Author : adama umar Secret Pen Category : Complete Novels
ta bar.musu falon don tasan da zata kara magana Ammi zata iya kai mata
duka ita kuma bason abunda zai taba lafiyarta take.yanzu ba
Haka sukaci gaba da hirar biki Ammi tana fada mata shirye shiryen da sukeyi Nanna
kam na gefe kaman ruwa ya cinyeta don tasan halin da ake ciki da badan ta dakatar
da Hafsat ba ai da basuma san inda takeba balle su mata wannan maganar ko kumq
sudinga shirye shiryen biki .
Kaman yadda aka shaidawa Ammi haka abokansa suka kawo kaya masu shegeb yawa kaman
na budurwa anata bude kaya ana yabawa amma ko fitowa Hafsat batayiba zuwaira ce ta
nufi dakinta ta sameta tana kwance man gadon ta fada ta ce
Wow besty yakamata kizo kiga kayannan kinga kaya kuwa gaskiya kizo muje ki gani
Ta karisa fada tanajan hannunta ,fisge hannunta tayi ta ce
Dallah malama sakeni ku tattara kayansa ku mayar masa bayida dukiyar da zai sayeni
ko soyayata kuje can kuyita rawar kafa akan kallon kayansa ,nidai KO kallo baki
isheniba balleshi
Jiki a sanyaye ta fito saga dakin amma ta basar suka koma sunata ribibin kaya .
Yau cikin farin ciki take ta shiga kitchen gadan gadan don hadawa yayanta kayan
abinci, dafawa kawai takeyi ita kanta tasn yayi kadan ya cinye wannan abincin a
cikinsa amma dafawa kawai take saida taga ta cika daining din sannan ta hakura ta
koma dakinta tai wanka tafito rike da makulkin motarta ahannu da jakq da wayarta
kallon Ammi tai tace
Ammi bari inje in dauki taya kinsan jirginsu yana daf da sauka
To shikenan saikin dawo ki hqnzarta
shikenan
Agogon hannunta tak kallo hakan yayi daidai da bullowar wani ingarman soja cikin
kakinsa wanda hakan yake shaida shi sojan kasa da kasane tafiya yakeyi cikin isa da
takama kakkarfan namijine fuskarsa tana dauke da saje baki mai kyau ga hancinsa
madai daici bakinsa dan karami yanada manyan idanu farine tass idan baka saniba
zakace shiba dan nigeria bane ,tqna hangosa ta tashi da sauri ta nufeshi ta fada
jikinsa shima rumgumeta yayi suna sauraron bugun zuciyar junansu wani nitsuwa yake
ratsata saitaji ta manta da duk damuwarta sakin junq sukai ta juya tana leken
bayansa kaman zata hango julabib kqman yadda suka saba zuwa amma ina babu shi
hawayene masu zafi suka zubo mata yasa hannu ya share mata yana gurgiza mata kai ya
ce
Meyasa kike kuka kin manta julqbib yana cewa kuka baya miki kyau don haka karkiyi
kuka bazai ji dadiba kuma ai kina tare dashi domin annabi muhammad yace kowa yana
tare da abunda yajeso don haka kina tare da julabibi
Rungumeshi tayi tana murmushi shiyasa takeson yayanta akullum yana kwantar mata da
hankaki akan damuwarta ,gida suka nufa jamian tsaron da aka turo su tarbeshi suka
rufa masa baya a bangare guda kuma jamian airport din suna sara masa duk da ba wani
respond yake ba ,gida suka nufa da sauran jamia tundaga bakin layin kowa zai gane
babban general yana cikin anguwar, parking sukayi sukazo suka tarar dasun Ammi a
bakin farfajiya suna jiran isowarsu yana fitowa yazo ya rungume Nanna a gaskiya
yanajin tausayin tsohuwar ya sumbaceta ya juya wajen Ammi itama ya rungumeta ya
sumbaceta babu bata lokaci duk suka dunguma suka nufi cikin gidan sauran jamiai
kuma aka musu masauki a BQ don su huta suci abinci ,suna shiga cikin gida ya baje a
kan kujera Nanna ce ta matso tana cire masa takalmin kafarsa murmushi yayi ya tina
kullum haka take musu idan sun dawo shida julabib ,tun yana yaro zuciyarsa take
