Advertisements
Chapter 26 Reading Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kuruciya Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Untichlobanty Category :  Complete Novels

Chapter   26 / 45

75K to 78K   out of 134.5K words

ma kallon wajen yayi abin Kamar tafi basuga sanda ya tashi ba balle yahau sama. Tace baki jamal yayi yace kika bibiya yaje ya damu yar mutane ne amma mu Duba jikinta zamuyi ance batada lafiya. Mom tace kaide ka Shiga uku,Ni babu ruwana.

Abinda basu saniba kuwa mom tana fara maganan abinci yazeed ya mike da Sauri Kamar zai tashi sama ya nufi dinning ya dau plate ya ajiye a gabansa tare da rike suka da fork su mom kawai yake kira.

Mom Suna shigowa ya sauke ajiyan ajiyan zuciya mom tace yazeed?maza ara huna(me nake gani anan) Yunwarce? Daga yanda take magana zakaji tsuran mamaki a muryarta.

Washe baki yazeed yayi ba tare da yayi magana ba. Yazeed yace bari in kira su tala suyi serving mom tace bari kawai zanyi kasan a can bana motsa jiki kwata kwata.

Bude flasks din tayi taga alala tace yanzu ne gida ya zama gida. Sauko gida daya tayi sawa Jamal sannan ta saka masa sauce yayinda jamal ke fadin Gaskiya amarya ta iya reno mom kin lura da yadda wannan abin yayi kina kuwa?yazeed yace nine Abu?mom tace zaku fara kenan ko? Su kace sorry a tare. Kwalli biyu tasa a plate dinta sannan ta rude flask din Sauri yazeed yayi ya riko hannunta yace mom ban gan ganeba. Tace kamarya ?yace nifa? Tace kai me yace abincin....

Jamal Wanda ya kurbi kunu sanda ya kware yana tari yace WHAT? Abincinnan zakaci alala ne fa. Yace babu ruwanka. Mom Kamar an zuba mata ruwa a jiki ta bude ta yanko rabi'u tasaka masa.

Murmushi yayi ya karbi serving spoon din ya zaunar da ita.

Gida 4 ya zuba tunda na gwangwami ne. Mom batasan sanda cokalin ta ya fadi ba.

Adan tsorace ta taba goshin sa amma lafiya lau yake shikam jamal dama ya bar Komai ya ninke yana binsu da idanu.

Murmushi yazeed yayi yace sweetheart zauna lafiya na kalau.

Zama tayi ta fara cin abincin Adan tsorace yazeed ya cika mug dinsa da kunu sannan ya fara harba loma kan kace me ya tada alale guda 2.

Sanda ya cinye Tass ya shanye kununsa ya kalli su mom yaga Jamal ko canja position dinshi baiyiba balle yaci abincin mom ko tayi tagumi ta saki baki.

Knocking table din yayi聽 mom sai alokacin ta lura da tagumin da tayi gira ya Daga musu alamar yadai ?

Mom ta girgiza kai yayinda Jamal yafi gaba dacin abincinsa.

Shikam yazeed alale guda 2 ya dauka ya nufi dakin minal domin ya tasheta taci abinci dukda sama allurar da akayi mata ba'a bukatan aci abinci.

馃尮馃崁馃尮馃崁馃尮馃崁

Zakiyya ko kuka take rizga sosai sahir yace ki rabu dasu momy Daga yau bazan kara kula brother safwan ba. Girgiza kai zakiyya tayi tace don't say that kaji he is your brother I will talk to him okay? Yace Okay. But...... Tace no buts.

馃尮馃崁馃尮馃崁............

Zaune take kan kujera ta mimmike kafafu wayanta akan kunnanta tace GET READY FOR THE NEXT PLAN....

WAITING FOR YOUR COMMENTS馃憗馃憗



Bari naga comment din waye yafi dadi in masa kyauta me girma.....

Takuce karamarsu babbarsu miss untho...

*my apology FANS bana celebrating new year so karkuce ban muku wish ba.*

mzz_untichlobanty馃挄

1 January, 2020.

*??KURUCIYAR MINAL??*

?by miss untichlobanty

?

*?CHAPTER 61?*

Make sure kunyishi ba tareda wani kuskure ba!

Ta dayan Abangaren akace yes ma an gama.

