Advertisements
Chapter 23 Reading Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   23 / 45

66K to 69K   out of 134.5K words

sanda nasa hannuna na goge masa ba. Me yake shirin faruwa ? Me hakan ke nufi? Me yasa yake kuka Dan nace bana sonshi? Yana sonane?

MY POV

Yazeed ne ya rasa yanda zaiyi Wai kuka yakeyi?kardai dagaske Sonta yakeyi to amma yaushe ya fara sonta? Ganin shirun yayi yawa yasa ya hade bakinsu Ba tareda yayi Komai Ba abinda ya basa mamaki shine mayar masa da tayi Dan haka baisan lokacin daya kara zafafa lamarin Ba. Sanda yaji zasu mutu saboda rashin numfashi ya sake mata baki.

A Dan kunyace ta tashi ta fice Ba tareda suncewa juna komai Ba.

Dunkule Hannu yazeed yayi sannan ya naushi iska. He ruined everything! What if da haske take bata sonshi?yayi gaggawa wajen nuna mata abinda ke ransa even though it was not intentional. Shima bai Shirya ba, yanzu ya zaiyi ya gyara abinda ya bata.

馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮

Zaliha kam though time take bawa Yan Maiduguri Dan Cewa tayi dole a miyar da ita Kaduna. Duk masifar inna sanda ta hakura ta bada gari.

Nan aka lallaba zaliha akace tayi hakuri gobe gobe zasu dawo Kaduna amma sai ta yarda tasha tsuminta.

馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮

Ya Abubakar yana shigowa Laila ta danno da gudu ta rungumesa. Shidai baisan me ya faru ba amma ganin yadda take farin ciki kuma ta wartsake yasa yasan Cewa alkhairi ne ya faru.

Janyota yayi har suka zauna yana dariya yace aunty fadamin abinda yasa Laila na irin wannan farin ciki.

Dariyan manya aunty fauziyya tayi kamin tace kafin wannan yanzu dai ka saketa tunda ba'a daura auren ba sai a lokacin ya lura da yadda suka kankame juna cikin jin kunya Laila ta gudu ciki yayinda ya cire hula yana sosa keya.

Aunty fauziyya tace ja'irin yaro ina ganinka Kamar salihi murmushin borin kunya yafi yace ba haka bane aunty.

Tace to Nide albishirinka yace goro kuma fari kamin ma ki tambaya.

Dariya tayi tace todai in fada maka babu abinda ya Shiga tsakanin Laila da Dan iskan yaronnan.

Nan ta fada masa yadda ta gano da yadda suakyi da likita.

Godiya ya dinga yiwa Allah harda sujjada baisan sanda hawaye ya zubo masa ba. Zaunar dashi tayi akan kujera sannan ta Dafa kafadan sa tace ba kuka zakayi ba hamdalan da kayi shine dai-dai addu'a zaka cigaba dayi allah ya kareku Daga sharrin makiya yace ameen.

Kicewa lailan ta samoni a mota zamuje gidansu yazeed tace Toh sannan ta Shiga ciki.

Fita yayi ya kirawo almajirai. Nan ya dinga daba musu kudi sanda ya raba sama da 10k.

Laila da ta fito sai murmushi take har tayi wani Dan kyau hakannan. Kai kwanciyar hankali dadi gareshi.

Gaba ta Shiga ta kwame ya Abubakar ma ya Shiga driver's sit. Belt yasa sannan ya kunna motan hannunta ya kamo ya sumbata ta warce tana turo baki yace ya akayine gimbiyata? Tace ba'afa daura auren ba kake rikeni yace astagfirullah wallahi duk cikin dadin ne ni na manta ma Allah ya yafemin tace Ameen.

Motar su suka fita Suna masu jin dadi sai gidan oga yazeed.

馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮

Abangaren su yazeed kuwa minal cikin yar iskar rigannan ta nufi kitchen kuma bilhakki da Gaskiya yunwa takeji Dan 10am ma ya wuce ko time din canja Riga batada shi.

Hamdala tayiwa Allah Dayasa akwai sauran Mara 3 a tuwonsu na jiya Dan da babu da idomie zata dafa.

Aiko nan ta daura dumame ziciyarta na wurin yazeed da yanayinda ta barshi yayinda takejinsa a jikinta.

