Advertisements
Chapter 7 Reading Mummunan Zato 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Mummunan Zato 2 Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 12

18K to 21K   out of 35.6K words

ya raWa mata inji wa ya ce ba girmana ba ne? Ko ke kanki ba sai in Wau abina ba,ta ce haba dai? Ya ce to bari ki gani,ya kai hannu ta ja baya tare da cewa,ana fa kallonka,ya ce na san su Suwaiba a gurin sai na?i wasa da Bebyna? Ta ce to muje, suka jera yana ri?e da ledar, suna fitowa nan ma'aikatan tun daga kan mai ba fulawa ruwa zuwa direbobin sun zo don su amshi ledar amma duk ya hana su, sai dai jakarshi ta Ofis ce ya ba Jabiru.

A'isha ko hakan ya yi matu?ar bata mamaki, shi da kan shi ya buWe mata ?ofa ta shiga sannan shi kuma ya koma can gefen inda Jabiru ya buWe mishi,yana zama cikin hannunshi ya saka nata. Yanayin susar da yake mata a hannu ya sa tajin kasala, har ma bata san lokacin da idanunta suke lumshewa ba,sai da suka hau titi sannan ya ce, "Jabir mu fara zuwa gidan Nafisa mu sauke Beby,ya ce to maigida. Hannu yasa ya kwanto da ita kafaWarshi,a hankali ya raWa mata cewa, jikinki yana da laushi Beby, ina son ?amshinki, Wan murmushi ta yi tun jiya yake faWin wannan kalmar.

Wayarshi ce ta shiga ruri,ya ciro ta daga aljihun suit Winshi, ya kalli fuskar wayar ya shafa kumatunta tare da cewa, Abbanki. Da sauri ta Wago daga kafaWarshi tare da cewa, don Allah? Bai bata amsa ba sai dai taga ya Waga wayar yana cewa, "Assalamu alaikum, Friend an tashi lafiya? Bayan sun gaisa ne yake shaida mishi cewa dama batun bikine zai sanar da su na yarinyar ?anwar Umma da za'ayi ranar juma'a mai zuwa Win nan,in sun samu zuwa to,in ma basu zo ba ba matsala.


########
[12/13, 17:32] Ummi Tandama=??: *=???=??? Pages 9*



Aisha duk tana jin su, bata san sanda ta dafa bayan Uncle Win ba,tana faWin "?an bani don Allah Uncle ba ni Abban." Tana magana tana girgiza shi, cikin yanayin irin na shagwaSaSSu, ya ce to gama Beby Win,da zumuWi ta amsa,ta ce Abbana ina ?wana? Bayan sun gaisa ta ce, bikin Naja ko na Sauda? Ya ce na Naja ne za'ayi ranar juma'a,cike da zumuWi ta ce zan zo insha Allahu, Abba ya ce a'a in mijinki ya ce a'a ba komai dama dai don ku sani ne,ta ce dama zan zo hutu,ya ce to sai kunzo bawa maigidan naki,ta ce to ka gaida min su Umma." Ta mi?a ma Uncle,suka koma kuma kan batun kasuwancinsu, daga bisani kuma suka yi sallama kan cewa sai sun zo. Suna isowa gidan Nafisa, suka shiga harabar gidan suka sauke ta,ta ce "Uncle ba zaka shiga ba?" Ya ce, nayi latti, idan na dawo Waukanki zan shiga, ta ce to. Ya mi?o mata ledar, tare da cewa,sai na dawo,ta ce to ka dawo lafiya,ta nufi hanyar da take zaton nan ne ?ofar falon. Shi kam zamanshi ya gyara tare da yin ajiyar zuciya,sakin fuskar Beby a yau ya samu ?wanciyar hankali.

Ta ?wankasa ?ofar ana ukun ne Nafisa ta iso,ta le?o sannan ta buWe cike da zumuWi,tana cewa Bebyn bros ce? A'isha ta shiga tana cewa,amare, Nafisa ta amshi ledar tana cewa, kawo in taimake ki. A'isha ta ringa juyi cikin ?aton falon mai shegen tsari tana cewa, wow Anty Nafisa falonki ya tsaru,gaskiya maigidanki ya iya zaSen guri.