cike da kaunar Nanna bayida wani buri da yawuce ya auri Nanna ,babu wani sura ko
kyau na mace da yake gani a idonsa saina Nanna ya zauna a cikin turawa amma duk
surarsu baya burgesa kaman na Nanna ,sautin muryar Hafsat ne ya dawo dashi
hayyacinsa tanq mika masa kofin ruwa karba yayi ya kafa kai saida ya shanye sannan
ya mika mata kallonsa tayi ta ce
Yaya muje kaci abinci
No bazanje daining ba kikawomun nan
Haka ta tashi ta dauko leda ta shumfuda ta fara jera masa abinci tana dura masa
sunata dariya bayan ya gama tace yaje yayi wanka akwai maganar da takeso
suyi ,hakan kuwa akayi bayan ya fito saga wankaya kirata a waya ta sameshi a
dakinsa hakan kuwa akayi taje ta sameshi yana tsokanarta amarya amarya bata masa
maganaba guri ta nema ta zauan tace
Gaskiya yaya banasoj auren nan
What bangane bakyason aurenba
Eh yaya domin ja tsaneshi babu wanda na tsana kaman shi shine yasani a bakin cikin
da harna mutu bazan manta ba
Ok fadamun meya miki kika tsaneshi
Akwai wani lokqci...............
.
Shin me asalin su Hafsat kuma ta wacce hanya aka haufesu shin sunada yan uwa
Ya zata kaya tsakanin Abdulmallik da Hafsat zaayi auren ko kuma idan akayi auren
wani irin zama zasuyi shin yazata kaya tsakaninta da zuwaira
Shin me Abdulmallik yayiwa Hafsat kuma wani tabo yayi mata ,wai ina cikin da yake
jikinta shin menene sanaar Abdulmallik kam
Wai meya samu julabib ne kam shin meyayi ajalinsa ,munada bukatar sanin tarihin
julqbib shi kansa
Kunji wata sabuwa wai ra'is yanason Nanna ,karku manta Nannafa mahaifiyar julabib
ce ,wai zafa yarda ta aureshi kuwa shin ya zata kaya
.
Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
STORY &WRITEN
BY
ADAMA UMAR
SECRET PEN
07081940768
LOVE AND ROMANTIC STORY
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
6️⃣
PAGE FIVE
Akwai wani lokaci kuna iraq kaida julabib ,lokacin ina dauke da cikin ,ina zamqn
zamana kawai wata zuciya tace inziyarci zuwaira aikuwa babu msu na dauki makullim
mota na nufi gidanta naje nq sameta a damuwa na matsa Mata ta fadamun Take shadamun
kodawani lokaci mijinta za I dawo a buge yake shigowa gida ta rasa ya zatayi gashi
har gun aikinsa sun koreshi ita taje ta bada hakuri akaj bashida lafiyane shiyasa
yakeshan maganinda suke bugar dashi ,ta shaidamun saura sati daya hutun ra suka
bashi ya kare gashi har yanzu bai sanja dabia ba kuka take sosai na tausaya
mata ,kaman yadda muka saba na kwantar mata da hankali saida ta fara murmushi na
shaida mata yunwa nakeji aikuwa babu bata lokaci ta nufi kitchen nikuma na haura
dakinta na kwanta domin cikina yqna sani bacci sosai ,kaman yadda ya saba haka ya
shigo gidan cikin maye bab ruwansa ya juya bai kalleta ba sai ya nufi dakinta yana
zuwa yasa key yabar key a jiki ya fara kallona ,kallo yakemun na shaawa a inda
nikam bansaniba haka ya kariso wajen gadon ya danneni ,kaman a mafarki naji ana
wasa da jikina a firgice na tashi ,na razana sosai lokacin da na kalli Abdulmallik
hakan yasa na fara kiran zuwaira murmushi kawai yake yana tande baki kaman zaki mai
farauta tattaro karfina nayi na yunkura an tashi amma ina ya danneni kokawa muka
fara ina kiran sunanta ta fito a rude ta fara buga dakin amma ina ya rufe sunasa
take kira kaman ranta zaifita amma ina ko saurarronta bayani haka saida ya cimma
kudurinsa akaina tun bai gamaba jini ya fara bina amma sai sambatu yake
