Advertisements
Chapter 3 Reading Mummunan Zato 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Mummunan Zato 2 Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 12

6K to 9K   out of 35.6K words

shiga ya tarwatsa su tare da yi musu tatas. Ya ce, ina Jumman da ta Waure muku gindi? Cikin maye Sofy ta ce,ta yi tafiya tun jiya, al'ajabi ya cika shi,ya nufi Wakinshi ranshi yana matu?ar zafi. Ya zauna bakin gado ya soma kiran layin ta, ga mamakin shi tama ?i tafiya,a ?arshe ma sai aka ce a kashe layin yake.

Wasa-wasa har wayewar garin ba ta babu labarin ta, kazalika ci gaba da neman layinta ko zai samu,shiru kai daga baya sai ya soma tunanin ko dai ta Wan fita unguwa ne, ta samu matsala ko mota ta kaWe t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a haka? Yin wannan tunanin ya saka shi kiran danginsu, har da nata wato makusantanta,yana sanar dasu rashin ganinta tun jiya. Ya san ba nisa tayi ba,don ba ta fita da mota ba, kuma bata saba tafiyar ?wana ba ma in dai ba ?asar ta bari ba, komai dangatakar ku da ita ba zata taSa zuwa ta ?wana don zumunci ba,nata ganin ?as?anci ne ta ?wana gidan da suka fi su kuWi, amma gata can ai ta ?wana a bukka,nan fa hankula suka tashi.aka shiga neman asibitoci,ranar basu iso ba sai daf da magriba,kai tsaye gida kowacce ta nufa, lokacin da ta iso gidan yana cike da dangi shi kuma yana daga harabar gidan in da wani Wan sandan ciki yake neman ?arin bayani daga bakinshi.

Sai kurum gata ta shigo, ganin maigidan yasa ta ji faWuwar gaba,don sam ba tayi zaton zai riga ta dawowa ba, amma da yake tana zaton yau ya dawo,tun da haka suka yi dashi, sai ta isa gurinshi tana cewa "Sannu da zuwa Alhaji, har ka iso? Na Wan fita ne" bai iya ce mata komai ba, sai dai ya dubi wannan (C.I.D) Win ya ce shi kenan ma gata nan ta dawo.

Suka yi sallama ya tafi, shi ko ?in shiga ma gidan ya yi,yana tsaye cike da mamakin ba?in halayen da Jummai ta zo mishi da su yanzun yi,abin har ya kai ta da yin ?wanaki. To ina taje? Ya na nan har aka kira sallah, ya shige masallaci, ita ko tana shiga cikin gidan ta same shi cike da dangi ana ta jaje. Turus ta ja ta tsaya, tana son sanin wanene ya mutu? Shin ko dai A'isha ce har ta mutu kafin ma ta dawo? Ta yi amfani da maganin? Kai in ko haka ne lallai zata sake komawa ta mishi sabon biya,don ya cancanta,haba shiyasa taga Alhaji a waje babu fara'a,ya ma kasa amsa ta,ta dubi jama'a sannan ta ce, "HaWarin mota ne?" Nan kuma sai taji sun Wauki salati, suna tambayarta a ina abin ya faru? Sai kuma ta yi sororo tare da cewa,wai dama me ya tara su haka? Nan suka shaida mata labarin Satanta,nan fa ta hau masifar cewa inji uban wa? Ita da taje biki? Shi ne za'a ce wani ta Sata? Wata Yarsu ta ce, to mu dai maigidan ki ne ya yi waya tun jiya kuma sai nemanki ake yi cigiya gidajen radiyo da na talabijin. Ta ja tsaki, "To ni biki naje, shima bayanan ne kuma na kira shi a waya ban samu ba." Nan dai kowa ya tashi yana Allah to ya kiyaye gaba, gaskiya ta ji haushi don duk tasa ma ranta cewa A'isha ce ta mutu.

Sai bayan da kowa ya tafi sannan ta kira su Suwaiba,tana tambayarsu yaushe ne Alhaji ya dawo? Suka shaida mata tun jiya, kuma ya tambaye su sun ce ta yi tafiya. Cikin War-War ta zauna,shi kam bai ma shigo gidan ba da ya yi isha'i gidansu Hajiyarmu ya nufa, don ya sanar da su dawowar Jumman,nan har yake yiwa Hajiyarmu complain Win halayen da Jummai ta shigo da su, ya ce ada bai san ta da duk waWannan halayen ba, sai yanzun.

