Advertisements
Chapter 4 Reading Mummunan Zato 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Mummunan Zato 2 Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 12

9K to 12K   out of 35.6K words

wani likita zan gani a Indiya, saboda matsalar haihuwata,don naga wata mai irin matsalata kuma ta haihu,na gane in na ce zan tambaye ka ba yarda zaka yi ba cewa zaka yi ina ne ba mu je ba ance ba zan haihu ba."

Ya dube ta cike da zargi, sannan ya ce, "Ki bari zan shirya muje tare." Ta Wan zaro idanu,ni dai ka bar shi kawai inje ni kaWai, tunda kaga kai baka da wata matsala." Ya mi?e yana cewa, "Jummai waWannan sabbin halayen da ki ka Wauka sam ba zan Wauke su ba, tunda ki ka bar gidan nan har ?wana biyu ba ki gidan danginki ba ki gidan nawa, zuciyata ta soma zargin kin canza layi.....


#####
[12/11, 17:18] Ummi Tandama=??: *=???=???Page 5*



Sakamakon yawo da kawayan banza,to ba za kije ba,kuma kada inji kin saida wannan gidan,ta ce ai ba gidanka ba ne,ya ce to shikenan. Amma ki sani halayanki sun gundure ni,baki zaman gida ke ba ma'aikaciyar gwamnati ba,kullum sai shegen yawo,ni kaina yaushe rabon da ki shigo dakina? Koda kin zo baki iya tsinana min komai,sai dai ki min jungum kina tunani,don haka ni ba karfe ba ne ina da bukatar kulawa. Aisha tana makaranta,ke kuma baki da lokacina."

Ta dube shi a hasale,to ka dauki mataki mana." Ya fita yana fadin "shikenan."

Gidan su Hadiza ya nufa yau,saboda yana son bin umarni,sannan Hajiya Jummai ta bashi haushi. Daga waje ya tsaya ya aika kiranta. Hajiya Lanti ta ce,maza a bude mishi kofar falo ya shiga. Hadiza kuwa murna tamkar me,don tana bala'in son shi,ba wata hira sukayi ba. Bayan gaisuwa ya ce,mata shi fa yazo ba ta hakuri ne,da zata daure ta nemi miji. Nan ta soma kuka tare da rokonshi,ya ce mata shi kenan sai dai fa ta san yana da mata har biyu,kuma suna zaman lafiya don haka kada ta yi kokarin rusa mishi tsarin gida. Ta ce,in Allah ya so ba wannan. Nan dai suka yi sallama ya tafi.

Tun daga ranar bai sake zuwa ba,sai dai ya kan kira ta a waya. Kafin wani lokaci labari ya watsu cikin dangi,Nafisa da bata so ba,don gaskiya tana ganin za'a kwari Aisha ne,tunda duk cikinsu ita ce karamar yarinya,haka ma su Aunty Fatima suke cewa.

Shi ko da ya tuno cewa bai sanar da iyalanshi ba,duk sai ya damu,musamman Hajiya Jummai,yanda ta daga hankalinta lokacin auren shi da Aisha,amma don Aisha yasan ba zata damu ba,tunda ita yarinya ce sannan ba ya tunanin ta ma san mene ne ma auren,don haka bai damu ba. Sai dai yana tunanin ya ya zai tunkari iyayanta da batun auren shi? Ko me Friend zai kawo a ranshi in ya ji batun auran? Kullum ya kan yiwa kanshi wannan tambayar.

Hajiya Kari ce ta jiyo zancan auran a gari,jin wannan labarin daga gidan mitin din su na gungun mata aiko gidanta ba taje ba,gurin Hajiya Jummai ta nufo,ta same ta zaune tana aikin gyaran kumbunanta. Hajiya Kari ta ce,ke Aminiya,dama wata ta taso shine baki sanar da ni ba?" Hajiya Jummai ta ce "Um zo zauna dama ina nemanki." Kari ta ce, kice muna kukan targade sai kuma ga karaya ta samu? Hajiya jummai ba tare da damuwa ba a zatonta fa zancan hana zuwa Indiya ne sai ta ce ai kan batun nike neman ki wai ni zan yi mishi dabara,sai kuma na rufta.Ya hana tafiya yanzun ya ya ki ke ganin zamu yi? Hajiya Kari ta ce,ke da Allah can,ba wannan zancan nake miki ba, ina miki zancan auren shi, ashe aure zai ?ara? Hajiya Jummai ta yi mutuwar tsohuwa a zaune, kusan minti biyar Hajiya Kari ta girgiza ta sannan ta ce, "Aminiyata me ki ke tunani ne haka?" Hajiya Jummai ta ma rasa ta cewa, zufa ce kurum take keto mata, duk kuwa da (AC) da ke Wakin.

