Advertisements
Chapter 2 Reading Dangina by adama umar Secret Pen BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dangina by adama umar Secret Pen

Author :  adama umar Secret Pen Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 7

3K to 6K   out of 20.5K words

ne domin furucin Ammi ya doketa
dukar da kanta tayi tana rushe da kuka Ammi kuwa dakinta ta nufa ta dinga kuka
kaman ranta zai fita Nanna ce ta shigo dakin jikinta a sanyaye domin taji duj hirar
da tawanzu a tsakaninsu kusa da Ammi ta shigo ta fara rarrashinta kafun ammi ta
ɗago kanta ta ce

Dama haka alhakin iyaye yake Nanna nasani ko istigifari bazanyiba Alhakin iyayen
mune yake bibiyarmu tundaga kan abunda ya faru da Hafsat nafara gane haka gashi
yanzu yara sunzo kuna tambayata ina yan uwanmu da wani baki zan musu bayani taya
zan musu bayanin abunda muka aikata nida mahaifinsu ,shin wani hali zasu shiga idan
sukaji asalinsu wayyo Allah nanna wlh da rayuwarmu tanada remote dana sarrafa
na.maida komai bai faruba

Hawayen dake zuba a fuskar nanna ta share ta ce

Hakane hjy kisani kowa da kalar kaddararsa ki sani wannan itace kaddararki keda
alhaji marigayi ,kuyi neman gafarar Allah zai yafe muku sannan tunda kinga yara
sunason sani su suwaye ayi hakuri a waiwayi gida domin gudun gori

Haka ta dinga rarrashin Ammi kafun ta fito ta nufi dakin Hafsat ,kqman yadda tayi
tinani tana zaune tana rike da hoton julabib tanata kuka karban hoton tayi ta ce

Haba Hafsat yanzu akan wannan magana shine zaki famewa kanki wani ciwon da warke a
zuciyqrki

Rungume nanna tayi ta ce

Meyasa Ammi ta dage akan saian auri Abdulmallik wlh banasonsa nafiso in zauna banyi
aureba ta hakane zan nunawa julabib soyayya ,wlh idan nai aure kaman naci amanarsa
ce


Ba haka bane Hafsat ki sani shi kanshi julabib Allah ne ya bamushi amma ya dauke
abunsa kiyi addua Allah yasa son da kikewa julabib yadawo kan Abdulmallik shikenan
zaki samu saukin rayuwa

Shin Nanna bakisan abunda ya shiga tsakanina da Abdulmallik bane

Na sani nasan komai bana bukatar karin bayani kidauka kaman wannan abun bai
faruba ,ki dauka kaman baayi komaiba,ki daukeshi mijin ƙawarki kawai ki aureshi
kije kicigaba da ibadar aurenki ,ki manta da julabib ki manta da wani an halicceshi
waishi julabib ki manta kunyi zaman mata da miji

Haba Nanna kina mahaifiyar julabib kike cewa in manta dashi

Kwarai ki manta dashi duk da cewa nina haifeshi amma nace ki mqnta dashi ,akullum
idan na kalli julabib nakan tina mahaifinsa amma gashi Allah a daukesa ,nashiga
kunci sosai amma da karfin addua Allah yasamun dangana don haka kema ki miƙa
alamuranki gurin ubangiji

Hawayenta ta share tayi shiru tana tina rayuwarta da julabib

Flash back
Kwance take akan kirjinsa hannunsa daya akan cikinta ya kalleta ya ce

Baby yanzu zuwa dan lokaci zaki haifa mana baby ko ,wow waya hangoni da baby a
hannuna

Juyowa tayi ta shafa gemunsa ta ce

Wlh my bibi koni ina burin Allah ya kaini wannan lokaci kafun Allah ya dau raina

Haba mesa kike fadar haka ai bakisan waye gawar fariba

Hakane bansan waye na farko ba amm da zaa bani zabi zan bada raina ka rayu kaida
baby na nasan zaka kula da Ammina da Nannanmu ga baby na amma ni katafi ka barni
bakin cikin missing ɗinka ma ya isheni nima na bika