Yazeed ko shiru yayi kawai Dan bai Masan me ya dace yayi a halin yanzu ba kawai sai ya mike ya fada wanka bai wani bata lokaci ba ya fito dai dai lokacin wayarsa ta dauki ruri dubawa yayi yaga mom ne hakan yasashi yin murmushi Dan yayi kewarta Rabon dayaji muryanta tun sanda tayi masa fada.

Dauka yayi tare da fadin my sweetheart kaif asbahati? Murmushi tayi Dan itama tayi kewan Dan nata tace lallai Abu yayi dadi tunda har ka fara manta lokaci nida nake India ne yanzu safiyata? Yace sorry sweetheart kinsan Nayi missing dinki fah.

Murmushi tayi tace abinda yasa na kiraka kenan Dan gobe ina tafe. Murmushi yayi amma saboda shekiyanci irin na yazeed yace noo!sweetheart karki dawo zaki batamin honeymoon dina.

Kama ha'ba tayi Kamar yana kallonta tace dannan kace Abun naka ya girmama ! Lokacin Dana aurama ba iskanci zaka min ba? Ta fadi hakan sounding like a drama old lady.

Dariya yazeed yayi yace Allah ya kawomin ke lafiya my sweetheart kinsan fa you are my first and last love. Mom tace first dindai amma last din kam....

Yace tunda kince haka to hakan ne. Kinji abinda ya faru da zakiyya kuwa?tace me ya faru? Yace ai.............

Nan yazeed ya kwararo mata bayani tace subhanallahi Allah ya Kare na gaba toh, yasa kuma haka shine mafi alkhairi yace Ameen. Muryan Jamal ya jiyo yana Cewa my man zan biyo mom fa Dan wallahi inaso inzo in kalli love show kyauta Ba tare da na yanki ticket ba. Mom ne ta make keyarsa yace ouch da zafi fa. Mom tace araftu(na sani).

Nan su kayi sallama yazeed nata dariya yayinda mom Keta surfawa Jamal masifa Wai a gabanta zaina mata zancen soyaiya tsabar bashida kunya.

Anyway, don't forget to menene ma?yauwa comment andddd share馃槈

Takuce karamarsu babbarsu

Miss untichlobanty

12 december,2019.

[1/11, 5:13 PM] Mzz_Untichlobanty馃挒: *馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳*

*馃尮by miss untichlobanty馃尮*

*CHAPTER 56*

Bayan Kamar 2 mins wayan yazeed ta sake ringing dubawa yayi yaga mom ne yayi murmushi sannan ya dauka kamin yayi magana mom tace my son bari muyi video call koh? Kasan na Dade ban ganka Ba.

Ta cikin wayan yazeed yaji Jamal na Cewa mom anya shi kikeson ki gani ?mom tace Allah zanci gidanku Jamal, izhab ila sallajah wa hadirny alhaleeb wal kaub minal matbakh

"廿匕賴亘 丕賱賶 丕賱孬賱丕噩丞 賵 丨囟乇賳賶 丕賱丨賱賷亘 賵丕賱賰賵亘 賲賳 丕賱賲胤亘禺"

"Go to the fridge and bring me some milk and cup from the kitchen."

Dauko laptop dinshi yazeed yayi sannan ya kunna nan yaga mom tana kiransa ya dauka murmushi ya fara sheko mata tare da sauke ajiyan zuciya domin wani dadi yaji sosai daya ganta dukda ko Ba a zahiri bane.

Yace wow! my sweetheart kinga farin da kikayi kuwa?kin kara kyau! Turo baki yayi yace Gaskiya nima zan biyoki.

Mom tace dubaka kai baka kalli kanka bane ji yadda kayi 'kiba kayi fari har kumatu ka ajiye da Anyi magana kace "ni banasonta Gaskiya tayi yarinya" ta fadi haka tana kwaikwayon yadda yazeed din keyi.

Bata fuska yayi Kamar yadda yara keyi Idan aka bata musu rai yace ni Nayi fishi ma kuma banyi missing dinki Ba.

Tace naji dama nima zakin baki na maka baki nakeson gani Ba. Ina diyata take? Yace tana kitchen mana.

Tace yi Sauri kakai inga yadda ka miyar min da ita kuma Idan naga ta rame ka Shiga iku. Yace haba momy nifa Bana zalinci kinsani so bazan zalinceta ba. Tace ai wasa nake maka kai mata mu gaisa nagani ko jikoki na Suna kan hanya.