Can ta ce, "ko dai ba kiji dai-dai ba Karima?" Hajiya Kari ta ce, "Ki dai bincika." Ta suri jakarta tare da cewa, sai naji wayarki,don jin gaskiyar lamarin." Ta fita ta bar Aminiyarta cikin hawan jini.

Inda Hajiya Karima ta bar Hajiya Jummai,tana nan a gurin, har ?arfe tara na dare. Ta rasa wane irin tunani ma zata yi? Wayarta ce ta shiga ruri, ashe maigidan ne cikin ?arfin hali ta mi?e. Ta same shi da laptop yana harkokinshi,ta shigo ta zauna, jikinta ba laka, ya dube ta.

"Jummai ba ki jin daWi ne?"

Ta ce, "shi ne dalilin kirana don ka san ko ina jin daWi ko bana ji?"

Ya ce, "A'a." Ta ce "To yi maganar ka." Ya ce, "To dama kan batun aure ne da aka bani, cikin cijewa ya yi maganar, ya ci gaba su Baba Alhaji Sunusi ne suka ba ni mata," zaraf ta mi?e kana nufin Hadiza? Ya ce, ita, tayi wani guntun murmushi, sannan ta ce, "Allah ya bada Sa'a." Ta fita ya bita da kallo ya san gatse ta yi da ta ce Allah ya bada Sa'a.

Ya lumshe idanu, ya gama da nan sauran A'isha, duk da ba ya jin ta yasan ita ba zata ce komai ba.

Ranar ko runtsawa Hajiya Jummai bata yi ba,ta ma rasa me zata yi taji sanyi? Ta san Hajiya Lanti kamar yunwar cikinta, duk cikin dangin maigidan nata Sarayin mahaifinshi ba mafaWaciya irinta. In ma asirin ne take ta?ama dashi ta san zasu goga,don haka dolenta ta nutsu kada ta yi saurin nuna za ta Wauki wani mataki kan Hadiza,ta sani su Hajiya Lanti lashe money ce,ta jima tana son ?arta Hadiza ta auri Alhaji Saddi?,don dukiyarshi. Wannan lokacin bata damu da cewa ?ar ta mutu ko tayi rai ba,in har za su samu kuWi Hajiya Lanti gogaggiya ce ta samu duniya, ita ce mace mai faWa a ji cikin matan Alhaji Sunusi,ku san ita ce ke juya gidan son ranta. Ta taSa jin labarin ta gurin Boka na kan dutse. Lokacin da taje da bu?atar mallakar mijinta a hannu,Boka na kan dutse ya shaida mata cewa,wata Hajiya Lanti ita ce mace mai tsananin Sa'a, wadda ta samu mallaka ta ?arshe a gurin Aljanunmu.

Tun daga kanta har zuwa yau ba mu kuma ba da irin wannan mallakar ba, bata samu matsala a gurin gano kowace ce Hajiya Lantin ba, sai dai ta gano dangin mijinta ce, don haka ta ha?ura da ta so su haWa ?awance da ita, da irin waWannan tunane-tunanen ne gari ya waye mata.

Ita ko A'isha ba ta san me ake ciki ba, suna ta fama da jarabawar da ke fuskanto su lokacin bikin Uncle baifi sati biyu ba, da yake Uncle bai Wauki bikin da wani muhimmanci ba, ya yi zuwa gurin A'isha ya kai nawa, amma bai ce mata komai ba game da bikin nashi,hasalima shi mantawa yake yi da batun wani auran shi. Bai ma san dalili ba,in dai yana tare da A'isha ya kan manta da duk wasu lamura na shi, ballantana ma yanzun da ta mallaki abin kallo.

Yana son ganinta cikin kayan makaranta,ko na zaman cikin makaranta , har dai ace bata saka hijabi ba,?irjinta yana mishi ?yawun kallo. Sirantakarta ce kurum yake ganin matsala sai dai yana son yanda take da tsawo,dan tsayinta na sa shi jin alfaharin kasancewar ta matarshi,yana son taSa jikinta sai dai yanda take ba shi girma na saka shi yaji nauyinta.