Ah yanzu don na mutu kina nufin kema zaki bini ,gaskiya bakimun adalciba abunda
nakeso dake ko bayan raina ki saki ranki kiyi aure kicigaba da walwala ,kiyiwa
mijinki biyya kaman yadda kikemun koma fiye da abunda kikemun

Hawayene suka wanke mata fuska ta ce

Pls my bibi mubar magannan nan don wlh bana tinanin koda halinda zan shiga matikar
na rasaka
Rungumeta yayi yana share mat hawaye ,haka kawai yakeji bazai rayuwa me tsawo tare
sa Hafsat ba ...

Dafata Nanna tayi tai firfigit Ta dawo hayyacinta ta fashe da kuka hakan ya
tabbatarwa da Nanna halin tinanin nata ta shiga ,haka taita rarrashinta har bacci
me nauyi ya dauketa Nanna ta fita ta jawo mata kofar .


Haka ta ta shi jiki babu kwari gaba data.ta rasa ya zatayi ta rushe maganar aurenta
DA abdulmalik haka Ammi taita rarrashinta akan ta amince da maganar auren ,amma
gaba daya batajin zata iyq auren Abdulmallik ,yau ma kaman kullum yasha wanka yazo
gidan ya tura baba me gadi ya kirata babu jimawa ya dawo akan tana zuwa ,ammice ta
nufi dqkinta ta shaida mata ana sallama da ita haka ta fito da hijab ta nufi hanyar
waje Ammi ce ta kira sunanta ta juyo ta ce

Waike Hafsat haka zakina zuwa babu ruwan sha

Shiru tayi kafun tai murmushi ta nufi kitchen ,glass cup me kyau ta dauko ta bule
bold ta dumbuli barkwano ta zuba a cup din kafun ta nufi friedge tana zuwa ta zuba
exotic a cikin glass cup din ta fita girgiza kai ammi tai ta ce

Hafsat bazakiyi hankali ba

Tana zuwa yaata baza baki yana gyara zaman hularsa baijira ta masa tayiba ya karba
ya ce

Godiyq nqke da alama dai na fara samun shiga tunda har tarbata musamman nake samu

bata kulashi ba don tasan neman magana yake ,kallonta yayi ya ce

Anwuni lafiya kawarmu

Bata kulashiba yayi murmushi yana kai kofin bakinsa da sauri yq furzar jin wani
zafin barkwano ya ratsa bakinsa da makokoronsa kallonta yayi yqga kaman batasan
yanayi ba ya ce

Hafsat mena miki haka ,ashe tsanat da kikemun harta kai haka

Kwarqi tafi hakama kuma ta ninka shi sau dubu sabain ,wlh Abdulmallik idan ka
aurenitamkar ka auri tashin hankali ne gidanka da rashin zaman lafiya ,kai bari in
fada maka zan iya kasheka kuma in kashe kaina duk akan wannan lamari

Tabbas Hafsat da na dauka abun naki kaman wasane amma tunda maganar ksa ta shigo
ciki ai lamari ya baci don haka kiyi hakuri idan kika aureni zakiyi farin ciki
marar misaltuwa ,zan maye miki gurbin julabib kai harma na fishi

Wani tsawa ta daka masa ta ce

Karka sake fadan wannan kalma baa halicci wani namiji da zanso sama da julabib ba
sannan baa halicci wanda zausoni sama dashiba ,na yarda an haifeni ne da son
julabib bq koya nayiba ,kasani babu wata fuska da natsansna gani sama da taka babu
wani gunjin sauti dana tsana sama da muryarka babu wata mummunan halitta da banason
gani sama da kai don haka ka tattara kabar mana gidan mu tunda gidan bana hadin
cinya bane ko

Murmushi yayi ko daya maganganunta basu shigesaba shdai abunda ya sani zata gama
bakine daga baya ta dawo soyayyarsa don haka zai iya kokarinsa yaga ya kafa tutarsa
a cikin zuciyarta ganin yanda ranta ya baci yasa ya shiga motarsa mai gadi ya bude
masa ya bar gidan .