"haba zuwaira meyasa kike hanani kanki kinsan saboda kina hanani kanki shiyasa nake
shaye shaye don bazan iya zinaba ki taimaka kinaban kanki gashi yau kinfi ko yaushe
dadi "
Haka ya dinga sambatu da babatu wanda hakan ya tabbatarmun ya dauka da zuwaira yake
muamala said a lokacin nails nadamar shigowa dakinta na kwanta ,saida ya gama ya
bingire ya fara bacci no kuma want ciwoj madame main tsanani ya turnikeni KO daga
kafata na kasa DA kyar naja jiki na bude tashigo a rude ta rungumeni tana kuka
kaman ranta zai fita tana yiwa mijinta Allah ya isa ita da kanta ta daukeni ta
kaini asibiti likitoci suka karbeni kafun na haifi wani qbu kaman kadangare wanda
hakan ya tabbatarmun da bari nayi naji bakin ciki ta kira Ammi ta fada mata babu
jimawa saga Ammi da nanna bata boye musu komaiba ta shaida musu ,a bangarensa kuwa
saida ya gama baccinsa. ya farka yaga duk dakin jini hakan ya tabbatar masa ba
lafiyaba ,kiran numbern ta yakr amma bata daukaba kawai yayi amfani da yanar gizo
ya ga.inda suka ,tana cikin shaidawa Ammj kawqi saigashi ya shigo ya kallesu duka
ya ce
Lafiya kuwa.meke faruwa na tashi na ganni cikin jini
Kwarai ma kuwa Abdulmallik ka cuceni ka cuci abotata da Hafsat da wace fuska zan
kalli hafsat kayi sanadiyar zubeear cikinta farin cikinta daga ita har mijinta ,ka
fara qidayar kwanakin da sukw.rage maka a.duniya domin na tabbata mijinta saiya
kasheka kasan wayeshi
Shidai ya rasa maganar me take da badan shi kadai bane namiji da saiyace badashi
take ba .Hqka akayi mqsa bayani ya tqbbatar baya hayyacinsa yayi haka dominshi ya
dauka da matarsa yakr tare daga nan amma ta ce wannwn kaddarace kar in yadda
nadinga kallonsa da abun bance komai ba domin ni hukuncin da julabib ya yanke shine
nawa ,kasa hakura nayi na kira julabib nace yazo gida akwai matsalq babu bata
lokaci julabib ya sauka a nigeria muka nufi gidanmu da farko ban nuna masa komai ba
amma daga baya nayi masq bayani tashin hankali iya tashin hankali ni kaina na gani
a ranan ya dauki mota ya nufi gidan zuwaira ya samu mijinta bayanan ya tambayeta
ina yaje tace yayi tafiya compqny sun aikeshi daganan gida ya wuce yaje ya samu
nanna yake shaida mata umarni tabashi idan yayi wani abu bata yafeba hakan yasa
julabib ya kasayin komai amma yasa kansa a damuwa ko abincinya dainaci gashi
bayason ganina ban isa inzo inda yakeba saidai inga yanata hawaye munkasance a haka
tsawon sati biyu kafun ya tattara ya tafi ,bayan wata daya daga tafiyarsa bai
kiranba ban kirashiba kuma baya kulani a whatsapp ranar ina nafilan dare kaman
yadda nasaba naji karar shigowan sako wayata ina budewa naga sakon julabib
ne ,jikina yana rawa na bude na fara karantawa
"Assalamu alaiki Hafsat ki sani ina sonki son danake miki yasa nashiga tashin
hankali akan abunda ya sameki kuma mahaifiyata ta hanani daukar mataki hakan yasa
nake cikin damuwa wanda ya dawomin ciwon zuciya me tsanani a koda yaushe zaki iya
jin nabar duniya ina Alfahari dake matata
Kuka na fashe dashi lokacin da nagama kafanta sakon julabib aikuwq baifi satiba ka
kira ka shaida mana yabar duniya ,dqga nan na shiga cikin kunci da damuwa wanda
baya misaltuwa ,shikuma sanadiyar abunda ya faru ya daina shaye shayen miyagun
kwayoyi,wata rana inq zqune zuwaira ta kirani ta ce idan babu damuwa tanason
ganinan bankiba na tashi na shirya naje gidanta ananne take shaidamun tanaso in
auri mijinta ,hqka ta dinga basa labari har izuwa kan dauri auren dake tinkarosu .