Nafisa ta ce, maigidana ko maigidanki? Ai da gidan da abin da ke ciki har shirya gidan duk Uncle Winki ne. A'isha ta sake kallon falon "kai gaskiya Uncle ya San tasta, mutumin nan ya haWu da yawa fa, shiyasa kome ya zaSa zaka ganshi ya haWu. Nafisa ta zuba mata idanu tana dariya cikin mamaki ta ce, A'isha yaushe ki k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ayi baki haka? Wasa mijinki ki ke yi, ta ce Allah Anty Nafisa kinsan gaskiya na faWa, domin Uncle ko kaya ya saka sai kiga tamkar don shi aka ?era su. Nafisa ta ri?e haSa tana cewa, lallai A'isha kin shigo gari yarinyar,ta ja hannunta,to zo mu shiga cikin Waki. A Wakin ma haka A'isha ta yi ta santin gadon da sauran kayan tare kuma da koWa Uncle Win nata,ta zube kan gado tana kallon Nafisa tana cewa "Anty Nafisa ga shi kema kin yi ?yau, Nafisa ta zauna tare da dafa A'isha wai yaushe ki ka zama haka ne? A'isha tana dariya ta ce,me nayi wai? Sannan suka gaisa ta ce, ina Bros? Aisha ta ce, tare muke, ya yi latti ne shiyasa ya wuce, amma in ya dawo za ya shigo. Ya ya maigidanki?" Nafisa ta ce, yanzun za ki ganshi yau yana gidan uwargida ne.

A'isha ta taSa baki gami da cewa, don ma ku biyu ne, da ace kamar mu ne daga can gidan sai ya wuce wani gidan,don ma Allah yasa gida Waya muke. To yanzun kuma ke kaWai kike kuma Anty Nafisa? Ta ce "eh mana, sai dai ?an aiki na" Nafisa ta dafa A'isha tare da cewa,sai kurum ki kaji auren Uncle Winki? A'isha ta gyara zama tare da cewa,hum ai na ji mamakin auren Uncle,in kin ji takaicin da nayi sai da na kai zuciyata nesa, sannan fa na iya zana jarabawa.

Nafisa ta mi?e,bari inje in kawo miki abinci, A'isha ta ri?e ta,ban daWe da karyawa ba,bari sai anjima. Nan fa zan yini sai naci abinda nake so " Nafisa ta zauna tana cewa, "ai dukkanmu babu wanda ya so auren bros,ke shi kanshi ma fa ba wai yana son auren ba ne, don dai babu yanda zai yi ne."

A'isha ta ce,ni barni. Yana sonta har fita ya yi da ita waje."

Nafisa ta ce,"Amma dai kin san yafi son ki ko gaban waye yana faWa." A'isha ta ce, "Gaskiya ni ban gaskata ba." Nafisa ta ce, "saboda me?" Aisha ta ce don yana musu abinda ba ya min." Nafisa ta gyara zama "me kenan? A'isha ta taSa baki, duk garin nan Anty Nafisa ke kaWai ce nake gaya miki matsalolina,ni ko ba wai na matsu ba ne,kuma ba jaraba ba ce,hasali ma matsayina na budurwa kuma yarinya na san bai dace in yi wannan zancan ba. Amma zan gaya miki ne ba wai don ki faWa ma Uncle ba,sai don ki yarda cewa Uncle yafi son matanshi fiye da ni,kin san cewa Uncle bai taSa taSa ni ba?."

Nafisa ta zaro idanu,"kai haba?" A'isha ta ce wallahi, amma amaryarshi har da fita ?asar waje da ita." Nafisa ta ce,wai har yanzun? A'isha ta ce, Allah kuwa,ba wasa nake ba, da yana cewa ban isa ba, yanzun fa? A'isha ta ce God forbid,ai sai ya zata na matsu ne, Nafisa ta ce amma ai addini bai hana ba, kuma in da baki damu ba yanzun ai kin kai ki damu Win, tunda ba dutse bace ke, A'isha ta ce koda zamu tabbata a haka ba zan taSa ce mishi ?ala ba, tayi ?ar dariya tare da cewa kuma shikenan sai ince Uncle me yasa baka ?wana da ni? Suka yi dariya tare, A'isha ta ce Allah ko ke ce Anty Nafisa na san ba zaki ce ba. Nafisa ta ce bazan ce ba, amma zancan zan maka fuska. A'isha ta ce, "Ni fa ban damu ba,ni da ina makaranta ma,in ya saba min naje makaranta na damu fa? Haka dai suke ta hira har suka zo kan batun su Hadiza nan Nafisa ta shiga ba A'isha labarin wacece Hadiza,ta ce daga Hadiza har Jummai sun auri Bros ne, saboda kuWi,kuma dukkansu babu wadda bata buga duniya ba. Kuma shi Bros da Hajiyarmu sun ?i yarda cewa Jummai tana da hannu a cikin mutuwar kishiyoyinta, A'isha ta ce nima haka kawai sai inji zuciyata tana zarginta musamman da wannan ?awar tata Hajiya Kari.