Hajiyarmu kuwa ha?uri ta bashi tare da cewa, zatayi mata magana. Sai sha Waya saura sannan ya nufo gida,tana ta gadin zuwan shi,don haka tana kallon shigowarshi, sanda ta shiga Wakinshi yana watsa ruwa,ta zauna. Yana fitowa da ya ganta fuska ya Waure tamkar bai taSa dariya ba,ta rasa ta ina zata soma mishi magana,can dai ta daure ta ce, "Alhaji ka min ha?uri,na san ban ?yauta ba, amma wallahi na kira wayarka ta?i shiga,dama wata ?awata ce dake Kaduna ta ke aurar da ?arta," ya ce "to yanzun sai ki koma Kadunan," ta zaro idanu, Haba don Allah,ka yi ha?uri Alhaji, nayi laifi, ya eh da haka ni ne dama sarkin ha?uri shiyasa sai ki min abu ki ce inyi ha?uri to na gaji ba zan Wauki yawon gantali ba, don haka sai ki koma".

Tayi saurin zubewa gwiwa biyu a ?asa,don Allah ka rufa min asiri, insha Allahu ba zan ?ara ba,don Allah.

Ya ce ,don Allah ni tashi ki bar min Waki,shashasha wadda ba ta san darajar kanta ba,bare na aurenta,ke kenan yi nan yi nan,gara ma kin canza hali,don wallahi ba zan Wauki wannan rainin wayon ba. Ta fita dai tana mai jin zafin abinda ya yi mata, amma cikin ranta tana cewa,?wanan nan zaka zama zauna nan in Allah ya yarda,duk wannan cin mutuncin da ya yi mata sai ta rama.

Shi ko ?wanciyarshi ya yi tare da yi mata addu'ar Allah ya shirye ta, ita ko A'isha tana can gurin Ummanta, suna shan hira, tana ba Umma labarin yanda Uncle ya ke kashe mata kuWi,ko da Ummanta ta ce, to suna zaman lafiya da abokiyar zaman tata? Cewa ta yi suna yi har ma take bata labarin zannuwan da ta ba da a kai mata, Umman ta fahimci ?arta bata zuwa gurin mijinta a cikin hirar tasu, inda take cewa, ita sau Waya ta taSa zuwa Wakin Uncle ya ce ta gyara mishi shimfiWa, sai kuma taga shimfiWar a gyare.

Umma ta ce,ai yanzun ke don rashin hankali ba zaki shiga Wakin mijinki ba duk ranar girkin ki ki gyara safe da yamma?" A'isha ta yi shiru, Umma sai faWa take mata, ta ce "Lallai yarinya in ko haka za kiyi,za kuwa ki zama koma baya gurin mijinki,ai wannan gyaran Wakin shi ne zai sa yaji dake fiye da yanda ki ke labari yanzun, duk irin biyayyar da zaki mishi na banza ne in har ba zaki gyara mishi shimfiWa ba."



######
[12/10, 19:21] Ummi Tandama=??: *=???=??? Page 4*



Aisha ta ce , to Umma shi ne fa ya ce wai ba zan iya ba,wai sai nan gaba. Shiru Umma ta yi don ta san A'isha yarinya ce, amma har da ma shirmenta,in ban da haka yara ma ?anana waWanda ba su kai ta ba sun san aure bare kuma ita? Sam ta kula A'ishar ma bata gane me take nufi da gyaran shimfiWa ba.

Aisha ta ce, to in na koma ai zan ringa yin gyaran.

Kafin ranar dawowarta, Umma ta zaunar da ita ta koya mata shan kayan marmari masu saka ni'ima a jikin mace,duk da yanda Umma ta nuna mata cewa su kankana,shan rake,aya,ayi kununta da dabino shan romon kaza da sauransu,suna saka mace tayi ni'ima. A'isha ba ta gane wacce irin ni'ima Umma ke nufi ba,ga nata zaton jikinta zai yi fresh ko ?iba zatayi ko ko fari, Umma take nufin zata ?ara? Oho. Ita dai tana can ta soma amfani da su, sai wasu tsumi da dai sauran abubuwan sha na mata, waWanda basu da illa.

Itama nata gefen Hajiya Jummai ta gama aiwatar da komai nata,wato guzurin Nijar, don haka jiran sakamako kawai take yi.

