Author : adama umar Secret Pen Category : Complete Novels
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
STORY &WRITEN
BY
ADAMA UMAR
SECRET PEN
07081940768
LOVE AND ROMANTIC STORY
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
1
1️⃣
PAGE ONE
Zaune suke a falon kuna ganinsu kunsan suna tattauna abu mai mahimmanci ,yatsunra
yana sarke a cikin na yar uwarta ta sake kallonta ta ce
Dan.Allah Hafsat ki amince da buƙata ta dan Allah bamuda wata mafita da yawuce haka
babu abunda zamuyi mu goge lqifinmu a gareki saita wannan hanya pls ki taimaka
Kwarai Hafsat abunda zuwaira take faɗa miki gaskiya ne na roƙeki nima gani na
durkushe akan guiwowina dan Allah ki amince da buƙatar mu
Fisge hannunta tayi daga yatsun yar uwartata sannan ta dauki jakarta ta kallesu
kawai ta fita a gidan cikin hanzari sunanta suke kira amma ina ko juyowa batayi ba
balle kuma ta sauraresu ,kallon zuwaira yayi ya ce
Mucigaba da jarrabawa insha Allah wataran zata amince kinsan sai mun mata uzuri
yanzu tana cikin wani hali ,harna rasa da wacce irin fuska zan kalli hafsat
wlh ,amma mucigaba da kokartawa insha Allah wataran zata amince
Hawayen dake zuba daga fuskarta ta goge ta ce
Haba hafsat kibani dama kibani dama mana mu goge babban tabon da muka miki ,ki
amince mu cireki a cikin kuncin da kike ciki da bakin ciki
Tafaɗa tana kqra rushewq da kuka
Rungumota jikinsa yayi yana ban baki .
A banagaren hafsat kuwa Allah ne kawai ya kaita gida lafiya tana zuwq tayi park na
motarta sannan ta fito ta nufi ciki gida ,tana shigowa ta hadu da amminta tana
zaune tana karatuna alquran ta zare glass ɗin idonta ta kalleta ta ce
Wai hafsa lafiyarki kuwa ,gaba ɗaya yanayinki ya sanja wai me yake damun kine
Kwanciya tayi a kafadun wannan dattijuwa kana ganinta kasan mahaifiyartace ta ce
Wlh ammi na rasa ya zanyi dq zuwaira gaba day tasani a gaba akan wannan kudiri na
ta nikuma nama rasa ta ina zan fara amincewa kai bazan ma faraba domin wlh ita da
kanta zatayi nadamar faruwar wannan kudiri nata
Ajiyar zuciya Ammi tayi ta ce
Gaskiya Hafsat bazan boye miki ba ,kinsan nidai mahaifiyar kice ,bazan baki
shawarar da bata gari ba ,a ganinq kuma a abunda ya dace ni kaina ina mai baki
shawarar da ki amince da bukatar zuwaira da mijinta wannan itace mafita a gareki
Zubur ta tashi daga kan kafaɗarta ta kalleta Ta fara magana
Haba Ammi kema haka zaki fada,yanzu kina daya daga cikin mutanen da zasu goyi bqyan
wannan lamari ,gaskiya Ammi tunda kince shawara ba umarni ba gaskiya bazan yadda da
wannan kudirin ba .
Tanq gamq faɗar haka tq tashi da hanzari ta haura sama ,Ammi tq maida glass ɗinta
tq ce
Yaro yarone Allah ya ganar dake kamqn yadda ya nunqmun faidar hakan .
