Advertisements
Chapter 4 Reading Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 41

9K to 12K   out of 121.6K words

magana ba? Waye sa'anka a nan?"

Sai kuwa Nura ya hartsu?o kamar zai dake ta, yana cewa"Kar ki sake ki ?ara dukan shi, saboda ya tambaye ni? Da ke yake? Ba ki iya komai ba sai shirme!".

Ya tashi yana Waukar mukullin babur Winsa ya fice zuwa tsakar gida, yana kiran Salim Win, ya je ya buWe masa Wakin suka shiga, sai da ta ga za su yi lattin islamiyya sannan ta le?a tana cewa"Ku zo ku tafi makaranta".

Salim Ya no?e kafaWa yana cewa"Daddy ni yau ba sai na je ba".

Hasana ta ce"A kan me? Ai kuwa ya zama dole ka je!".

Nura ya ce"?yale shi, ?ila ya gaji ne".

Ta juya ta koma Waki, tana jin sanda suka fita, ya siyo musu biskit ya dawo da su, tana zaune ranta a Sace, saboda ta gaji da yadda yake Waurewa yaran akan rashin son karatun addini, ya ce"Ki biya musu karatun, tun da ba su samu zuwa ba".

Ko kallonsa ba ta yi ba, ya fice daga gidan. Ta ja kunnen yaron ta murWe tana cewa"Idan ka girma za ka gane ba gata yake yi maka ba!".

?arfe sha biyu na dare, Hasana ta kasa bacci, tana tunanin me Nura yake yi a halin yanzu? Ya yi bacci, ko yana ta waya da ?an mata? Tunanin ya kasa barinta, don haka ta tashi, ta saka hijjabi, ta buWe ?ofa a hankali ta fito, ta je daidai windon Wakin ta le?a, ta kuwa hango shi zaune ya yi WaiWai a kan katifa, yana ta danna waya, wani abu ya zo ya dun?ule mata ?irji, kamar ta buga masa ?ofar, sai kuma ta ga me ma za ta ce masa? Ta daWe tana kallonsa ba tare da ya sani ba, sannan ta juya ta koma Waki, ta kwanta, sai ta ji Wakin ma yau ya mata girma, gadon ya yi mata faWi, duk da dama yawancin daren da bacci suke raya shi, amma duk ranar da ba ya nan tana jin babu daWi.


08028966015
*ZUCIYAR MACE*



BY
SADIYA ABDULRAZA?


*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee

PAGE 5


Washegari da safe Hasana ta gama haWa abun karyawa, tana shirya yaran, Nura ya shigo yana cewa"Ki je ki gyara mini Wakina".

Ta yi kamar ba ta ji shi ba, ya sake cewa"Hasana magana fa nake yi".

Ta ce"Ni fa wannan raba Wakin ba lallai ya zama maslaha ga rayuwar aurenmu ba, saboda haka ya kamata a sake sabon tsari".

Ya tsaya yana kallon ta da mugun mamaki, ita kuwa da ba kallon shi take yi ba, ballantana ta lura da yanayinsa, ta cigaba da faWin"A gaskiya sai dai ni ma na koma can Win, idan saboda Aiman ne, ni zan dinga yin shimfiWata a ?asan katifar mu kwanta".

Takaici ya ma hana shi tsayawa jayayya da ita, dogon tsaki kawai ya ja, ya ce"Allah Ya raba mu da jahilci".

Ta ce"Ni ce jahilar!?"

"Duk yadda kika Wauka haka nake nufi!" Ya faWa yana jan kwanon abincinsa.

Ta shige Waki ta yi zaune a bakin gado, ta rasa ta hanyar da za ta bi ta da?ile wannan sabuwar bada?alar da yake son ?ullawa, sam ba ta yarda da shi ba, ta san bayan uzurin da ya kawo mata, dole yana da wata manufa ta raba Wakin nan da ya yi.

Haka suka gama karyawa suka fita tare da yaran, ya kulle Wakinsa yana mamakin sabon hali na raini da take son tsiro da shi a zaman nasu. Da azhar da ya Wakko su daga makaranta, yana shigowa fuska a murtuke, ya Wauki tsintsiya ya share Wakin, sannan ya haWa ruwan mopping, har ya fara zuciya ta ciyo shi, shaiWan ya yi zuga, ya fito a fusace, tana cirewa yaran unifom ya ce"Ke Hasana wai me kike nufi ne? ?an iska kika mayar da ni ko yaya?"