Tunda ta fara maganq yake binta da idanu wanda take kalarsu ta sanaja izuwa jaa
kaman wuta na tabbata da zaka taba to saita konaka kasa magana yayi domin yama rasa
taya zai bullowa wannan lamari shiru yayi kafun ya rungume yar uwarsa wacce kuka
yaci karfinta yana rarrashinta saida ya tabbatar ta hakura sannan ya dauko wata
daja ya fara fito da kayayyaki wasuma agogone zobbuna masu uban tsada hakan ya
dinga janta da hira saida ya tabbatar ta sake sannan ya rabu da ita ya Nata
tabbacin indai yana raye bazaayi auren nan a .
Bayan fitanta ya zauna shi kadai yqna nazari gaba daya abun ya kulle masa kai
meyasa julabib bai fada masa wannan lamarin ba har ya rasu ,shin wani mataki zai
dauka akan wannan mutum ai a cikin maye yake kuma ya dauka matarsa ce ,meyasa ammi
ta dage akan auren nan kawai don basuda asali to tabbas yayi alkawarin saiya samo
asalinsu kuma ya kawosu gaban Ammi koma mai zai faru ya faru bazai yiwu laifinsu ya
shafesu ba ,haka ya dinga zancen zuci kafun ya yanke hukunci mai karfi wadda yake
gani shine solution.
Anata ribibin biki wanda iya Ammi da zuwaira su suke kidansu suyi rawarsu ita dai
ko a jikinta don batadauka ma aure zatayi ba ,rana bata karya saidai uwar diya taji
kunya yau zaa daura auren Hafsat da Abdulmallik gaba daya hankalinta a tashe yake
ta nufi dakinsa ,shida Nannata samu yasata a gaba yana zubq shagwaba tana kallo
kaman julqbib dintane a gabanta kallon nanna yayi ya ce
Nanna na ta dan Allah kimun gwaten kuskus mana
Dato ta amsa ta tashi ta nufi Kitchen ,inda ta tashi nan hafsat ta maida mazaunanta
ta kalleshi ta ce
Hab Yaya yanzu hakq mukayi dakai kamun alkawari bazqkq bari ayi auren nan ba gashi
saura awannni shida a daura ,wlh aka daura auren nan mutuwa zanyi
No bazaki mutuba nayi mqgana da mama ta cemun batayafewa duk wanda yayi kokarin
dakatar da auren shiyasa na yanke hukunci a daura auren amma hakan bawai yana nufin
kin zama tashi bane
No yaya matiqr aka daura aure kqm ai aikin gama ya gama meyasa Ammi zatamun hakq
meyasa shin wai menene asalinmu daga ina muke shin ammq batada iyaye ne bare sasu
baki kodai cikin shegenmu tayi tq haifemu
Sam kunada asali kaman yadda kowa yake da nashi hasalima kunfi wasu bayin Allah
asali karku sake sa zargin ko bakwada asali ko kuma bata hanya mai kyau aka
samekuba ,ko daya ba haka zancen yake ba
Juyowa sukayi suna kallon Nanna da take rike da dan jaramin kwano a hannunta guri
ta nemq ta zauna da sauri rai's ya iso kusa da ita ya kama hannunta ya ce