Yau tana da lecture around 8:00 shiyasa ta tashi ta shirya da wuri ko break batayi
ba haka tayiwq Ammi bankwana ta fita tana zuwa makaranta ta nufi hall taji ankira
sunanta a hankali ta juyo ta kalli me siran sunan ta ,dafe goshinta tayi ganin
zuwairace ta kira sunanta ,agogon hannu ta ta kalla taga batada lokqcin bqtawa
aikuwa ta wuce ta shiga hall ɗin batare da ta tsaya ba,wuri ta nema ta zauna tana
jiran su gama lecture ta fito suyi magana don yau babu wanda zai rabata da hafsat
matikar bata amince da kudirinta ba ,To abangaren Hafsat ma haka gaba daya tinani
ta tsaya yi akan maganganun da ake mata ita gaba ɗaya kanta ya kulle kuma
kwakwalwarta ta toshe bata hango abunda ake faɗa ba ganin tinanin bqzai kaita ko
inaba shiyasa ta kwatsar da zancen ta maida hankali akan karatunta ,gqba daya
lecture ta dau zafi shiyasa gaba ɗaya a gajiye ta fito amma me tana fitowa tayi
karo da zuwaira tana jiranta kallonta takeyi kafun tai magana ta kariso inda take
ta ce
Dan Allah Hafsat bazan gajiya ba bazan karaya ba sannan bazan haura ba matikar baki
yadda da kudirna ba ,mena miki meyasa cike tsanata kumq kike ƙyamata ,shin guduna
kikeyi
Ohooo haba zuwqirq meya kawo maganar nan da zakice ina kyamqrki yaushe mukayi dake
inq gudunki kawai don naki amincewa da kudurinki shiyasa zaki yanke mun danyen
hukunci haka gaskiya kiyu hakuri ,karki manta yadda muka taso dake tamkar yan uwa
kudubq irin shakuwa da kaunar dake tsakaninmu kisani inaso ya daure harga
yayanmu ,amma ki sani matikar kudirinki ya cika zai iya zama sanadiyar tarwatsewar
muamalarmu ,hakan zai dawo gaba mai tsanani a tsakaninmu kuma harga yayanmu ,inqso
ki bari Allah ya zaɓamun duk abunda ya dace dani a rayuwata dan Allah karkiyiwa
Alla shishigi
Shiru tayi gaba dayata rasa me zata faɗawa kawartata hakan yasa ta fashe da kuka ta
ce
Da kinsan alkhairin da nake hangowa da baki faɗi wannan zantuttuka ba
Shin wani irin alkhairi kika hango wanda ni nakasa hangowa pls allow me to rest
banason damuwa
Bata jira me zatace ba ta nufi parking space tashiga motarta tayi gidq ,jiki a
sanyaye zuwaira tabar makarantar tana nazqrin shin taya zata fara bullowa da kawar
tata ta amince da ita .
Tana zuwa gida bata tsaya bata lokaiba ta wuce daining domin wata azababbiyar yunwa
da take damunta serving ɗin kanta ta fara sanna tafara cin abincinta hannu baka
hannu kwarya ,tana cin qbinci sai hoton lokqcin rayuwarta ta baya ya fara dawo mata
,tana tina yadda ta kasance da walwala da nishaɗi da farin ciki amma yanzu ya zama
tarihi ,ture abincij tayi domin saitaji duk abincin ya ginsheta ,tashi tayi ta nufi
dakinta ta ajiye hakarta ta kalli wayarta na ƙara ,dauka ta duba tsaki tayi ganin
sunan my besty ya bayyana ɓaro ɓaro ,jifa da wayar tayi akan gadon kafun ta fara
rage kayan jikinta ta faɗa bandaki ,tana shiga ta tsaya kallon kanta a madubi tana
duba shin ta kara ƙiba kota rage shin tumbinta ya karu koya ragu wannan ta kasance
dabiarta ce saida ta gama karewa jikinta kallo sannan ta fara wankan ,tana gamawa
ta fito daure da alwala ta dauko wata doguwar riga ta zura ta tada Sallah ,tana
tayar da sallah saiga Ammi ta shigo da waya a hannunta ,kara wayar tayi a kunnenta
ta ce
Ayyah zuwaira sallah take shiyasa bata ɗaga kiranki ba amma idan ta idar zan hadaku
Shikenan Ammin na gode
Saida ta idar da sallah sannan tai afduointa ta shafa tasawa kofarta kry ta kwanta
a lafiyayyen gadonta tana kulle idonta tana sauraron bugun xuviyarta da alama bacci
takeso ya dauketa ,wayarta ce ta fara ruri da alamar neman agaji tsaki tayi kibata
duba ba tasan wace me kira shiyasa ta dauko wayartasata a silent ta maids kanta ta
kwanta har bacci ya dauketa .