Ta ce"Kamar ya?"

Ya ce"Ta ya za a ce ga ki a gida ni zan share Wakina? Mene ne amfaninki!?"

Ta ce"Ka fi kowa sanin amfanina".

Ya ce"Ki je ki gyara mini Waki Malama, ku mata sam ba ku da tunani wallahi, ba dole ma mutum ya ?ara aure ba? Hmm Allah dai ya hore, zan huce takaici tabbas".

Hasana ta yi murmushin takaici ta ce"Ai wallahi ni na fi so ma ka ?ara auren, ta nan za ka san ha?urin da nake yi da kai".

Ya ce"Ki kwantar da hankalinki, ai in sha Allah aski ya zo gaban goshi, wallahi da wannan siyayyar da na yi, kuWin aure zan kai, to kawai na fi so lissafin komai ya tafi daidai shiyasa na jinkirta, amma kar ki damu indai aure ne dole zan yi shi".

Ta ce"Allah Ya nuna mana".

Ya yi ?wafa, ta fice ta shiga Wakin, ta ga wayarsa a kan katifa, ta raya ?ila mantawa ya yi, ta yi saurin Wauka, sai dai da pasaword kuma ba ta san mene ne ba, ta yi ?wafa ta ajiye ta, ta gama gyara Wakin ta fito.

Ta same shi a falo ta ce"Yanzu haka za mu dinga ganinka kai kana yin kallonka mu ko oho?"

Ya ce"Tun da haka kika zaSa ba!Na gaji da kai gyaran kayan kallo wallahi".

Amir ya ce"Don Allah Daddy a gyara mana".

Salim ya ce"To ai sai mu dinga yi a Wakin Daddyn".

Bai ce komai ba, ta kawo musu abincin rana suka fara ci, Nura ya yi kamar cokali uku ya taSe baki ya ce"Abinci ma ba za a nutsu a yi shi ba, Allah Ya kyauta".

Hasana ta yi kamar ba ta ji shi ba, don ita ma ta san gishirin ya yi yawa, ta manta shaf ta zuba, dab da za ta gama girkin ta ?ara zubawa, don haka ba ta da ta cewa. Ya sake tsaki ya ce"Wannan abincin dai ci kar ka mutu kawai, an zabga wa mutane gishiri a abinci" Ya sake tsaki.

A fusace ya ce"Ina ta magana...!"

Ta ce"To me kake so na ce? Ku maza dama haka kuke, sai mace ta yi daidai sau dubu, ba za ku tabe ta ba, amma idan ta yi ba daidai ba sau Waya sai kun yi ?orafi, hannuna ne ya kufce na saka da yawa".

Ya ce"Hmm! Gaskiya na yarda, duk wanda ya mutu da mace Waya shi ya ga ?arshen wula?anci, gida biyu maganin gobara, Allah dai Ya kai damo ga harawa!".

Ba ta sake bi ta kansa ba, har ya gama ya fice.

Yau da daddare da wuri ya dawo, hakan ya sa Hasana ta raya a ranta ?ila yau Win ya kira ta, amma sai ta ji shiru, don ko le?o su ma bai yi ba, tana jin lokacin da ya saka sakata a Wakin, bayan ya gama uzururrukansa, kamar awa Waya a tsakani ta tashi ta sakko daga gadon, ta kalli agogo, sai yanzu goma ta yi, ta manta rabon da ya dawo gida kafin ?arfe goma, sai dai idan ana tsananin sanyi, ko kuma da damuna. Ta saka hijjabi, ta fito a hankali kamar jiya, ta le?a ta windo, ta ga Wakin da hasken tv ga kuma sauti alamar ya kunna kallo, amma yana kwance a katifa waya kare a kunnensa ga murmushi shimfiWe a fuskarsa, da alama yana cike da shau?i, takaici ya rufe ta, duk abin da Nura yake yi mata na Sacin rai, har yanzu tana ?aunarsa, soyayya ce aka sha ta nuna wa sa'a kafin aurensu.