Ana saura sati Waya hutun A'isha ya ?are, Uncle ya yi mata waya cewa yana nan bisa hanya,don haka ta soma shiri da ya zo zasu juya. Tamkar kada ta tafi ta ji, sai dai wata damuwa tun jiya ta soma jin wata faWuwar gaba har ta sanar da Umma. Umma ta ce, tayi ta addu'a itama zata taya ta.

Sun tsaya a Kano sun yi siyayya, Uncle dai sai tuni yake mata da Amrif Cory, dariya ta ringa mishi, shi kam ya ce na yaba da ?amshinsa gami da WanWanonsa, duk tsarabar da A'isha ta zo da ita gurin Jummai ta kai ta ce gashi nan ta raba ta ba kowa.

Hajiya Jummai ta ce, a'a bani da wanda zan ba tsaraba,ki dai aikawa da su Hajiyarmu,ni kuma bari in Wan samu riWin.

A'isha ta ce, to da kanta ta ce don Allah Uncle ya kaita ta ba su Hajiyarmu tsarabar su. Sun yi godiya mai tarin yawa, a nanne ma take jin zancan auren Nafisa, lokacin da Uncle suke magana da Hajiyarmu, ashe wani abokin Uncle zata aura, mai suna Alhaji Bello,yana da mata Waya da ?a?a uku,fatan A'isha Allah yasa lokacin bikin suna hutu, har ma tayi wa Uncle ?orafin hakan, Uncle ya ce kada ta damu,in tana da rabon za'ayi tana nan to za'ayi cikin hutun. Lahadi tana zagayo wa Uncle ya haWa komai na makarantar A'isha ya maida ita. Sun maida hankali kan karatunsu yanda ya kamata.

Jummai kuwa, kullum cikin zuba idanu take yi taga ta ina aikinta zai fara? Amma shiru. Nan fa hankalinta ya sake tashi, ta shiga surutu ita wane laifi ta yi? Duk abinda ta yi ba ya ci,da yake an ce duk abinda ka ke yi shi kake zaton kowa yana yi,don haka sai ta bar abin kan cewa suna tufka mata asirine, shi yasa. Yin wannan hasashen yasa ta garzaya gidan Aminiyarta don neman wata mafitar.

Aisha ta zamar mata annoba, bala'i. Aminiyarta ta ce,sake neman wani gurin zamu yi da zai yiwu ni dai da mun dangana da Indiya, can ne ?arshen tsafi ba ki gani ko cikin fina-finansu? Jummai ta ce,don Allah kuma gaske ne yana yi?" Karima ta ce ,"Zauna nan,ai in zaki mi?e,mi?e sahibata wani aikin sai Indiya,ko Chaina, kafin ma mu dawo tun muna can za'a Wauki ran banza mu huta."

Jummai ta ce,ba zuwan ba,ba kuma kuWin nake ji ba,don sai na iya sa duk wani abu nawa a kasuwa in amshi kuWin,matsalata mutumin gidana, kin san cewa har zuwa yau ba mu koma normal da shi ba? Tun zuwanmu Nijar Win nan har yau,na kasa gane kanshi. Sai ya yi ta dakemin yana shan ?amshi.

Karima ta ce, "ke Aminiyata nemi kuWi in ma bai barki ba ni sai in je miki. Menene amfanin Amintakar? In ana zuwa lantsandan gaban lahira inji ?an magana to zani,in samo miki mafita game da kishiya. Ai ki daina damuwa,mu za'a gaya wa Boka? Jummai ta yi ajiyar zuciya, daWi ya rufe ta,a duniya bata da tamkar Karima, ta ce, "Aminiyata Allah ya ja mana ?wana,ni na san bani da masoyiyar da ta kai ki duk duniya."
Ji toshewar basira.

In sun samu hutu.
A'isha duk ranar girkinta,ta kan shiga Wakin Uncle Win ta gyara mishi gado har ma da sauran gurare, sannan ta saka mishi turaren wuta mai ?amshi, amma bata kwana tunaninta ma bai kawo mata ta ?wana Win ba, har ?wanakinta na hutu suka cika ya yi mata komai ta koma.

A'isha ta maida hankali kan karatunta, bata wasa sai dai zama da su Samira ya yi matu?ar wayar mata da kai. Su kan zauna suyi hirar samarinsu kamar yanda ?an mata kan yi. Amina kam kullum bakinta yana ba su labarin Kabir,Samira ma bata da zance sai na Adam.

