Advertisements
Chapter 22 Reading Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   22 / 41

63K to 66K   out of 121.6K words

siyo abubuwan da ake bu?ata sai mu fara".

Ta ce"Na gode".

Haka kuwa aka yi, washegari Sadiq ya fara koyawa Nuratu karatu, kuma tana ganewa sosai, Hajiya tana nesa da su tana kal???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?lonsu, ta fi gane na islamic Win, don haka sai suka karkata a nan, kullum da asuba za su yi Qur'an, da daddare kuma hadisai, dama Sadiq shi ne hafizin gidan, shekaru uku ya ware ya yi karatun addini.

Wannan karatun sai ya sa suka samu kusanci da Sadiq sosai, ya fara burge ta, idan yana karanta mata tarihi sai ta ji kamar su kwana a haka, sanadin karatun nan dai har suka yi musayar lamba suka kuma Waura zumunci ba irin wanda yake tsakaninta da sauran mazan dake gidan ba.

Zuciyar mace tana da rauni, tana da saurin mantuwa, ba tare da Nuratu ta ankara ba ta faWa kogin soyayyar Sadiq, duk da har lokacin Abdul yana ma?ale a zuciyarta, takan tsinci kanta da son kasancewa da Sadiq a koyaushe, idan yana yi mata karatu sosai take shiga shau?i, lokuta da dama idan ya yi wani abun tana ganin kamar shi ma ya kamu da son ta, haka take gani kamar yana yi mata kallon su, sai dai kuma ya ?i furtawa, a yadda ta karance shi ?an'mata ba sa gabansa, ba ta taSa jin ko cikin wasa an yi zancen buduruwarsa ko wani abu mai ala?a da soyayya ba, harkar gabansa kawai yake yi, ba ta taSa cewa tana son wani ba, don haka take ta jiran lokacin da Sadiq zai furta yana sonta, tare da yin abubuwan da ta san suna burge namiji, ko kasuwa zai je ko wani aiken sai ta ce za ta raka shi, a gaban Hajiya dai ake yin komai, kuma Nuratu ta san a yadda Hajiya take da fahimtar halin da mutum yake ciki zuwa yanzu ya kamata a ce ta gane wata ala?a na son shiga tsakanin ?a?an nata, amma ta yi kamar ba ta gane ba.

Sannu a hankali so ya fara yi wa zuciyar Nuratu kanta, ?arshen sha?uwa dai sun yi da Sadiq, har ta kai idan yana kasuwa tana kiransa a waya kawai ta ce masa ta kira ne don ta ji lafiyarsa, ya ce mata ya gode shi ma ya matsu ya dawo ya ganta, haka kawai zai siyo mata wani abun sha'awar ya ba ta kyauta, yanzu da daddare har chart suke yi bayan sun tashi daga karatu, firar dai ta duniya ce kawai, duk yadda ta so ta bugi cikinsa a kan sanin ko yana da buduruwa sai ya goce, ya sha faWa mata shi babu soyayya a gabansa, saboda ba zai samu wacce za ta so shi ba, wannan maganar tashi tana ba ta mamaki.

Akwai ranar da suna chart irin haka, ta ce"Yaya Sadiq kana da kirki sosai, ka san darajar mutane, ko mahaifiyarka ta ce duk cikin ?a?anta ta fi jin daWinka, duk matar da ta aure ka za ta yi dacen miji na gari".

Ya turo mata dariya ya ce"Idan zan yi auren kenan".

Ta ce"Wai ni me yasa kake yawan cewa ba za ka samu mai sonka ba?"

Ya ce"Kawai dai haka nake gani".

Ta ce"To Yaya Sadiq daga yau ka daina ganin haka, don ka samu, ?anwarka kuma Walibarka Nuratu tana sonka tana ?aunarka, kuma tana fatan zama matarka".

Ta yi saurin kashe data, don ta ji kunyar kanta, kuma tana tsoron jin amsar da zai ba ta, idan ya ce ba ya son ta ya za ta yi? Yadda ta kamu da son shi har mamakin kanta take yi.