Cikin kuka ta koma cikin gida domin ta tina da abun kaunarta julabib .


Tunda ya koma gida gaba daya jikinsa a mace ita kanta zuwaira ta lura da hakan
shiyasa ta ke tambayarsa

Waini dear meya faru ne meke damunka

Kallonta yayi ya ce gaskuya bazan boye miki.ba na janye raga maganar auren Hafsat

What ka janye kuma .......



Share pls
*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*



STORY &WRITEN


BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN


07081940768



LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI


4️⃣



PAGE THREE

Eh Tabbas na janye domin na gaji da fuskantar walakancin dq takemun nibama
walakanciba ki sani duk abunda tamun zan shanye amma bazan juri tana kiran sunan
wancan banzan a gaba na ba kuma koda munyi aure saita kira sunansa don ta bakanta
mun rai nikuma wbunda bazan jura ba kenqn

Haba honey damq na fada maka dole zaka fuskanci matsalloli kala kala karfa ka manta
da babban laifin da kayiwa Hafsat kaine sanadiyar rabatada danta sannan kaine
sanadiyar rabata da mijinta haba ko wannan laifin ta kalleka dashi ai bazata yafema
cikin saukiba nidan abunda nakeso dakai shine dole ka zamabmai juriya a
soyayya ,dole ka jure koma meye sanna kai kokari ka mallaketa ai duk wani qbu da
takeyi saboda taga yanzu baa karkashib ikonka take ba amma kana aurenta kagama da
wannqn babin
Shiru yayi yana nazarin maganarta tabbas a zancenta akwai kamshin gaskiya amma taya
zan fara tunkarar Hafsat da maganar aure haka yayi ta sakawa da warwarewa saukar
muryarta a kunnensa ne yasa ya juyo yana sauraron abunda take fada


Nasan tinanin da kake taya zata yadda a fara maganar aurenku ko ,to ba ita zamu
tinkara ba Ammi itace makaminmu da ita zamuyi amfani wajen cin nasarar wannan.yakin

Haka taita nuna masa matakan nasara a aurensu har shimq yq yarda suj warware akan
zataje ta samu Ammi idan ba matslaa manya su shiga lamarin .

Kaman yadda tayi alkawari hakan ta kasance zqune suke ita da ammi tana shaida mata
sakon da Abdulmallik ya turota akan a bashi dama ya turo wakilansa su nema masa
auren Hafsat ,Ammi tayi farincikin jin hakqn babu musu ta amince da suturo zuwa
anjima zataje ta samu liman suyi magana ,sannan zuwaira ta karisa dakin
Hafsat ,kwance ta sameta tanata sakawa da warwara domin taji duk abunda su ammi
suka fada kenan yanzu idan tayi sanya haka zaa aura mata wanda bataso anya bazata
shiga duniya ba kuwa kowama ya huta to ya ammi zatayi idan ta shiga duniya.wata
zuciyar ta tambayeta saikuma wata ta bata amsa da yazatayi kuma ai itama haka
tayiwa iyayenta tana cikin wqnan zancen ne zuwaira ta shigo dakin bata kalleta ba
balleta mata sannu da zuwa kusa da ita ta zauna ta ce

Haba haba.Hafsat bazaki rungumi kaddara ba ,zaki zauna kiyita zama cikin kunci haba
sai kace akanki akw fara meyasa kike hakane

Dallah rufemun baki munafukq ai nasani duk wannan alamari ke kike daɗa taazzarashi
wato zaa kawo kudin aurena ko to sai ayi auren mugani wlh ko gawata baa ganiba
balle akai cikin gidansa

Subhanallah anya kina cikin hayyacinki kuwa kike irin wannan kalamai ,anya kinsan
meyake futowa daga bakinki ,aure fa akace zaa miki ba wani abu ba kiamince da
Abdulmallik zakiji dadin zama dashi wlh bashida matsala ko kadan matsalarsa daya
kuma ke kanki kinsan ya daina to meya rage dan Allah ina rokonki da ki amince ki
yarda

Bangajrta tayi ta fita a dakin ta nufi bangaren Nanna domin ita ta gaji da jin
abunda take fada mata

Kaman yadda aka shirya Ammi ta kira aminan mijinta guda biyu ta sanar musu idan
babu abunda zasuyi gobe zaazo neman auren hafsat dukkansu sunji dadi sunsawa abun
albarka .

