Advertisements
Chapter 1 Reading Mummunan Zato 2 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Mummunan Zato 2 Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 12

1 to 3K   out of 35.6K words

??????>?? ???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F WordDocument????10Table????????H Data
????????????????????? P?6?KSKS?1?????????rr????????s??" " " " " " " " $ $??9*r??" " ????" c??c" ?" c?" " ??  ____________________________
*=???MUMMUNAN ZATO Book 2=???*

*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*page 1*



A hankali ta maida ?ofar ta rufe, sannan ta juyo da nufin ta ?araso cikin Wakin. Idanu ta zare tare da dafa ?irji, sannan ta ce "innalillahi" lokaci guda ta juya baya ta runtse idanu,duk ta yi haka ne sakamakon ganin Uncle ya fito daga wanka daga shi sai gajeren wando,yana goge jikinshi da tawul. Ta kama ?ofar zata buWe, ya ce "Beby" ta ce "Umm." Ta ce "bari....em....bari na dawo in ka gama ban san kana ciki ba ne,don Allah ka yi ha?uri." Ya ce "Me ki kayi min? Ki zo kiyi aikinki,kin ji ko" ta juyo amma ?asa take kallo tana tafiya ta ci karo da gado, da sauri ta Wago idanunta ta sauke su akan gadon, cikin mamaki ta tsaya kallon gadon sam bai kai nata girma ba, kuma shinfiWe yake da zanin gado an lailaye shi,ta Wago kai ta kalli Uncle tayi sauri ta kuma sunkuyar da kai don ganin har yanzun bai saka riga ba, kuma bai damu ba sai shafa manshi yake yi. Cikin in ina ta ce "An....an ma riga an gyara ashe?" Ya dube ta,duk ta daburce. Ya Wauki riga shirt fara mai gajeren hannu ya saka,ya tako zuwa gurinta.

Ya kamo hannunta ya zaunar da ita yana ri?e da yatsunta cikin nashi kanta yana kallon ?asa har yanzu bazata iya kallonshi ba saboda gajeren wandon bai rufe cinyoyinshi ba sannan duk cibiyoyinshi gashi ne, ya Wan murza mata yatsun "Beby bai haramta ki ga tsiraici na ba,ko ni in ga naki ba" ta dube shi da sauri ya ce "Yes saboda ni da ke halalin juna muke" Ta sauke kanta ?asa amma zuciyarta tana son ya fayyace mata komai don ita bata gane nufin shi ba,ya ce "yanzu dai Beby ni wanene a gurinki? Ma'ana menene matsayi na?" Ta dube shi sannan ta kuma sunkuyar da kai,a hankali ta ce "Miji" ya ce "me ake nufi da Miji? Ta yi shiru zuwa can ta ce "Wanda ya yi aure shi ne Miji" Uncle ya yi Wan murmushi don jin shirmenta, ya ce to menene aure?" Ta ce "Aure?" Ya ce "Umh" ta ce kamar dai yanda ake yi mutane su taru a Waura shi kenan sai kuma a kai matar" ya ce "to daga nan fa?" Ta Wan dube shi sannan ta rufe fuska, ya ce "Gaya min idan an kaita sai tayi me a gidan? Ta ce "zata rinka yin shara da wanke-wanke tanayin girki,ta rin?a kula da yara.

Ya shafa hannunshi yana cewa, "Good, ashe kin sani? Ta yaya akeyi ta samu yaran?" Ta ce "Iye!' Ya ce "Ya ya za'ayi ta samu yaran?" Ta ce, "Ita ce zata haife su." Ya ce, "Haka nan zata haife su?" Ta ce "Eh,in cikinta ya yi girma." Ya gyara zama don jin sun gangaro inda yake son ji, ya ce "To ya ya akeyi ciki ya fito mata?" Ta Wan yi jim,can ta ce, "Nima ban sani ba,?ila wani abinci ake ci." Dariya ta kufce mishi, duk cikin matan da ya aura babu wadda ba ta san kan zaman aure ba kamar A'isha, duk da cewa akwai sa'arta cikin su, ya dube ta.

"Kina son ki san yadda ake a yi ciki?"