Ta gama yankewa a zuciyarta sai ta hana shi sukuni, don haka ta koma ta wajen ?ofar ta fara ?wan?wasawa. Nura da ya nutsa a kofin soyayya da wata wacce ya yi mata la?abi da baba Leemat, sosai ya yi mamakin wannan bugun ?ofar, da ya dawo sai da ya duba ?ofar Hasana ya ga a rufe, kuma ya santa da baccin wuri, ya ce da baba Leemat yana zuwa, ya katse kiran yana haWe gira ya ce"Wace?"

Ta ce"Ni ce".

Ya zo ta buWe yana cewa"To ya aka yi, ni har na fara bacci ma?"

Za ta kutsa kai ciki, ya Wan tare yana cewa"Wai mene ne?"

Ta ce"Akwai wani film da nake kallo a bollywod, shi ne na ce tun da akwai wuta ga ka, ka dawo da wuri bari na zo na ci albarkacin turakar Oga". Ta ?arasa da murmushi.

Sai ya matsa ta shige ta zauna, ta canza tasha, amma gabaWaya hankalinta yana kanshi, wayarsa tana ta kawo haske ya ?i Wauka, can dai ya tashi ya fice daga Wakin, ya tura ?ofar Wakinta a hankali ya shiga, ya haska ya ga Aiman ya baje yana ta baccin shi, ya ji fanka, ya kai hannu ya fara jijjiga shi, yaro kuwa ya fara mutsu-mutsu, sai ya tashe shi ya zaunar, ai kuwa ya fara ?ananun kuka, ya yi saurin ficewa daga Wakin.

Ya koma nashi Wakin yana cewa"Na ji kamar kukan Aiman".

Ita ma ta jiyo sama-sama, don haka ta tashi, ta ce"Bari na Wakko shi".

Ya ce"Ina? Kin ga Malama ki yi kwanciyarki kawai, saboda ni ma bacci nake ji".

Tana fita ya mayar da sakata.


*********

Baba ransa ya kai ma?urar Saci, ya kai ya kawo a tsakar gida rungume da hannuwa a bayansa, ya ma kasa cewa komai. Can Mama Karime ta ce"Malam ba fa shiru za ka yi, kamata ya yi a bi sahunta tun kafin ta yi nisa".

Sai kuwa ya zaburo kamar mai jira, ya ce"To a gidan uban wa zan nemo ta? Ni dai na san abu Waya, yanzu Nuratu ba?inciki da hassada kawai take yi mini, wallahi saboda ta hango Wan abin da zan samu a jikinta shiyasa ta yi mini haka, amma babu komai". Ya shige Wakinsa.

Ita kuwa Nuratu motarsu tana harbawa titi, ita ma ta harba duniyar tunanin makomarta, sam ba ta hango haske a gobenta, ta san babu ta yadda za a yi Abdul ya karSi uzurinta, fatanta ya yarda da ita ko da ba zai aure ta ba, ita ta yarda ta sadaukar da mutuncinta don farincikinsa. Sai dai idan bai aure ta ba, wa zai aure ta ya kalleta da mutunci? Gani take shi ma Alhaji Hashimu da ya yi al?awarin aurenta ya yi maganga ne kawai a cikin mayen giyar so, bayan auren ba lallai ya ri?e ta da daraja ba, sannan yana da mata har uku da yaran da ba ta san adadinsu ba, ta tabbata wasu sun girme mata, yanzu ya za ta yi idan suka ji ta yi ciki a waje kafin auren? Anya gori zai bar ta ta zauna lafiya?

Da wannan tunane-tunanen fal zuciyarta aka ?arasa Kaduna, kowa ya sauka, ta samu babur ya ?arasa da ita unguwar da za ta je, sai da ta kai ?ofar gidan sannan ta fara fargaba, ta san dai wannan tafiyar ba gudu sunanta ba, don inda ta zo Win ba mafaka ba ce ba, kawai ta zo ne saboda ?wa?walwarta ta samu hutu, kuma zuciyar Baba ta yi sanyi, don idan ya tashi yi mata hukunci ta samu sassauci. Ta kai hannu tana ?wan?wasa get Win gidan, sai da ta buga sau uku, sannan daga ciki aka tambaya waye, ta Waga murya ta ce"Ni ce".

