Author : adama umar Secret Pen Category : Complete Novels
masa ta ce
"Idan zaayi saika hada da uwarka "
Juyawa yayi yana dariya.,ita kuma Nanna.kwafa kawai tayi batace dashi komai ba .
Suna dawowa suka sameta a falo da alama waya takeyi ganinsu yasa ta kashe wayar ta
nufo gunsu tace
"Lafiya kuwa ammi meke faruwa ?"
Ganin yanayin Nanna yasa ta gane itace bata da lafiya zasu wuce da ita daki Rais
yace sam saidai su dawo falo taci wani abu haka suka dawo yaje ya hado tea ya kawo
mata ,kin karba tayi ganin zai bata a baki yasa ta karba a kafa kai taanasha a
hankali kaman bataso ,sannan aka bata magungunanta tasha.
Waya Rais ya dauka yasa aka turo masa maaikata sojoji suka karbi aikin gidan da
nanna takeyi ita kuma aka cigaba da jinyarta ita da ,har yanzu babu wanda yasan
maganar da tashiga takanin Nanna da rais ,saidai alakarsu.taja.baya hakan
yasa.julabib a matikar damuwa ,yanzum bya zaune yake cikin yaransa kuma abokansa
sojoji suna wasa suna dariya ,kaman da wasa sako.maganarsa da Nanna ,babu laifi sun
masa.dariya da ihu kafun kowa ya fara bashi shawara wani.ya ce
"Ni a ganina ka tursasa mata ta.aure ka kawai yunda kana da dama."
"No ni aganina kawai ka saceta saita amunce zata aureka ka dawo da ita "
"No ni aganina kawai ka nuna mata zaka.iya mutuwa akanta har fiya fiyan karya kasha
"
"Like how ,kaman ya zansha.fiya fiya?"
"Ka saku bottle na fiya fiya.ka.bayar a wanke maka ya fita saika saka olive oil a
ciki saika mata kalamai a karshe kace zaka iya kashe kanka ma idan bazata aureka ba
ai tanasonka kawai.tana tinanin taya duniya zata kalleta ne "
"Ok haka zaayi but.kai zaka wanke bottle din sannan ka fara sha ”
Dariya sukai dukkansu ........
Tofa ana wata ga wata ,rais fa ya dage ya kuke gani
Shin mijin nanna na raye idan yana raye ya.zaiyi da rais
Shin wani.mataki ammi zata dauka idan taji wannan zancen
Kai wannan lamarin abun dubawa ne.fa
Ina jiran amsoshinku a comment section
Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
*STORY &WRITEN*
*BY*
*ADAMA UMAR*
*SECRET PEN*
*07081940768*
*LOVE AND ROMANTIC STORY*
*Ina masu so a tallata musu hajarsu to ga dama ta samu ,duk maiso a tallata miku ko
kaya ko magunguna to tuntubi number nan*
07081940768
A SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
Kaman yadda suka samu kwalban fiya fiya aka zuba olive oil a ciki suka bashi ya
nufi dakin Nanna tana kwance yaje shiga daga jin muryarsa ta gane shine ya shigo
shiyasa ma taki dago kanta kaman tana bacci murmushi yayi don yasan dalilinta nayin
hakan yazo kusa da bed side din ya zauna yana kallon fuskanta ,taarguwa tayi hakan
yasa ta bude idonta aikuwa suka hada ido ta bata rai ta ce
"Me kakemun a dakina "
Murmushi yayi ya ce
"Laifine don masoyi yazo wajen masoyiyarsa "
Rintse idonta tayi jin abun ya mata banbara kwai ta bude idonta cikin fushi da
bacin rai ta ce
"Ka saka idonka a nawa Rais ka kalleni da kyau ,ni a matsayin mahaifiyarka nake