Kanta yana ?asa ta ce, "Eh" ya yi Wan murmushi ya ce, "In na tambaye ki abu Waya yanzun ba ki san shi ba, idan baki san shi ba,zan haWa su in miki bayani. Amma in kin san shi to zan bar ki har ki sani da kanki,wato zai zama assignment,amma fa ba zaki tambayi kowa ba,kin yarda?" Ta ce"To ya ya za'ayi na sani in ban tambayi kowa ba?" Ya ce "Zaki sani,yau da gobe." Ta ce "To yi tambayar in ji". Ya ce "Kin san Haila? Da sauri ta saka kanta cikin cinyoyinta,don ya taSo mata abinda ta fi jin kunya a rayuwarta,don in tana Haila ko Ummanta tana jin kunyar ta sanar da ita, sai dai ta yi ta nu?u-nu?u har Umman ta gano da kanta, ballantana Uncle wanda bata daWe da saninshi ba,ba su yi sabon da zata yi mishi wannan maganar ba. Cikin dariya ya ce, gaya min mana Beby,kin taSa yi ne? Mi?ewa ta yi har tana cin karo ta fita da gudu.

?aki ta koma ta faWa kan gado zuciyarta tana ta bugawa, ita dai tana matu?ar jin kunyar Uncle,shi bai sani ba ne zai mata wannan tambayar?.

Shiko dariya ya dinga yi,lallai dole ya ha?ura da A'isha yanzu don ba ya son takura mata. Ya fi son a yi komai cikin sau?i kuma cikin ilimi.

Jummai kuwa tana Waki cikin murna haka nan wani gefe sai ta ji ranta ya Saci, da tana da iko ko macen ?uda ba zata yarda ta saukar mata a kan miji ba, balle mutum, shi yasa ta sha alwashin ko zata tafi tsirara ne sai ta halaka duk macen da ta ce zata zauna zaman aure da mijinta. Ta sani goben nan yarinyar nan ta zama gawa,don haka ita ranta kar yake, insha Allahu. ?wana ta yi tana kai-kawo cikin Wakinta,don ba zata iya runtsawa ba.

A'isha tana zaune tana tasbihi , sai kurum taga an turo mata ?ofa da ?arfi. Cikin tsananin firgita ta mi?e tsaye, ganin Hajiya Jummai tuni ta soma karato addu'a cikin zuciyarta. Hajiya Jummai ta yi sororo ganin A'isha tsaye. Ta ce, A'a, ihun wa nike ji? Sai na ji kamar kakari a nan Wakin." A'isha ta ce, "Kai,anya nan ne?" Ta Wan yi tsaki tare da cewa, "Gaskiya ba nan ba ne." Hajiya Jummai ta shiga waige-waige, zuciyarta tana mai tabbatar mata ihun A'isha ta ji, amma abin al'ajabi A'ishar ce gabanta tana mai tabbatar mata cewa ba a Wakin ba ne. A'isha ta ce "Allah ba nan bane Hajiya." Sannan ta Wan rusuna ta ce, "ina ?wana Hajiya?" Tsaki mai ?arfi taja sannan ta fita a fusace, tare da sakin ?ofar da ?arfi. Aisha ta yi shiru,a ranta tana son sanin me hakan ya ke nufi? Daga baya sai kurum ta taSe bakinta gami da Waga kafaWarta alamar su dai suka sani,ta koma ta zauna tana nazarin hirarsu da Uncle ta jiya. Daga bisani ta mi?e ta nufi kitchen ba don Uncle ba ne ya yi mata wannan tambayar game da Haila da zata ce Wan iska ne,Don dai ta san halin Uncle shi ba ya iskanci. Uche ta samu yana aikinshi, suka gaisa sannan itama ta shiga haWawa Uncle abin karyawa. Uche yana Wan taya ta,Wakinta ta nufa da tiren, tana shiga ta same shi zaune bakin gado cikin shirin fita. Ta dubi agogo,ta?was saura ?wata, ta ce Uncle har ka fito?" Ta dire tiren a gabanshi ta shiga haWa mishi tea. Ta mi?a mishi sannan ta soma zuba mishi dankali da kwai tana saka mishi bota jikin bread,ya ce har fa na manta ina karyawa a gida,bari na sakko ?asa Beby" ta mi?e ta Wauko dardumar sallah ta shimfiWa mishi, ya zauna ya shiga karyawa, sannan ta zauna tana gaishe shi. Ya amsa cike da jin daWi, sannan ya ce "Ya gajiyar gudu jiya daga tambaya Beby sai ki ka gudu ko?"

