Advertisements
Chapter 5 Reading Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 41

12K to 15K   out of 121.6K words

ai kina da abin da za ki taimake da shi" Ya ?arasa yana yi mata kallon ?an bariki.

Ta ce"Inda ina da shi, da ban zo neman alfarmar nan ba".

Ya ce"Idan har za ki amince mu tsallaka wancen hotel Win na kusa da mu, cikin mintuna za ki taimaki yayanki".

Gabanta ya faWi, ta ce"Amma sai wannan kaWai?"

Ya ce"E, idan kin duba ai ba wani abu ba ne mai wahala, saboda idan ya tafi zai yi miki alheri fiye da yadda kika yi masa, ?ila ma idan aurenki ya zo shi ne zai yi miki kayan Waki, sannan kamar kin taimaki iyayenki ne".

Ta ce"Zan yi shawara".

Ya ce"No, ki je kawai, na faWa miki yau ne last".

Ya Wauki waya ya yi danne-danne ya kara a kunne, ya ce"Wannan list Win ku cire sunan Abdulmalik Ibrahim, zan tura muku sunan da za ku saka a kai".

Hawaye ya zubo mata, ta ce"Don Allah Oga ka taimake mu, zan dinga kawo maka kuWin a hankali".

Ya ce"Ki je kawai, ba shi da rabon tafiyar".

Ta tuna wane ne Abdul da yadda yake ?aunarta, sai ta ga ya cancanci har sadaukarwar rayuwa ta yi masa, don haka ta ce ta amince, nan take suka fita, suka je Nuratu ta mi?a kanta, babu shawara babu tunanin ta tafka kuskure, ta manta wane ne namiji, ba ta tunanin ba kowane zai iya yi maka halakci har ?arshen rayuwarku ba.

Shigowar Nawwara ce ta katse mata tunani, ta kai hannu ta share hawayen fuskarta, Nawwara ta ce"Ki fito falo yana jiranki, fita zai yi".

Ta tashi ta bi bayanta. Ta zauna kanta a ?asa, Kabir ya ce"Nuratu me ya kawo ki? Ni ma gobe nake shirin tafiya gaisuwar fa, aiki ne ya yi mini yawa".

Sai ta fara kuka, Nawwara ta ce"?an'uwanki ne, tun da kika zo wajen shi na tabbata kina da ya?inin samun sassaucin damuwarki, saboda haka bai kamata ki Soye masa komai ba" Sai ta tashi ta shiga Wakinta, don ta ba su waje.

Nuratu ta kasa faWa masa komai, sai kuka da ya ci ?arfinta, ?arshe ya Wauki waya ya kira Babanta, wanda ke a matsayin ?anin uba a wajen shi, wato dai Wan wa da Wan ?ani suke da Nuratu, amma Allah Ya haWa jininsu sosai, har ma ya so ta koma gidansa da ya yi aure, sai Mama ta hana, sai dai ta je hutu ta kwana biyu ta dawo gida.

Suka gaisa da Baba, ya ?ara yi masa gaisuwa, sannan ya faWa masa ga Nuratu ta zo tana kuka, ta ?i faWar komai.

Baba da yake kwance a Wakinsa abun duniya ya ishe shi, ya mi?e zaune yana cewa"Alhamdulillah! Gidanka ta zo ashe?"

Ya ce"E ga ta nan".

Nan Baba ya kwashe komai ya faWa masa, Kabir ya yi mamaki sosai, saboda duk cikin ?an gidansu ya fi ganin nutsuwarta, ya shiga yi mata faWa, tana ta kuka, ?arshe ya tambaye ta wane ne ya yi mata haka? Nan ma dai ta ?i faWa, don takaici ko sallama bai yi wa matarsa ba ya fice daga gidan, a waje Baba ya sake kiransa ya ce lallai-lallai gobe ya sako Nura???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?tu a mota su dawo, ya ce masa da kansa ma zai kawo ta.

