Author : adama umar Secret Pen Category : Complete Novels
". "Eh Aisha mun tashi a wannan gidan amma kizo anguwar
ogbia deden wajen babban madallacin jumaa idan kunzo zaku ganni ," ya fada yana
tashi ya sharce hawayen dake zubowa daga idanunsa ya nufi cikin gida dama a kofar
gida yake yana shiga ya fara maimuna ,maimuna fito kafun na baki labarin maza kiyi
adduar shukur yau Allah ya amsa adduarki yanzu Aisha ta kirani tana neman inda nake
na kwatanta mata da badan bani da mita ba da dakaina zanje bazan iya jiraba ,kafun
ta gama jiran mai zaice zaice har takai goshinta kasa na godiya ga Allah ,ta bude
dukkan kofofin hancinta ta rangaɗa guɗa , ta matsa kusa da randa ta kamfato ruwa ta
zubeshi a kasa ta kurbr tsabar jin dadi ,gidan madaidaicine amma yana dauke da
dakuna guda biyar gaba daya an mishi siminti a cikinsa hatta suturar jikinsu ta
gani kasan ta masu karamin karfine ,yana ganin ta rikice yasa ya fita yaje deden
masallaci ya tsaya ya kurwa wayarsa ido yana jiran kiransu ,yana tsaye ya shafe
sama da minti 30 yaga wasu tarin motoci suna nufoshi dan matsawa gefe yayi yana
cigaba da kallon wayarsa ,kiranshi akayi ya daga da sauri ganin wannan numbern yasa
yace
"Aisha kun isone"
"Juyo bayanka Abba"
Juyawa yayi ya kalleta tana tsaye wayar dake hannunta ta fadi sai hawaye ,nan ta
zube akan guiwarta ta fashe da kuka da sauri ya karisa kusa da ita ya kamota ya
rungumeta ,a jikinsa yana ba kuka zakiyi ba Aisha ki godewa Allah daya sake sada
fuskokinmu .
Manyan taburmai naga an baza a wannan tsakar gidan da aka malalashi da simiti ammi
kan tana mamanta ,wayarsa yake dannawa babu jimawa aka dauka bai jira yayi magana
ba ya ce "kayi sauri kazo yayarka ta dawo " dagowa ammi tayi ta ce
"Baba kana nufin mama ta sake aihuwa bayata" ,"kwarai ma kuwa ta sake haihuwa har
guda biyu ma ,abubakar da rakiya ,uta rakiya tana gidan yar uwarki asiya tace mu
tana tsoron taimaka mana saboda babanta amma bazata bar rakiya a wahala ba "
"Waini Babba mai yafarune kuka sayar da gidanku kuka dawo nan da rayuwa "
"Labarine mai tsawo ,tun bayar tafiyanki Abdulwahabu yake bani baki akan in kawo
kudi akai gun malamai ayita addua ,haka na dinga bashi kudi nima kuma inatayi idan
nayi istihara saina ganki kina cikin rayuwar jin dadi shiyasa hankalina ya
kwanta ,kasancewar na yadda dashi shiyasa na sake masa komai nawa haka yace ya
kamata mu gina masallaci saboda mahaifiyarmu ,bankawo komai a rainaba na yarda na
sa hannu a takardan da bakomai ,ashe haintata yayi domin yaga mahaifiyarki tana da
juna biyu bashi da gadona idan ya kashe ni shiyasa ya hada baki da lauyana sukamun
haka ,watarana.kawai akazo mun wuta wuta in tattare komai nawa gida.ba nawa bane da
kadarorina babu yadda na iya haka muka hada dan kayanmu lokacin ana goyon abbakar
saida muka fito zamu dauki mota aka shaida mana bayan suturar jikinmu babu komai
namu a gidan ,hakan yasa muka fito saiga Abdulwahabu a nafe ya.fito mukasa kayanmu
da komai yanata.bani hakuri akan zaiyi bincike mu zauna anan zai shigar da
kara ,manyan abokanaina suna ta kirana kowa yayi wani yunkuri sai a nuna masa
wannan sa hanu dole suyi shiru daga haka muka hakura muka mika lamuranmu ga Allah,"
Gyara zamanta tayi ta fadawa su baba dalilin barinta gidan da yacce tayi rayuwa