Kowacce in tana labarta yanda take ji game da abin ?aunar nata, A'isha kam baki take saki ta yi ta kallonsu. Samira ta ce, A'isha wai ke kullum tamkar ba ki waye ba, haka ki ke jin kike wai baki da saurayi ne? A'isha ta girgiza kai tare da cewa,ni bani da wani saurayi.

Amina ta ce,ni wallahi ban da ina da Adam Wina ko da sai na ce don Allah ki haWa ni da Uncle Winki mana? Samira ta ce,ai gayen ya yi ne, A'isha ta yi Wan murmushi, sannan ta ce,shi Uncle ba fa yaro bane. Samira ta ce ji wannan ai ba yarinta ake kallo ba a maza,?walitis ake dubawa, shi Uncle Win ki yana da duk ?walitis Win da ake so ga namiji."

Aisha ta ce,ni ban san wani ?walitis ba fa da kuke magana" Dariya suka shiga yi mata, A'isha ta ce,kun ji lokacin sallah ya kusa, ya kamata mu soma shirin shiga Masallaci."

Duk lokacin da suke ire-iren wannan hirar, A'isha kan tambayi kanta, menene wannan Win da su Samira suka damu kan su dashi? Ita dai ta san burgewa kamar Uncle in ya yi ?walliya,yana matu?ar birgeta, bayan wannan ba ta san komai ba.

?wanci tashi su A'isha an shiga (SS3) duk da batayi wata ?iba ba, amma ta ?ara tsawo.

?irjinta kuma ya bun?asa har yana Wan rinjayarta, shi ne ma sanadin yin Wan rusunawarta wanda wasu ?an makarantar nasu suka fassara shi da yanga, zuwa yanzun ta san mene ne aure,me ake yi in anyi shi? Sai dai ita mai tsananin tsoro ce.

Shi kuwa Uncle har yanzun ba ya tunanin taSa ta, domin yanzun ya gama yarda cewa ?wanciyar da yake yi ne da ?a?an jama'a suke mutuwa, duk da yana tsakanin bu?atar hakan, saboda yanzun Hajiya Jummai,damuwarta ma tai yawa,don ta ce an sa mata hannu na asirin da tayi bayi ci,tana nan dai tana fafutukar haWa kuWin zuwa Indiya ko Chaina.

Aisha wadda yanzun shekarun ta sha ba?wai kenan ta samu shekara biyu gidan Uncle Winta.

Ganin haka ya sanya jama'a suke ta kai-kawo kan cewa Alhaji Saddi? dai yanzun mata sun daina mutuwa a gidanshi, sai dai haihuwa shiru,don haka mutanen da a baya suke zaginshi sai kuma suka shiga kawo mishi tallar ?a?ansu.

Nuna musu yake yi ba shi da ra'ayin sake aure,don haka su yi ha?uri.

Yau bayan tashinsa daga Office,gidan Hajiyarmu ya nufa, ya samu Alhaji Sunusi wan mahaifinshi,amma ?a?a maza suke. Alhajinmu yana jin maganar Alhaji Sanusi sosai, domin yanzu ku san shi kaWai ne ya rage mishi a maza, cikin dangi. Alhaji Saddi? ya zauna suka gaisa,ya juya ya gaida Hajiyarmu, Alhaji Sunusi ya ce wannan zuwan naka ne fa Abubakar, Uncle ya dube shi tare da gyara zama sannan ya ce, to ina jin ka Baba. Alhaji Sunusi ya yi gyaran murya sannan ya ce, maganar Hadiza ce ta kawo ni, Uncle ya dube shi wace Hadiza fa? Alhaji Sunusi ya ce,ai ba ka ma san ta ba? To Hadiza ta gidana, tun lokutan baya na sani kaima ka sani tsayawa ta yi tsayin daka kan cewa kai take so, amma a lokacin kowa ya?i saboda kai ba a son ra'ayinka ba,to sakamakon haka har izuwa yanzun ta?i kowa ta ce ita dai sai kai, gashi an tashi bikin ?annanta su Hussaina shi ne muka yanke shawarar aura maka ita kawai.