Cikin cinyarta ta saka kanta,ta ?i Wagowa me zai sa Uncle ya dinga irin wannan maganar? Ai wannan kamar na ?an iska ne. Ita fa ko a school ba ta wannan hirar da ?awayanta,nata ganin bai dace ba.

Ya ce "shin wai Beby menene abin jin kunya? Ta ce "Uncle don Allah ni dai ka daina wannan zancan." Ya ce "na daina Beby, shikenan?" Ta Waga kai alamun "Eh" ya ce "To oya ci abincin ki." Ta ce, Uncle nifa sai anjima zan karya, wannan duk naka ne" Ya ce,ya ya zanyi da wannan Beby? Ai babu tsari ga kowane musulmi ya zauna ya yi mugun ci, Manzon Allah (S.A.W) yana kasa cikinsa kashi uku ne, Waya abinci, Waya ruwa, da kuma ya sha?i numfashi dashi,don haka kin ga tunda da shi muke koyi, sai mu ma mu ?watanta. Zaka ci ka ?oshi amma ta yanda ba zaka kasa tashi ba.

Aisha ta ce, "Haka ne." Sai kusan tara ya fito daga Wakin,yana son yarinyar ta shiga ranshi,ba ya gajiya da zama da ita yana son shirmenta,wani sa'in ta yi magana tamkar babba, wani sa'in kuma ta yi masa aikin ?uruciya,waton shirme.

Kai tsaye Wakin Jummai ya nufa,don yi mata sallama kamar yanda ya saba,in ba ya Wakin ki zai zo ya yi miki sallama da safe in zai fita. Tana zaune abin duniya duk ya taru ya yi mata yawa, yanzun haka jin ta take yi tamkar ta yi hauka,don tsabar ba?in ciki. Ina ma kuka zai ?wace mata ko zata samu sassauci. Sallamar maigidan ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, tsayawa ya yi yana kallonta. Itama ta Wago idanunta jajir tana dubanshi, ya ajiye jakar hannunshi ya nufi gurinta ya tsugunna a gabanta cikin sassanyar muryarshi, ya ce "Jummai" ya kamo hannunta, "wai shin Jummai me yake damunki ne cikin watannin nan duk kin rame kin lalace,dube ki don Allah sai ka ce wata tsohuwa?" Kalmar da tafi tsana kenan a kira ta da ita, wato tsohuwa. Hawayen da take ta so su zubo ko zata samu sau?i suka ?i zubowa, sai gasu yanzun sun zubo masu zafi ma,ta ce dole ne ka ce min tsohuwa tunda yanzun ka samu yarinya ?arama wadda zata iya haihuwa,ba irina ba juya. Ya mi?e tsaye cike da jin haushi, "kinga matsalarki ko? Kin gani ko? Me yasa ne ke har kullum ba ?ya fahimta? Nifa ina son sanin matsalarki ne ba wai ina kushe ki ba ne,in baki son in san damuwarki Jummai ai sai in barki tunda ke ba ?aramar yarinya ba ce. Ace kullum bawa ba zai sakawa zuciyarshi salama ba,koda yaushe sai ba?in rai. In kina da matsala ne ba sai ki faWa min ba? Ta ce "Ni dai don Allah je ka kawai,ka bar ni inji da kaina." Ya Wauki jakarshi tare da cewa, "Allah ya ?yauta." Ya fita.

Ihu ta saka ita kaWai,a ruWe su Suwaiba suka shigo suna cewa, "Lafiya Anty Jummai?" Tana huci ta ce "ku bar ni zanci uban yarinyar can" Sofy ta ce, "Me tayi miki ne Anty? Yanzu mu je muci ubanta? Ta ce a'a ku bari ba yanzun ba,ni zan yi maganinta. (Waya ga sa kai a uku) Yinin ranar Jummai sun ?ule ita da Aminiyarta, suna neman mafita. Ta rantse ta kuma rantsewa cewa maigidan yana kusantar yarinyar gashi an ce zata mutu shiru bata mutu ba,ta dubi Kari,ko dai zan sa mata guba ne? Kari ta ce "a'a komawa zamu yi gurinsu." Ta ce dibi asarar da na yi ta kuWi, amma ace maganin bai ci ba? Kari ta ce,mu koma musu kawai gobe ke in abin ma ya ?i wallahi sai mu nufi Nijar,zan binciko miki wani malami ko ince Boka.