Nafisa ta ce, kamar kin sani ke dage da yin addu'a, amma batunki da Bros zamu ga yanda zamu yi yanzun dai ki barshi ya gama amarcin da Hadiza, yanda in ya juya kanki zai san kuna da banbanci. Haka ta yini suna hira suka shiga kitchen.

Biyu dai-dai mijinta, Alhaji Bello ya shigo. Nan A'isha ta saki baki tana kallon yanda Nafisa ta ruga da gudu ta rungume mijinta,ta ma manta da wata A'isha a gidan, sai da ya tafi sannan Nafisa ta samu natsuwa. A'isha ta ce tabWi,Anty Nafisa kina sha'aninki, ina ma zan iya na dinga yiwa Uncle Wina haka? Ta ce kin ko san da kin ?ara haskawa cikin zuciyarshi. Hadiza zata iya shi yasa ki kaga tana Wan jan hankalinshi. A'isha ta yi Wan tagumi ta tsurawa mirrow ido tana tunanin shin zata iya? Ta dubi Nafisa ta yi Wan tsaki ina jin nauyin Uncle shi ne matsalar amma ina son in burge shi. Nafisa ta ringa yi mata dariya.

Biyar dai-dai Uncle ya kira Nafisa,wai ga shi a ?ofar falonta, suka fito suka buWe mishi ya shiga. Nafisa ta yi kicin, A'isha kuwa kamar yanda ta saba, ruwa ta kawo mishi ya amsa yana kallon fuskarta, sannan ya ce A'isha Allah ya shayar da ke ruwan Alkausara, yanda ki ke gusar min da ?ishina, shiyasa ko bana ?asar nan duk lokacin da naji ?ishi,sai kin zo raina kuma sai na miki addu'a. DaWi ta ji sosai sannan ta ce, "Allah yasa in sha tare da kai Uncle." Ya ce, "Amin Bebyna."

Nafisa ta iso da abinci,ya ce wa zai ci? Tayi turus kai mana Bros ya ce ni kam sai kuma nan da tara na dare. Na riga na ci na rana. Yanzun Beby ta fito mu wuce gida. Bayan sun fito, Nafisa ta ce to telan fa bai san measurement Win ki ba, A'isha ta ce,zan aika da kayana sai ya yi min girman su, masu ?yau inji Uncle. Nafisa ta ce kada kaji komai Bros, bayan sun shiga mota ta mi?o ma A'isha tsarabar da ta bata, tare da ki fa yi amfani da shi yanda na miki bayani, A'isha ta ce to na gode,sai mun yi waya.

Bayan Jabir ya Wauki hanya ne sannan Uncle ke cewa, tsarabar me ki ka samo Beby? Ya kai hannu gurin ledar, kawo in gani. Ta yi saurin Soye ledar ba fa wani abu ba ne,ya yi Wan murmushi tare da cewa, "Mata ba ku rabuwa da tarkace."

Tun fitar su A'isha, Suwaiba da safiya suka shiga gurin Jummai,suna bata labarin abinda A'isha da maigidan sukayi har ma da ?arin gishiri,wai ya rataya jakarta. Jummai ta ce jaka fa ku ka ce? Suka ce jaka mana, kuma ta ratayawa ko kunya da girmanshi da komai,tsaki ta ja ni ku daina gaya min tunda ku baku da fus cikin gidan,ba ?wa taimakaman da komai. Safiya ta ce in mun yun?ura zamu daki banza sai ki ce a'a," ta ce Allah wadaran halinku tunda ba ku da wata dabara sai ta duka,ku fitar min daga Waki, ance muku yanzu ana ya yin duka ne? Sai dai na ?ar?ashin ?asa. Suwaiba ta ce to ba sai ki nuna mana yanda zamuyi ba? Ta ce,ai yanzun duk zamanku tare da ni ba ku Wauki wani darasi ba? Allah wadaran zamanku tare dani, ta mi?e ta nufi toilet tana masifa,shegu kun iya yawon bin ?ana nan yara suna rarake ku, amma baku iya sanin yanda za ku zauna da mutane ba, yanda za ku ?untata ma yarinya, ya gagare ku.

