Author : Untichlobanty Category : Complete Novels
Kiran kawarta na tsohuwar makarantar kamin ayi Mata transfer da shike kawar a kano suke.
Tana dauka race Mata ta turo Mata da account number zata tura Mata kudin da za'a ciyar da mutane 20 na kwana uku Allah ya cika Mata burinta.
Kawar Ta ta me suna fati tace ke ko menene wannan buri naki kuma ni ince wa iyayena me? Zayya tace haba fati AI kin fini dabara zakisan abinda zaki fada musu. Kinga kudin da mikewa shi a hannu kenan zan turo miki Dan Allah kiyi min taimakon nan. Fati tace toh shikenan ai. Sannan sukayi sallama.
Shiryawa tayi ta fito har lokacin su minal suna zaune a parlour amma kabir yayi bacci an kaisa daki. Sim sim ta wuce ta dauka basu ganta ba . Ba tare da sun kalleta ba yazeed yace hajiya ina zuwa? Ji tayi kamar ta fashe da kuka Dan bataso sun lura da ita ba. Tsarewa tayi zata fice minal tace kina kara taku daya zan karye miki kafa.
Kukan shagwaba ta fara kamin ta koma dakinta ta fada gado tana kuka. Sahir ne ya shigo fuskar sa a tamke. Rigarsa ya cire ya dale gado baice Mata komai ba. Jin alamun kamar an shigo dakin yasa ta dago kallonsa tayi taga ya kwata ba tare da ya Mata magana ba. Kwafa tayi tace wato kai baka damu ba ma baccin yamma zakayi bayan ni ina nan ina fafatawar yadda zan haihu......
Datseta yayi ta hanyar cewa ke ni banason shirme ance miki haka ake haihuwar? Ko ma zaki haihun a wannan haukar zaki haihu? Ihu ta fasa masa harda bori. Dama nasan ba sona kake ba kawai saboda abbana yace ka aureni yasa ka aureni. Toh ta Allah ba taka ba ko dakai ko ba kai sai na haihu..... tana kaiwa nan ta shige ban daki tare face majina.
Sakan baki yayi yana kallon ta. Shi ya dauka da wasa take ashe de batasan me takeyi ba. Dariya ma ta bashi yace toh sannu fagal dole ma sai dani in ba haja ba sunan danki shege. Ihu ta kara kurmawa yace ke ni fito ki kawomin ruwa insha. Tace anki din....
Yazeed ne ya Kira sahir a waya yace kacewa matar ka idan na karajin giunta saina karya Mata kafafu.
Zama tayi a ban dakin tasha kukan ta koda ta fito har yayi bacci. Cire masa safa tayi ta wulla a kayan wanki tana fatan Allah ya karbi wannan aikin ya bata ciki Dan aikin alkhairi baya yawa baya kadan balle na miji?.
Har tsawon kwana uku kullum sai tayi kokarin fita amma sai an kamata hakan yasa ta Nemo numban malama AMINA (untichlobanty). Tana kira aiko taci sa'a ya shiga, sallama tayi kamin suka gaisa tace dama shawara ce take nema , yaya zatayi ta samu haihuwa? Malama tace maya da fari dai shi haihuwa nufi ne na Allah wato ba'ayi masa dole. Kyautace ya bawa Wanda yaso ya hana Wanda yaso bawai Dan baya sonka ba sai Dan ya gwada imaninka. Wasu sai suyita wahalar nema amma Allah bai basu ba. Wasu kuma basu nema ba sai Allah ya basu da ko wahalar renon ciki basu sha ba. Dan haka ki dage da addu'a sannan kije ke da me gidanki a duba ku domin tabbatar da lafiyar ku. Saide kuma muryanki batayi kama da na babbar Mata ba balle ace kundade babu haihuwa da har zaku fara nema. ku kara hakuri sannan..... kamin malama ta karashe zancenta layin ya tsinke kuma babu wata hujjan Dan ba rashin network bane ashe tabawa tayi da hannunta bata sani ba koda ta dake kira busy ake ce Mata dan haka ta hakura.
Tsalle ta daka tace ashe ashe shine sirrin da aka ki a fada mini wato dai wasu suna Haifa ne wasu kuma Allah ya basu ba tare da sunyi renon cikin ba wato ba tare da sunyi cikin bama. Ita ta dauka haka malama ke nufi batasan malama na nufin ba tare da ansha wahala ba ma Dan a tunanin ta babbar mace ce shiyasa batayi Mata fashin Bali ba.