Haka ta wuni a Waki, duk yadda ta so Abdul ya fahimce ta abu ya ci tura, babu kalar bayanin da ba ta yi masa ba, amma yanzu ya ma daina duba sa?on, kuma yana online.

Shi kuwa a Sangarensa shi kaWai ya san halin da zuciyarsa take ciki, yana da matu?ar kishi, musamman a kan Nuratu da ya yanke a ransa da ita kaWai zai rayu, ya kasa ganin da gaske halakci ta yi masa, ballantana ya yi mata sassauci a hukunci, abu Waya kawai yake yawo a kansa, Nuratu ta yi masa butulci, kuma zuciyarta ba mai kyau ba ce, yana tunanin da aurensu ma za ta iya aikata hakan, da sunan taimako.

Amma ta duniya za ta kalle shi da iyayensa, idan aka ji domin shi ta aikata? Saboda haka zai yanke wani hukunci, zai aure ta na Wan lokaci, daga nan duk wanda zai ji tarihinta a bazawara zai santa, kenan ba za ta samu wata matsala ba a duk yadda mijin da za ta rayu da shi ya same ta.

Ya kira mahaifiyarsa a waya, ya tausasa murya, ya fara ro?onta yafiya, ya yi mata shimfiWar ?addara, sannan ya faWa mata kafin ya tafi shaiWan ya shiga tsakaninsu da Nuratu, har ma tana da cikinsa, mahaifiyarsa ta shiga tashin hankali sosai, ta san idan ta sanarwa mahaifinsa zai iya ?arasawa, don haka ta faWawa Wan'uwansa, wanda yake waliyin Abdul Win, duk faWan da aka yi wa Abdul ya yi ha?uri ya jure, a ganinsa wannan ne halakcin da zai yi wa Nuratu kawai, ya rama wa kura aniyarta.

Haka ?anin babansa ya je wajen Baba da daddare ya faWa masa halin da ake ciki, Baba ya dinga sababi, don dama Abdul Win kaWai ya zarga, tun da ba ta kula kowa bayan shi, nan ya rarrashe shi, ya ce Abdul zai turo sadaki a Waura auren cikin satin nan, idan ya dawo sai ta tare, nan Baba ya ce bai yarda ba, su je kawai Allah Ya isa, amma ita Allah Ya rufa mata asiri, tana da miji.

Washegari Kabir ya saka Nuratu a gaba suka dawo, nan suka zauna da Baba a gabanta yake sanar masa Abdul ne ya yi mata ciki, kuma ya ce zai aure ta. Ta ji zuciyarta ta buga da ?arfi, sai ta rasa farinciki take ciki, ko akasinsa? Ashe Abdul zai jiSanci lamarin nan, har ya amsa laifin da ba nashi ba? Ta babbata ita da Abdul ruhi Waya ne a gangar jiki biyu, ashe ya nuna fushi ne kawai saboda ya hora ta, sai ta ji kamar ta fita daga duka damuwar ma.

Kabir ya ce"To Baba ai ta kwana gidan sau?i, dama wanda ya dama kunun ai shi ya kamata ya shanye, kuma suna son junansu, tun da ta ga za ta iya jiransa sanda ya bushi iska ya dawo sai su tare".

Baba Ya ce"Ai ba a nan gizo ke sa?ar ba!". Nan ya ba shi labarin Alhaji Hashimu, ya Wora da faWin"Ka ga shi ya ji ya gani, sannan babba ne mai hankali, ba kamar Abdul ba da ?uruciya, bar ganin shi ya yi aika-aikar, tsaf zai wula?antata a hakan hakan, shi kuwa wannan mai rufin asiri ne, wula?anci mai kuWi ya fi na talaka sassauci a zuciya, ko banza dai a gidansa za ta fi ?arfin komai, sannan yanzu ta riga ta san daWin namiji, ba lallai ta nutsu ba, ?ila ta cigaba da shashancinta shi yana can, tana kwasar zunubi, kuma ni ina ma zargin tilas za a yi masa, idan ya ?i dawowa ya zan yi da ita?"