Washe gari

Da musalin karfe 6:09 na yamma Ta dawo daga makaranta cikin gajiya.ga shegen yunwa
dake ibarta har wani jiri takeji ,gaba daya tayi nadamsr zuwa makaranta don babu
abunda ta gane tsabar damuwa ,shigowa falon tayi ta ajiye hakarta tana kallon
Ammita ce

ammi sannu da gida

Yauwa sannu yadai karatunne ya dawo daie haka

Eh wlh ammi gaba daya karatun ya bamu wahala

Ok kije gacab abincinki maza ki dauka

Tashi tayi taje ta dauki abincin ta dawo falo har yawunta tsinkewa yake tsabar
yunwa ,kusa da ammi ta zauna ta fara cin abincin kallonta qmmi tayi ta ce
Yauwa Hafsat dazu DA hantsi magabatan yaron nan sunzo neman aurenki kuma anbasu.har
ansa muku lokaci nan da 2 weeks ga sadakinki ma ankawo

Abincin da takecineya shiga kofofin hancintq aikuwa nan take tari ya sarketa ta
fara ba gaggautawa ruwa ammi tabata sannan tarin ya tsagaita gaba daya idonta sun
fito waje tsabar wahala kallon Ammi tayi ta kalli kudin ta ce

Ammi wani karya naji kunnuwa na sunamun kaman an kawo kudin aurena naji kince kuma
da Abdulmallik

Kwarai ka kuwa kuma auren babu jimawa domin kuba yara bane kuma kunsan juna tunba
yauba

Haba.Ammi wannan wani irin tozarcine ,saikace wata kaza zaku daukeni kubada aurena
kuma nanda sati biyu saikace auren tattabaru gashi yayana baya gari zanyi aure
gaskiya ammi bazan yarda ba

No na kira yayanki shima yana hanya nan da sati daya

Why Ammi meyasa zqki yanke hukunci batare da neman izinina ba kinsan yanzu ni nake
da daman nemaw kaina miji fa

Eh kwarai na sani kuma na zaba miki ,wlh Hafsat idan baki maida hankalinki ki nitsu
waje dayaba zakiga yadda zamuyi nida ke


Tunda Ammi tai mata maganar aure taji abincin ya fita a akanta cikinta ya toshe ko
yunwarma bataji,tashi tayi ta nufi dakinta tai kuka son ronta tana cikin kukw kaman
wacce aka mintsina ta firgita ta tashi dauko daya daga cikin akwatunan ta ta fara
zuba kaya a ciki saida ta shirya tsaf sannan ta ajiye a cikin drower ta dauko
babbar jakarta ta zuba wayoyinta da system da charger saida ta gama hada komai nata
ta nufi bandaki tai wanka ta dauro alwala ta fito ta tayar da sallah ,bata tashi
akan dardumanba saida ta gabatar da isha sannan ta koma kan gado tana saka tana
warwara wata zuciyqrta tana shaida mata abunda take shirinyi ba abu me kyqu bane
amma batada mafitar da yawuce haka da tayarda a mata auren dole ya lalata rayuwarta
har abada domin matikar aka mata auren nan shi zaikaita har cikin wutan jahannama
domin bazata bawa mijin hakkinsa ba kuma bazata masa biyayya ba gwanda kawai tayi
iya kokarinta kar ayi auren don matikan akayi auren nan to an lalata mata rayuwa
tana cikin wannan tinani taji anyi knowking izinin shigowa ta bayar tana share
hawayenta ,Nannace ta shigo tai murmushi irin nasu na manya domin taga hawayen da
take gogewa kusa da ita ta zauna tana dafa kafadarta ta ce