Girgiza kai kawai yayi yana murmushi yace you will be disappointed kuwa tace wato mai hali bata fasa halinsa yazeed yace ehm gado Ba karanbani Ba. Dariya dukansu suka kyalkyale dashi dai dai lokacin yazeed ya iso kitchen.

Ajiye laptop din nasa yayi akan kitchen island din Yanda yake hasko minal sannan yayiwa mom alamun tayi shiru.

Sansadawa ya farayi dai dai lokacin kuwa minal tana rufe flask din data juye dumamenta tana wanka Hannu a sink.

Rungumeta ta baya yayi zata zabura ya matseta tareda rada mata shh nine and mom tana kallon mu.

Zaro ido tayi tana kokarin cire hannunshi tare da fadin yaushe ta dawo?rikota yayi kem yace a laptop dinane zo muje.

Daukanta yayi cidak Kamin ya juya ya nufi wajen laptop din da ita mom kam bakinta har ya fara ciwo saboda murmushin jin dadin ganin yadda taga 'ya'yan nata. Addu'a da fata take Allah ya karesu daga Sharrin dukkan mai sharri.

Sauketa yazeed yayi tare da riko hannunta yana fadin mom ga yar taki karki kiramin Yan sanda dariya mom tayi tace Gaskiya yazeed ka iya kiwo. Irin wannan kiba da daughter tayi sai kace ana hurata da iska masha Allah tabarakallah.

Minal sai lokacin a kunyace ta gaishe da mom saboda irin yanayin data ganta da yazeed ga rigar dake jikinta sai a slow.

Hira mom ta fara janta dashi yayinda yazeed ya tafi dakin zakiyya ya fara bude drowers dinta har sanda ya samo na ribbons sannan ya dauko 5 colours sannan ya dauko comb ya taho dashi. Koda ya shigo kitchen din ya zamu minal tadan saki jiki Suna hira da mom.

Comb din daya dauko ya fara yaje mata kai shareshi tayi taci gaba da hiransu.

Baki ya fara tsoma musu yayinda yaketa fafutikan daure mata gashin dai dai lokacin Jamal yazo yana lekowa yace wow bro masha Allah matarka badai kyau Ba Allah nima yar naija zan aura.

Hararansa yazeed yayi tareda matsar da minal Daga gaban cameran yace ayi Hiran a haka. Dariya Jamal ya kyalkyale dashi yace fadi Lanka tsaye kishi kake. yazeed yace ai bisa hakkina nakeyi.

Mom tace kai Jamal banson iskanci me yakai idonta kan matarsa nan dai sukayi sallama.

Yazeed ya kalli minal yace baby me kika Daga mana ne ?yunwa nakeji tace dumamen tuwo ne. Yamutsa fuska yayi yace dumamen tuwo kuma ? Tace eh yace please ki mana wani Abu mana tace anjima zan maka sounding serious dole yazeed ya bada gari. Zama su kayi akan island tasa Hannu ta fara fita masa tuwo. Mayan loma take tura masa yace na koshi, hararan sa tayi irin yadda kiyaye keyiwa yaransu Idan sunki cin abinci shiru yayi taci gaba dashi. Mutumin ka kan ace me ya lunkume Mara daya.聽 Wasa wasa kan minal taci nata loman ya cinye nashi. Daga karshe ya tsoma Hannu. Bayan sun gama ci yace mata zaije asibiti Daga nan zasu fara Shirye Shirye gyara guest side na gidan ind a su lukman zasu zauna.

Har kofa ta rakashi baiyi tsammanin zatayi pecking dinshi Ba to his surprise tayi pecking lips dinsa sannan ta buya zata tafi rungumeta yayi yace please karkiyi fushi dani! Tace banyi fushi dakai Ba ai. Yace kin tabbata ?ta gyada kai.

Neme neme ya farayi tare da waige waige tace me kake nema ne? Yace matsa kiga, matsawa tayi can ganin neme nemen bazai kareba tace Wai me kake nema ne yazzy baby? Duk ta kidime saboda yadda taga yana cube cube da alamu Abu mai mahimmanci ne.

Hannu yasa ya tallafo kumatunta tare da pecking goshinta murmushi tayi yace shi nake nema tace me? Yace murmushin ki! Shi nake nema tun dazu kika daina min murmushi sai mom kika yiwa kuma ya sokeni har cikin zuciya. Ya karasa magana yana Daga saitin zuciyar sa.

Dukansa tayi tace shine duk kabi ka rudar dani na dauka ma wani abinne me muhimmanci.