Uncle ya dubi gefen da Hajiyarmu take zaune,tana ta nazarin littafin ?awa'idi, ya sani tana jin su sai dai ba zata taSa magana ba. Sannan duk ?wa?warka ba zaka iya gane me ke fuskarta ba, ma'ana zancan ya yi mata daWi ko ko akasin hakan, sannan ya dawo da dubansa ga Alhaji Sunusi wanda ya san yanzun nan zasu hau sama su faWo in dai ya bashi amsar da ke bakinsa, ya ce Alhaji ai ko lokutan baya na san an?i in auri Hadiza ne saboda matsalar da ke tare dani, ta mutuwar matana, yanzun kuma an yarda ne saboda an ga nayi aure matar bata mutu ba,don haka ni dai a bawa Hadiza ha?uri, ta nemi mijinta kawai."

Alhaji Sunusi ya ce, inji wa ya ce maka don wannan matsalar ne? Mu dai burinmu mu ga ?a?anka."

Alhaji Saddi? ya ce, "Gaskiya ba ni da ra'ayin mace fiye da biyu, kuyi ha?uri."

Ran Alhaji Sunusi ya soma Saci, don haka cikin fusata ya ce, "Abubakar ba wai na zo neman izininka ba ne, umarni na zo baka domin ko mahaifinka ne na bashi umarni baya tsallakewa,in ma mahaifiyarka ce zata zuga ka to ku sani daga kai har ita aure babu fashi."

Uncle ya ce, "Allah ya huci zuciyarka,ba ruwan Hajiyarmu cikin wannan zancan, Hajiya da ke jin su ta rufe littafin hannunta, sannan ta dubi wan mijin nata ta ce, Yaya Allah yasa alkhairi, kuma yasa muna da rai za'ayi." Jin haka yasa gaban Alhaji Saddi? ya faWi, ya sani zancan ya tabbata tunda Hajiyarmu ta amince, Alhaji Sunusi ya mi?e yana cewa, "Duk yanda muka yi zaku ji gurin Alhajin gidan nan." Ya tafi.

Shiru Alhaji Saddi? ya yi,yana kallon ?asa,shi da yake tunanin lokaci ya kusa da zai daidaita tsakanin shi da A'isha,don yin zaman aure cikakke, sannan sai kuma a kawo mishi batun wani auran? Shi fa ya sani ya so ya auri Hadiza a lokacin yana cikin tsananin son haihuwa, amma yanzun sam babu Hadiza a ranshi, duk da ko can da Win ma ba itace ta ?i shi ba, dangin mahaifinshi ne suka ?i, musamman Hajiya Lanti da Alhaji Sunusi mahaifanta yanzun kuwa ya sani ganin daWewar A'isha a gidanshi ne yasa su amincewa.

Hajiyarmu ta katse shi da cewa,ka ci gaba da addu'a,zamu taya ka. Ka zama mai biyayya sannan ka shiga shirin bikin,to kurum ita ce kalmar da ta fito bakinshi, ya mi?e tare da cewa,ni zan ?arasa gida. Duk ?an ?wanakin yana cikin damuwa.

A'isha tana school, Hajiya Jummai kuwa damuwarta ta sha ?arfin tashi,don haka ita bata ma kula da me yake ciki ba, ganin haka yasa yau ya shiga har cikin Wakinta tana ta waya ne da Hajiya Kari,kan cinikin wani gidan ta wanda shi ne kurum ya rage mata. Saboda tsabar ba ta cikin natsuwa sam bata ma san ya shigo ba, sai da suka gama sannan ta gan shi ta Wan razana don ta san yaji me suke zantawa.

Ya zauna kusa da ita, ya maida hankalinshi kanta cikin sanyin murya, ya ce "Jummai wai menene matsalarki? Me ke damun ?wa?walwarki? Ta dube shi da idanunta da suka yi jajir duk kwanakin nan haka yake ganinsu, ta ce ba komai me ka gani? Ya ce,haba Jummai, duk wanda ke gidan nan ya san kina cikin matsala, ta ce ni dai bana cikin wata matsala, ya ce to shikenan, yanzun menene dalilin ki na saida gida? Ta ce, matsala gare ni, kuma na san in na ce ka bani ba bani zakayi ba,don haka gara na saida ?adarata, ya ce wacce irin matsala ce? Ta yi shiru tana son ta tuno me zata ce?.

Ya sake tambayarta, ta ce,zan je ne in dama dai

3 / 12