Shiryawa tayi yauwa kamar kullum ta sansado ta fita aiko Allah ya bata sa'a babu Wanda ya ganta har tabar gidan taxi tahau tace a kaita inda ake samun yara. Shiru yayi sai yayi tunani ko orphanage gidan marayu take nufi . Sai ya kaita can tan saukowa kuwa ranan ana wani celebration Dan haka iyaye da yawa sunzo da yaran su manya da jarirai domin taya marayun murna.
Wata ta gani da ganyen jariri tace la wancan ma ta samu dan haka ta tare ta gaisawa sukayi tace Dan Allah ina kika samu dan nan? Matar tace ban gane ba lafiyar ku kuwa Dana ne.. wuceta tayi tana mamakin yadda shigewarta lafiya lafiya amma kamar tababbiya zayya kam tabe baki tayi tanajin dadi tayi wa yar uwarta wayo ba sai ta wahala ba ma zata samu da.
Haka tayita bin mutane tana musu tambayar mahaukata har aka samu wasu yarabawa suka biyota da gudu sanadiyyar daukan jaririn su da tayi a karkashin bishiya a tunaninta Allah ne ya aiko Mata nata. Har tuntube tayi ta gurde kafa.
A takaice de taci bakar wahala kamin ta dawo gida tayi lubus aiko ta samu anyi cirko cirko ana nemanta. Tana shigowa yazeed da tsumagiyarsa a hannu ya daga kamar zai tsula mata tsurewa tayi ta turo baki tare da kneel down ta fara kuka.
Zama sukayi yazeed yace maza yi bayani, hannu tayi ta fara ABBA Dan Allah kayi hakuri ni wallahi naji jiki na hakura da haihuwar ma tunda naga kowa ba so yake na haihu ba..... tsaro musu labarin tayi tundaga sanda ta dawo ta tarar sahla na da ciki har zuwa yanzu. Hajiyar zuciya yazeed ya sauke yace ba haihuwa bane banason kiyi, munson ki Haifa mana jikoki mana. Irin maganar nan ce ba ayinta gatsau kinji? Kuma wa yace miki tsinto da akeyi ? Ni wannan maganar ba hurumin bace idan kin kara girma zaki fahimta. Bazance nayi nadamar aure dake ba amma gaskiya akwai kura dariyar da sallah ke rikewa ne ya kuce tace ABBA dama kaima ka iya cewa akwai kura? Murmushi yayi yace me zai hanashi kuwa? Ai nima sanda naje matashi sissi kwaro ne ni. Dariya kowa yayi banda zayya da ta tashi sumul sumul ta haura dakinta. Minal ne tayiwa sahir ido alamun ya bita yana haurawa ita da zaliha suka tafa. Yazeed da luku sukace Mata da gulma. Yazeed ne ya kalli mashkur yace tuzuru wai bazakayi aure bane har ka mutu? Shafa gemunshi yayi yace kwantar da hakalinka AI a asibitin nan na kyallo nafeesa kanwar bushra da alamu da ita za'ayi yazeed yace yafi maka.?
Jamal ne suka shigo shi da zakiyya sundawo daga koyar tafiya Dan yanzu ta ajiye karfen koyan tafiyan. Jamal yace me akeyi babu mu naga ana raha kamin a amsa mishi wayar yazeed tahau ringing. Mom ce ke kira ya dauka tace Dan albarka kuzo ku yanzunnan kaida daughter mun Kira iyayenta ma akwai magana.