Ba ita ta farka ba sai misalin ƙarfe 3:00 na rana aikuwa a gurguje ta tashi tayi
wanka Hafsat kenan sarkin tsafta haka take kaman wata agwagwa.kullum cikin wanka
take ,bata fitoba saida ta dauro alwala sannan tafito ta shirya ta nufi falo ,tqna
fita ta tarar da Ammi tadan mike kan sofer maakaciyarsu nanna tana mata tausa
karisowa tayi ta rungume Ammin ta ce
Kai ammi yau nasha wahala gaskiya shiyasa dana dawo ban nemiki ba
Na sani kuma naje dakinki a rufe nasan bacci kike abunda nakeso dake ki tashi ki
dauko mayafinki inaso ki kaini anguwa
Shikenan Ammi amma bazamu jirq mu gabatar da sallar laasar ba saimu fita
Shikenan bari inje indauro alwala saura minti 5
Tashi tayi ta nufi dakinta ,kallon.Nanna tayi.macece mai dan shekaru don a ƙalla
zatakai shekara 40 gashi tanada nitsuwa ga ilimi ita kanta tashi tayi taga Ammi da
Nanna domin batai aure bama me gadin gidan aka aura mata sannan ya rasu ya tafi ya
barta da yaro daya tilo dagananbata sake aure ba ko zancen aure Ammin tayi tayi
harta gaji ,ajiyar zuciya tayi tace
Nanna dan akwai abunda nakeso in tambayeki kinga.dai ke babbace watakil kema ki
hango abunda na kasa hangowa
Jinjina kai tayi ta ce
Ina jinki hafsatu
Kaman yadda kika sani Zuwaira ƙawata tace kuma...
Kiran sallah ne ya katseta ta ce.
Kibari hjy nanna idan muka.dawo nida Ammi zanzo har dakinki inbaki labari bari inje
inyi sallah
Shikenan to Allah ya dawo daku lafiya
Tafaɗa tana mikewa itama ta.nufi dakinta ,bayan sun idar da sallah kowacce ta fito
da shirin fita sannan suka shiga mota suka fita a gidan ,suna ciki tafiya Hafsat ta
kalli Ammi ta ce
Ammi wai ina zamuje ne sai tafiya mukeyi
Murmushi ammi tayi ta ce
Gidan zuwaira.
Fuskarta babu alamar wasa ,hakqn yasa Hafsat tadan haɗe rai ta cigaba
da.drinving,dede kofar gidan taja tai parking Ammi ta kalleta ta ce
Me kike nufi kina nufin bazaki shiga ciki bane kome
Gaskiya Ammi ni bazani ba.kije ki kawa...
Bata karisaba.kawai taji saukar mari kan kuncinta ta dafe.ta juyo a mamakance tana
kallon Ammi.
Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
STORY &WRITEN
BY
ADAMA UMAR
SECRET PEN
07081940768
LOVE AND ROMANTIC STORY
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
2️⃣
PAGE TWO
tabbas Ammi tana.wasa da yara amma tanada zafi.kuma ga zuciya macece tsayayya akan
yayanta duk da ta.kasance ita ta rainesu amma hakan baisa tarbiyyarsu ta
lalaceba ,batayi magana ba ta buɗe marfin motar ta fita aikuwa Hafsat ta rufa mata
baya domin taga babu alamar wasa alamarin Ammi .
