Advertisements
Chapter 35 Reading MUTALLAB Sirrika Masu Kisa By Nimcyluv BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

MUTALLAB Sirrika Masu Kisa By Nimcyluv

Author :  Nimcyluv Category :  Complete Novels

Chapter   35 / 64

102K to 105K   out of 191K words

son aurar dani ne?"""

"Zama ya yi yana kwantar da muryarsa ya ce ""Ba komai Jaanah, rayuwa ce ta yi tsada tun bayan rasuwar"

"iyayenki nake ta fama yanzu ™arfina ya ™are idan na aurar dake wani nauyin zai sauka a kaina"" tana kuka ta ce ""Shekaruna 14 baba, aurar dani shine mafita? Shikenan na amince amma ina dukiyar da aka mutu aka bar mini?"" Jikin Baba na rawa ya ce ""Wacce dukiya? Waya faWa miki na sake jin wannan maganar sai ranki ya yi mugun Saci Jaanah"" fashewa ta yi da kuka sosai, tabi Baba da kallo har ya fita waje. Ta yi kuka"

son ranta a lokacin an yi sallar magariba ta saka hijabi ta saka takalmi ta nufi inda zata samu Mutallab.

"Yana zaune a waje kamar koyaushe shi kaWai ya hango ta, ya yi ta kallon ta yana mamakin ina zata? Sai"

"yaga ta nufo shi, tana zuwa ta dur™ushewa a gefen ™afafuwansa ta fashe da kuka mai raunata zuciya. Ya yi shiru don bai san me zai ce mata ba, ganin kukan ba mai ™arewa bane ya saka ™afa ya zungure ta, yana mi™ewa tsaye ta mi™e tana kare fuskarta ya dinga kallon ko'ina yaga ba mutane ya yi ™asa da murya ya ce"

"""Mee?"""

"""Baba ya ce an kawo sadakin auren mu Wazo"" sai ta kuma fashe masa da kuka jikinta har rawa yake, ya"

"bubbuWe idanunsa yana dire kokarar hannunsa a ™asa, bunjimar rigar farautar dake jikinsa na kaWawa."

"""To, shi ne na kuka?"""

"""Na tuna abin da malam ya ce ne, idan an yi musamman ™anan yara masu ™arancin shekaru wai ana"

"samun yoyon fitsari idan akai tarayya tunda shekarun basu kai ba, kuma idan yarinya ta samu ciki zata iya mutuwa, kaga shekaruna 14 fa"""

"Ya bubbuWe manyan idanunsa da tsoro shima ya ce ""To! Mun shiga uku, kar mu yi yoyon fitsari to"" ya"

faWa cikin nutsuwa da alamun gaskiya cikin maganarsa.

"""To ai kai namiji ne, ni ce zan samu cikin ai kuma ni ce ™arama"""

"Ya ce ""Ni kuma nine mai yin cikin ai, shekaruna 14 nima"""

"""Innalillahi yaya za mu yi, ashe da gaske malamin ™awa'idi yake?"" Ta sake fashewa da kuka tana girgiza"

"kai, ya matsa dab da ita ganin kamar zata fita hayyacinta ga dare ya yi, ya du™a fuskarsa daidai tata ya ce"

"""Jaaa. """

"Ya kira sunan nata, ta ce ""Jaanah ne sunan ai"" ""Oh... Da gaske ban isa bawa mace ciki ba, ni tsoro nake ji"

"kije gida ba abin da zai faru ko?"""

"""To ba za ka yi mini cikin ba? ˜awayena sun ce idan aka biya sadaki wai amarya na biya"""

"Ya dinga kallon ta, da gaske suka su biyun shekarunsu sha huWu, amma ™uruciyar Jaanah ta girmama. Ya"

"numfasha ya ce ""To za ki biya ni sadakin kenan yanzu?"" Ta™i magana ta dinga kuka tana diddire masa ™afa ya sake matsawa kamar zai kama hannunta sai ya fasa, bai tsammata ba yaga ta Wora kanta a gefen ™irjinsa ta fashe da wani irin raunataccen kuka, bai ce mata uffan ba ta dinga kuka hawayenta na ji™a masa riga, da gaske yana son ce mata wani abu amma ba zai iya ba. Ta janye kanta a hankali ta ce ""Zan"

"je gida"""

"""Hmmm"" ya ce tana kallonsa sai ta juya tana share hawayen idanunta shima ya juya mata baya zai tafi"

"gida, ™arar sautin muryarta ya ji a kunnensa, tana kiran sunansa, ya ji kiran ya sauka har ™asan zuciyarsa,"

"da sauri ya juyo wani irin sandarewa Mutallab ya yi ganin yadda Jaanah ke salati tare da ihu wuta na cin jikinta, cin bana wasa ba, wuta ce wacce kamar gas ya kama haka take ci a jikin Jaanah."