A hanzarce suka shirya zasu fice minal har zata kwankwasawa su zayya yazeed ya hanata janyo hannunta yayi yana Mata wani irin murmushi me kashe jiki . Mannata yayi da kirjinsa tare da shinshina wuyarta. Kunnenta ya Dan ciza sannan ya rada Mata bakyason jika ne? A hankali tace ina..so har tana mamakin yadda muryarta ya sarke lokaci daya. Yazeed yace ana making mana baby shine zaki datsesu? Bige kirjinsa tayi tace kai baka tsufa da wannan abun ne? shekara hamsin fa kake dosa Yar dariya yayi yace ji yadda muryanki ta? sauya tsaban mayata amma ni ake cemin bana tsufa ?? Handsome dani irin haka? Yanzu dai zo muje daki sai mu gani ko na tsufa.... tace kiran mom din fa? Yace ba matsala zai iya jira kinsan fa ya kamata muyiwa twins dinmu gambo. Dukan kirjinsa tayi a wasa ya dangwali hancinta
Luku ne yayi gyaran murya yace malamai akan tsakiyar beni kuke kuma har a makantar min da yaro. Kallon kabir da zaliha tasawa hannu ta rufewa ido sukayi yayin da yake kyallo ido daya yana gulma. Ganin takura tayi masa yawa yasa yace mummy ni ki barni menene ban gani ba dukda cewa ke da dad kuna fada wani lokacin ina kallonku idan muna parlour sai inyi kamar ina bacci. Ina gani kukeyi K.I.S.S yayi spelling musu. Minal da yazeed ne suka wuce suna fadin this one pass our level yayinda luku ya kalli zaliha yace tabbas na miki godiya da kikasa mukayi masa dakinsa daban tun yana shekaru 3. Dariya yayi yace da anji kunya ko daddy? Shiru lulu yayi kamin yace my boy ka dena itin wannan maganan babu kyau kaji jai karami ne babu kyau kaji? Yace okay daddy.
Bayan su yazeed yaron yayi kamin luku yace dole mu kara kiyayewa da alamu yaronnan yanada wayo. Wani likitan laifin iyaye ke sawa yaransu su baci. Murmushi tayi taja kamatunsa tace for the first time(a karo na farko) ka fadi magana wacce nayi amanna da ita babu musu.
A dakin su zayya kuwa.......
KU BIYONI A CHAPTER NA GABA KUMA CHAPTER NA KARSHE DOMIN JIN YADDA ZAMU KARE WANNAN LABARI MAI FARIN JININ NAKU WATO KURUCIYAR MINAL.? SHIN ZAYYA ZATAYI CIKIN KO YAYA ? ME YASA MOM KE NEMAN SU YAZEED? Ko ciki ne da ita? Cabdi........
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty ?
4th June, 2020.
?? *KURUCIYAR MINAL*??
? _By miss Untichlobanty_ ?
? *CHAPTER 98 (FINAL)*?
RECAP
Bayan su yazeed yaron yabi kamin luku yace dole mu kara kiyayewa da alamu yaronnan yanada wayo. Wani lokutan laifin iyaye ke sawa yaransu su baci. Murmushi tayi taja kamatunsa tace for the first time(a karo na farko) ka fadi magana wacce nayi amanna da ita babu musu.
CONTINUATION
A dakin su zayya kuwa sahir yana shiga ya fincikota yace ke wai wace iriyar yarinya ce? Ke bakiga cewa kin girma bane bazakiyi kiyi da sahla ba? Kuka ta fashe dashi tana Jan majina tace toh Dan Allah ni menene laifi na Dan nace inason haihuwa? Ba duk Kaine da lefi banda sanda nace muku haihuwa nakeso amma kujera min fada kaki la taimaka min mu samu da sai kace ni ba matar ka bane.
Dafe kai yayi San yanzu ya gane cewa zayya yarinyace sosai. Dafe kai yayi tare da sauke ajiyan zuciya murmushi ya Mata a hankali ya riko hannunta yayi pecking zaro ido tayi kunya ya rufe ta. Shikam ma dariya ta bashi amma ya rike zaunar da ita yayi anakin gado yace haihuwa kikeso ko? Ta daga kai yace toh zo in baki yana me daurata a cinya.
Bakin laffayar ta taja ta rufe fuska wai ita jin kunya a hankali tace kunya kikeji ta daga kai kamar doluwa. Kamin tana shan hannu idonta a kasa tace ni idan zayya tana kallon film me irin sumba rude idona nakeyi saboda ba kyau. Lakutar hancinta yayi yace AI ba barsa take kalla ba film ne shiyasa ta fiki wayewa. Rufe idonki yanzuma, rufewa tayi kiri daga nan labari ya canja salonsa......
Su yazeed kuwa suna isa suka tarar da kowa an dallara su ake jira. Bude taro da addu'a akayi sannan Alhaji mansur ya fara magana
Ba komai bane ya tara mu anan wajen sai wani abin mamaki da ya riske mu lokaci daya Wanda zaiyi ma wasu dadi wasu kuma bazaiyi musu ba.