domin kasha nonona kaga babu wannan maganar tsakaninmu ,shiyasa kullum nake maka
kallon danda na haifa wannan soyayyar da kake ji a kaina ka maidashi soyayyar da da
uwa domin bazqn taba zamw.matarka ba har abada "
Tunda ta fara magana yake kallonta yanaji kaman ya daura hannu aka ya tsala ihu ,
me kunnuwansa suke jiye masa ne me Nanna take nufi kenan soyayyar da yakeji a ransa
irin wacce yake yiwa umki ne innalillahi wa inna ilaihirrajiun ,tashi yayi yana
gauraya hanya ya nufi dakin Ummi ko sallama baiyiba saida ta tsorita da ganinsa ta
ce
"Lafiya Rais ka shigomun daki ko sallama babu "
"Sorry Ammi nazo gunkine "
"Ok i hope lafiya ko "
"Eh lafiya kalau ,dama Yanzu nakejin wata magana wai Nanna ta taba shayar dani "
Murmushi tayi ta ce
"To mene don ta ba shayar dakai din ko zakayi amai din abunda tashayar dakaine "
"No ammi kawai kibani amsata "
"Eh watarana na tafi company na babanku domin yin setteling da maaikata to na barka
a gida ,na dauka zan dawo da wuri har yazamana kanata kuka idan kaga zaa bawa
julabib mama hakam yasa kawai ta baka kashe saida ka koshi me yake faruwa "
Fita kawai yayi a daki ba tare da ya bata amsa ba ya koma dakinsa yana kuka yana da
nasanin abunda ya furtawa nanna ,saida yasha kukansa ya koshi sannan yayi
bacci.harya makara sallan azahar .
Haka rayuwa taita tafiya daga Nanna har rais babu wanda yake cikin walwala har ammi
taso ta fahimci abunda yake faruwa halan yasa ta kira Rais take tambayarsa meke
faruwa ya shaida mata yana shirye shiryen yacce zasu tafi garinsu ammin da abbansa
,saida gabanta ya fadi jin abunda ya fada hawaye suka cika idonta tana tsoron jin
mummunan labari game da iyayenta shiyasa bata wauwayi gida ba shinya Mommynta ta
kasance bata saniba haka ta dinga ti ani har Rais ya fahimci ta tafi wata duniya ta
daban ta tabata ta farga ya ce
"Haba ammi meye rage kuma ,ki godewa da ya kawoki wannan lokacin da ranki ya kamata
ku waiwayi gida ammai ki duba Abbanmu shin yana taye ko ya mutu waya sani so
yakamata mu waiwayi gida mu sanar musu da halin da ake ciki ,ni kuma na tura letter
akam inaso ma fara bincike akan abunda ya sami su daddynmu banma nuna mahaifina
bane kuma ina da tabbacin zaa ban daman hakan don haka ya kamata muje musan wani
hali kakaninmu suke ciki "
Shiru tayi gaba daya ya kashe mata jiki da abunda yake fada.ta rasa ima zatasa
ranta tabbas maganarsa gaskiya ce a kullum mutuwa kara tu karota take dole ta
waiwayi gida tauiwa hajiya bayanin abunda ya faru
Kallon Rais tayi ta ce
"Shikenan rais.na baka wuka da nama ka fara shirye shiryen tafiyar namu ,idan kasa
rana saika sanarmun don inaso mu dauki formal manager namu "
"Shikenan Ammi bamatsala"
Haka ya sa shirye shiryen tafiyansu gadan gadan yasa nan da kwana uku xaau
tafi ,aka fadawa manager shima ya shirya ,da kaman Nanna bazataje ba amma ammi ta
matsa mata saida ta shirya zaa tafi da ita .