Wani daWi yake ji duk lokacin da ya riki tafin hannunta, ta tsaya mishi cikin zuciya kuma bai rufe mata ba,yana yawan shaida mata yanda yake jinta cikin zuciyarshi, wanda ita kuma haka yana saka ta jin daWi har ma tayi kewarshi,in ya yi kwanaki bai zo ba.

Yau saura sati Waya bikin shi,ya yi dai ta maza ya kira Abbanta a waya ya shaida mishi cewa an bashi mata,wan mahaifinshi ya cigaba da cewa Friend wallahi ba da son raina zan yi auren nan ba, zan yi ne kawai don bani da yanda zan yi, maganar ta biyo ta gurin Hajiyarmu da Alhajinmu ne. Abba ya ce, "Haba Friend,ai ko kai ne ka gani ka ce kana so koyi kayi da sunna, ina fata dai A'isha bata Waga hankalinta ba? Don ka san mata ba su da hankali, yanzun sai taga cewa ita ba'a yi mata daidai ba, bayan Allah ne da kanshi ya umurce mu, Uncle ya ce, "Ai ita wannan baiwar Allah ce, wallahi friend tunda yarinyar nan ta zo gidana ko sau Waya ban taSa ganin fushinta ba, kullum cikin fara'a take. Abba ya ce, Alhamdulillah, sai in mun zo insha Allah zan zo Waurin aure."

Uncle ya ce "To shi kenan, sai ka zo kenan."

Washegari Sunday (lahadi), Uncle gurin Beby ya nufa, suna zaune suna fuskantar juna, ta rasa dalili in tana kusa da Uncle sai ta samu kanta cikin wani yanayi da ba zata iya cewa wane iri ba ne.

Ya dube ta da murmushi, Beby kullum ?ara ?yau da girma ki ke yi,ta ce ko dai tsawo? Ya ce,kinsan cewa tsawonki yana Waya daga cikin abinda yasa nake sonki? Ta rufe fuska da dogayen tafukan hannunta, sannan ta ce, wai da gaske kana sona? Ya ce, sosai ma, kada ki ga yanda na ?osa kuyi hutu wannan karon domin na san yanzun kinsan abinda ake yi a samu ciki ko? Cikin cinya ta saka kanta, sannan ta ce ni ban sani ba fa,ya ce to ai koya miki zan yi,kina so? Ta girgiza kai alamun a'a,ya ce amma da ai kin ce in nuna miki kenan kin bincika kamar yanda na ce,kafin ta yi magana wayarshi ta soma ruri,yana cirowa yaga Hadiza ce, bayan sun gaisa take cewa wai ?awayanta zasu zo amsar kuWi gurinshi zasu zo ko gurin abokanshi? Ya ce, mata ba ko Waya,su gaya mata ko nawa ne sai tayo mishi waya zaya aiko a kawo mata, ta ce shi kenan. Ya dubi A'isha wadda zuciyarta ke son sanin wacece Hadiza? Ya ce Beby dama na zo ne da magana sai kuma na manta kin san cewa in ina kusa da ke ina manta komai da komai ne? Ta yi ?ar dariya tare da cewa, wace magana ce? Ya ce, "Beby mata aka bani." Ta kafa mishi idanu,ko ?iftawa sannan ta ce,ban gane ba? Sai kuma ya samu kanshi da Wari-Warin gaya mata, sai dai dole ne ma ya daure ya sanar da ita saboda ance magana zarar bunu, kuma ya riga ya furta. Ya ce, "kin san Baba Alhaji Sunusi?" Ta girgiza kai ni ban san shi ba,ya ce kin san Hadiza? Haushi ya ma hanata magana, kallonshi kawai takeyi,ya ce ita ce aka bani ?ar wan Babanmu ce,yau saura ?wana shida bikin."

Idanu A'isha ta zaro, saura ?wana shidda? Ta taSe baki, sannan ta mi?e tsaye tare da cewa, "Allah ya ba da zaman lafiya." Ta nufi cikin makaranta,sam bai za ci haka daga gareta ba, ita ko ko gani batayi, ta isa Wakinsu kan gado ta ?wanta, ga mamakin ta sai kurum ta ji hawaye suna ?waranya a kan kumatunta.