Sun bar zancan a kan zasu koma in basu ga dai-dai ba,su nufi jamhuriyar Nijar, Allah ka tsare mu,Amin.

A'isha ko sam bata ma san hidimar da suke yi ba. Ranar ?u?ewa ta yi tana ta ?o?arin yiwa Uncle Winta gurasa da miyar taushe. Ta haWa zoSonta mai daWi, Uche ne ya taimaka mata ,Marka mai aiki taje ta sanar da Hajiya Jummai ta same ta suna magana da Karima,don haka ta sanar da su Suby cewa, amarya ta samu sake, tana can kitchen ta girka banza da wofi. Nan ko suka nufi kitchen Win suka shiga buWe mata kuloli, suna cewa, me wannan ?wamacalar wannan ?azamiyar ?ar ?auyen ta ke yi ne haka?" Aisha ko da kallo ta bisu, Sofy ta ce, ashe ma abincinsu ne irin na ?an ?auye. Suby ta ce,ke gaja wa kikayi wa wannan ?waWon? Ita dai kallonsu take yi ranta yana zafi,ta ce ina ruwanku da kayana? Duk suka haWa baki gurin cewa,sai mu zubar dashi,dube ta ?ar matsiyata kawai, A'isha ta Wauki kulolin ta ta nufi Wakinta ta dawo ta ?washe sauran kayan,su kam sai dariya suke yi mata,suna cewa in dai Alhaji ki kayi ma wannan ?azantar ba ci zai yi ba ?ar neman gindin zama,zaki gane kuranki. Tagumi ta zuba tana zubar da hawaye,tuni ta kula waWannan za su takura mata.

Yau tun huWu Uncle ya dawo, domin tunda ya kira A'isha sau uku bata Wauka ba,ya soma tunanin ko dai bata da lafiya ne? Ita ko sam bata ma san inda ta jefa wayar ba, kuma damuwar da take ciki bata tuna mata cewa tana da waya ba, domin dawowarta a jiya ne ma ta Wauki wayar. Amma ba sa zuwa makaranta da waya. Lokacin da ya shigo tana wanka,zama ya yi yaga fitowarta, da Waurin ?irji ta rufa da tawul ta Wan yi ya?e tare da kallon agogo tana faWin, har ka dawo? Shi ko ita yake kallo yana son gano halin da take ciki,jin bai yi magana ba ne yasa ta maida kallonta gareshi ya ce "Beby me yake damunki?" Ta zauna bakin gado cikin irin murmushin takaicin nan,ta ce ba komai. Ya dawo kusa da ita wani guri yana miki ciwo ko? Ta ce "a'a,me ka gani ne Uncle?" Ya ce, "Sau uku ina kiran wayarki ba ki Waga ba, sannan yanzun na zo sai na same ki ba yanda ki ke ba.

A'isha baki kai lokacin da zaki haWiye damuwa ba,sanar dani matsalar ki?" Ta girgiza kai "Yi ha?uri Uncle,ka bar zancan,maganar waya kuwa ni na ma manta ina da waya saboda ka san zaman makaranta yasa na saba da rashin waya." Ya ce, "Ni fa Allah sai kin sanar da ni." Ta ce, "to ni ban san me zan ce maka ba." Ya ce, wani guri ne yake miki ciwo? Ta girgiza kai tare da cewa, a'a.



#######
[12/9, 07:33] Ummi Tandama=??: *=???=??? Page 2*



Ya ce, To mene ne? Hawayen da take ma?alewa suka soma zubowa,ta ce su Suwaiban nan ne, ya ce Suwaiba? Ta Waga kai "Me suka yi miki?" Ta ce, Ni dai kawai ka ce musu ba ruwansu da ni in ina abuna, tunda dai ni bana shiga cikin harkarsu, ya ce to kiyi ha?uri zan musu magana." Ta share hawayenta, ta mi?e ta kawo mishi ruwa mai sanyi,yana sha taa ce, "Yau fa na maka abinci,baza ka ci na Uche ba, Allah yasa zaka iya ci?" Ya ce, "Me yasa ki ka ce haka? Ta ce, saboda ban ?ware ba,ni kuma gani da son yin girki." Ya ce,zan ci koma ya ya ne,ai Beby kina da ?o?ari, na san nan gaba zan huta da cin abincin masu aiki ko?" Ta yi dariya, ya ce, sannan kada ki ce na dawo da hannun agogo baya,shin me ya haWa ku dasu Safiya? Ta Wan Sata rai ganina kawai suka yi ina girki cikin kitchen sai suka hau buWe min suna zagina wai ?ar ?auye ina haWa ?wamacala,na samu sake.