Ranar dai haka ta yini cikin ?uncin zuciya, gefen Hadiza yau kam a cike da A'isha ta yini ga takaicin jiya,nata ganin ya danne mata ha??inta, sannan yau ba girkin A'isha ba, amma ya fita da ita don itama tana kallonsu ta window Winta, nata ganin ya fi son Aisha. ?aramar yarinya tana juya shi son ranta,don haka koda lokacin ?wanciya ya yi,ya yi sallama da sauran matan nashi ya shige Wakinshi ba tare da ya shiga gurin Hadiza ba,don ta san ita ce dashi,?in zuwa ta yi, dole tana fushi, shima bai neme ta ba, kuma ko washegari bai le?a inda take ba,hakan ya ?ona zuciyarta.

Ranar Alhamis suka sauka Jigawa,ni?i-ni?i da tsaraba,ga kuma gudunmawa. Aisha ta tattala dubu biyar Winta zata bada, sai kuma ta ji Umma da Abba suna mata godiya,wai Uncle Win ta ya bada dubu hamsin, talatin nata, ishirin na shi. Tun ranar A'isha suka wuce Gumel, ita da Umma,su Abba sai gobe in sun zo Waurin aure. Inna Rabi ta ji daWi sosai da wannan gudunmawa,nan A'isha ta zama tauraruwa gidan bikin kowa sai birge shi ta ke yi.

Washegari ana gama Waurin aure Uncle ya yi mata waya cewa ta le?o suyi sallama shi zai wuce, lokacin suna cikin gidan ma?ota, tare da su Naja da ?awayanta. Nan ta fito ta same shi cikin mota,ta shiga ta zauna ya rufe. Sannan ya ce Beby ?wana nawa za kiyi? Ta ce, duk sanda ka ce Uncle zan shirya in jira ka. Ya ce, to zamu yi waya? Ta Waga kai alamar eh,ya sa tafukan hannunshi biyu ya Wago fuskarta. Kallo Waya ta mishi ta lumshe idanunta,tana jin nauyinshi. Cak numfashinta ya tsaya lokacin da taji saukar leSunanshi kan nata leSunan ?amshin turaranshi ne ya doki hancinta.

A hankali ta buWe idanunta,na shi idanun a lumshe ?yak?awar fuskarshi irin ta fulanin Katsina KT cike da annuri. Ba zato shima ya buWe nashi idanun zata rufe nata, da idanu ya yi mata alamar kada ta rufe. Suka zuba ma juna ido, Kasa jurewa ya yi ya jawo ta zuwa jikinshi, sannan ta yi ajiyar zuciya tare da runtse idanunta sakamakon jinta cikin wani yanayi, muryarshi a sar?e ya ce Beby yaushe zan zo in tafi da ke zanyi kewarki da yawa. Ta ja numfashi muryarta ?asa-?asa ta ce,nace duk randa ka zo. Ya Wagota tare da cewa shi kenan sai nazo kanta yana ?asa don kunya ta ce, to . Ya Wauki kuWi daga gaban motar ya ce gashi,ta dube shi ka fa bani kuWi jiya, ya ce ki ?ara Bebyna, sai mun yi waya? Ta ce,eh ya kuma kama tafin hannunta ya sumbaci tsakiya,tsigar jikinta ta yi yar,ta kalleshi, sannan ta fita daga motar. Ta koma ciki bayan ta Waga mishi hannu alamun bye-bye.

Kano ya ?wana,sannan washegari ya nufo K.T lokacin da ya shigo gidan tsit, wannan lamarin yana taSa zuciyarshi, kullum ya shigo gida tamkar ya shigo ma?abarta. Ya buWe Wakinshi ya shige kan kujera ya zube, sannan ya jingina da bayan kujerar,kai wannan abu yana damun ?wanyar shi, duk gidan abokanshi in sun shiga,ya kan ji hayaniya sa'an nan ?a?an su kan shigo suna oyoyo, saSanin gidanshi kullum shiru mata biyu a ciki amma ko T.V da wuya, ya shigo ya taras an kunna kowace tana Waki tana ?wance, ya ja tsaki shi yasa in A'isha tana makaranta ko son tuno gida ba ya yi,ita kaWai ce wadda in ya kalleta ya ke jin annuri.