Wato ita Uncle zaya yi wa haka? Wai an bashi mata kenan, ita ba son ta yake ba,dama bai wani damu da ita ba,shi kenan yanzun zaya daina gaya mata kalamai masu daWi, haba ita ta sani in ba baya son ta ba ai bazai kasa kula ta ba,bai taSa neman ta ba haba ya ci ace tun tuni ma ta gano wannan matsalar, amma ba komai yaje ya yi ta yin auran, Umma ta ce,in bana gyara mishi shimfiWa sai ya ?ara aure, duk hutu sai ta gyara mishi Waki amma hakan bai sa ya sota ba. Tana cikin wannan halin su Samira suka shigo, cikin sauri suka isa gurinta, nan suka shiga tambayarta abinda ya same ta. Sun ruWe ?warai,domin ba su taSa ganin A'isha musty cikin wannan halin ba.

Samira ta ce,"A'isha Musty me ya same ki ne? Don Allah tashi ki ji mu." Jin lallashin da suke mata ya saka ta kukan sosai,ba ta iya cewa komai ba,sai da tayi ma isarta sannan ta share hawayenta. Samira ta ce,me ya same ki? Wane ne ya Sata miki rai? Ta ce, Uncle Wina ne. Amina ta ce,me ya yi miki suka haWa baki gurin cewa, Uncle Win ki dake matu?ar ji da ke? Ta ce,wai fa aure zai yi, dariya ta kama su,don zai yi aure ke ba abin murnarki ba ne? Ta yi shiru ita ta manta ma da ba su san cewa Uncle mijinta ne ba,don haka sai ta ce ai ba zaku gane ba ne, duk yanda muke da Uncle wai ace sai yau zai gayan bikinshi saura ?wana shida bayan duk sati sai ya zo,ni kun ji damuwata." Suka ce ki mishi uzuri,ki ka sani ko abin ne yazo mishi ba cikin shiri ba?" Ta ce,Umh, daga nan ba ta sake cewa ?ala ba, domin ta gane ba zasu fahimce ta ba.

Tun daga ranar ba ta da sukuni, duk bayan awa Waya sai ta lissafa sauran ?wanakin da suka rage na bikin Uncle Win nata,su ko su Samira mita suke mata kan cewa ta yi wa Uncle Winta afuwa, tare da ba shi uzuri. Ita ko Amina cewa take ina ma ba lokacin makaranta ba ne,su zo mata biki har ma su ga Antin tata,wato amaryar Uncle Win nata,a cewarsu ta yi dacen miji. A'isha kan ja tsaki tare da cewa, "Allah ya sutura,ta zama Antynta,su kuma suce dole ne tunda tana auren Uncle Winta. Aisha kan yi tsaki ta yi shiru kurum.

Shima Uncle na shi gefen yana cikin damuwa, wato damuwar Beby ita ce ta Waga hankalinshi. In ya tuna yanda ta wuce yana kiranta Beby-beby tamkar ba ta ji shi ba haka ta yi. Dama Beby tana fushi? Itama kishi kenan gare ta? To me yasa ba ta kishi da Jummai sam? Koda yaushe tunanin A'isha ke ranshi, tamkar ya ce ya fasa auran yake ji. Cikin haka aka shiga bikin.

Abba ya shigo Katsina,ana gobe Waurin aure ka ji daren da ya hana mutum huWu bacci, A'isha ?wana tayi sallah tare da addu'o'i, tafi maida hankali ne ga ro?on Allah ya rage mata kishi cikin zuciyarta. Jummai kuwa ?wana ta yi neman mafita inda ta farka da mummunan ciwon kai...



########
[12/11, 21:33] Ummi Tandama=??: *=???=??? Page 6*


Hadiza kuwa ta ?wana da farin cikin samun mijin nunawa Sa'a ga kuWi ga ?warjini,shi kuwa Uncle tunanin Beby ne ya hanashi bacci,ya ?osa gari ya waye sati ya je school Win shi da Abbanta.

