna zaune a falo su duka kamar yanda suka saba idan sun gama cin abinci,
Hajiya ta kalli fatima tace "yakamata kibada izini aje 'kauyenku gurin baffa Lawal
Neman aurenki,
*'Rassss* Fatima taji gabanta yayi mummunar fad'uwa, lokaci guda tanemi
nutsuwarta ta rasa dan ko kad'an bataso ayimataaganar 'kauyensu dan yariga yafitar
mata arai, garin da aka 'kuntata mata aka muzantata, garin data wayi Gari yunwa da
'kishirwa sun kusa halakata saboda tsana da tsangwama da suka nuna mata.

Hannu tasa ta goge hawayen dasuka 6ata mata fuska, Hajiya tace "ki saurareni
fatima, kinsan indai mace na neman mutunci to anemi aurenta gun dangin mahaifinta,
shiyasa kikaga na matsa akan aje gun baffa Lawal d'in....

Fatima ta fashe da wani sabon kuka tace "dan Allah Hajiya ki taimaka min ki barni
kada inje 'kauyenmu, wallahi banison zuwa, ba yanzu bane lokacin dana yanke zanje
'kauyenmu, nayimaki Al'kawarin idan muna raye inshaAllah ba sai kinyimin maganar ba
da kaina zan gayamaki zanje....

Jidda tayi karaf cikin fuskar tausayi tace "dan Allah Hajiya ki barta, idan lokacin
yayi zataje da kanta.

Cike da tausayi Mukhtar yace "Hajiya dan Allah kiyimata Alfarma ki barta duk
lokacin data bu'kata sai taje....

Hajiya tayi murmushi tace "tayaro kyau take bata 'karko, idan kunce inbar fatima
kada taje 'kauyensu waye ze zama wakilinta ranar Aurenta?

Jidda tayi sauri tace "Hajiya ga 'yan'uwankinan, dan Allah su zama wakilanta.

Fatima ta taso jiki sanyaye ta dur'kusa gaban Hajiya ta d'ora hannunta kan
'kafafunta tace "Hajiya kece uwata, kece ubana,

7 / 10