Ta tare shi da ruwa mai sanyi ko zoSon nan nata mai daWi, ya kai hannu kan leSunanshi yana son tuno yanda ya ji lokacin da leSunanshi suka mannu da nata,ya sauke ajiyar zuciya, sannan yasa hannu cikin aljihu ya ciro wayarshi. Layin A'isha ya nemo lokacin tana shafa mai,ta fito wanka, tana cikin Wakin inna Rabi, cikin uwar Wakanta, da sauri ta Waga wayar.

Ta ce, "Assalamu alaikum! Uncle ina ta neman layinka network ya ?i shiga, ya yi Wan murmushi gani na sauka gida yanzun nan, ta ce ina ka ?wana? Ya ce Kano mana,ta ce ka sauka lafiya?" Lafiya lau Bebyna,ki kula min da kanki. Tayi murmushi,nima haka. Ya ce ke ma me?" Ta ce, yanda ka ce,ya yi ?ar dariya, zanyi yanda ki ka ce,kafin ki dawo ki cigaba da kula dani...


#######
[12/14, 07:15] Ummi Tandama=??: *=???=??? Page 10*


Ta ce na manta kana da wasu masu kula da kai Win har su biyu, ya ce "ai Beby yanda kowa ke kula dani daban, sannan in muna tare da ke ki ringa ji a zuciyarki ba kowa cikin duniyar nan daga ni sai ke,kin ji ko?" Ta ce to Uncle, ya ce yauwa Bebyna, bari na watsa ruwa, ta ce to. Suka yi sallama.

Ya yi shiru, ya kula A'isha tana matu?ar son shi, kunya ce kurum ke Wawainiya da ita, shi yasa shima yake jin nauyin yi mata wasu abubuwan, amma yanzu ya san ya Wauko gangarar cimma burinshi.

Bayan ya yi wanka ya fito zuwa (Dinning table) bayan ya yi wa Uche waya kan cewa ya kawo mishi abinci, ya dubi Uche ba kowa a gidan ne? Uche ya ce Madam ta fita, amma bai ga fitar amarya ba. Zuciyarshi ta tafi ga tunanin yaushe rabon da ya samu kulawa daga Jummai? Ba zai iya tunawa ba, domin tun lokacin da ya zo mata da labarin auranshi da A'isha, ta canza har yau bai gane kanta ba. A fili ya ce, "Allah ka shirya wannan baiwa taka." Yana rufe baki tana shigowa,ta nufo shi "ka dawo ne? Wallahi nima na je gida ne na duba Innarmu." Idanu kurum ya zuba mata.

Ta ja kujera ta zauna,ba ka yarda ba ko? Ta soma magana cikin karya murya, irin ta wanda ke cikin damuwa Winnan, ta ce ni yanzun ai ko zan haWiyi Al?ur'ani ka daina yarda da magana ta, duk abinda na faWa ?arya ka ke Wauka, tun da ka samu yara masu jini a jika, ni ko na tsufa."

Ya ajiye cokalin hannunshi.

"Jummai don Allah ki zauna ki yi tunani, irin yanda ki ke tafiyar da gidan nan matsayinki na uwargida ya dace? Ni kaina yanda ki kayi watsi da duk lamurana,ki ka kama ?awayan bariki masu kai mutum ga halaka,yawo tamkar an yi miki ?auri da kan kare. Da na miki magana sai ki kawo duk maganar da ta zo bakinki ki caSa min." Ya nuna tebur Win gabanshi "Look at, yanzu tafiya fa na dawo ku biyu cikin gida amma sai kuku shi ne mai kawo min abinda zan ci, shima Win sai da na ro?a. A ce kamar ni bani da wata ?ima cikin gidana?"

Ta ce, "To kai ne ai duk ka canza min, yanzu A'isha ce a gabanka." Ya ce,"Ita ce take ganin girmana, amma fa duk wanda na kawo na ajiye ai so ne ya kawo haka ba wai ?i ba. Ni dukkanku ina sonku,ki kula da wani abu A'isha, yarinya ce kuma ba mazauniya ba ce,ku ko kullum muna tare da ku, amma duk da haka sai

7 / 12