Can bayan magriba ta sake kunna data ta ga ashe ma da ya duba sa?on bai ce mata komai ba, yau Win kuma sai ta ji tana kunyar haWuwa da shi, tana jin dawowarsa ta ?i fitowa, saSanin da da ita ce take zuba masa abinci, su yi ta fira, ko da lokacin karatu ya yi ma sai da ta ?ara lokaci ba ta fito ba, har Hajiya tana cewa"Yau ba ku da karatun ne?"

Ya ce"?ila ta gaji".

Hajiya ta ?wala mata kira, ta fito tana satar kallon Sadiq wai ko za ta iya gane inda sa?onta ya dosa a kan fuskarsa, amSa ba ta ga komai ba, fuskarsa tana nan yadda ta saba gani, Hajiya ta ce"Yau ba za ku yi karatun ba? Ko kin gaji ne?"

Nuratu ta ce"Wanka na yi, dama zan fito, Hajiya ya zan gaji ni da ake taimakawa?"

Ta kalle shi ta ce"Yaya sannu da zuwa".

Ya ce"Yawwa, to yau babu jakar kuma?"

Ta yi Wan murmushi, ta koma ta Wakko, ya buWe littafi yana kallo ya ce"Nuratu me wannan sa?on naki yake nufi? Da gaske sona kike yi?"

Ta ce"E duk da na san ka wuce ajina, wallahi laifin zuciyata ne, na kasa jure yadda nake ji a kanka".

Ya yi shiru tsawon lokaci kamar ba zai ce komai ba, sannan ya ce"Anjima za mu yi magana ta waya".

Sannan suka fara karatu kamar ba su tattauna komai ba.

Wajen sha Waya na dare ya kira ta, ta Waga gabanta yana faWuwa, suka gaisa ya ce"Na bar ki da fargabar jiran amsa ko?"

Ta ce"Sosai ma, inda ba ka kira ni ba ba zan iya bacci ba".

Sadiq ya sauke numfashi ya ce"Nuratu na gode sosai da nuna ?aunarki a gare ni, to amma sai dai..."

Ya yi shiru, ya kasa ?arasawa.

Ta ce"Yaya Sadiq idan nan yi maka ba wallahi babu wata matsala, ni dama na san ka wuce ajina kuma ?ila kana da wacce kake so".

Ya danne maganar da ya so faWa mata da farko, ya ce"Sam ban fi ?arfinki ba, idan ?ar ?ure za a yi ma sai dai a ce kin fi ?arfina, sannan ni ba ni da kowa wallahi, ba na soyayya don ba ta dace da ni ba, sai dai ina fatan yanzu na fara, na kuma samu mai share mini hawayen da na jima ina zubarwa a kan soyayya".

Ta ce"Kenan a baya ka yi soyayya?"

Ya ce"Na yi soyayya amma ta wauta, wacce ba ta amfane ni da komai ba sai nadama, sannan ta bar mini tabon rai".

Nuratu ta ce"Subhanallah! Yaya me ya haWaku da ita kuka rabu?"

Ya ce"Nuratu ?yale zancen nan kin ji? Na amince da soyayyarki, sannan ni ma na so ki tun kafin yau da kika furta mini".

Ta sauke ajiyar zuciya tana cewa"Na gode".

Ya ce"Ki yi bacci gobe za mu yi magana, kafin nan soyayyarmu tana da sharaWi, sai kin amince za mu cim ma gaci, ?in amincewa daidai yake da rugujewar ala?armu".

Ta ce"Wannan wane sharaWi ne Yaya?"

Ya ce"Za mu yi soyayya ba tare da Hajiya ta sani ba, za mu kaucewa duk wata hanyar da za ta gane akwai soyayya a tsakaninmu, sannan don Allah kar ki tambaye ni dalili". Ya katse wayar.

Ta bi wayar da kallo zuciyarya cike da mamaki, ta ya zai ce haka? Indai soyayyar aure ce ai dole Hajiya ta sani, to me yake nufi da ita? Da wannan tunanin bacci ya Wauke ta.



08028966015
30

Washegari duk yadda ta so daurewa sai da ta tambaye Sadiq dalili, da daddare tana kitchen tana ?arasa tuwo, ya shigo idan ta gani daidai ma kamar a tsorace yake, yana Wan waiwaye kar wani ya gansa, ya ce"Na zo zance".

Ta yi dariya ta ce"Haka ake zuwa zance? Ai sai dai ka bari idan na shiga Waki ka aika a kira ni".