??

Ayush ne ta Shiga dakin zakiyya tace sister zakiyya tace yes kina bukatan wani Abu ne?

Still idonta Adan kumbure. Kamo hannun zakiyya ayush din tayi ta zaunar da ita a bakin gado tace sis nikam tunani na zauna Nayi naga Cewa tunda dai kishiyarki ta rusa miki gida nima an kwacemin saurayi why not muje mu nemi taimako.

Zakiyya tace taimako kuma? Wani irin taimako ? Gyara zama ayush tayi tace akwai wata kawata tacemin akwai wani malami aikinsa Kamar yankan wuka. Indai kikaje wajensa Toh matsalarki tazo karshe ga aikinsa babu wani tsada kuma ance.....

Zakiyya tace dakata! dakata!! dakata!!! Ke yanzu da ilminki da wayewarki zaki dinga yarda da irin abubuwannan ?kuma wa yace miki malamine? Boka ne shi babu wani malanta fakewa kawai yake a inuwar malantaka.

Yanzu ke akan abin duniya kikeson Nayi shirka? Toh bankai nan ba bari kiji tun wuri gara ki cire wannan Abu a ranki ku ko a modern way ai that is madness ba class dinki bane please! Use your sense duk macuta ne malamannan.

Ajiyan zuciya ayush ta sauke tace kuma fa Gaskiya kike fadamin da na kusa In tafka babban kuskure amma na gode da kika fada min Gaskiya Allah ya saka da alkhairi.

Shafa kanta zakiyya tayi tace what are sisters for?Idan ban fada ma little sis dina Gaskiya ba wa zan Fadawa ? Dariya ayush tayi tace am not that little fah. Shekaru nawa ma kika bani ko 9 bai kai bafa.

Dungure kanta zakiyya tayi tace munji dai na girmekin Ashe.

Dan abin tausayi ayush Tayi tace sis Dan Allah Kuban key din motanki inaso inje in siyo wani abu. Zakiyya tace ki bayar a siyo miki mana yaushe muka iso garin ai akwai gajiya. Ayush tace abin is a little bit private kinga ne ai? Zakiyya tace okay bari in canja kaya muje tare mana nima dama inason inje shopping ayush tace yanzu fa kikace akwai hajiya ki bari gone sai mu fita ko? Zakiyya tace to kije dasu sahir mana kinsan birthday din sahir ya kusa he will be six years next month. Ayush tace nima ba dadewa zanyiba, gobe ba sai muyi Komai da Komai ba?

Zakiyya tace okay ba matsala amma karki Dade fa.

Ayush tace okay na wuce Toh saina dawo.

Fita tayi tana tafiya tadan kunna waka tana gyada kai abinta tana rausaya wa. Birki ta taka taji shiru kara takawa tayi still taji shiru ihu ta fara yi yayinda Motan ya fara kobo da ita akan titi.

Bata ankare ba motanta ya Shiga kasan wani trailer.

Mutane ne suka cika wajen makil ga hasken rana ya dallo wal bari yayi zafi Motan da ayush ke ciki bazaka dauka mutum zai fita ba saboda yanda Motan yayi raga raga ga ayush kwance agefe cikin jini atake akayi asibiti da ita.

Wayanta wani ya dauka wayar ma tayi raga raga. Cire sim din yayi yasa a wayarsa sweet sis ya gani Dan haka ya kira

Zakiyya zaune akan gado tana sulhu tsakanin sahir da safwan Cewa Idan suka raba Kansu kowa zai iya Shiga tsakanin su Wayanta yayi ringing ganin ayush ne yasa ta dauka da yar fara'arta amma labari da ya risketa shi ya gigitata tana kasa yin Komai.

Tashi tayi a zabure ta fice ta zauna dabas a parlour Kamar yar bori ta Cire wig dinma Ashe tanada gashi ba laifi rashin godiya wa Allah yasa ta yin karu ihu ta fara yi

Waiyo Allah na,na Shiga uku!YAZEED ka taimakamin yar mutane shikenan ta mutu !ta mutu waiyo ni Allah na.

????????

Yazeed zaune a gefen minal fuskannan babu alamun wasa hannunsa rikeda takalmi. Minal ma fuskannan babu fara'a sai zunburo baki take Wai saboda dance taci abinci kamin yaje wajen mom Idan ba haka ba tasha takalmi.