Wato alokacin da aka gwada mu domin bawa bushra bargo munyi mugun mamakin yadda akace babu Wanda nashi ya hau da nata hakan yasa likitan a sirrance yayi mana gwanin DNA yayinda ake gwada na sauran yan uwa dukda ko ba'a tsammace ya hau ba.
Ga mamakin mu sai tahau Dana matar ka ya fadi haka yana kallon yazeed. Shiru kowa yayi yaci gaba da cewa ba abin mamaki bane Dan hakan zai iya faruwa amma anfi tsammanin ya dace Dana yan uwanka na jini.
Lokacin sakamakon DNA ta fito amma likita baima nina mana yayi ba saida yayi na kowa inda ya tabbatar mana babu shakku cewa bushra ba yar mu bace yar malam Yusuf ne mahaifin minal. Zaro ido kowa yayi ana kimanin ya haka ta kasance.
Yaci gaba da cewa na gasta ne duba da kamanceceniya da sukeyi sosai idan ba ka lura ba sai ka kasa banbanta su. Wanda run a fari naji mamaki .
Yanzu Abu daya nake son tabbatarwa kallon minal yayi yace shekarunki nawa tace 36 jinjina kai yayi yace rana da wata fa tace 2nd September.? Yace tabbas wannan ranan aka haifi bushra. Babu shakku ku yan biyu ne kuma yadda akayi kuka rabu Allah shine masanin.? Fatan mu Allah ya hada kanku.
Baban kowa ne yayi godiya bayan sallama yace toh tunda ta tabbata yata ce amma ku kuka rikota ni bazan harbeta ba na bar muku Abu daya de za'ayi dole abi ka'idar manzon Allah ta canja sunan mahaifi amma nikam na bar muku ita tunda har tayi aure ma ba anfanin na karba.
Godiya Alhaji mansur yayi daga nan aka dan jajanta mutuwar safina kamin kowa ya warware. Inna da tsufa ya fara kamata Dan ta dara shekaru? hamsin da biyar tace tace ina kishiyar tawa ne akace hajiya zayya AI gida muka barota tana wani aiki. Tace Allah yasa na arziki ne ba shirme ba. Kallon kallo sukayi sukace ameen.
Bayan watanni sahla ta sambado baby girl dinta amma CS aka Mata. Har ta fara zama zayya ta haifo yan biyunta mace da namiji.
Ranan suna bakin kabir har kunne hotonta ake dauka shida yaja gefe ya tsaya sanda aka gama mai hoto zai tafi yace mai hoto a dakata. Tsayawa mai hotan yayi yayinda hankalin kowa? ya dawo kansa dogon kujera? ya zauna yana gyara link dinsa ya zaunar da yar sahla a gefensa sannan ya karbo jinjirar ya daura a cinya. Yace kai me hoto ka daukeki nida Matana sannan ka yi mana irin rantamemen hotan nan domin acan za'a lika.
Daya...biyu... uku aka watsa hotan yana me washe wawulonsa yayinda hular nan tayi coroi a tsakiyar ka.
Yace SHEGE NI ME MATA BIYU kowa ya fashe da dariya ??
ALHAMDULILLAH! ANAN NA KAWAO KARSHEN WANNAN LITTAFI NAWA MAI FARIN JINI DA ALBARKA DA FATAN AN ILMANTU KUMA AN NISHADAN TU.
IDAN HAR KUKAYI COMMENTS MASU MUGUN ZAFI TOH INADA WANI GAJEREN LABARI DA ZAN BAKU ME CHAPTER KASA DA GOMA. SUNANSA (YARINYAR CE TAYI MIN FYADE) DAGA NAN SAI IN SAKO MUKU SABON LABARI MAI SUNA (DAN RAININ WAYO)
AMMA FA IN BABU VOTES DA COMMENTS TO SHIKENAN SAI IN HUTA KAMIN IN FARA DAN RAININ WAYON BA TARE DA NAYI GAJEREN LABARIN BA.
DAN HAKA AFITO KWAI DA KWARKWATA AYI MA KURUCIYAR MINAL BAKWANA.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
miss untichlobanty ?
6th June,2020.