Hannu yasa a kunkuminta ya janyota tare da farin murmushin ki abune me muhimmanci da tsada a gareni. Duk Wanda ya rabaki dashi zan rabashi da farin ciki sannan duk Wanda ya saki murmushi to zan faranta mai.

Hannun sa guda daya ta kamo da hannayenta biyu tace na gode sosai kuma Insha Allah nima zanyi iya kokarina wajen ganin na faranta maka.

Rungumeta juna sukayi Suna masu jin dadi yazeed ya dauko wayansa yace selfie!

Nan suka dinga watsa pictures tare da yin fuskoki iri iri abin gwanin ban sha'awa kamin yazeed ya fita badan ranshi yaso Ba.

Nasan babu yawa amma Kuyi manage.

Karku manta Kuyi commenting.

Love you all馃槝

Takuce karamarsu babbarsu

Miss untichlobanty馃挄

15th December, 2019.

[1/11, 5:13 PM] Mzz_Untichlobanty馃挒: *馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳*

*馃尮by mzz_untichlobanty馃尮*

*CHAPTER 57*

Yazeed yana fitowa yayiwa lukman alamun ya karaso kusa sannan suka nufi guest side nan ya bashi dakuna guda uku tareda parlour yace zasu iya tarewa kan lukman ya gama gininsa tunda yaki yarda yazeed ya masa kyautan wani gida acewarsa yanason zama kusa dasu Dan haka ya siya wani gida kusa da mansion dinsu a unguwar zai gyara.

Godiya sosai lukman yayiwa yazeed Inda yazeed Kece masa Idan yanaso zai fitar dashi wajen yayi karatunsa na sojoji yace a ah yafiso ya kara karatu akan business inyaso sai ya fada kasuwanci Dan yanzu Idan kanaso kayi securing future na family dinka to ka tafi kasuwanci kawai amma aikin gwamnati kam Ba tseratar dakai zaiyi Ba.

Yazeed yace hakane nima ina tunanin Idan nakai 40 years zanyi retire in Koma business dina kaga sai ka fara Kumar min dasu kamin na iso ko? Lukman yace hakan ma yayi.

Asibiti suka nufa Inda yazeed yace bayason convoy,musa da ezikel kawai suzo su rakasu Inda ezikel shi zai tuka motan yayinda lukman da yazeed zasu zauna a baya.

Direct hospital sukayi daya ke asibitin yazeed akakai Jennifer kuma nan akakai ummi. Dakin da Ummi take suka Shiga suka samu ya Abubakar da Laila aciki.

Gaggaisawa sukayi Inda suke tambayan ya jikin Ummi ya Abubakar yace saide ace Alhamdulillah amma babu improvement. Shiru yazeed yayi domin he is planning on calling Dr mashkur wani abokinshi Wanda suka hadu a university sanadiyyar shan cuppucino.

FLASH BACK

Yazeed ne ya shigo wani caf茅 me Suna untichlobanty cafe tareda neman sit dake gefen window ya zauna .

Waiter ne yazo yana murmushi saboda ya ganesa tunda regular customer ne yace good day sir!(barks da zuwa yallabai! )Welcome back to untichlobanty cafe! What will you like to have?(sannu da dawowa untichlobanty cafe! Me kakeson a kawo maka?)

Yazeed yace my favorite cappuccino and some pancake.(cappuccino din Dana fi da pancake)

Waiter James yace with syrup or honey? (da syrup ko Zuma?) Yazeed yace with honey(da zuma)

Tafiya waitern yayi dai dai lokacin kararrawan kofan yayi kara alamun wani ya shigo. Table din da yazeed yake zauna yace salam yazeed wace alaika assalam miko masa Hannu yayi sukayi musabaha yace my name is mashkur ahmad and I am a MBBS student yazeed yace nice to meet you. (Sunana mashkur Ahmad kuma ni dalibin karatun likitanci ne. Yazeed yace naji dadin haduwa dakai)

I am yazeed abdulmajeed Umar Army student.(ni kuma yazeed ABDULMAJEED Umar sannan ni karatun soja nakeyi.)

Mashkur yace can I sit with you yace yeah sure (zan iya zama dakai yazeed yace eh ba matsala)dai dai lokacin waiter James ya dawo da murmushi dauke a fuskansa domin ya ganesa yace welcome sir. What will you like to have? Mashkur yace my favorite cappuccino just like his.