Suna ta yi min,ni kuwa na fita dan sun ce zasu zubar min." Ya ce, "Ke da wanene cikin kitchen Win?" Ta ce,ni da Uche ne,yana taya ni, ya ce to kiyi ha?uri.

Koda ya fita Wakin Hajiya Jummai ya nufa,tasha adonta tamkar ba ita ce cikin damuwa ba Wazun, shawarar Karima ta Wauka wadda ta shawarce ta da cewa ta yi ?o?arin Soye sirrinta cikin ranta ta daina bari ana gane damuwarta. Ya dube ta "Jummai ina yaran nan ne?" Ta ce, "Sannu da zuwa,ka dawo?" Ya ce, "Eh" ta ce, "Su Suwaiba?" Ya ce "Eh," ta Wauki waya ta kira Safiya ta ce,su zo Wakinta yanzun. Koda suka shigo, ganin Uncle sai suka yi tsimi-tsimi ya ce kece ki ka tura su su je suyi wa A'isha rashin mutuncin nasu? Ta dube su,me ku ka je kukayi mata? Suby ce ta soma cewa,nima dai ban sani ba, Allah Anty sharri ne. Sofy ma ta ce, to mu yaushe ma muka ganta ni na ma san ta dawo ne? Bai yi magana ba ya ciro wayar shi ya kira Uche, ya ce ya same shi a Wakin Hajiya Jummai. Nan a gabansu ya tambaye shi cewa ya gaya mishi gaskiya me ya faru tsakanin A'isha da su Suwaiba. Ya Wan soma inda-inda, Alhaji ya ce, daina kallonsu,ni ne na Wauke ka aiki kuma ni ke biyanka don haka bana son kana kallonsu,in zakayi magana." Nan dai Uche ya sanar da su duk yanda aka yi, duk da yana tsoron masifar su. Nan ko Alhaji ya soma faWa,ya ce maza su fita hanyar matarshi, domin kan A'isha kowaccensu zata iya kama hanyar gidansu,a cewarshi don A'isha ba ta da gidan da yafi wannan, tunda nan ne gidan aurenta.

Hajiya Jummai ma dai ta daure ta ce musu su fita harkarta,ta yi musu faWa a gabanshi, amma yana fita ta ce,lallai yarinyar nan har ta samu guri ta soma kai ?ara? TabWi,lallai zata san da wa take yi. Su Suwaiba ma sun sha alwashin cewa sai sun ?untata mata.

Ita ko bata san suna yi ba ma,don bai ce mata ?ala ba. Koda ya shigo rashewa ya yi a tsakar Waki nan kan sallayarta ta shiga jera mishi kayan gabanshi,ya buWe babbar kular tare da cewa, tunda kin ?i gaya min sunan abincin da ki kayi min bara na duba da kaina, ganin gurasa luhu-luhu ya sa shi sakin baki, sannan ya dube ta cike da mamaki, "Allah ke ce ki kayi wannan gurasar Beby? Ta ce,ba tayi ?yau ba ko? Cikin fargaba take magana,ya ce ina dai mamakin iyawarki. Ya Wauki Waya ya yaga,ya saka cikin bakinshi yana taunawa, ya ce Beby kin yi zaman Kano ne? Tana dariya ta ce, Uncle abinda ya yi Kano ai shi ya yi Jigawa,ya ce haka ne,ba zan ci gurasar nan ni kaWai ba, bari na kira abokina wanda duk sa'ilin da ya shiga Kano sai ya shigo min da gurasa. Ya ciro wayarshi ya kira Alhaji Salis,ko gaisawa bai bari sun yi ba, ya ce mutumina don Allah ka zo gidana yanzun ka sha mamaki. Alhaji Salis ya ce to bari na ci abinci

1 / 12