Zaune suke a falon dukkansu suna kan rug itq kuma Ammi tana kan kujera ta gyara
glass ɗinta ta fara magana kamar haka
Wato Abdulmallik komai ya faru mu daukeshi mu kaddarine daga Allah dan adam bazai
taɓa maka qbunda Allah bai maka ba ,mu sani komai ya faru a cikin duniyar nan dama
alƙalami ya rigada ya rubutashi don haka komai ya samemu karmuce wane ne ya
mana ,Allah ne kawai yake iya yin yadda yaso da bawa saidai wani ya zama
sila ,wanda shima a sanadiyar wannan silan zai gane ya shiga wata jarrabawa
ce ,kusani dukkan mu musulmaine don haka bazamu taaya ɓatawa kanmu lokaciba mu
yafewa juna komai ya faru ya wuce har abada banason daya daga cikinku ya kara
kallon dan uwansa da abunda ya faru ,kuma naju dadin hukuncin da zuwaira kika yanke
hakan ya nuna kinada kaifin tinani don haka inaso dukkanmu mu taru.mu rufawa juna
asiri abun mun nan yazamana tuwona maina
Tunda ta fara magana Hafsat take hawaye tasan ba wani abu Ammi take ba.illa ta
yarda ta amince da Abdulmallik amma anya zata iya aurensa kuwa shin dawani ido
zatana kallonsa tabon daya mata bazai taɓa gogewa ba don haka bazai yiwu ma ta fara
haɗa inuwar wre dashi ba.,saida Ammi ta gama koro zance sannan suka mata godiya ta
tisa hafsat a gaba suka nufi hanyar gida ,a hanya take faɗa mata ta sani kozata
rayu kozata mutu sai andaura aurenta da Abdulmallik don haka idan zata saki ranta
ma ta sake ta amince dashi kuma tana gama makaramta zaayi aurensu nan da 6
month ,maganar ta doketa gaskiya me Ammi take nufi ,Ammu tana nufin zqta mata auren
dole gaskuya bazwu yiwuba sannan zatai iya kokarinta na ganin ta cusa tsanarta a
zuciyar Abdulmallik da matarsa zuwaira.
Suna komawa gida ta nufi dakinta tasa kuka ra rufe ,kukq kawai take me cin bataso
ta tin rayuwarta ta baya amma y zame mata dole matikar zatana ganin Abdulmallik
dole ta tina da wannan banzar rayuwar tanq cikin haka saitaji wayarta tana ruri
tana dubawa ta saki wani kayataccen murmushi ta dauka wani kuka ne ya kubuce mata
ta ce
My derling bro
Tq faɗa tanq fashewa da kuka ..
Rarrashinta yq fara domin ta saba mishi shagwaɓa duk lokacin da yakirata ,saida
yasha aikin rarrashi sannan ta hakurayake tambayarta me yake damunta kaman zata
fada masa abunda yake damunta saikuma tayi tinani zata iya tayar masa da
hankali.shiyasa ta hakura ta boye masa domin tasan kalar zuciyar yayanta zai iya
daukqr mummunan mataki wanda zai kaita ga shiga fushin ammi hira suka taba kadan
sannan yakashe wayar ,sai taji sassauci aranta ba kaman daba .
Suna zaune a falo suna dan taba hira duk da ba sosai Hafsat take responed ba gaba
daya kwakwalwarta ta cushe ta rasa taya zata bullowa wannan alamari kaman daga sama
taji karar shigowar sako wayarta tana zudewa taga zuwairq ce ta.mata sako kamat
haka
Gaskiya.kawata naji dadi sosai kuma na gode miki da kika amince da auren
Abdulmallik bansan da wani baki zan miki godiya ba ki shitya yau.Abdulmallik zqizo
kudan fita don ku kara fahimtar juna
Tsaki tayi wanda ita kanta batasan.tayi tsakinba mamaki take da alajabin wai wacr
irin zuciya ce a kirjin kawar tata anya zuwaira tanada zuciya kuwa ,taya zata fara
zaman kishi da zuwaira tabbas tasan tanada kishi bazata.duba wai don zuwaira
kawarta bace babu damuwarta yanzu zqta.keta mata.rash in mutumci indqi akan abunda
zuciyarta take sone amma qi batason Abdulmallik shit as take gamin bazata taɓa
yarda ya zamo mijinta ba.kaman yadda ya cusa mata bakin ciki itama saita cusa masa
koda kuwa zai mutu ne bazata taba.amincewa va ,haka taita zancen zuci har Ammi ta
lura.da condition ɗin da take ciki sunanta ta kira cikin sanyin murya ta ce
Yanzu Hafsat bazaki cire damuwa a xuciyarki ba kenan kindinga ririta wannan maganar
haba meyasa kikeso kija da ikon Allah kisani komai ya faru dake kaddara ce ta
ubangiji babu wanda ya isa yayi miki abunda Allah bai miki ba don.haka ina mai.