Ya zaro ido ya ce"Wa zan aika? Rufa mana asiri, wannan soyayyar tamu fa ta sirri ce".

Ta ce"Yawwa don Allah me yasa ba ka so Hajiya ta sani? Ni a ganina za ta yi farinciki da hakan".

Ya ce"A'a, ba za ta yi farinciki ba, na san ba zai yiwu ta yarda ba, shiyasa na faWa miki mu yi komai cikin sirri".

Za ta yi magana suka ji muryar Hajiya ta taho kitchen Win tana cewa"Nuratu ba ki gama ba?"

Sadiq ya fara kame-kame, ya buWe kular sauran abincin rana yana cewa"Ai Hajiya ni ma yunwa ce ta kawo ni kitchen Win, bari na ci wannan sauran".

Hajiya ta tsaya tsam tana karantar yanayinsu, Sadiq ?irjinsa sai bugawa yake yi, ya zuba abincin ya fice. Hajiya ta bi shi da kallon tuhuma, sannan ta ?arasa shiga kitchen Win ta ce da Nuratu"Kar zaman waje Waya ya sa ki manta Sadiq ba muharraminki ba ne, ki dinga kame jikinki da shi".

Jiki a sanyaye ta ce"To Hajiya".

Bayan sun gama karatu yau ma sai da suka yi waya, kuma da ta sake yi masa zancen, ya ce ta bar maganar kawai. Daga nan ta share, suka fara soyayyarsu a Soye, cikin ?an?anin lokaci sha?uwa ta shiga tsakaninsu, da soyayya mai tsanani, wacce har ta saka ta fara mantawa da Abdul, lallai zuciyar mace kulawa kaWai take bu?ata.

Yayinda Nuratu ta sakankance a duniyar sabuwar soyayya, shi kuwa Kabir yana can yana ta shirinsa, sai da ya gama komai hatta gidan da za su zauna ya kama haya sannan ya sanarwa da Baba zai turo a yi magana, Baba ya ce babu wata damuwa dama shi yake jira, babu wanda ya sanarwa Nuratu haka aka karSi kuWin auren Kabir dubu Wari da hamsin har sadaki, sai a ranar Baba ya kira Hajiya suka gaisa da fara'arsa ya ce"To Hajiya sai ku fara shiri fa, yau an kawo kuWin auren ?ar taki, an tsayar da rana sati huWu masu zuwa, ina ga satin auren sai ta dawo gida tun da a nan za a Waura, inyaso sai a mayar da ita can Win, ya ce har ya kama haya, a nesa da unguwar taku".

Hajiya ta ce"To ma sha Allah! Allah Ya tabbatar mana da alkhairi ya ba su zaman lafiya".

Baba ya amsa da amin suka yi sallama.

Da yamma suna zaune Hajiya ta ce"Nuratu kun yi waya da Babanki yau?"

Ta girgiza mata kai alamar a'a, ta ce"Kabir fa?"

Ta ce"Duk ba su kira ni ba, me yake faruwa?"

Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce"To Kabir ya kai kuWin aurenki yau, Wazu Baban naki ya kira ni ya sanar da ni, sai ki fara shiri, sati huWu kawai aka saka".

?irjin Nuratu ya yi wata irin bugawa, ta ce"Hajiya da gaske!? Kabir, innalillahi na shiga uku"

Sai ta tashi za ta bar falon. Hajiya ta ce"Zo ki zauna".

Ta dawo ta zauna har idonta ya kawo ruwa.

Hajiya ta ce"Nuratu me kike nufi ne? Ba kya son Kabir Win?"

Ta fara kuka ta ce"Wallahi ni ban taSa son shi ba, shi ma kuma ba son gaskiya yake yi mini ba, ni ba zan iya aurensa ba".

Hajiya ta ce"A'a kar ki ce haka, ko babu komai shi Wan'uwanki ne, sannan na ga Baba yana son auren nan, ni a ganina ki amince kawai ki yi ha?uri, ki yi addu'ar Allah Ya sa hakan ya zame muku alkhairi, ban ga amfanin zaman naki haka babu aure ba".