Gyara kai waiter James yayi sannan ya juya ya tafi. Mashkur ne ya kalli yazeed yace are you from Nigeria?(kauna Dan Nigeria ne?) Yazeed ya Daga kai yace masha Allah kace kanajin Hausa yazeed yace eh. Mashkur yace that's good to know.

Kana yawa zuwa nanne? Yazeed yace sau uku nake zuwa or hudu. Mashkur Yace wow! Nima haka ai inason cappuccino dinsu is the best shi kadai ma nake sha. Yazeed yace nima haka.

Mashkur yace we are cappuccino buddies kenan suka Dan kashe.

Mashkur yace sorry fa Mr yazeed kar kace na fiya surutu amma Gaskiya you look worried. Yazeed yace babu Komai kawai de na gaji ne Mashkur yace amma Ba haka idonta ya nuna ba. Yazeed ya Dan dara tareda Cewa ba Komai kawaide dad dina na tuna. Mashkur yace kana missing dinshi kenan ka kirasa a waya mana. Yazeed yace ya rasu ai, Idonsa cike da kwalla.

Daga kafadansa Mashkur yayi yace ai sorry buddy Allah yaji kansa. Yace Ameen dai dai lokacin aka kawo nashi cappuccino din suka sha sannan suka tafi after sin bawa juna.su phone number da address.

END OF FLASHBACK

Number din Mashkur ya kira ringing 3 ya dauka tareda fadin buddy kwana dayawa! yakake?yazeed yace lafiya amma ba lau ba.

Mashkur yace subhanallahi wani Abu ne ya samu madam din naka? Yace eh Toh hard a itama amma Koran na daban ne. Wato akwai patients har gida biyu da nakeda su and both of them are in coma.

Mashkur yace subhanallah ya akayi haka yazeed yace sai ka iso dai kawai na turo maka kudin enough please kazo nan if possible gone ma kazo. Mashkur yace right away kuwa Kazan ma na Dade banzo kasar ba tunda Nazi bikinka da madam zakiyya. Dan Sosa kai yazeed yayi cikin jin kunyan rashin kyautawan da yayi yace sorry buddy na manta ban gaiyaceka second marriage dina ba.

Mashkur yace wow!kanason kacemin ka kara aure YAZEED yace yeah. Mashkur yace congrats man! Idan Nazo zanci girkin Amarya kenan hope ta iya traditional food?

Yazeed yace sosai ma kuwa,Mashkur yace kace Idan nazo zansha labari. Yazeed yace Gaskiya kam har sai ka gaji. Nan suka danyi hira kamin Daga baya sukayi sallama.

Wajen Dr Muhammad yazeed yaje sannan ya bashi update akan yadda yayi da Dr Mashkur Dr Muhammad yace hakan ma yayi domin shi din babban likita ne an sanshi sosai ai.

Sallama sukayi kamin yazeed ya nufi office dukda yana yin aikinsa a gida amma sai yad'an Duba saboda abinda ba'a rasa ba.

Bayan Anyi asr yazeed yacewa lukman ya nemo musu abinci a favorite restaurant dinshi saboda ya yadda dasu kuma ya Dade baici abincinsu ba saboda ba zuwa office yaje ba kuma dams ba wani son cin abinci yake ba. Koda aka kawo yazeed kasa ci yayi domin ji yayi ba dadi ba dandano kwata kwata. Haka ya hakura yabar lukman yana fafatawa.

Koda suka dawo gida magrib yayi Dan haka suka tsaya har akayi isha'i ya Shigo gida yanajin yunwa sosai saboda ya kasa cin abincin dazu.

Zama yayi akan three sister tare da kwalawa minal kira.

Baby!baby sweetheart!! Kina inane?

Finally! Toh fans na gode da support dinku 14k reads ba wasa ba.

Don't forget to comment.

Love you馃槝

Your karamarsu babbarsu

Miss untichlobanty馃挄

16th December, 2019.

[1/11, 5:13 PM] Mzz_Untichlobanty馃挒: *馃弳馃弳KURUCIYAR MINAL馃弳馃弳*

*馃尮written by miss untichlobanty馃尮*

*馃崁MEDIA CONTACTS馃崁*

*INSTAGRAM:* miss_untichlobanty

*WATTPAD:* miss_untichlobanty

*EMAIL:* amishettima@gmail.com

*CHAPTER 58*

Saukowa minal tayi cikin navy blue Arabian gown. Murmushi take sakewa yazeed harta iso Inda yake zaune ta tsuguna tareda fadin

23 / 45