Aisha ta farka damuwar da Wan sauki,ta yi tunanin gara ta rungumi ?addara tunda auren babu fashi,sai dai matsalarta Waya,dama Uncle ba ya son ta? Ta kan ba kanta amsa da cewa eh,tunda gashi ya yi wata a madadinta. Tana son samun natsuwa badan komai ba sai don jarabawar da ke tunkaro su,nan da satin da zasu shiga,ta sani ?ar?ari nan da sati uku za su yi hutu maimakon Uncle ya bari sai sunyi hutun ya yi auran. Sai kuma tayi tsaki ta ce, ita dai tana son cire batun auren nan na Uncle daga zuciyarta.

An Waura auran Uncle da Hadiza da misalin ?arfe Waya da rabi na ranar asabar, bayan an tashi daga sallah,ko jiran walimar abokan da nashi suka shirya bai yi ba,yaja Abba da cewa su zo suje gurin Beby a makaranta, Abba ya ce a'a ka barta kawai,ni yanzun zan Wauki hanyar garinmu."

Uncle ya ce "friend dole muje ka ganta,zata ji daWi saboda wancan hutun nan kaita gida ba." Abba ya ce,shi kenan muje.

Suna kan hanya, Nafisa ta kira shi tana cewa, "Brother,tun jiya na ke son ganinka,ya ce gamu nan zamu je gurin mutuniyar ki ne makaranta." Nafisa ta ce,ku gaishe ta,sai ka dawo zamu haWu." Shima yana son ganinta tun bayan bikinta bai ganta ba.

Sanda suka iso makarantar, lokacin tana ?wance. Tun safiyar yau gabanta ke mugun faWuwa, musamman in ta tuna sauran ?an awanni a Waura auran Uncle Win ta, lokacin da take zaton cewa lokacin ne ake Waurin auren sai ta samu kanta da kasa koda zama ne, saboda faWuwar gaba, tabbas dole ne a ce an zo yiwa duk matar da mijinta zai ?ara aure dannar ?irji,dama haka ake ji? Kafin ta ba kanta amsa, sai ga sallamar Momy Win da ke kula da gefen su, ta ce ?ar gidan Uncle ki zo inji shi. Wani sabon takaicin taji ya rufe ta,ta ce Momy ki ce mishi bana jin daWi ba zan iya fitowa ba. Momy ta ce,da kin daure kin Wan lallaSa A'isha, ta ce,ki dai gaya mishi.

Momy ta tafi tana cewa,zaki sa hankalin Uncle Win ki ya tashi kenan. Da yake kusan yawancin malamai zuwa Waliban makarantar sun san shi a duk lokacin da makarantar take bu?atar wani abu da zarar ya samu labari zai ba da, haka nan tunda A'isha ta shiga wannan makarantar,bai taSa biyan school Win ta ita kaWai ba, sai ya haWa duk ajin ya biya, shi yasa A'isha Musty ta yi suna cikin makarantar ga ?o?ari.

Lokacin da Momi taje musu da batun A'isha ba ta ji daWi, sai hankalinsu ya tashi. Uncle ya ce, sosai ne? Me ya same ta? Momy ta ce da Wan sauki Abbanta ya ce kice ta Wan lallaSo Abbanta ne. Koda Momy ta shaida mata sa?on da sauri ta tashi zaune tana cewa, su biyu ne? Momy ta ce eh.

A'isha ta zura hijabi suka tafi, Abbanta yana zaune shi ko Uncle yana tsaye ya kasa zama. Ta shigo da sallama suka amsa, Uncle ya nufo gurinta yana cewa, Beby me ke faruwa da ke ne? Bata ko kalle shi ba ta nufi Abba,tana cewa, Abbana yaushe ka zo? Ya ce, jiya na zo, yanzun nan kuwa ina kan hanya ne dama na zo Waurin auren friend ne,ta ke ta canza fuska, tare da canza magana,ta ce Yaya Umma fa? Ya ce,da tare zamu zo sai kuma su Jafar ba su ji daWin jikinsu ba.

A ranta ta ce,lallai Umma, wato da auren Uncle za ta zo? Ta Wan taSa baki sannan ta rusuna ta gaishe su, suka amsa. Uncle ya sake tambayarta,me ya same ta? Ta ce,mura ce,kuma ta samu sau?i. Wayarshi ta yi ringing,ya Wan fita don amsawa. Ai nan take zuciyar A'isha ta yanke mata hukuncin cewa amaryar tashi ce ta kira shi,don haka sai ranta ya kuma Saci. Abbanta ya kula,don haka ya ce, "A'isha ki

4 / 12