Hafsat shin amminki ta sanardake maganar aurenki da akasa nanda kwanaki jalilan

Wani murmushi ta kakalo tayi ta ce

Eh nanna ta fadamun

To wani hukunci kika yanke

Tinanin da nake kenan har yanzu ban yake hukunci ba shawara nakeyi da zuciyata

Kisani ba koda yaushe zuciya take baka shawara mai kyauba ,a wasu lokutan takan
baka marasa kyau don haka inaso kiyi shawara da kwakwalwarki bada zuciyarki ba

Hakane Nanna nagode

Shikenan yanzu qbunda nakeso ki tashi kiyi istihara saiki kwanta Dafatan Allah ya
nuna miki aurenki dashi alkhairine ko kuma akasin haka

Shikenan Nanna in sha Allah zanyu kokarin yin hakan

Mikewa tayi ta nufi bandakin dake cikin dakin Nanna kuwa harta mike tana kallon
jakar da take shakare da kaya bude jakar tayi taga wayoyi d sauran abubuwan bukata
da sauri ta.bude drower taga akwati ,yawancin kayanta babu ,jinjina kai tayi ta
fita tana zancen zuci ,bayan fitan Nanna hafsat ta fito babu alamar ruwa a fuskarta
ta ja jakarta ta dauki wayarta ta fara dannawa .


Gidan yayi shiru babu qlamar mutane da dukkan alamu kowa na gidan yayi bqcci tafiya
take cikin sqnɗa da akwatinta akanta sannan ta bude kofar falon a hankali ,motarta
ta nufa ta bude boot tq saka kayanta ta jinginq tana karewa gidan kallo wasu hawaye
masu zafi suka wanke mata fuska ji take kaman ta fasa abunda tayi niyya amma ina
zuciyarta ta kekashe bude marfin motar tayi zata rufe taji an rike marfin kofan da
sauri ta fito don ganin waye ,zaro ido tayi ganin .........



Share pls

*DANGINA*
*[AKA RABANI DASU]*



STORY &WRITEN


BY

ADAMA UMAR
SECRET PEN


07081940768



LOVE AND ROMANTIC STORY

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI


5️⃣




PAGE FOUR

Nanna a tsaye tana rike da marfin kofan fitowa tayi jiki a sanyaye Nanna tasa hannu
ta zare key din motan ta kama hannunta suka koma cikin gida bangarenta suka nufa
sannan ta zaunar da ita ta ce

Haba hafsat wani kuskure kikeson aikatawa ne ,shin kinaso tarihi ya sake maimaita
kansa ne ,kinaso kiyi nadamar da haryau Amminki tana cikinsa meyasa haka meyasa
Wlh Nanna bazan zauna a auramun wannan mutumin ba karki manta da abunda yamunfa
kuma yazo yace yana sona na fada masa banasonsa amma duk da haka ya dage saiya
auren don haka gwanda in barmusu garin kowamq ya huta Gwanda tarihi ya maimaita
kansa

Ba haka sakiyi ba yanzu idan kikw tafi idqn yayanki ya dawo me zamuce masa wani
hali kike tinanin zai shiga ,yanzu kiyi hakuri har Allah ya dawo da yayanki lafiya
saiki masa bayani yana da hakkin dakatar da auren ba shikenan ba

Shiru tayi tana tinanin maganganun Nanna tabbas a amaganarta akwai kamshin gaskiya
don tasan matikar ta fadawa yayanta batason auren nan anfasa shima angama nan take
wani kayataccen murmushi ya kamata ta ce

Shikenan Nanna bari zqn jira ba ammi tace yana hanya nanda one week ba
Kwarai yana hanya saiki masa bayani nasan shi zai fahimceki,nasan me Ammi take
tsoro shiyasa ta amince da auren nan

Haba Nanna kenan kinq nufin kinsa asalinmu kumq kinsan tarihin su Ammi da Abba

Kwarai nasan komai amma nayiwa mahaifiyarku alkwari bazan taba fadawa wani wannan
zance ba matikar ba bukatar hakan ta taso babu yadda aka iya ba ko kuma ita ta
amince

Dan Allah Nanna kiban labarin asalinmu daga ina muke mu yan wani garine suwaye yan
uwanmu ki taimaka


Bazaki taba jin wannan zance a bakinaba matikar ba wannan dalilai biyu dana fada
miki ba

Shiru tayi don tasan tunda tace bazata fadaba to bazata fadaba .