Babu jimawa aka buWe, wata mace ce wacce za ta kai shekara ashirin da bakwai ta buWe, ta Wan saki fuska ta ce"Nuratu" Tana kallon tsohuwar akwatinta.

Nuratu ma ta Wan saki fuska ta ce"Anti Nawwara".

Ta matsa mata, ta shiga jaye da akwatin, Nawwarar ta yi gaba tana binta har zuwa falo, ta zauna, ita kuma ta ?wala wa mijinta kira"Honey!".

Sai ga shi ya fito, yana gyara agogon hannunsa, ya yi turus ganin Nuratu, da mamaki ya ce"Nuratu, ke ce kuwa?"

Sai idonta ya kawo ruwa, ta ce"Ni ce, Yaya Kabir ina kwana".

Bai amsa gaisuwar ba, ya ce"Amma dai ba lafiya ba ko Nuratu?"

Nawwara ta ce"Ina fa lafiya? Ko sadakar ukun babarta ba a yi ba, ka ga ta yo nan ai ka san akwai matsala".

Ya ce"Mene ne ua faru Nuratu?" Sai ta fashe da kuka.

Nawwara ta ce"A'a yi ha?uri, ta huta tukunna, kafin nan zuciyarta ta yi sanyi ma".

Ta ja hannunta, ta kai ta Waki, ta zaunar a bakin katifa, ta koma kitchen ta haWo mata shayi da biredi, har ma da sauran dankali da suka rage, ta kai mata, ta ce"Maza ki ci".

Dayake gidan ba ba?onta ba ne, sai ta fara tashi ta yi wanka, ta canza kaya, sannan ta ci abincin, ta Wakko wayarta, ta kunna data, sa?onni suka gama shigowa tass babu na Abdul, hawaye ya sakko mata, ta san yana can cikin ?unci, ta yi masa sallama a rubuce, ba ya online, babu jimawa kuma ta ga tik biyu, alamar ya hau, ya duba sa?on nata, sai ya fara typing, tana ta fargabar abin da zai rubuto, har ya gama ya turo, "Wannan shi ne sakayyar soyayyata a gare ki ko? Na gode Nuratu, Allah Ya saka da alkhairi". Abin da ya rubuta kenan, sai ya bi bayansa da stika ta namiji yana kuka sosai.

Ita ma kukan ta fara, ta danna viice ta ce"Na san ban cancanci ka saurare ni ba, amma don Allah ka daure ka ji bayanina, ba don halina ba, na yi komai ne saboda cika maka burinka, rayuwarka ta inganta".

Bayan ya saurara ya tura mata emoji na mamaki, ta sake yin voice ta ce"Don Allah ka yi ha?uri, ka fahimce ni, na fi kowa shiga ?unci sanadin wannan kuskuren da na yi".

Ta typin ya ce mata"Cikin wane ne? Kar ki ba ni amsar da za ta wuce kalma uku, don ba ni da lokacin sauraron tsarinki".

Sarai ta san halinsa, tun da ya ce haka, idan ta ba shi amsa akasin yadda ya bu?ata, zai iya yin blocking Winta, don haka ta rubuta masa "Agent Win da ya yi maka hanyar tafiyarka ne" Ta tura masa.

Abdul yana karantawa, ?irjinsa ya doka da ?arfi, ya fara karanto innlillahi wa inna ilaihi raji'un! Ya fara tunanin yanzu a kan shi ta ba da kanta ga wani banza? Nan ya tuna ranar da yake tunanin abun ya faru, da abokinsa Usman ya ce masa, ya ganta ta fito daga mota tare da Agent Win nan, amma Abdul fir ya ce ba ita ba ce, sannan a ranar mutumin ya kira shi ya yi masa al?awarin tafiya. Ya kashe data yana mamakin irin _zuciyar mace_.


08028966015
*ZUCIYAR MACE*



BY
SADIYA ABDULRAZA?