Bahaushe ya ce rana bata karya saidai uwar diya taji kunya ,yauce ranar tafiyarsu
Rais an shirya manyan motoci na alfarma sannan an shiya.motan sojoji.guda shida
gaba uku baya uku daga ganinsu kasan a shirye suke ,akwatuna aka dinga fito
dasu.ana sawa a mota su Rais kam sai zumudi yake shida Hafsat amma banda ammi dake
gabanta yanata faduwa tana cikin firgici shin iyayenta suna rayr ko baffanta ya
kashesu shida dansa inuwa sun hau kan karaga sannan tana tsoro ta ina zata fara
yiwa hajiya bayanin ina takai mahaifinsu ,gana daya tana cikin firgici
hakan ,hafsat ta lura da halin da take ciki hakan yasa take mata hira nan suka
daukin hanyar birnin gombe ,tsoron ammi ya kara tsananta lokavin da ta lura sun
kama hanyar birnin gombe babu abunda takeyi sai adduoi ,Nanna kuwa ji take inama
itace zataje taga iyayenta ,da asalin dangin mijinta ,adduoi ta fara turawa
iyayrnta da dukkanin musulmai baki daya ,haka suka dinga tafiya suna wuce garurruwa
da kauyuka sun taso karfe 10:00 na safe qmma sub iso cikin gombe da la'asar saboda
babu ruwansu da gosilo suna tare da sojoji ,kallon Rais Ammi tayi ta ce
"Rais ya kamata muje mu kama hotel wanda zamu sauka don bamusan wani irin tarba zaa
mana "
Murmushi yayi ya dauki wata waya.yayi magana nan sojojin dake gabansu suka sanja
akalar motar zuwa wani babban.hotel ,suna zuwa sojojin.suka.shiga suka kama musu
daki kafun suzo su musu iso ,saida suka gabatar da Sallah sannan Rais ya daukesu
suka dunguma zuwa anguwar ,in banda jiniya babu abunda kakeji amma dake anguwar
shiru ne babu ma wanda ya lura dasu ,Numbern gidan ammi ta basu nan motarsu ya faka
a bakin gate din gidan ,daya daga cikin sojojin ne ya sauka ya kwankwasa aka
bude ,kaman da Nanma wani mutum ne.da.ganinsa ya cika kakkarfa yana ganin sojan
ya.sara masa ya kame saida ya amsa sannan ya fito yana karewa tarin motocin
kallo ,rais ne ya fito ya ce.
"Ka shiga ka bude mana gate munzo wajen hajiya ce "
"Ok sir "
Kawai yacr ya koma ya zuge gate din gidan nan.suka.danna hancin motarsu cikin gidan
da jiniyarsu ,kallon me aikinta hajiya tayi ta ce
"Ke saade kaman karar jiniya nakeji a cikin gidab nan "
"Eh hajiya nima haka kunnuwa na suke jiyemun "
"Maza jeki duba mana idan yan sandane ki tambayesu wa suke nema "
Tashi tayi ta nufi hanyar waje tana bude kofar main falor kawai tayi arba da manyan
motoci sojoji sunata fitowa suna kamewa ,shaaninka da dan kauye nan cikinta ya
hautsina ta juya a guje ta ce
"Hajiya mun shiga uku zo kiga ba yan sanda bane masu.yakin nanne sukazo mun banu "
"Ah bari in haura sama in taso da Alh.yazo ya ganewa.idonsa watakil bakinsa ne "
Ta dauki sandarta ta fara tafiya ta shiga wata korido ,ganin tsayuwa bazai karbeta
ba yasa ta haura sama da gani wata ko wani zata kira.tana zuwa wajen dakin ta fara
kwankwasawa da karfin cin tuwo tana kiran
"Aunty Nihad ,aunty Nihad ki bude!! "
A razane budurwar ta tashi ta bude kofar duk da.ba wani kayan kirkine a jikinta ba
ta ce
"Meke faruwa ne sa'ade"
"Mun shiga uku wasu ne sukazo da bindigogi "
"What yan fashi.da rana tsaka."
"Ah ba yan fashi bane jamiaine "
"Muje na gani bazan iya da shirmenki ba ."