GyaWa mata kai kawai ta yi ta tashi ta shige Waki, ta zauna ta fashe da kuka, sai yanzu ma ta ji ta fara son Sadiq kuma ba ta shirya rabuwa da shi ba. Ta Wakko wayarta ta nemo lambarsa ta kira shi, yana Wagawa cikin kuka ta ce"Yaya Sadiq ka gani ko? Ka ga abin da tsarinka ya janyo mana, ga shi yau Yaya Kabir ya kai kuWin aurena, wai an saka rana sati huWu, don Allah me yasa ba ka son Hajiya ta gane muna son juna?"

Sadiq ya rasa abun cewa ya ce"Wannan maganar ba ta waya ba ce, ki bari idan na dawo za mu yi magana".

Ya katse kiran, Hajiya da ke tsaye tana jin wayar gabanta ya yi mummunar faWuwa jin abin da Nuratu ta ce, tabbas da Sadiq Wanta take waya, yau ta tabbatar da zarginta, ashe Sadiq zai iya munafurtarta? Ta jinjina kai ta koma Wakinta ta zauna ta zuba tagumi, dama ta biyo bayanta ne don ta rarrashe ta, to ashe matsalar babba ce ma har da ita a ciki, zuciyarta ta cika da takaici da mamakin munafurci irin na Wan yau, Sadiq kawai take jira ya dawo ta ji ta bakinsa.

Dab da magriba yake dawowa gida, saboda haka masallaci yake wucewa idan ya idar da sallah sai ya shigo gida, amma yau sai ya tsinci kansa da jin nauyin shiga gidan, saboda ba shi da bakin yi wa Nuratu bayani, yana ta harhaWa dabarun da zai yi don ya yi nasara ta bijirewa auren Kabir har isha'i ta yi, bayan ya idar ya nufi gidan, Hajiya kaWai ya tarar a falo, ta cika ta yi fam, don dama yanzu take shirin kiran nashi sai ga shi ya shigo, sai da gabansa ya faWi ganin yanayin fuskarta, ya ?araso yana cewa"Hajiya sannu da gida, ya na ga kamar ranki a Sace?"

Ba ta ce komai ba, ta ?arasa inda yake ta dam?i hannunsa wanda ya ji kamar zuciyarsa ta dam?a saboda yadda ?irjinsa ya buga da ?arfi, ta shiga jansa har sai da ta kai shi Wakinta ta zaunar da shi a bakin gado ta kafe shi da ido, fargaba ta cika zuciyarsa zai yi magana ta ce"Ba na son jin komai sai amsar tambayar da zan yi maka!".

Ya gyaWa mata kai jikinsa ya fara kyarma.

Hajiya ta ce"Sadiq mene ne tsakaninka da yarinyar nan Nuratu?"

?irjinsa ya buga dam, ya san idan ya yi mata ?arya za ta gane, babu rami babu abin da zai kawo maganar rami, ?ila ta rutsa Nuratu ta faWa mata gaskiya, don haka gara kawai ya faWi gaskiyar shi ma.

Ta ce"Ko sai na maimaita?"

Ya ce"A'a Hajiya, dama...ba komai ba ne, soyayya muke yi".

Yana rufe baki ta Wauke shi da wani fusataccen mari ji kake tau! Ya sunkuyar da kai hawaye ya fara zubo masa, a fusace ta ce"Ashe ba ka da kunya ba ka da kirki Sadiq!? Ni za ka muna furta ka raina wayona ka mayar da ni ban san komai ba? Soyayya da Nuratu? Ashe ba ka da hankali!".

Ta ce"FaWa mini a ina da ina kuke haWuwa? A cikin gidan nan ko a wani wajen!? Ni za ka tonawa asiri ka saka ni jin kunya, na Wauki amana ka karyata ni ko?"

Ya ce"Wallahi Hajiya ba irin wannan soyayyar ba ce, ni ba mu taSa haWuwa..."

Marin da ta sake sauke masa ne ya katse sauran maganarsa, ta ce"Ka faWa min gaskiya kun haWu da Nuratu!? Idan na bincika na ji kun haWu wallahi babu ni babu kai!"

Ya ce"Wallahi gaskiya na faWa miki, ki tambaye ta ki ji ma, ni dama son gaskiya nake yi mata".

Ta ce"Dalla rufe mini baki, Nuratu sa'ar aurenka ce? Ai ka san kun riga kun yi hannun riga, ko da wasa kada ka sake kula ta, amsa gaisuwarta kaWai na lamunce maka har zuwa sanda za ta bar gidan nan, duk wata magana da ta wuce wannan ban yafe maka ba!".