*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 6


Shiru bai ma sake kunna data ba, ballantana ta ji hukuncin da zai yanke, ta sake tura masa sa?o, ta ce"Ka yi ha?uri don Allah, ni ban ce dole sai ka aure ni ba, kawai dai ka yarda ba yaudara ce ta saka na yi haka ba, ba kuma son abin duniya ba, kawai na yi ne saboda na taimake ka".

Ta ajiye wayar tana tuna ranar da ya zo ?ofar gidansu, jikinsa a mace, yana faWa mata Agent Win ya ce yau ce rana ta ?arshe, idan bai kawo kuWin nan ba, babu shi a tafiya, sai dai ya sake nema a gaba, abokansa uku duk sun biya, shi ne kaWai ba shi da shi, ga shi mahaifinsa yana zaune a gida, jinya ta saka shi a gaba, a ?a'ida ya kamata a ce yana asibiti, amma yanzu yana gida sai maganin Hausa ake ta banka masa. Ya ce"Nuratu macuta sun yi yawa a ?asar nan, a gabana ya cikewa mata biyu, kuma ina zargin sun ba shi kansu ne, Wayar ma buduruwa ce, tsananin rayuwa ya sa take son tafiyar, na ga bayan ta fito ta tsaya tana kuka, ita da ya kamata ta yi farinciki, ni kuma da nake namiji kuWi ne kaWai zai fitar da ni, na rasa yadda zan yi, ba na so tafiyar nan ta kufce mini, domin na san haka ke ma za ki kufce mini".

Nuratu ta ce"Allah Ya kiyaye, wallahi ba zan taSa kufce maka ba Yaya Abdul, zan jira har ka samu aiki".

Ya yi guntun murmushi ya ce"Wa ya san nan da shekara nawa za a samu? Ai ni ma ba zan so tauye miki rayuwa ba".

Ta ce"Yanzu babu wata hanyar?"

Ya ce"Ba ni da komai wallahi, kin ga babata duk ta siyar da kayan Wakinta, akan tafiyar nan idan ba ta yiwu ba akwai damuwa".

Haka suka dinga tattaunawa, ?arshe da zai tafi ta ce ya ara mata wayarsa za ta yi kallo, dama yana ara mata, don haka ya mi?a mata ya tafi. Ta shiga Waki ta yi zaune da wayar tana tunanin mafita, kafin ta bi shawarar zuciyarta ta Wauki lambar Agent Win, shi ne wanda suka yi waya na ?arshe, ta saka a wayarta, ta danna kira, ya Wauka suka gaisa, ta ce"Ni ?ar'uwar Abdul ce".

Ya ce"Wane Abdul?"

Ta ce"Abdulmalik, wanda kuka yi waya Wazu, wanda bai samu ya cika kuWin tafiyarsa ba".

Ya ce"Ok ya aka yi?"

Ta ce"Dama ina son mu haWu, akwai alfarmar da zan ro?a idan zai yiwu".

Ya yi mata kwatance, Allah Ya taimake ta Mama ba ta nan don haka ta saka hijjabi ta tafi. A bakin titi ta tsaya, ya turo aka shiga da ita, ta shiga har ofishinsa, ta zauna ta gaishe shi, ta sake yi masa bayanin kanta, sannan ta Wora da faWin"Abdul yana cikin matsalar rayuwa, shi ne babba a gidansu, ga mahaifinsa ba shi da lafiya, don Allah ka taimaka masa ya samu tafiyar nan, daga baya sai ya biya ka".

Ya ce"To ?an'mata ai haka tsarin yake, mu babu ruwanmu da ?arfin matsalar mutum, kamfani ne, dole yadda aka tsara ake yi".

Ta ce"To amma me zai hana ka Wauke ni a nan Win ko na shara ne, sai ka dinga ri?e albashin nawa da haka har ya biya ka?"

Ya yi Wan murmushi ya ce"Wannan lokaci ya ?ure masa ai, yau ce kaWai damarsa, ni kuma ba zan yi masa aiki bashi ba".

Idonta ya kawo ruwa, ta karaya sosai, ta tashi tana cewa"Shikenan na gode".

Har ta kusa fita, ya kira ta, ya nuna mata kujera ta zauna, ya ce"Ya kuke da shi?"

Ta ce"Yayana ne".

Ya ce"To indai da gaske kike son taimakonsa,

4 / 41