Advertisements
Chapter 33 Reading Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   33 / 45

96K to 99K   out of 134.5K words

ba Dan kawai?? kallon yanda ya kidime take tare da yadda yake motsa bakinsa. Kai Anya baifi yazeed kyau ba kuwa( Nace a ah hajiya ta kede kawai so ya rufe miki idanu) tissue yasa Mata kamin ya tisata har company clinic dukda ko tayita magiya ai ciwon ba babba bane amma fa deep down dadi takeji kamar ta mutu.

Dariya minal ta sheke dashi tace kina wuta mutumiyata kamin suka tafa minal tace ni fa na matsu ayi aurenku fa. Zakiyya tace ke?! Rufamin asiri nace miki muna soyayya ne? Dariya minal tayi tace saima kin fada toh wallahi ko fans din KURUCIYAR MINAL aka tambaya sunsan cewa kina sonshi. Fans ko karya nayi?

TOH ANAN ZAN DASA AYA MASOYA SAI KU AMSAWA MINAL TAMBAYARTA.

ME ZAKU IYA CEWA GAME DA LAMARIN ZALIHA DA LUKMAN?

YA LABARIN AUREN SU YA ABUBAKAR ? KU BIYONI A SANNU TARE DA COMMENTING DOMIN SAMUN AMSOSHIN TAMBAYARKU.?

WANNAN PAGE SADAUKARWA NE GA NAMECY @?Ma'ani??? ALLAH YABAR KAUNA.

KARKU MANTA TAKUCE KARAMARSU BABBARSU

miss Untichlobanty ?

2nd February, 2020

??KURUCIYAR MINAL ??

?by miss_untichlobanty ?

*WATTPAD:* miss_untichlobanty

*INSTAGRAM:* miss_untichlobanty

*TWITTER:* miss_untichlobanty

*EMAIL:* amishettima@gmail.com

?CHAPTER 73?

Haka duka dinga musu daga karshe zakiyya tace taji ta yarda ta dan fara sonshi amma kar minal ta fada ma kowa.

Da daddare minal na dakin yazeed tana? hada kayan tafiyansu domin karfe 2 dare jiginsu zai tashi yazeed yace baby kin taba hawa jirgin sama girgiza kai tayi yace tab ai kina hawa ki fara tunowa da Allah Dan idan ba ragewa da addu'a kukayi jirgin kifawa zai daku yayi adungure sallar mage. Zaro ido tayi tace kace Allah? Dariya yayi yace zan miki karya ne? Girgiza kai tayi kayansa ta hada masa kaf shiko ya cigaba da game dinsa can yaga kamar? bata saka nata kayan a box din yace a wani akwati zakisa kayanki ne girgiza kai tayi jiki a sanyaye. Alamu ya Mata da tazo, ta taho kafafunta na hardewa. Zaunatta yayi a tsakanin kafafunsa yace ya akayi ? Danshi yama manta da cewa ya tsokaneta dazu.

Muryata na rawa tace na fasa tafiya ne. Tace kamar ya kin fasa tafiya ? Me yasa? Kuka ne ya kwace Mata tace ba kai kace jirgi zaiyi adungure sallar mage dani ba? Dariya ce taso kwacewa yazeed amma ya matse kwantarta yayi a jikinsa yace ai ba kowani lokaci bane yake kifawa sai idan masu zunubi sunyi? yawa a ciki, bakiji nace kiyi addua ba? Kallonsa tayi tana goge kwalla tace nidai gaskiya bazan shiga ba kawai mu fasa tafiyannan. Zaro ido yayi yace ku fasa kuma? Idan mun fasa toh ya batun babies dinmu ? Alamun tunani tayi yayinda yaketa kunshe dariyarsa. Tace toh ka tafi kai daya, turo baki yayi yace dama bakya sona? Girgiza kai tayi tace toh tare zamu tafi. Wani kwalla ne ya sake tsiranyowa daga fuskarta har tausayi ta bawa yazeed. Haka ta hada kayanta tana kuka dan gani take daga daren yau sunanta gawa. Tunanin zucin da take ne ya baiyana. Tace oh su nima an zama labari, Dariya ce ta kufcewa yazeed yayi saurin mayar da ita tari.