Ihu suka fara jiyo sama sama yazeed ya ajiye takalmin ya nufi kofa yana farin wannan Kamar muryan zakiyya minal ma dauko sandan ta tayi tana fadin aiko itace.

Harara yazeed ya aika mata yace Koma ki zauna. Tace Allah sai na bika ganin Idan ya tsaya fada da ita zai bata lokaci yasa ya ficewar sa.

Zakiyya suka riska sai ihu take duk ta birkice. Durkusawa yayi a gefenta a tsorace dan bai gaba ganinta a irin yanayinnan ba yace menene? Sweetheart me ya faru? Menene?

Kuka taci gaba dayi tana farin shikenan an kashemin ita an kashemin ayush. Ta mutu ! Ta mutu

Yazeed yace what? Me ya same ta? Tana...tana asibiti trailer ya taketa.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ne ya kacame parlourn domin mom da Jamal ma sun fito.

Atake suka dunguma suka nufi asibiti

Koda suka isa su sahir da safwan sun jigata saboda kuka nan suka nemi Inda take akace ai har anshiga theatre da ita domin har Yan sanda sun gama aikinsu.

Zakiyya muryanta har ya fara dashewa ta fara ganin bibbiyu.

Ta zama abin tausayi idonta sun kumburo. Minal matsowa kusa da ita tayi da Dan crutches dinta ta dafa kafadarta tace Kiyi hakuri aunty zakiyya Insha Allah zata warke. Zata tashi Kiyi hakuri.

Office din likitan suka dunguma sukayi. Bayan sun shigo likitan yace ma yazeed menene alakar ka da patient ? Yace shi yayanta ne doctor din yace okay amma nikam Kamar Kaine captain yazeed ko?

Yazeed yace yeah nine Dan Allah ka fada mana halin da take ciki ajiyan zuciya ya sauke yace a Gaskiya ikon Allah ne yasa ta rayu domin kuwa a irin ciwon da taji ba'a magana yanzu de she is out of danger amma she is in coma sannan jini ya Shiga kwakwalwarta dukda Mun Cire there is possibility zata manta wasu abubuwa or zata iya samun recognition disorder.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine abinda suke furtawa.

Daga kafadan yazeed minal tayi tace tace Allah ya nasu lafiya karku damu zata warke. Amma Dan Allah inada tambaya.

Kallonta sukayi dukkansu alamun sunaji tace kowa daga wani Abu ya sameshi sai a ce ya Shiga coma yanzu mutum uku Suna coma Wai coma dinnan menene.

Likitanne yace coma wani yanayi da mutum yake Shiga Wanda yayinda wani shock ya samesa ko yayi hatsari psychological issue ne which is cause by a traumatic event.

Minal gyada kai tayi bawai Dan ta gane ba. Wayar yazeed ne ya fara ringing. Dr Mashkur ke kiransa hakan yasa ya dauka tareda sallama.

Amsawa Mashkur din yayi yazeed yace harka iso kenan?Mashkur yace da izinin Allah gani a kasata kuma a garin Kaduna.

Yazeed yace masha Allah Toh gamunan zuwa saide wani hanzari ba gudu ba ka samu extra patient. Mashkur yace oh shit ! Buddy kar abin yayi yawa mana har 3 patients.

Yazeed yace aikinka ne ai so....

Mashkur yace of course what am I here for?

Sallama sukayi yazeed yace zan kawo maka surprise. Mashkur yace and explain why na jika so sad not as cheerful as you use to be.

Dafa zakiyya yazeed yayi yace sweet zamuje dauko Mashkur kinji karkisa damuwa a ranki Insha Allah zata tashi.

Riko hannun minal yazeed yayi tareda yiwa lukman ido alamun muje ko?

...............

Mashkur ne ya fito Daga departures door a airport din Inda ya hango yazeed yana Daga masa hannu.

Runguman juna sukayi sannan suka kashe. Mashkur yace buddy irin wannan kyau Wai miye sirrine?

Yazeed yace tsaya nan gauranci ya kasheka. Lukman yace koni nan da ka ganni da aurena yanzu.