Nanna dama kinsan asalinmu kinsan suwaye mu meyasa kuka mana haka keda Ammi kuke
boye mana mu suwaye sannaj kuce karmusa shakku a cikin zuciyarmu ai wannan dolene
dan Allah ki fada mana mu suwaye
Girgiza masa kai tafara alamar bazasuji komai daga bankintaba ,magiya suka fara
mata suna rokonta wanda hakan yadawo mata tilas ta shaida musu su waye kodan ta
dakatar da auren dolen da zaayiwa Hafsat kallonsu tayi ta ce
Zan fada muku amma sai kunmun wani alkawari
Mun yadda komeyene zamu miki
Kubari ayi auren nan a watse tukunnan sannan kudau duk wani mataki da kukeso
Kqllon juna sukayi rai's ya jinjina mata kai ya ce
Mun Amince my nanna
Gyara zamqnta tayi tana ajiye flat din hannunta ta ce ..........
Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
STORY &WRITEN
BY
ADAMA UMAR
SECRET PEN
07081940768
LOVE AND ROMANTIC STORY
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
7️⃣
PAGE SIX
ASALIN AMMINKU
A garin bayelsa akwai wani attajiri mai kudi Alh Usama ,Alh Usama yana da ƴa guda
daya tilo domin an jima ana haihuwa a gidansa amma yaran basa zuwa da rai ,cikin
ikon Allah aka haifa masa ya mace duk da itama daga farko batayi kuka ba har ancire
rai saidaga baya ta fara kuka nanda nan murna ta karqde dangi anata murna dake Alh
usama yanada jamaa gashi yana kyautata wa yan uwa Alh Usama yana da kaninsa
Abdulwahab ,shikuma Abdulwahab yanada yara maza sunkai hudu sai mace daya itace ta
zama saar Aisha wato yarinyar da aka haifa itace Ammi ,sun an mahaifiyarta maimuna
it a din yard asalin kasar Niger ce amma mahaifinta dang Nigeria ne shiyasa ta
dauko kyawun mahaifiyarta ,Ammin ku tatashi cikin gata da kulawa ta dukkan bangare
kama daga dangin mahaifi dana mahaifiya,haka akasa amminku a makaranta ajinsu daya
da yar baffanta Asiya suntashi tare komai Alh Usama baya nuna warayya hakan yayiwa
kqninsa Alh Abdulwahab dadi yafara shirin hada aure tsakanin amminku da yaronsa
babba Inuwa ,lokacin da Amminku takai shekara goma shatakwas ta gama secondary
mahaifinta ya fara mata cuku² sama mata karatun gaba da secondary nan dangi suka
masa ca akan bazai yiwu yarsa tacigaba da karatu batare da aure ba Hakan ya damesa
shiyasa ya samu Dan uwansa akan ya bashi shawara nan kuwa ya gabatar masa da
bukatarsa na hada aure ,Alh Usama yayi farin ciki sosai ya dawo ya sanar da Mqimuna
bataji dadiba domin hankalinta bai kwanta da hadin auren ba amma babu yadda ta iya
haka ta hakura ,lokqcin da aka shaidawa Amminku batace komaiba ita dai damuwarta
ayi auren kuma ta cigaba da karatunta na likitanci .