Haka suka kwanta tare da saita alarm din karfe 12:00am minal kam ta kasa rintsawa sai juyi take tana lissafa abubuwan alkairin da tayi wanda take iya tunawa,ajiyan zuciya ta sauke tace da sauki ma ko na mutu ina sa ran shiga aljanna. Yazeed yana Jinta domin shima baiyi bacci ba Dan sai nuku nuku take a jikinsa ga ruwan hawaye dake jika masa Riga. Haka alarm ya kada suka tashi suka shirya minal sai kuka take tana fadin ni banason injeeee??!? Koda sukaje yiwa mom sallama taga yanda idon minal ya kumbura tace lafiya ko bakida lafiya ne? Shiru tayi tana tsittsilla ido kamar mara gaskiya yazeed yace cikinta ne yadanyi Mata ciwo amma gashinan dai yanzu tasan warke. Mom tace toh Allah ya kara sauki a ya stare hanya haka kowa ya taso akayi musu rakiya har airport bayan anyi clearing dinsu kamin su wuce ne minal ta kebe da zakiyya. Suna shiga toilet din zakiyya tace lafiya minal tace don Allah zakiyya kin taba shiga jirgi ko? Zakiyya tace sosai ma kuwa wani abin ne? Tace wai da gaske ne yanayi 'kolin 'koli da mutane ya 'kwala da kasa. Zakiyya tace wa ya fada miki? Idonta ne ya ciko da hawaye tace yazeed ne. Zakiyya ta gane franking dinta yayi shiyasa tace ehhh toh bai fiya yi ba amma dai id.....

Kuka mai karfi minal tasa hakan ya hana zakiyya karashe maganarta, nan fa tahau lallashi ana cikin haka yazeed ya Kira wai suna inane? za'a fara boarding.

Koda suka zo kasa kasa da murya zakiyya tayi tace Allah kaide yazeed bakada Kirki dubi yadda kabi duk ka ruda yar mutane. Dariya yayi kasa kasa tace zakiyya kenan babu ruwanki media kice na tuna miki da sanda na tsoratar dake akan tsaka. Dariya sukayi a tare tunowa da yadda zakiyya ta rude lokacin hannu ta daga zata makeshi kamin ta tuna da cewa ba mijinta bane. Hakan yasa dariyar fuskassu ta dauke murmushi tayi tace Allah ya kiyaye hanya make sure idan zaku dawo ku dawo da mai dadi, ku tafi ku biyu ku dawo ku uku. Jinjina kai yayi yace da izinin Allah daga nan ya kamo hannun minal suka wuce.

Koda fa minal taga jirgi da girmansa sai hankalinta ya kara tashi. Cije wa ta fara yi yazeed yana janta yace ke menene haka wai? Hawaye na? dawafi a fuskarta tace nace na fasa, wallahi na hakura. Dafe kai yayi yace AI ba komawa yanzu kina komawa za'ace ke yar boko haram ce. Tace toh ai ni matarka ce kuma ai soja bazai zauna da yar boko haram ba. Yace toh ai karin matsala kenan cewa zasuyi na kasheki a take kawai a huta kuma kinsan bazan iya ba kinga za'a ce mun hada baki sai akashemu duka biyu kinaso a kashemu? Tace a ah yace toh maza muje haka suka shiga kirjinta na duka dib! dib!! dib!!! dib!!!! dib!!!!! dib!!!!!!

Kadawa cikinta yayi koda suka zauna tace inane toilet dan Allah ? Nuna Mata yayi tayi using tana shirin fitowa taji ana announcing za'a tashi babu shiri ta fito kamin ta karaso sit dinsu wani ya? kamata kurrrr! Cikinta ya bada sauri Allah ya taimaka Dan ma class dinsu babu mutane dayawa da ace irinsu economy suka shiga da an Sami matsala ai. Wani zubin auren me kudin ma nada dadi.

Zama yayi tare da riko yazeed 'kam 'Kam a tsorace tace yanzu zai tashi ko? Yace eh,habawa jin sautin engine din jirgi take wani fitsari ya matsota. Yazeed yace kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru. Tafiya jirgin ya fara tace kai ashe ma kamar mota ne naketa jin tsoro, window ta kalla taga still suna kan kwalta tace toh amma ya muke tafiya Akan kwalta bayan kuma n......... tashin da jirgin ya farayi yasa minal kasa karashe maganarta kara riko yazeed tayi tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta.