baki shawara ida zqku saki jiki ku fahimci juna to kisaki idan kuma zaki tsaya
lusaranci ga fili ga mai doki bazan sakr shiga wannan maganar ba kinsan dai
hukuncin da na yanke
Hawayen dake zuba a idonta ta share ta tashi ta nufi dakinta tai kuka saida ta
koshi wani bacci ya dauketa ,kqman daga sama taji ana knowking kaman bazata budeba
kawai ta mike ta bude Ammi ta gani tsaye tana binta da kallo ta ce
Kinsan kina da bako shine zakizo kihau bacci to maza ki tashi yana jiranki yanzu ki
fito
Daga mata kai kawai tayi ta maida marfin kofan ta rufe ,dq badon fishin mahaifiya
balai bane a gareta da wlh bazata fita ba amma babu yadda zatayi dole ta bishi ,ba
wani shiri tayiba ta fito rike da mayafinta a hannunta ko sallama bata yiwa Ammiba
ta fita a gidan ,yana jingine a jikin motarsa yana waina makullin motar kallo daya
tayi masa ta dauke kai tazo taja ta tsaya batayi magana ,murmushi yayi ya ce
Barka da wannan lokaci hjy Hafsat ,kinfito lafiya duk cewa kin shanyani zaman
jiranki amma banga kin jima ba domin na jima ina kallon kifa domin inga takunki mai
jan hanka
Hannu ta daga masa ta ce
Wlh Abdulmallik wlh dabadan Ammiba kayi kaɗan in fito wai don kazo saidai kazo ja
gaji da zuwa ka tafi ,kasani bana sonka kuma bazan taɓa sonka ba ,kaine namiji na
fako dana tsana a rayuwata ina mai baka shawar kaje ka samu Ammi kace ka fasa
aurena karmuzo munayi nadama nan gaba
Murmushi yayi ya ce
Shin bakisan kiyayya tana iya komawa soyayya ba kuma soyayya tana iya komawa
kiyayya ,don haka a shirya nake domin na karbi kowanni irin hukunci daga
gareki ,nasani Hafsat kowani mataki kika dauka a kaina bazaki huceba domi nasan na
kuntata miki na bakanta miki gwargwadon iyaka amma ina neman yafiyarki kuma ina
menan gafarrarki kiyi hakuri ki bani dama in bayyana miki soyayya ,ki bani dama in
goge tabon dana miki ,ki bani dama pls kibani dama
Tsaki kawai tayi ba tare da tabashi amsa ba wannan Shi ake kira da ihu bayan hari
wannan shi ake cewa nade taburman kunya Allah ya hana ramar da gari zai wayeta
kalli Abdulmallik a matsayin mijinta da takalli wannan ranar gwanda ta mutu inyaso
akai masa gawarta cikin gidansa ,tana cikin wannan zancen zuci taji ya ce
to shikenan tunda yanzu haushina akeji shikenan yanzu kizo muje inkaiki
shopping ,pls kibani dama in kyautata miki koda sau dayane
Waye ni kasani bakada dukiyar da zaka sayeni da ita wlh ,badai ni kace kanason gani
a matsayin mataba to kashirya duj ranar da natare a gidanka to bakinciki kunci da
takaici ka shirya dasu keda kun kulla abota mai karfi ,don kaga tafiyata idan ka
gama tsayuwa zaka iya tafiya .