Atare suka fito falo dasu hajiya sun tsaya sunyi carko carko sun gagara fita ,a
waje kuwa snata shan fama da ammi akan ta fito taki ko daga kafanta hakan rais ya
rike hannun Hafsat suka nufi gidan duk da suma suna tinanin irin karbar da zaa musu
kofan suka tura da yake saade bata rufe nan suka kara zaro ido suna jiran wazai
shigo sukaga wani saurayi da wata budurwa sunshigo kansu a kasa ,a hankali ya fara
daga kansa ya fara kallonsu tun daga kafarsu yazo har suka hada ido ,zaro ido sukai
dukkansu suna toshe baki ,Da sauri ta fara dan gwala sandarta don ta tabbatar da
abunda idomta yake gane mata shin mafarkine ko kuwa ,saida tazo deden Rais ta dauki
hannunta ta shafa fuskarsa nan taji wani jiri ya dauketa ta nufi kasa da sauri ya
riketa su kuma suka yiyo kanta suna kiran sunanta ..........
Tofa muje zuwa meya sumar da yar tsohuwa
Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
STORY &WRITEN
BY
ADAMA UMAR
SECRET PEN
07081940768
LOVE AND ROMANTIC STORY
1️⃣3️⃣
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
Salati sukai dikkansu suka nufeta ,Nihal ta daga masa hannu ta karbi mahaifiyarsa
tana jijjigata ,saade kam da gudu taje ta dauko ruwa ta kawo aka fara shafawa
hajiya ,Alh ne ya dago yana kallon Rais tabbas wannan daga ganinsa jinin Muhammad
ne ,da badan yaga wanan da fuskan yarinta bama da yace muhammad ne ,zuciyarsace ta
buga lokacin da qata tambaya ta ziyarce ,"shin ina muhammad din yake".hajiyace ta
fara sambatu "Haba muhammad ka tafi kabar mahaifiyarka ashe zan sake gainika ,ashe
Allah zai nunamun wannan ranar ,kai hakuri muhammad ka kawo ta zan aura maka ita
basai kamun horo da tafiya ka barni ba na rokeka ",gaba daya jikinsu yayi sanyi da
maganganunta ita dai Nuhal taji Hajiya tana maimaita sunan da tajima tana yawan
fada wai yayanta to ai yanda aka bata labarin yayanta ai yaci ace shekarunsa yafi
haka ,hajiya ce ta tashi ta kishingida a kujera idonta kur akan Rais hannu ta mika
masa alamar yazo da sauri ya sake hannun Hafsat wacce take matikar kama da Ammi
tazo gareshi ,kallo ta ksre mishi ta ce ," saurayi ina mahaifinka yake na sani ko
astagfirullah bazanyiba saboda nasan ku jinin muhammad da matar sace ,ina suke ita
suka shiga karkucemun sun mutu ban sake ganinsu ba ,waya fada muku inda kuke "ganin
bazata daina tambayarsu banr ya ce "kiyi hakuri hajiya iyayena suna raye sune suka
fada mana inda kuke yanzu haka ina tare da mahaifiyarmu ,mahaifina kuma yaje wani
wajr aiki amma shima yana nan tafe zuwa gareki kiyi hakuri hajiya" ya fada yana
jara rungumeta a jikinsa ,yana kuka kaman ransa zai fita ,Da sauri Nihal taje ta
rungume Hafsat jin itace yar yayanta da ta jima tanajin.hajiya tana begensu ,kuka
kawai.ya.karade falon harda ammi da take cikin mota wanda uta kukanta tana tinanin
wani hali ke ciki ,hajiyace ta fara kokarin tashi ta ce " bari inje in tarbo
surkuwata da irin wannan gagarumin ziyara da takawomun "dukkansu suka rufa mata
baya suka fito daga main falo bude marfin motan da Ammi take ciki akayi ta daga kai
wa zata gani Hajiyace take rike da marfin kofan hawaye ya wankr mata fuska ta bude
dikkan hanayenta ,da sauri Ammi ta fito kaman wata yarinya ta fada jikinta suka
sakr barkewa da sabon.kuka ,kowa yana sambatun abunda ke cikin ransa .