hatta halin da mijinta yake ciki bata boye musu ba ,kuka Baba ya dingayi yana sawa
ammi albarka ya ce
"Wato gidan nawa ma an rushehi an dawo dashi company"
Eh baba domin.munga tabbacin hakam baro baro a bakin company din
Rais ne yayi gyaran murya yace ina neman wata alfarman abani dama inyi bincike akan
wannan lamarin ,babu musu aka bashi ,ya tattari maaikata suka nufi wannan company
din suna zuwa suka shiga inuwa ne wanda ya gina company din dan haka suka nemi da
akaisu office din C E O babu mata lokaci suka kwamusheshi suka nufi deppot din dake
bayelsa suka mikawa mazashi saida yasha jibaga sannan ya kura mahaifinsa yayi masa
bayani ,gaba daya hankalinsa ya tashi ya kira yan sanda jin inda dansa yake yasa
sukace aikin yafi karfinsu ,karshe dai saida ya kawo wannan takardun shima yasa
hannu ya mallakawa Alh Usama aka fiddashi a duk gidan da yake da komai su Alh usama
suka koma anata sawa Rais albarka ammi tanajin alfahari da aikin danta koba komai
ya share musu hawaye.
A bangaren maaikata kuma sun tsananta bincike sun gane cewa kiran da Aka yiwa Alh
muhammad na karyane babu wasu baki da yayi sannan kotarsu ta fada cikin kogin bakin
gada inda akasa manyan maaikata suka shiga cikin ruwa suka fito da ita ,basuga ko
alamar kashi ba hakan ya tabbatar musu da cewa sacesu akayi akajefa motar cikin
ruwa ,manager din da ya kirasa ya shaida masa bakin sunzo aka kwamushe da yasha
jibga yake shaida musu shima wasu ne suka sace matansa akan saiya kirashi ,bashi da
zabi shiyasa ya kirasa daga nan suka kama hanya suka fita ,tambayarsa sukai baiji
wata magana da ya danganci inda suke ba ya ashaida Musu babu abunda yaji duk da
tsufa ta kamashi amma dayaji bugu saiya tina address din da aka bayar akaisu Alh
muhammad ,bibiyar adress din akayi aka tabbatar bana nigeria bane nan suka mika
aikin wa sojojin south africa , shaaninku da zafin nama suke aikin bilhakki da
gaskiya shiyasa baasha wahala ba aka turo musu da rahoton cewa wani babban mai
arzikine yasa aka saceshi domin akwai wani aikin nuclear da zaizana masa ,taurin
kan da yayine kuma ya shaida musu ya fita a kaidansu shiyasa sukasa a kamo musu shi
suka hada harda bello ya dawo kaman mai taimaka masa ,yanzu haka zanen nuclear ta
kammala har yabayar a kera masa ita inda yace bazai sakeshi ba har sai ankawo yaga
babu wata matsala ,inda suke masa bara zana da idan bai musu aikiba zasu kashe
iyalansa ,domin yana ganin iyalansa sannan yana sanin halin da suke ciki ,haka suka
maida shi kaman bawansu yana yiwa manyan ƙasashe aiki su kuma suna karban kudi
yanzu haka a yadda rahoto ta nuna daga bakin daya daga cikinsu gobe nuclear zata
iso kuma ana tinanin nuclear na isowa yaga zanenta yayi daidai zai kashe Alh
muhammad domin karya sake zana irinta , jin wannan rahoto ya gigita shi hakan yasa
ya tara kowa da kowa yayi musu bayani nan aka fara adduoi da sallah ,shikuma ya
tattara runduna mai yawa harda sojojin south africa suka nufi wannan tsobirin ,sun
hadu da haradi masu yawa wanda dole saisun shareau kafun su isa haka suka dinga
haduwa da manyan yan caskale da masu suburbuda duk suka kara dasu inda suma sunyi
rashin jamaarsu sosai ,a gida nigeria kuma gaba daya tashohin television duk sun
dauka anata sanar da abunda ke. Faruwa sai adduoi ake musu na fatan