Shirye shiryen biki ya kankama Ammi ta dage tanqtq hidima taje gurin gyaran jiki
tayi booking amma tabita akan ta shiryq ta fara zuwa sam taki haka ammi tarabu da
ita don tasan ita da kanta zata nema a mata kaman kullum suna zaune a falo
jewelry's ne da yawa a gaban Ammi ta rasa wanne zata zabawa a marya itako gogar
taku kaman bata falon ,zuwaira ce tai sallama ta shgo Ammi ta amsa cikin faraa da
murmushi kusa da Hafsat ta nemu giri ta zquna ko kallona batayi ba dayake batada
zuciya ta ce


Amarya bakya laifi ,kinsan gidan nan yadda ya dauku haramar kamshi kuwa tundaga
bakin gate nake jin kamshi kowa yasan tabbas gidan nan akwai amarya

Banza tai da ita kaman batasan tanayi ba ta juya ta kalli Ammi dake murmushi ta ce

Yauwa Ammi dama Abdulmallik ne ya turoni ya ce wai ku shiryq gobe abokansa zasu
kawo kayan aure da abubuwan da bazaa rasaba

ah masha Allah to shikenan Allah ya kaimu lokacin

Yauwa Ammi amarya bata fitar mana da anko bane don kinsan nice babbar kawafa

Ah gaki gata bi narasa wani irin aure Hafsat zatayi babu abunda take shiryawa ko
gyaran jiki nida kaina naje na biya kudi amma nayi nayi taje sam taki ,nq tamayeta
idan batason sintirin zuwa ne in kira wakiliyarsu tazo qmma ta ce itada ba auren
soyayya zatayiba wani gyara zatayi Gatanan da ki mata fada idan zata gyara ta gyara
ehen
Kallon Hafsat zuwaira tayi ta ce


Haba besty me kike nufi kenan don bakyason Abdulmallik shikenan bazaki gyara
jikinki bw kumw bazayi shirin bikiba to idaj bazakiyiba mu zamuyi don haka zan samu
sauran kawayenmu na school na fada musu kuma nida kaina zan tafi kwari in fitar da
anko inke bazakiyiba ni zanyi

Dallah malama banason shishigi kawai kiyi sabgar gabanki ,tsabar rashin zuciya
zaayi miki kishiya shine kik wannan rawar kafar kije can kiji da bikin mijinki babu
ruwanki dani kowa yayi sabgarsa na jima da fada miki hakan

Ke Hafsat anya kinsan waye a gabanki kuwa zuwaira ce fa your pen friend me Inna ke
nufi karkiga anbarki da hankalinki ki nemi rainqwq mutqne wayo sai yanzu na tashi
na faffalla miki mari kinsan zan iya.koran kaiki gidan mijine zan.miki shegen duka
ba damuwata bane


Haba Ammi ai abun yayi yawa ga mari ga tsinka jaka nasani ko kaffara bazanyi
ba.zuwaira ita ta fadawa mijinta.akan ya nemi aurena nikuma basonshi nakesba
aisaiya hakura amma kun nace ina rokon Allah.ya.dauki rayuwata kafun auren kowa mq
ya huta


Ko kin mutu sai ankai gawarki gidansa kuma shine zaisaki a kabari


Ah ah Ammi Hafsat tana bukatar lallabine a ayanzu saikuma anusheta muhimmancin
aurensu bawai a zageta ko.duka ba

Kirabu da yarinyarnan dani take zancen ba taga na barta bane ahiyasa take duk
rashin kutumcin da takeyi

Mikewa tayi

2 / 7