Tana bude kofar sukayi ido hudu da Ammi tana zaune ta zuba mata idon ka da kanta
tayi ta magana tace
Harkunje siyayyan ne
Shiru tayi ta fara inda inda tace
Zakije ku tafine kokuma sai nadauki mataki akanki
Batayi magana ba ta juya tana fita takallesa ya juya babu shiri ta shiga bayan
motar ta zauna kallonta yayi baiyi magana a yaja motar suka bar gidan ,wani babban
mall ya kaita ya ce ta zabi duk abunda takeso bata kulashiba ta shiga ta fara dauko
kayayyaki komai hannunta ya dauka akai saida ta dauka saida ta cikq basket guda
biyu har suka euce kata sannan sukazo akayi bill suna fita ta tara almajirai d mata
ta fara rabamusu saida ta karar dasu tas sannan ta juyo ta kalleshi tai tsaki ta
nufi bakin titi aikuwa hakan yayi daidai da zuwan me nafef ta shiga saida ta kusa
isa gida ta tsaya a wani dan karamin provision ta siyi kayan ciye ciye ta mishi
trnf ta wayarta sanan ta nufi gida tana zuwa ta ajiye Ammi kayan ta nufi dakinta .
Gaba daya tanajin haushin kanta meyasa ta bishi suka fita ai wanan kaman taci
amanar julabib ne shin idan ranar alƙiyama ta hadu a julabib mezata ce masa shin ta
lalata qljannar daya bata ,ce masa zqtayi tayi aure akan nasa me hakan yake nufi
wayyo Allah wlh ko duniya zata tsaneta bazata auri Abdulmallik ba haka ta wuni kuka
gaba daya tana cikin damuwar da babu mai fahimtarta babu wanda zai fahimci halin da
take ci
Nifa fans tambayoyina sunfi nqku
Shin meyasa Ammi ta dage akan auren nan duk da yarta bataso
Shin wani abune Abdulmallik yayiwa hafsat data tsaneshi
Shin waye julabib
Shin waye yayanta kuma yana ina
Shin abunda zuwaira takeson hadawa bazai dameta ba kuma kundaiji furcin hafsat
Shin wace Nanna kuma waye danta
Ku biyoni akwai sarkakiya me yawa wanda ni kadai nasan yazan warwareta .
Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
STORY &WRITEN
BY
ADAMA UMAR
SECRET PEN
07081940768
LOVE AND ROMANTIC STORY
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
3️⃣
PAGE THREE
Yauma kaman kullum suna cikin break a daining abunda zai baku shaawa shine harda
Nanna ake cin abincin( wata xuciyata tana faɗamin wannan nannar tana da wani
matsayi a wannan family),saida kowa ya gama cin abinci Ammi ta kalli nanna batayi
magana ba nanna ta fara tattara kwanuka kallon Hafsat Ammi tayi ta ce
Wato Hafsat bazaki cire wannan damuwar a ranki bako kina dqi ganin halin da muke
ciki idan kikace bazaki auri Abdulmallik ba kinsan wanine zaizo neman aurenki kuma
idan suka nemi yan uwanmu mezqn labarta musu don haka kiyi hakuri da wannan lamari
ai auren nan
Waishin Ammi ina yan uwanmu suke ina yan uwan mahaifinmu shidan nasan ya rasu amma
ina iyayensa ina yayyensa ina kawunensa ina baffanunsa washin kema Ammi ina naki
yan uwan suka shiga,meyasa bazqki gabatar damu a garesu ba karki manta mun fuskanci
kalubalem rayuwa kala kala tun muna yara akan gorin asali sannan yanzu ma akan
rashin asali zaki aura mun Abdulmallik umma kodai ta hanyar banzw kika samemune
Tass taji saukar mari a kuncinta wanda hakan ya tilasta mata da yin shiru
tanakallon Ammi sa hawaye ya wanke mata fuska ,kallon Hafsat Ammo tayi ta ce
Idan kika sake tambayata asalina kona mahafinku wlh ban yafe mikiba
Shiru tayi taji duniyar da take ciki ba nata ba