nasara ,masallatai tsangayoyi ,islamiyyoyi duk anatayi ,cikin ikon Allah da
taimakon adduoi da suka samu suka kubuto da su daha hannun mugaye inda basu hakura
ba suka dinga binsu da ruwan bindigogi amma suka tsallake ,su kuma aka tattara su
nuclear kuma aka dan kata a hannun sojojim nigeria domin nigerian ne ya kerata
hakan yasa aka karawa Rais matsayin bigeanty a soja inda kasa nigeria ta karade da
farincikin ,gaba dayansu suka nufi bayelsa inda kowa da kowa na family ake
tare ,Alh muhammad dai sai kallon wannan saurayi mai kama dashi yake wanda ake kira
da Muhammad muhammad suna zuwa dama anyiwa gida waya ga tarin yan jarida nan da
gidan rediyo suka fito a mota,ammi kam tun dazu sai murza ido take ko tana. Tinanin
mafarkin da tasaba shine taleyi amma ina kaman ba mafarki bane wannan da gaskene
bata tabbatar ba saida rais ya kama hannunta ya dankashi cikin na Alh
muhammad ,hakan yasata wani suman tsaye wanda jamaa suka.yiyo kansu suna
salati ,kici kici ta farayi da numfashinta tana salati .........
Share pls
[9/12, 7:58 PM] ADAMA UMAR (SECRET PEN):
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*
STORY &WRITEN
BY
ADAMA UMAR
SECRET PEN
07081940768
LOVE AND ROMANTIC STORY
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
1️⃣5️⃣
Bsnda farin ciki babun da yakeyi gaba daya sai hasken camera yake tashi a wajen ya
juya ya fito da Alh bello mijin nanna shima ya danka mata hannunsa a nata ,kukan
dadi kawai yake tashi ganin abun bazai kareba yasa aka nufi cikin gidan Alh Usama ,
dama an gama shirye shirye da komai komai suka zube a baban.falo anata jajantawa
juna ,karshe dai farincikin da ya watse sama da shekara 25 ya dawo cikin wannan
iyali da salo na daban bayan an gama hajiya ta kalli Alh muhammad ta ce
Yana da kyau akaikuma masauki kuyi wanka kuzo kuci abinci
Sunkuyar da kai yayi yana tinanin ta ina zai fara bawa nahaifiyarsa hakuri domin
tun dazu zulumin da yake kenan ,rarrafowa gabanta yayi ya kama kafanta ya ce
Hajiya ,kiyi hakuri da kuncin da nasaki ,kiyi hakuri da abunda na miki na rashin
daidai ,hajiya naga tashin hankali kala kala asanafiyar bijire miki da
mukayi ,munga rayuwa kala kala ,Hajiya ki yafemun ko zansamu farin cikina ya
tabbata
Dagoshi tayi tana rike da hannunsa ta ce
Haba muhammad akan me zakace ka bijiremun da baka gudu da ita ba da zaku haifamun
wadannan tsala tsalan jikokin ,koda kun taimaki wannan baiwar Allah da mijinta
wanda suka dawo tamkar yan uwa a gareku ,karka damu karkaji komai najima da yafe
maka ku tashi akwai wani part mai 2 bed room kuje akaiku can ,tashi yayi jiki ba
kwari ,Maman ammice ta kira daya daga masu aikinta ta musu iso saida suka tafi ammi
da nanna sai kallon juna suke ,ji suke kaman su ruga a guje su bisu amma saboda
kunyar iyayensu sukai shiru domin ji suke kaman in suka tafi bazasu dawo ba ,hajiya
da ta lura da hakan ta kira sunan ammi ta ce
Me kuke mana anan bazaku tashi kuje wajen mazajenku ba ,me zaku mana anan to maza
ku tashi ku tafi
Dama jira suke nan suka tashi cikin jin kunya ,Abbakar yayi gyaran murya ya ce
To nidai hajiys diyar kinnan nakeso kibani zan aura ,zanyi na biyu da ita
Kulle fuskanta Nihal tayi domin dama ta jima da harbo jirkinsa tun daga kallon da
yake mata ,Hajiya kam fatan alkhairi kawai tayi musu da sauran jamaan dake falon .