Wata budurwa daketa kallonsu tun dazu sai dariya take. Koda jirgi ya daidaita a sararin samaniya budurwa tace kai gaskiya sister kinada abin dariya sai kace yau kika fara hawa jirgi? Hannu yazeed yasa yana goge wa minal hawaye kamin yace baby na kede kinji kunya,minal jam turo baki tayi tareda yiwa wannan budurwar gwaliyo? tace kede kice kishi kike bakida mijiiiii

Wani saurayi dake gefen budurwar ne yace my love rabu da ita da alamu bata ganine. Kallon yazeed yayi yace nikam wannan kamar captain yazeed ko? Murmushi yazeed yayi yace nine,musabaha sukayi kamin suka dan fara hira kamin kace me tuni sun saki jiki sun fara hira saurayin me suna Ahmad yace kamar yadda muka fada muku mu sabin ma'aurata ne so zamuje honeymoon ne yazeed yace aiya mu medical treatment zamu je daga nan sai mudan huta. Matarsa mai suna ameera tace gaskiya kanada kunada kirki sosai. Daganan kowa yaci gaba da sabgar gabansa. Minal tace wai ina sojojinka ne ko an hana musu Visa ne murmushi yayi yace aisu military ne so zasu iya fita amma da guda daya na taho idan naje can zasu bani na kasarsu. Tace da wa muka taho toh ? Yace kiyi guessing tace Joshua? Yace kin manta ya mutu? Tace Ezekiel? Yace nope Ezekiel ai yake kauyensu tace toh ni ban sani ba. Murmushi yayi yace da lukman na taho ihu tayi tace da luku da zaliha mukazo? sauran mutanen dake wajen suka kallosu danna duka duka su 10 ne.?

Zaunar da ita yayi yace ke Shashasha bakisan a cikin mutane muke ba ? Sannan ko kin manta da cewa jirgi ne da kike kokarin tsayawa tace au na manta ne.

Ameera tace lafiya take ihu? Minal tace albishir yamin shiyasa kamin suka cigaba da magana tace toh ya basu zauna tare da mu ba yace saboda wasu sun rigamu kinga babu dadi ace anyi cancelling saboda a bamu a rashin Adalci ne ko? Ta daga kai yace yanzu suna business class idan mun sauka zamu hadu.

Surutu taci gaba da mai har bacci ya dauketa. Gyara Mata kwanciya yayi kamin ya kunna film abunsa.

ALHAMDULILLAH!

Anan na kawo karshe littafi KURUCIYAR? MINAL da fatan an karu kuma an fadakartu.

Toh wasa nake su o oh har an rude za'ayi min caa aka?

Don't forget to comment in kunason update me yawa

See you soon a next CHAPTER.

Takuce KARAMARSU BABBARSU wato

Miss Untichlobanty ?

4th February, 2020.

*??KURUCIYAR MINAL??*

?by miss Untichlobanty ?

*?CHAPTER 74?*

RECAP.....

Surutu taci gaba da mai har bacci ya dauketa. Gyara Mata kwanciya yayi kamin ya kunna film abunsa.......

Koda jirginsu ya iso tashinta yayi tunda ba halin ya dauketa, ta departures' door suka fito suka fito suka hango cars gida biyu ga wani ya daga carbon paper an rubuta captain yazeed abdulmajeed wajen motan suka nufa nan sojoji sula Sara masa direct hotel din da zasu sauka akayi dasu minal da zaliha an saki baki yayinda luku ke cin magani dan yanzu baya sakar wa zaliha fuska.

Akwana atashi anyiwa yazeed aiki kuma its successful. Nan fa su minal aka rikice nesa yazo kusa. Dakyar da dubara akayi abin, kunya duk ya isheta Dan gani take kowa yasan abinda ya faru.

Wasa wasa yau watansu 3 a Germany amma shiru kake ji babu ciki babu alamarsa ga yazeed yabar aiki jingim kuma next week za'ayi bikin kara masa girma wato ya zama major general yazeed abdulmajeed Umar.

Haka suka tattara ya nasu ya nasu suka dawo mom duk ta damu saboda tanason taga jikokinta kamin rai yayi halinsa tunda batasan sanda zata tafi ba.