"[1/7, 9:35 PM] Sis Fauzy: Chapter 26: Who are you"

Paid book #500

Pay before you read 08164069385

Follow on Arewabooks

Not edited

"Jaanah was screaming, tana ihu da salati lokaci guda tare da kiran sunan Mutallab,wutar na ™ara cin"

"naman jikinta. Mutallab ya yi cak idan akwai abin da ya tsayar da tunaninsa waje guda, ™wa™walwata ta daina moving ™irjinsa ta daina bugawa shine ganin Jaaanah na ci a cikin wutar, and he can't do anything to help her. Wani irin mazari jikinsa yake kamar ana kaWa masa ™ahon gangi cikin azama ya ™arasa wajanta daidai lokacin ya daina jin sautin fitar muryarta, yana ™o™arin cikin wutar ya bata kariya da gangar jikinsa ya ji an yi saurin janye shi. ""Ina zaka? Cikin wutar zaka shiga? Kar a kwashi gawa biyu domin ita kam ta riga data rasu sai ha™uri"" Mutallab ya juya ya zubawa Kimiyya idanunsa da suka koma launin rawa-rawa kamar bana mutum ba, yadda ™irjinsa ke rawa haka haka gangara jikinsa ya kasa furta komai a lokacin mutane har sun fara taruwa, maganar ta isa kunnen Baba Umaru sai gashi da sauri yana"

kururuwa.

"""Ya kashe mini yarinya, ya kashe ta jama'a a taimaka mini kaico, wayyo Zaraha'una wayyo Jaanah"" kuka"

"yake da ™arfinsa mutane suna ri™e shi, lokacin wutar ta mutu dalilin ruwan da aka she™a mata, sai dai Jaanah rai ya yi halinsa, she died with smile on her. Baba ya ™an™ame gawar Jaanah da jini ke zuba wajan wutar da ta ci ""Allah Ya WaiWaitaka in sha Allah a rayuwa ba zakaga daidai ba, ba zaka taSa yin farinciki ba, ka kashe mini marainiyyar Allah"" ya girgiza kai sai ya kuma rushewa da kuka ya ce ""Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wanne irin zalunci ne wannan? Wanne irin rashin imani ne, lafiyar Allah yarinya ta fito ashe wajanka ta zo shine ka kashe ta kamar yadda ka kashe matar da za'a aura maka ta farko? Kenan yanzu"

"duk ´an'matan unguwar nan sai ka kashe su?"""

"""A'a baba bafa shi ya kashe ta ba, tsautsayi ne kuma lokacinta ne ya yi kamar kowanne mumuni"" Kimiyya"

"ya faWa a raunace idanunsa kuma akan Mutallab ganin jikinsa har yanzu rawa yake yi, ya kafe gawar Jaanah da idanunsa."

"""Kenan ™arya zan yi masa? Kowa yana da labarin Diyna yadda ta babbake a cikin wuta a ranar da yaje"

"wajanta, gashi yanzu ma a ranar da aka kawo kuWin sadakin aurensa shi da Jaanah itama ta babbake a wuta, ya kashe har mata biyu daga cewa za'a aura masa su waye ya san gawarar gaba? Wallahi ran Jaanah ba zai taSa tafiya a banza ba"" Ya sake rushewa da kuka ya ce ""Ashe shi ya sa Wazo da yammaci ya je mana har cikin gida yana ™o™arin bin bayanta zuwa cikin Waki, bamu sani ba yana shirya yadda zai kashe ta ne, Malam Abdullahi ya yi haihuwar asara ya haifi tsinanne"". Ran kimiyya a Sace ya ce ""Malam ko ´an'sanda zaka kira dole sai bincike ya nuna musu shaidar gisan da ya yi wa Jaanah, kuma they find"

"nothing, actually nothing, mu Wauki ™addara"""

"""Dame yake ta™ama da zai dinga kashe rayukan raya mata daka ance za'a aura masa su? Allah ya isa na"

"wallahi"" cewar Baba Umaru."