Yazeed yace wannan auran maka dashi da babu ai kusan daya. Lukman yace haka kace?yazeed yace kwarai ma kuwa Idan ba haka ba gobe muga amarya a dakinta tunda an gama Komai.

Lukman yace is that a challenge? Yazeed of course is a challenge.

Shaking Hannu sukayi yazeed lukman yace challenge accepted.

Mashkur ne yace kudai gaskiya bakuda kirki yanzu ace duk kun? yi aure babu gayyata? Sukace sorry man abunne yazo a murde.

Tsuguna minal tayi tace ina wuni. Sai a lokacin Mashkur ya lura da ita domin ta labe a bayan yazeed sai tsilla ido take. Yo tazo airport bata tana ganin jirgin sama ba sai a TV ko photo.

Baki Mashkur ya saka yana Kate mata kallon kamin yace Masha Allah tabarakallah.

Buddy wannan surprise din yayi kace kai ka tanadomin. Shine baka taba fadamin Kanada kanwa zukekiya irin wannan ba? Yazeed yace kai bawan Allah Dan yanzu ba wani buddy wannan da kake gani matata ce.

Mashkur yace matarka? Yace yup itace amaryar tawa ai.

Date saitin zuciyarsa yayi yace amma kaide baka kyautawa wallahi ya zakayi ta aure kyawawan to ni in auri me?

Finciko shi lukman yayi tare da yin tsaki ya dannashi a mota yace ni wuce mu tafi Dan Allah mutum sai surutu halinku daya da Jamal.

Gida suka nufa suka bawa Mashkur masauki yaci su abinci sai Santi yake yana kurba kunu. Daura minal yazeed yayi a cinyarsa sannan ya rada mata a kunne baby anjima da daddare kiyimin pancake. Murmushi tayi tace me yasa sai da daddare. Yace saboda banason kowa yaci. Ahankali sosai tace marowaci yace naji fa. Ta ai na manta Ashe kunnen aljanu gareka. Hancinta ya Dan gwala yace ke dinnan ko.

Tsaki lukman yaja yayinda Jamal yace please Ku nemi daki ka wani kakabe yar mutane a cinya yazeed yace yar mutane kuma matata ko ba haka bane baby? Daga kai tayi tana rufe fuska.

Yazeed yayi pecking dinta Mashkur Yace ni ban kalli wannan scene din ba yayindalukman yace son Allah ka bari kana sa yar mutane jin kunya.

Daukanta yayi in bridal style yace naga alamu duk kishi ke damunku sannan yayi gaba abinsa.

Toh me kuma kikeso ki karanta bayan chaptern ya kare??

Su o o karkiyi kuka ai zan sakeyin update.

Karku manta kuyi Sharing and commenting.

Takuce a kullum karamarsu babbarsu mai jama'a

Miss untichlobanty?

6th January, 2020

*??KURUCIYAR MINAL ??*

*?BY MISS UNTICHLOBANTY?*

*?CHAPTER 62?*

Laila zaune a dakin da aka kwantar da ummi tana karanta wasikar jaki yadda Komai ke faruwa cikin gaggawa har zuciyanta ya saba da damuwa yanzu ya zama normal taga hannun ummi na motsi da Sauri ta matso kusa da ita tare da dafa hannunta tana hamdala kamin ta fara fading ummi?

A hankali ummi ta bude idonta tun bata gani har Komai ya wartsake mata murmushi ta sakarwa Laila a gajiye da gudu lailan ta fice sannan ta nufi room din da doctors din jeedmar family suke domin an ware ward musamman jeedmar patients kawai ake kwantarwa.

A gaggauce doctor Muhammad yazo yayi attending ummi Inda yayi hamdala. Tambayanta yayi ko akwai wata matsala ta girgiza kai alamun babu yace ko zata iya iya tashi tayi tafiya ? Mikewa tayi da taimakon Laila jiri yadan dibeta,sannan tadan taka da alamu dai babu batun paralyse bude baki tayi tanason tace a bata ruwa. Taci dib! Ta sake gwadawa same thing hankalinta a tashe ta tunawa Dr Muhammad bazata iya magana yace wannan ba wata matsala bace within 2 months or less than that zata fara magana Insha Allah.

Kiran yazeed yayi ya sanar dashi ummie ta farka amma tayi loosing voice dinta temporarily, bazata iya magana ba.