A bangaren su ammi kuwa saida suka shigo part din sannan kowacce ta shiga part din
da aka ajiye mijinta a tare suka tura kofan ,Alh muhammad yana zaune bakin gado ya
hada kansa da guiwa ,yana ganinta ya taso da sauri ,inda ita kuma ta tsaya daga
bakin kofa ta kasa karisowa ,tasowa yayi ya ce
Meyake faruwa ne Aisha ,akwai matsace ,hankalina ya fara tashi da naga baki biyonba
kodai kin sake wani aurene
Kuka ta fashe dashi tana mai rungumeshi ta ce
Bazan taba auren wani mutum ba bayan kai na gwammaci na koma ga Allah ban auri kowa
ba akan na auri wani ,duk da cewa na maka takaba amma na kasa yarda da ka
mutu ,amma na godewa Allah da yabani da daya tamkar ya dubu na gode naka .
A bangaren nannama makamancin tambayoyin da ya mata kenan ciki ya hada mata da ina
julabib bata boye masa ba ta sanar masa da komau yayi masa addua kafun su shiga
shirya mazajen nasu .
A bangaren Asiya kuwa tunda taji Aisha ta dawo ta tattaro yayanta duka akwai namiji
wanda bazai wuce saan Rais ba koma ya fishi da kadan sannan akwai mace wacce itama
tana da yara kanana sai kuma yar autarta wacce itama macece budurwa bazata wuce 21
years ba ,cikin farin ciki da murna ta shigo gidan kafarta har hardewa takeyi cikin
na juna duk da mahaifinta ya kirata akan idan ta taka gidan bai yafe mata ba amma
hakan baisa ta mishi biyayya ba tubda ya kaucewa Allah da mazonsa ,cikin falon ta
shigo inda taga wadu dandazon mutane anata hira da sauri kanwar Abbakar ta kariso
wajen Maman ammi ta ce
Mama ina yaya take ina take ina yaranta da mijinta jiya munga komai a tv mama
Murmushi mamanta tayi ta juya wajensu Asiya ta ce
Asiya ku shigo mana ,tunda autar asiya ta shigo idonta ya sarkafe a cikin na Rais
ko kauda kai batayi ,jin Asiya ta ce
haba suhana me kike kallone haka
Dan dibirbicewa sukai suka fara sosa keya sannan suka nemi wajen zama aka fara
hirar yaushe gamo ,suna cikin haka Ammi suka dawo hannu sarkafe a cikin na
mazajensu suna dariya da lama wata hirar suke ,suna shigowa Asiya ta tashi da
saurinta harda sassarfa taje ta rungume ammi suna kukan rabuwa .
Agurguje pls .
An bawa su Alh muhammad tarihin duk abunda ya faru a bayansu na kokawa sun koka na
murna sunyi ,nan aka shiga yiwa Alh bello taaziyar julabib dinsa.