"Mutallab ™afafuwansa na rawa ya dur™ushe dab da inda Baba Umaru yake zaune, ya saka hannuna yana"

"shirin ri™e hannun Jaanah Baba Umaru ya ce ""Karka sake ka taSa mini gawar yarinya bayan ka kashe ta"" Moh, ya Waga idanuna ya kalli Baba Umaru dasu cikin sauri Baba Umaru ya Wauke kai ya kasa cewa komai,"

"Mutallab ya dam™e hannun Jaanah muryarsa na rawa tana fita da ™yar ya furta ""Na faWa kada a aura mini ke, ni ina da taSin hankali ina da matsalar ciwon hauka. ,"" ya yi shiru ya sauke Soyayyiyar ajiyar"

"zuciya ta cikin ™irjinsa ""Da gaske ni na kashe ta ban sani ba, sai dai ba zan iya kashe Jannaa ba, ki yafe mini na kasa ceton ki na kasa, na kasa kamar Wayar"" ya kasa cigaba da kukan lokacin Aby ya zo hankali tashe, ya dinga Wauke Mutallab da maruka babu adadi babu kalar zagin da bai yi masa ba sai wanda ya"

manta.

"""Ko shakku ba zan yi ba kai ne ka kashe musu ´a, irin mutuwa Waya Jaanah da Diyna suka yi, ni dai ka"

"zame mini masifa a cikin rayuwata ka cutar da zuciyata ka saka mini rauni da giSin da ba zai taSa gogewa ba"" sai kuma ya fashe da kuka jin yadda ake cewa Mutallab Šan'malam ya kashe Jaanah da Diyna. Har aka Wauke gawar Jaanah Mutallab ya kasa motsawa, Kimiyya nata bashi ha™uri da ban baki. Suna nan sai kuma jiniyar motar ´an'sanda ta karaWe wajan. A ruWe kimiyya ya ce ""Mutallab tashi ka gudu, police ne ka tafi kar su kama ka"" amma ko gezau bai ba har suka ™arasu wajan suka zagaye su a gun. "" Heee, Who"

"is Mutallab?"""

"""Gani"" Mutallab ya ce."

"""Arrest him officer"""

"""Wallahi bai kashe kuwa ba, kar ku tafi da shi don Allah, Please let go of him, wallahi bai kashe ta ba ina"

"da wajan sanda abin ya faru he is innocent"" ko ta kan kimiyya basu bi ba, su kama Mutallab zuwa cikin mota, tare da jan motar da gudu."

"Shi ba zai iya cewa ga adadin lokacin daya shafe cikin wajan da aka saka shi ba, yana takure ya yi shiru"

"tare da tunani fal a cikin ransa, mutuwar Jaanah ta tsaya masa a zuciya, tun ihun da ta yi na farko tare da sautin daya fito da kiran sunansa ya ji wani abu ya tokare masa ma™oshi, ya tsaya masa a ™irji ya haWu da ciwon dake wajan na rasuwar Muneeberh suka tattaro tare da zame masa wani tabo, tabon daya gino a zuciyar kamar Wigar dalma a fata wanda ba zai taSa gogewa ba da wannan raWaWin da Wacin zai wanzu a duniya. Ya ji tsoro da shakkar sake haWa idanu da kowacce Wiya mace a duniya. Yana dur™ushen aka buWe"

"™ofa, bai Wago ba kuma motsa ba wani ya ce ""Sir wannan shine wanda ake tuhuma"""

"""Wanda ya kashe ´an'mata har biyu? Me suka yi masa? A wajan bada statement me aka ce?"" Officer ya"

"ce ""Sir, yarinyar daya kashe ta farko sunanta Diyna, ita ce yarinyar da mahaifinsa ya bashi umarni ya je ya gano ta idan ta yi masa a Waura musu aure, a ranar da ya je gidansu Diyna a ranar ta mutu cikin dare ta mutu tana ihu tare da kiran sunan Mutallab, wanda yake bada tabbacin shine ya kashe ta. Yarinya ta biyu kuma ita ce Jaanah, bayan rasuwar Diyna mahaifin Mutallab ya sake bashi umarni ya je ya gano ´ar wajan Malam Umaru mai suna Jaanah, ya je har ya ce ya amince da auren, a ranar da aka kai sadakin auren Jaanah ta fito daga gidansu cikin dare zuwa wajan Mutallab a can inda yake zama, ba'a san abin da ya faru sai gani akai wuta tana ci a jikin Jaanah shi kuma Mutallab Win na tsaye a wajan ya™i taimakon ta,"

"duk da irin kiran sunansa da yarinyar take yi matsayin ya zo ya taimaka mata"""

"Dig Johar ya jinjina kai ya ce ""Ya kashe mata biyu kenan? A lokacin da ake shirin aura masa su, baya son"