Wata rana kanin mahaifinta yazo shida Inuwa mahaifiyarta ta umarceta akan ta kai
musu abunsha babu musu ta dauka ta nufi dakin baki tazo daf da shiga taji sunacewa
wato ina fada maka inuwa idan kasamu ka auri yarinyarnan shikenan duk kudin
mahaifinta ya dawo hannunka da ita zakayi ammafani kana karban kudi a hannun
mahaifinta idan shekaru sukaja ya mutu ta gajeshi shikenan kazamo attajiri
Wlh.da gaskiyarka baba nifa kasan wani abu idan mukayi aure da wasu shekaru zansa a
kasheshi kawai itama bayan ta haifa mana yara saina kasheta yadda kudin nawane da
yarana
Gaskiyanka ne inuwa kaga ka mallake komai kenan
Karar kofunan da sukaji a waje shiyasa sukai shiru da hirar tasu suka fita suna
rokon Allah yasa baaji hirarsu ba ,cikin flower suka hangota sukai kanta da sauri
suna mata sannu kallonta Inuwa yayi ya ce
Haa kanwata lafiya kuwa meya faru
Murnushi ta kago ta ce
Ina tahowa ne Ammi tace in kawo muku ruwa Shine nai tuntume na fadi
Ayya kanwata sannu kinsan kedin ba.kalar wahala bace shiyasa don haka idan mukai
aure bazan barki kiyi aikin komai ba
Murmushin dole tai tana tina abunda taji yana fada tai qjiyar zuciya mai karfi suna
cikin haka saiga Alh Usama suka karisa daga ciki
Dakinta ta nufa ta turo cleaner akan ta kwashe kwalaben ,tunda ta shiga dakinta
take tinanin qbunda kunnenta ya jiye mata batada bakin da zata samu mahaifinta ta
shaida masa wannan lamari ,to kota fadawa Amminta tane hakan ma taga ba mafita bane
,tina yadda sukai da mahaifinta tayi lokqcin da yake shaida mata maganar auren
Inuwa akan tana da zabi dan batasonshi ta yanke hukunci zata samu mahaifinta ta
shaida.masa batason Auren Inuwa a sokeshi ,hakan kuwa akayi da safe ta samu
mahaifinta ta shaida masa batason aure amma yayi fafur yace kozata mutu sai anyi
auren ,babu yadda batayi ba amma haka mahaifinta yaki ,dakinta ta shiga taita kuka
ta rasa wace mafita zatayi kallon akwatinta tayi hakan ya bata idea ta gudu aikuwa
babu watata ta shirya kayanta ta dauki kudin da tasan zai isheta taje ko ina a
nigeria ta dauki A TM dinta bayan ta gama hada jayanta taji an turo kofa da sauri
ta juya tqga Ammin tace rungumeta tayi ta fashe da kuka nan taita rarrashinta tana
bata baki harta hakura ,suna cikin haka kiran Alh Usama ya shigo wayarta alamar
yana nemanta tashi fitar da tayi kuwa yasa amminku ma ta fita ta juyo ta kalli
gidan ta ce
Kayi hakuri Abbi bazan iya auren wanda yakeson yaga bayanka ba sannan zanyi tafiyar
nan ne domin in tsiratar da rayuwarka da tawa idan da rabon zamu gana zamu sake
haduwa
Haka amminku ta tafi tasha ta samu guri ta zauna kusa da wasu mata saitaji suna
cewa ,
Kai ladidi yau zamusha tafiya daga bayelsa zuwa gombe nan kusa ne ai zamusha tafiya
mai nisa sosai
Gaskiya kam nima na fara tinanin wannan tafiyar
Hakan da suka fada ya bata daman shiga motar gombe aikuwa babu jimawa motarsu ta
tashi direct har gombe
Bayan sun gama tattauna tsakanin Ammi da Abbu sun yanke hukunci saidai ta fada musu
kwakwaran dalilinta na fasa auren to zasu daina zance auren kwata kwata ,dakinta
ta taho don ta kirata suji ta bakinta amma abun mamaki tqzo ta samu batanan a
tinaninta ta shiga wani gurine a cikin gidan amma ina ta bincika ko ina batanan
wayoyinta ma duk a kashe ,mahaifinta ta shaidawa nan suka fara bincikq gidan yan
uwa da abokan arziki amma ina babu