Kai kawai yake gyaWa mata, yana jin kamar zuciyarsa za ta yi bindiga, Hajiya ta juya ta buWe Wakin ta fice, shi kuwa sai da ya ci kuka kamar mace sannan ya tashi ya fito ya shiga Wakinsa, wanka ya yi ya kwanta kansa cike da tunanin abubuwa da dama.

Nuratu ta idar da sallar isha'i tana kwance a Waki ba ta da niyyar fitowa karatu, saboda halin da take ciki, ba ta san wainar ma da ake toyawa a gidan ba, sai ga kira da ba?uwar lamba, ta Waga ta ji Kabir ne mai kira ya ce"Ina ?ofar gida, ki fito don Allah".

Dama tana son ganinsa don ta tabbatar masa ba za ta aure shi ba, don haka ta saka hijjabi ta fito, ta samu Hajiya a falo ta ce"Hajiya Kabir ne ya zo".

Ta ce"To, ai gara ku shigo ciki ko?"

Ta ce"A'a ba daWewa zai yi ba".

Ta fice, Hajiya ta bi ta da kallon tausayi, auren dole ba shi da daWi, amma a wannan yanayin aure ne ya dace da Nuratu, idan ta hana Baba ya aura mata Kabir ba ta yi gaskiya ba, tun da ba ta da wanda za ta bata.

A ?ofar gidan ta same shi, ta daWe ba ta gan shi ba, ta tsaya nesa da shi, ya matso yana murmushi yau fes yake jin ransa, sai ma yake jin tamkar ta riga ta zama tasa, ya ce"Nuratu babu ko gaisuwa?"

Ta ce"Ai ba ka sanar da ni gaisuwata ka zo karSa ba".

Ya ce"Ba wannan ba, ina fata zuwa yanzu kin san matsayina a wajenki? Kun yi magana da Baba?"

Ta yi shiru zuciyarta na ?una, inda a ce Kabir bai bayyana mata ba?in halinsa ba tun farko ta sigar aure ya zo mata, da babu abin da zai hana ta amince da aurensa, don a baya ba ?aramin kallon mai kirki take yi masa ba, har tana yi wa Nawwara murna, ashe abun ba a fuska yake ba.

Ya ce"To yau dai na kai sadakinki, shaidu kawai suka rage da shafa fatiha, shikenan kin zama mallakina".

Nuratu ta ce"Ka daina mafarkin zan zama mallakinka, ka ce dai gangar jikina za ta zama mallakinka, saboda ba zan taSa ba wa zuciyata ?ofar da za ta so wanda bai cancanta ba".

Ya yi wata ?ar dariya ya ce"To ko iya gangar jikin na samu Alhamdilillah! Ni dai burina a ce kina gidan nawa a zaune matsayin matata".

Ya ce"Ina fatan yanzu kin yarda wannan tsohon mijin naki mara amfanin dama ba son gaskiya yake yi miki ba, inda yana sonki kamar yadda kike son shi wannan vedion guda Waya ba zai zama silar sakinki ba, ya kamata ki farga ki dawo cikin hayyacinki, ki ba ni daka mu yi rayuwar farinciki, Nuratu na sani a baya na yi kuskure amma yanzu son gaskiya nake yi miki wallahi".

Yana rufe baki suka ji ?arar buWe ?ofar gidansa, Nawwara ce ta fito a fusace ta tunkaro su. Ya ce"Nuratu kin ga shiga gida kawai, za mu yi waya".

Ta yi kamar ba ta ji shi ba, tana jiran ?arasowarta.

Tana ?arasowa ta Waga hannu ta tsinkawa Nuratu mari, shi ma bai jira komai ba ya fesa mata marin yana cewa"Nawwara ashe ba ki da hankali? Me ta yi miki? Ai ni za ki daka ba ita ba!".

A fusace ta ce"Wallahi ka ji kunya Kabir, ka rasa wa za ka so sai wacce ka ri?e a matsayin ?anwa, me za ka yi da yarinyar nan da ta gama barbaWa da maza a titi?"

Nuratu ta ji zafin maganar har ta ji ba za ta iya shiru

22 / 41