A bangaren abubakar fa soyayya tayi karfi tsakaninsa da nihal ,sannan Rais ma baa
barshi a baya ba ya jone da suhana suna shan soyayya ba laifi ya samu karbuwa sosai
,ganin akwai fahimtar juna tsakaninsu yasa akasa surensu nanda sati biyu tunda
komai akwai a wadace ,ammice ta fara yiwa amare gyaran jiki kaman ba gobe ,idan aka
hadawa Amare tsumi ta debo musu susha domin sunyi alwashin cirewa mazajensu
kishirwan shekara da shekaru ,babban abokin Rais ya taso tundaga lagos daurin
aurensu yaga Hafsat aikuwa baiyi nauyin bakiba ya kada kuriarsa nan aka hada da
nashi auren anata shirye shirye .
A bangaren abdulmalik kuwa yana hasasho abunda zaiyiwa su Hafsat amma ganin abunda
ya faru a tv yasa yasha jinin jikinsa ya manta da komai ya rungumi matarsa .
Rana bata karya saidai uwar diya taji.kunya ,yauce ranar daurin auren iyalai guda
shida wanda suka kasance cikin farinciki da kaunsr juna anyi komai.cikin soyayya da
wasa da kudi tamkar ba gobe anyi duk wani event na sojoji da ya kamata babu wanda
aka bari a baya ,bayan an gama biki amare sun sauka a part a gidan Alh Usama kuma
sunsa ramar dawowa kano zasu ziyarci kabarin iyayen Alh bello Sannan zaa siyawa
ngwaye gida ,shima Alh usama ya ce zaibar bayelsa domin yayi nisa zai zaba zai dawo
kano ko gombe ta inda ya yanke.hukuncin zama a gombe anguwar bypass .
Bayan sun dawo kano sun ziyarci iyayen alh bello inda gari ya iso wajen ya biya
kudi a kudin aka gina islamiyya a kusa da kabarin nasu ,Zuwaira taji dadin zuwan
kawarta gidanta da mijinta da sauran amare inda ta kaga bata shawsrwarin aure yadda
zata kama.mijinta dakyau.
Bari mu leka sashin su ammi
To ammi dai.amarci yayi dadi domin dukkanninsu sunyu guzurin ciki a jikinsu ,inda
suka tsorata aihuwa da tsufarsu ,sai bobboyewa suke amma ina tuni Mama da
hajiya.suka harbo jirginsu daga ganin yadda basason cin abinci sai kayan kqadayi
hakan yasa suka ajiyesu suka murna ,sunji kunya kam amma suna farin ciki sa cikin
musamman nanna.d yaronta ya rasu ,lokacin da cikinsu yakai hsihuws sukaje aka musu
bucking na c section suks tafi ma babu wanda ya sani,ganin baasan mezai faru ba
yasa aka kira Mama da hajiya ,sukazo an shiga dasu suna bakin treather saiga Hafsat
ta taho daga ganinta bata hayyacinta itada Rais da matarsa da Abakar da Nihal ,tana
zuwa ta ce munje gida bakwanan akace duk kuna asibiti meke faruwa nan aka shaida
musu take jiri ya kama Hafsat aka riketa sai gado ana musu gwaji aka tabbatar da
suna da ciki , anyi aiki cikin
Lnasara an fitowa da Nanna yan biyu mace da namiji ita kuma ammi an fito.mata da
namiji an yi murna sosai inda akasha shagali sosai aka maida sunan julabib in
kiya .
Bayan wata tara amare suka sunkuto yayansu inda Rais yayiwa Hajiya mai suna ,ita
kuma Hafsat ta ce Mama zatasa ,Nihal kuma tasa mai sunan Alh muhammad .
Tammat bi hamdilkah
Ina godiya ga dukkan masoyana da suke a fadin duniya alkhairin Allah ya kaimuku a
duk inda kuke ,ina godiya ga Allah da yabani rai da lafiya na karisa wannan
littafin.
Albishir gareku masoya
Shin kunsan da sabon littafina mai suna
Hakak dina
Kaman yadda suka sani Alkalamin na dabanne shima salon na dabanne
Ku biyoni domin jin dan dano
Share pls