Hamdala yazeed dake kwance akan cinyar minal yana bata labarin Mashkur yayi yace Toh ai haka akeso gamunan zuwa asibitin dama ina planning ayi transfer din Aisha cousin din zakiya zuwa hospital dinmu saboda wancan is a public hospital ba kayan aiki sosai Nasan abin gwamnati though gwamnatin mu yanzu tana kokari sosai. Doctor Muhammad yace hakane Allah dai ya taimaka shugaban kasan mu ya kuma? kare beloved country Nigeria. Allah ya rabata da corruption and corrupted people yazeed yace Ameen ai aikin da muketa kokarinyi kenan kasan wani zubin ba laifin manyan bane na kasa damu dinne though ba duka aka taru aka zama daya ba kuma akwai wasu manyan Wanda suka sunada laifinsu saide gyaran Allah. Harkan tsaro ma Muna daidai kokarinmu matsala rashin hadin kai ne.

Dr Muhammad yace hakane yazeed yace bari gamunan zuwa amma zamu biya ta dayan hospital dincan sai muga yana za'ayi transfer din aishan ko?? Dr yace okay.

Kallon minal yayi wacce take kallonsa da alamu tana jiran karun bayani though ta fahimci abinda ya wakana confirmation take jira. Gyada kai yayi kamina ya mike ya zauna yana gyara gray T-shirt dinsa .

Gani yayi minal ta tsaya tana kallonsa tana murmushi yace lafiya dai ko? Matsowa tayi ta dale cinyarsa shide kallonta yake ga mamakinsa yaga ta riko fuskarsa da hannuwanta guda biyu sannan a hankali ta hade goshinsu.

Wani irin yanayi suka fara Shiga dukkansu biyu kamin ahankali minal ta rude gap din dake tsakanin bakinsu.

Firgigit yayi ya dawo Daga tunanin daya Shiga sanadin zama da minal tayi a cinyarsa? tana jijjigasa cikin yanayin da yara Yan naci ke magana tana fadin yazzy baby tashi mu tafi mana tsaki yaja saboda haushin datse masa tunani da tayi.

Matso da fuskar nata ta farayi kusa dashi Kamar yadda ya gani a daydream dinsa. Goshinsu ta hada tana masa murmushi yayinda ya rufe idonsa yana jira yaji lips dinta kan nashi saide kash booo! Tace yadda yara keyi Idan zasu tsoratar da mutum kamin ta kwasa a guje.

Jagwal fuska yazeed yayi Kamar zaiyi kuka yace you are such a fool to believe that she will kiss you.

Why?why? Wai ita Komai saina koya mata ne? I should have known since from the beginning that this will happen.

Kwalla mata kira yayi yace you better hurry up ! tace yes boss yazzy baby.

Gurnani yayi yace not this name again. At least kan ba kwando bane.

Fita yayi ya sanar dasu Jamal improvement da aka samu aiko sunji dadi daganan yace su Shirya yanzu zasu fice. Mashkur yace ba Inda zani Daga isowa. Yazeed yace ai haka isa ba ka wuce kawai mu tafi. Dan dole Badan yaso ba ya tashi yana fadin Allah kamin nabar kasarnan ka samomin mata Kamar amaryarka. Hararansa yazeed yayi yace Allah ka dauke idonka akan matata. Hade Hannu Mashkur yayi yace sorry ubale (sarcastically= cikin gatse).

Dai dai lokacin minal ta fito tana fadin yazzy baby yanzu inna suka dawo kuma sunce direct asibiti zasu su Duba jikin ummi dayake Suna Dan dasawa kuma tace zata taho da mutuniyar.

Yace aiya nalama khadijatu ba dama ai kinsan mutuniyata ce sosai. Muje ko jin shiru abokan NASA basu amsa mishi ba yasa ya juyo ya kallesu aiko suka sheke da dariyar shekiyanci kamin suka hada baki wajen Cewa YAZZY BABY???? dariya suka kuma fashewa dashi harda rike ciki. Kicin kicin yayi da ido yana kallon minal atake ta make kafada tare da fadin ba laifina bane sabo ne.

Tsaki yaja ya hade rai kamin ya fice Dan

26 / 45