To bayan gari yadan sha kowa ya gama jimami nan Alh ya kalli Rais ya ce "wato kai
abokina shine kaje ka dawo soja wacce bazan iya takara dakai ba kenan" dariya
dukkansu sukai Ammi ta kalli hajiya batasan lokacin da ta zame akan kujeran ta
durkusa ta ce "hajiya ki yafemun ,ki yafeni,nice sanadiyar rabaki da
danki ,sanadiyar bijirewa iyaye mun ahiga kalubalen rayuwa kala kala ,har Allah ya
kawomu wannan lokacin ',murmushi hajiya tayi ta ce " nagode miki ai kekam bakida
laifi domin kome kikayi ai ke macece shidai muhammad din zai dawo daga aikin zaizo
ya samen saiya fadamun dalilinshi na barina kuma bai waiwayenba ,baya tinanin halin
da zanshiga na kadaici dan Allah ya tausayamun ya bani Nihal a lokacin da nacire
rai da haihuwa"maganganun Hajiya sun daurewa ammi kai kenan tana nufin batasan
muhammad ya rasuba ,kuka ta fashe dashi tana jinjina alamarin da wani ido zasu
kalli Hajiya suce mata muhammad ya rasu me zai faru ,ganin zasu sake rikicewa ne
yasa Alh ya ce "yanzu kam komai yazo karshe munq godewa Allah don haka yanzu zaa
baku masauki ku shiga ku huta zuwa gobe da safe zaayi hirar rayuwa ,domin muna da
tari Tambayoyi a cikinmu "Nihal ce ta tashi ta ce "nikam zan wuce da yar yaya
dakina ,zan shiga dakina da ita nan zan mata masauki"ok kaikuma soja ka.dauki
rundunarka ku je sashen mahaifinka dasu ,murmushi yayi ya ce to shikenan ,Ammi kuwa
hajiya ta ce babu inda zataje tare zasu zauna ita da Nanna ,Nanna kam sai addua
take Allah yasa ammi taga iyayenta kaman yadda akaga na Abbansu , bayan kowa
yaje.ya huta a bangarensa ,washe gari da safe aka shirya lafiyayyen karyawa aka
gayyaci kowa ya halarta anaci ana farinciki da kaunar juna saida aka kammala sannan
aka koma falo ana bada labarin bayan rabuwa ammi kam labari ta fara basu tu daga
kan wacece ita da asalinta da komai inda suka dinga mamaki ana samun yaya irinsu a
duniya ,shiryawa sukai dukkansu suka tafi wajen Baba mai masa suka kaimata ziyara
tayi mamako kuma tayi murnar saboda itama har perison an kaita wai an hada baki da
ita aka sace dan masu gida daga baya kuma akan sakota ,ammi ta mata kyauta mai
tsoka sannan suka sallameta .bayan sun dawo kowa ya nufi dakinsa ,Rais kam dakin
ammi ya nufa yana zama ya ji sako ta shigo wayarsa ya bude ganin an bashi izinin
bincike ne yasa ya fara murmushi .....
Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]
STORY &WRITEN
BY
ADAMA UMAR
SECRET PEN
07081940768
LOVE AND ROMANTIC STORY
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
1️⃣4️⃣
Juya wayarsa yake yanajin tsantsar farin cikin samun dama binciken da aka
bashi ,sai juya wayar yake Ammi ta shigo ta sameshi ta ce " lafiya shiru baka fito
ba?" "Eh ammi ina nan ina duba sakon daya sameni na bani daman binciko
abba"murmushi ammi tayi tana gani kaman mafarki take wai dan da suka haifa shi
zaiyi bincike akan abunda ya faru da mahaifinsu ,kallonshi tayi ta ce "nidai addua
ta shine Allah yasa mahaifinku yana raye bai mutuba ,nidai har yau na kasa yadda
mahaifinku ya rasu ,duk da cewa naga gawan da akacemun masune amma na kasa yadda"
"ammi ki kwantar da hankalinki.in sha Allahu na miki alkawarin zai binciko gaskiya
kuma in sha Allah Abbanmu bai mutuba yana nan da ransa" " innalillahi wa inna
lillahi wa inna illaihirrajiun me kunnuwa na suke jiyemun mahaifinku ya mutu
Muhammad dina ya mutu kuke boye mana gaskuya ". " Haba kakata yanzu dagajin ya mutu
sai kice Abbanmu ne wani mai laifine fa muka kama ya mutu " " haba dan nan ai tunda
jatumarka ta fara magana nake jinku dama nasan tunda kukazo akwai abunda kuke boye
mana ku fadamun gaskiya me yake faruwa da Muhammad dina". Ganin zata rikice musu
yasa ya kamata ya zaunar da ita a bakin gadon ammi ya ce " kinaso na miki bayani
dalla dallah to saikin cika wannan sharadin na farko bazaki tayar da hankalinki
ba ,na biyu kuma zaki tayamu da addua domin ke mahaifiyarsa ce ," kai kawai ta
jinjina masa alamar zata cika sharafinsu yasa ya koma ya zauna ya bata labarin duk
abinda yake faruwa ,hawayen idonta ta dinga sharcewa ,kallon ammi yayi ya ce ammi
ku shirya dukkanku zamu wuce bayelsa Allah yasa muji alkhairi game da
kakanninmu ,bqi jira wata wata ba ya fita ,wani file ya mikawa daya daga cikin
soldier dinsa ya ce ka tatttara dukkan bayanan dake cikin wannan file din ka turasu
headuarter ina bukatan cikekkan labarin meyq faru bayan fitansu Alh muhammad ,sara
masa yayi ya karba ya shige masaukinsu .
Washe gari duk sun shirya harda Baba mai masa suka wuce bayalsa sunsha tafiya kam
kafun nanms sukaje suka kama hotel sukayi salla sukaci abinci ,daga nan suka wuce
anguwar ,suna shiga titin anguwar gaban ammi ya fara faduwa tana karanto adduoi a
bakinta ,dayake da gps suke amfani har motansu ta faka a bakin wani nakeken gate
fitowa sukai dukkansu suna kallon gate din daga gani baiyi kama da gida ba ,kallon
daya daga cikin excot nashi yayi yamai alama da ya bincika ,hannu ya dauka ya
kwankwasa aka bude ,wani sojane nan take ya sara masa ,nan sukai yan maganganu
sannan ya juyo ya ce "this is note a house, is a big modern bakery company "
kallon ammi yayi da hankalinta ya fara tashi kafun yayi magana ta isa gaban gate
din ta ce "yallaboi nan gidan Alh usama ne mana hamshakin mai kudi "
"Sorry hajiya banjima da fara aiki ananba dan haka idan babu damuwa zan muku iso ku
samu manager na company din ku masa tambayoyin kaman zakufi samun bayani daga
gareshi" ,dakatar dashi Rais yayi ya kama hannun ammi suka koma mota kallonta yayi
ya ce "ammi ki kwantar da hankalinki in sha Allah babu abunda ya faru yanzu ki bamu
koda numbern mahaifinki ne mana "shiru tayi kaman mai tina wani abu ta dauki
wayarta ta fara bincikawa kaman mai duba wani abu ta nuna masa wata lamba ,bai jira
mai zaiceba ya kira numbern akayi Sallama ya amsa da sauri ammi ta kwace wayar ta
ce
"Abba Abba Abbana ina kake ina kuka shiga"
Muryar da bazai taɓa mantawa a rayuwarsa ba ta shigo kunnuwansa tashi yayi tsaye
yana" Aisha ,Aisha koba Aisha bace " "nice Abba nice wlh nice gashi nazo gidanmu
bakanan Abba ina kuka koma