Koda suka dawo Nigeria har anayi auren laila da ya Abubakar da kuma zakiyya da Jamal ba tare da bata lokaci ba. Yanzu haka laila nada cikin wata da sati biyu daya ma minal da fari ta dau abin wasa amma da taga cikin Laila abin yadan fara damunta amma ganin ai ba'a wani Dade ba yasa ta kwantar da hankalinta, yazeed na lura da ita kaf amma ya zuba Mata ido.

Shiri suketa yi yayinda minal da zaliha keta yin fada akan lallai sai minal tayi kwalliya yayinda ta dage cewa bazata yi ba.

Zaliha tace kinsan Allah idan dai bazakiyi kwalliyar nan ba zamuyi fada ? Bakisan cewa za'a dauke ki a camera bane ga yan jaridu da gidan talabijin dukzasu zo minal tace tunda ba gasar kyau za'aje ba bazanyi ba kuma ai miji akewa kwalliya ba ?artin banza dawofi ba. Kuma ni ance miki zanje ne dan adaukeni? Zanje ne Dan mijina. Dauko gyalen da zatayi rolling tayi Dan kayan da tasa baya bukatar hijab ta dau Jakarta ta fice dan zaliha ta bata haushi.

?

A bakin kofan side dinta tayi kicibus da yazeed ciccibarta yayi yana fadin wa ya tabamin baby na? Dauke kai tai tana kumbura yace my minal fishing harda ni ne? Sharesa tayi bai dirar da ita ko ina ba sai dakinsa, dakyar yashanyo kanta suka sha romance ganin yana neman zurfafawa yasata guduwa.

Haka akayi bikin Karin matsayi akayi su pictures kowa na farin ciki aka watsesaide kash basusan cewa nanne farin matsalar su ba.

Yazeed kwance kan cinya minal a parlour suna kallon wani Indian series tsabar abin tausayi minal batasan sanda ta fashe da kuka ba dariya yazeed keta Ma ta wai ta jona Shaun asararru masu yiwa film kuka sai turo kanshi take tana ya tashi tunda abin hakane daidai lokacin luku ya tsindumo babu ko sallama sai haki yake da alamu gudu yayi. Yace ina wayarka inara kiranka baka daga ba? Yazeed yace ba wannan yafi muhimmanci ba, wa ya baka izinin diro min cikin bangare ba ko sallama. Tsaki lukman yaja cikin haki yace kai dalla share wannan bakas....... bai karashe ba yazeed yakai masa naushi tsabar kishi. Minal tayi saurin rikeshi tare da kallon luku tace ya akayi? Yace government tasa an rufe gaba daya account din yazeed saboda ana zargin wai ya hada baki da yan siyasa anacin kudin kasa sannan bazai iya sayar da kadarorinsa ba ma atakaice de har company yanzu duk NASA ne amma suna under government so he does not have a say a kansu har nanda 3 months? Abu daya aka barma daga gidannan sai ka zabi mota daya. Yanzu haka EFCC suna bin cike kuma you can't use your passport kamar kasan ba kuma baza'a baka Visa bama koda emergency har sai 3 months ya cika.

Yazeed ya zama shock ma dan shi baya ko irin kai wa yan siyasa ziyara da akeyi balle ya saci kudi daga jin magana akwai tuggu a ciki. Bakinsa na rawa yace menene hadin companies din mahaifi na da za'a saka a ciki ? Luku yace saboda idan ta tabbata gaskiya zai zama na gwamnati wai shine hukuncin ka.

Yace ya batun Wanda na bayar dasu ga families Dina? Luku yace eh wannan basu da harka dashi tunda yanzu ba naka bane ajiyan zuciya ya sauke tace atleast munada yadda zamuci abinci maza ka hada meeting da uncles Dina baki daya on Saturday, Luku yace sure kamin ya fice.

Gumi ke tsattsafowa yazeed domin ba dukiya daya rasa bane ta dameshi yadda aka bata masa suna bai ji ba bai gani ba. Rungume sa minal tayi tare da kwantar dashi a kirjinta tace yazzy baby karka damu komai zai wuce is part of kaddarar mu.

Haka yaci gaba da basa baki har yayi bacci a kirjinta sai alaokacin ta lura da yadda hawayensa ya kika Mata Riga. Ajiyan zuciya ta sauke kamin tayi nata kukan Dan ta daure ne kar ta karya masa guiwa.