"auren ne ko wani laifi suka yi masa wanda suka cancanci ya kashe su? Hakan yana cewa duk macen da akai yun™urin aura masa zai kashe ta ne kafin auren?"" Dig Johar ya ™are maganar cikin Wacin zuciya musamman idan ya sake kallon Mutallab sai ya ji kamar duniyarsa zata jirkice ne. Officer Win ya rusuna"

"cike da girmamawa ya ce ""Sir, a record ma kamar an taSa kawo shi cikin wajan na"""

"""Na sani"" cewar Dig Johar. Kana ya numfasa ya ja kujera ya zauna idanunsa akan Mutallab da ya™i Wago"

"kansa, balle ya kalle su Dig Johar ya ce ""Kuma lafiya yake baya shaye-shaye? An tabbatar?"" Officer ya ce ""Binciken da muka yi ya nuna baya shaye-shaye, kawai dai shi mafauri ne yana shiga jeji ya yi abin da zai ya kamo naman dawa"". ""Good, lafiyar ™wa™walwa fa?"" Officer ya ce ""Sir ban sani ba"" Dig Johar ya Wan yi murmushi iya laSSansa kana ya ce"

"""Mutallab"" a hankali Mutallab ya Wago kai ya kalli Dig Johar, kallo Waya ya Wauke kai. ""Mene matsalarka"

"da matan da kake kashewa?"". Mutallab ya yi shiru, domin bashi da abin faWa da gaske ""Yin shiru ba shine mafita ba, ka bani haWin kai mu yi magana kai yaro ne shi ya saka nake tauysawa ™uruciyarka"""

"""Bani da matsala"" Dig Johar, ya ji muryar Mutallab ta sauka a cikin kunnuwansa a kumbure cikin rashin"

"tsoro kafin ya yi magana ya sake ji ya ce ""Idan maganar kisa ne, e da gaske na kashe su a shirya kashe ni domin sau™a™a mini zaman wajan nan, Moh ya kashe Diyna da Jaanah tabbas"" baki buWe Dig Johar ya ce ""Kana cikin hankalinka kuwa? Ka kashe su kace fa?"" Mutallab ya Wago rinannun idanunsa kamar za su zazzago waje ya ce ""Gaskiyar kenan, ko gobe aka nema ma™ala mini wata macen za'a wayi gari babu ita a"

"duniya"""

"""Ko yana da matsalar ™wa™walwa ne?"" Dig Johar ya bu™ata yana juyawa tare da kallon officer."

"""Sir, sai dai a yi bincike a family nasa, akwai wata ´ar'uwarsa a nan waje"""

"""A binciko yanzu, immediately"""

"Bayan fitar Officer, Dig Johar ya yi shiru yana ta kallon Mutallab babu jimawa kuma officer ya dawo ya ce"

"""Sir, Mutallab yana da taSin hankali, domin har takardar zuwa Dawanau likita ya bashi, kuma dai ba'a shari'a da mahaukaci"" kafin Dig ya yi magana Mutallab ya ce ""˜arya ake yi, lafiyar tunanina lau, ba mahaukaci bane ni, na kuma kashe Diyna da Jaanah tabbas, na kashe su da hannuna ™warai basa raye tabbas haka ne"" Dig ya mi™e tsaye ganin jikin Mutallab na rawa ya kalli Officer ya ce ""Ga alama nan ma ai ya nuna, kaje waje ina zuwa"" Officer ya jinjina kai ya yi waje, Dig ya dur™usa gaban Mutallab ya yi ™asa da"

muryar ya fara masa magana.

"Tana tsaye a reception idanunta ya kumbura saboda kuka ta ji an ce ""Yaya"" ta yi sauri Wago kanta,"

"hannunsa ta ri™e ta ce ""Allahamdulilah na Ammo sun sake ka, ma sha Allah"""

"Ya jinjina mata kai, sai kuma ya yi shiru yana kallon Sa'adah bai magana ba yana ji ta kama hannunta"

"suka fice, a bakin gate na shiga state cid Win suka ™ara cin karo da Prof ya dinga kallon Mutallab, 2 times yana ganin yaron nan a wajan nan wanne irin babban mai laifi ne shi? Ya ji yaron bai masa a zuciyarsa baya jin tsanar mutane amma kana ganinsa ka san bashi da cikakkar tarbiyya. Ya yi saurin shigewa ciki, Mutallab kuma fuska kamar narkakken hadari haka ya haWe fuska idanunsa na shigewa ciki sai WaWWaga kafaWa yake yana jin Sa'adah na cewa ""In sha Allah ka yi zuwan ™arshe wajan nan, babu ™addara da zata"