?????????

?Darius take shekawa abinta tare da cewa kai nifa shegiyace duk wadda ya taboni toh shida kwanciyan hankali sun raba kafa kamar aljanna da wuta.

Mummunin Alhajin da take zaune a cinyarsa ne ya sheke da dariya yace kaji shegiya wai dama kinsan akwai wuta da aljanna kike wannan tsiyar? Hade rai yayi Tace me kake nufi? Daidai lokacin wayanta yayi ringing ta dauka tace ya akayi ta dayan bangaren akace gaskiya fa madam mugu(bokanta) yana korafi cewa idan dai bazaki dinga zuwa yana biyan bukatar sa ba to saide ko dinga aiko da jarirai uku idan ba haka ba ku ?a?e. Tsaki Taja tace ni rabani da jarabarsa ban iyawa ga warin da yake zan karo ma 500k a samo Karin jaririn akai masa. Ta dayan bangaren akace hakan ma yayi.

Daga nan ta kashe wayan Alhaji yace amma baby wai me suka miki hakane kika tsanesu da kike kashe irin wannan kudi? Murmushin rashin imani tayi tace hmm bazata gane ba. Yace ada na barsu ganin abokin hamaiyar tawa ya mutu amma yanzu Dana hadu dake sai naji dole ma in ga kayansu musamman yanda dan ke nema yafi uban yin nasara.

Sauka tayi daga cinyarsa tare da fara safa da marwa a dakin tace kiyaiyar danake musu tafi Wanda kafirai keyiwa annabi na samesu fiye da yadda na tsani mutuwa ta kai Alhaji bari kaji idan har zanga sun kaskanta sun wahalu a duniya toh wallahi babu ja in ja na yarda in shiga wutar jahannama indai sun wahala. Banida matsala koda kuwa za'a ha?a ni da shedan a wuta a matsayin roommates.

Jinjina kai yayi kamin ya tattaro ya harhado tumbinsa ya Mike yaje ya rungume ta ta baya yace yanzu ne na ha? da macen data dace wacce bata tsoron ta baci indai saurinta zai cika gaskiya wannan jawabi naki ya kara sa min kaunarki a zuciyata.

Juyawa tayi tace Allah Alhaji na? Yace kwarai ma kuwa yanzu yadda zamuyi dasu Dan nima a shirye nake tsanani dai ace wuta za'a samu toh ni ALHAJI TUKUR GADON ?AYA na bada ticket din aljanna ta Dan in kuntata ma ahalin ALHAJI ABDULMAJEED UMAR. Dariya suka fashe dashi tace kaga mu hanzarta domin na koma gida daga nan suka shiga aikata ashararancin su.

WANENE ALHAJI TUKUR GADON KAYA? WANI ATTAJIRIN MAI KUDI NE WANDA SUKAYI TASHE TAREDA ABDULMAJEED WATO BABAN YAZEED INDA YAKE DAUKE DA MUGUN HASSADA MA ABDULMAJEED SABODA YA FISHI YIN NASARA.

DA FARI JEEDMAR A BAUCHI SUKE DA ZAMA TAKURAR DA TUKUR GADON KAYA YA MUSU YASA SUKA KOMA GOMBE NAN MA YA BISU,SUKA LULA ADAMAWA,YA BISU SUKAYI KANO, YA BISU SUKAYI, SOKOTO LOKACIN AN HAIFI YAZEED AMMA YA BISU NAN MA SAI SUKA KOMA ABUJA TOH ANAN NE SUKA ZAUNA NA SHEKARA 4 KAMIN YA SAKE BIYOSU SUKA KOMA KADUNA ANAN NE AKAYITA TA KARE TUNDA ABDULMAJEED DIN YA MUTU BA SHIKENAN BA? TOH ASHE

DAI BAI HAKURA BA GASHI KUMA YA SAMU WACCE TA FISHJ DAUKAN ZAFI LAMARIN SAI YADDA ALLAH YAYI.

Ina mai lallashin ku na rashin jina da kuka yi abubuwa ne suka Dan taso min da fatan za'a min uziri?

Shin me zaku iya cewa gameda batun Alhaji TUKUR GADON KAYA? Ya kuke ganin lamarin nan zai kaya a tsakanjn su ?

Shin

33 / 45