"sake sawa kazo, babu bincike ba komai kawai a kama ka? Haka ake yi daman?"" Shi dai bai kulata ba, har"

suka shiga napep ya kifa kansa a ™arfen jikin napep Win yana fisgar numfashi can ya Wago ya kalli Sa'adah

da ™yar ya iya juya bakinsa ya ce

"""Yaya"" ta kalle shi ta ce ""Autan Ammo ya aka yi? Sun dake ka ne? Mene ya faru?"" Ya jujjuya idanunsa ya"

"ce ""Jaaanah "" Ya yi shiru sunan ma ya tsaya masa a ™irji Sa'adah ta ce ""Sai dai addu'a kwanan Jaanah"

"biyu a gidanta na gaskiya, ka yi mata addu'a tare neman gafara wajan Ubangiji"""

"""Hmmm"" ya ce daga nan bai sake furta ko a ba, duk da jan shi da surutu da Sa'adah ke yi har suka isa"

"gida. Sa'adah ce ta fara yin sallama ta shiga, lokacin Malam yana yin alwala hannunsa ri™e da buta da wani zabgegen carbi a gefe, kafin ya amsa Mama Zaituna ta fito tana cewa ""Basu bari kin ganshi ba ko? Kema dai Sa'adah iska na wahalar da kayan kara, sun ri™e shi kenan fa idan ba sa'a akayi ba sai dai mu Wauki gawa"" Sa'adah ta yi murmushi ta ce ""Mama kenan, Allah baya nuna mana wannan ranar ba, tare"

"muke da shi ma"" da sauri malam ya mi™e tsaye yana faWin ""Shi wa?"" Ta ce ""Mutallab, Malam"""

"""Su ´an'sandan wiwi suke sha da suka sake shi?"" Sa'adah ta ce ""To dai sun sako shi, da kuma yana da laifi"

"ai ba za su yi gaggawar hakan ba"" Malam zai yi magana ya fasa ganin wanda ke tsaye ya dinga kallonsa ya kasa cewa komai. Shi kuma ya fesar da iska daga cikin bakinsa ya ce ""Sannu Aby"" tsaki ya yi tare da yin waje bai amsa gaisuwar Mutallab Win ba, shi kuma ya yi tsaye ya kasa shiga Wakin Ammo, ya jima a nan sai kawai ya Wauki buta ya zuba ruwa ya yi waje jin ana cewa a daidaita sahu. Mama Zaituna ta shige"

Waki

"Sa'adah ta girgiza kai ta ce ""To shi malam tunaninsa yi wa Mutallab aure shi ne mafita? Don Allah Ammo"

"shekarar Tayo nawa a duniya, anya baku shiga cikin lamarin Ubangiji ba? Me ya Wauka a duniyar mema ya sani da Wan ™aramin yaron da ya kamata ace yana ™ar™ashin kulawarku wai shine kuke tunanin yi masa aure? A wannan zamanin masu hankali ma ya suka ™are da lamarin aure balle Mutallab? Haba don"

"Allah"""

"Ammo ta ce ""Wa'azi kenan kike mini Sa'adah?"""

"""Nina isa Ammo?"""

"""To sai ki bari idan mahaifin naku ya shigo ki sanar da shi kin gane ko? Bana bu™atar jin wannan magana"

"ki kiyaye"" a sanyaya Sa'adah ta ce ""In sha Allah, amma zan sanar da Anty Hameeda halin da ake ciki Ammo"""

"""Ki ce mata me? Ubanku na cin zalin Wan'uwanku? Ko ubanku na shirin aurar da Wansa? Ko Wan'uwanku"

"ya kashe mata har biyu? Me za ki faWa mata daga ciki? Ri™e shin da hukuma ta sake yi, ko batun taSin hankalin nasa?"" Ta jero mata tambayar a raunace, Sa'adah ta kalli Ammo jin yadda muryarta ke yin rawa kafin ta ce ""Duk abin da ya kamata na faWa masa zan sanar da ita"" Ammo ta ce ""Ban amince ba ko a kan idanuna ko a bayan idanuna idan kin san ni ce uwarki, tabbas ban amince ba"" ta ce ""Yadda kika ce haka za a yi, amma Ammo har a zuciyarki kina jin kun bawa Mutallab tarbiyya da kulawar daya kamata a bawa kowanne yaro? Kin san yadda tarbiyyar namiji take da wahala kuwa? Gwara Wiya mace a koyaushe tana tare da iyayenta, Ubangiji yana cewa ´a´a kiwo ne a gare ku, lallai akwai watarana da zata saka ku dawo gare ni na tambayi yadda kuka gabatar

35 / 64