Kabir ya ce"To gaskiya da wannan ma, indai shi Alhajin ya ji ya gani, ina ga gara ma kawai ta aure shi Win, shi Abdul mu bi shi da Allah Ya isa kawai".

Baba ya ce"Yawwa Wan gari, ashe ka gane".

Nan suka gargaWe ta akan kar ta sake ta amsa auren Abdul, wanda ta kalli maganar a wani abu da ba zai taSa yiwuwa ba, domin tana ganin indai har sun yarda Abdul ne ya yi aika-aikar kuma suka zargi zai iya wula?antata bayan aure, to shi Alhajin waliyyi ne da zai ?yale ta? Ta saka a ranta ba ta da mijin da ya fi Yaya Abdul Winta.



08028966015
*ZUCIYAR MACE*



BY
SADIYA ABDULRAZA?


*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)


https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY



PAGE 7


Yau kuwa kafin Nura ya dawo Hasana ta ci kwalliyarta, wata ?aramar rigar bacci da ta daWe ba ta saka ba, ita ta Wakko ta saka, ta fesa turare, ta zauna tana jiran dawowarsa. Yana dawowa ya shiga wanka, kafin ya fito ta tafi Wakin nasa ta haye katifa ta zauna, har da kunna kallo, ya fito daga wanka yana tura ?ofar Wakin ya ganta zaune tana yi masa murmushi, ya haWe rai ya ce"Lafiya?"

Ta ce"Lafiya ?alau, an dawo lafiya?"

"?alau" Ya amsa a da?ile.

Ta ce"Dama fira na zo taya ka, na ga ka dawo da wuri, ga wannan Wan abun taSawa ne".

Ta ?arasa tana mi?a masa Wan kwano mai Wauke da ilokar da ta yi da rana. Ya yi tsaki ya ce"To wace irin fira cikin daren nan?"

Ta ce"Fira dai irin wacce kake yi a majalisa, na yi zaton ka fara dawowa da wuri ne saboda ka ba ni lokacina, mu dinga fira muna tattaunawa game da rayuwarmu da ta ?a?anmu bakiWaya".

Takaici ya ishe shi, shi kam ashe ya gudu bai tsira ba, yanzu haka daga wajen ?awarta Ramla yake, kuma sun yi da ita za su yi vedio call su sha fira, sai ga shi ta kwaso jiki wai ta zo su yi fira, ya saka kaya ya nemi waje ya kwanta, ta ce"Baban Salim, ba ka sha ilokar ba".

Ya ce"Ki ajiye zan sha".

Ta ce"Ni kuwa Baban Salim sai na ga malaman makarantar yaran nan kamar sun fara shirme, sai a kwana uku ba a ba su home work ba".

Ya yi kamar bai ji ta ba, ta ce"Ni dai kamar na je na ji dalili, saboda...."

A fusace ya katse ta da faWin"To tashi ki tafi! Wannan wace irin takura ce haka, na dawo gida kaina yana ciwo ba za ki bar ni na huta ba, wannan ai masifa ce! Ka ware Wakin ma ba ka tsira ba!".

Ranta ya Saci, ta ce"Allah Ya huci zuciyarka, ni dai ban ga abun faWa a nan ba". Ta tashi ta fice ta janyo masa ?ofar.

Ya je ya saka sakata, yana tsaki, a ransa yana ayyana sai fa ya taka mata burki a kan shigo masa Waki.

Hasana ta zauna a kujerar falonta, tana tunanin yadda za ta yi, har ga Allah ba ta son mijinta ya zama Waya cikin masu lalata tarbiyyar yaran jama'a ta waya, ta taSa ganin chart Win banza sau Waya a wayarsa, har ta kasa shiru ta tare shi da maganar, ya yi mata kaca-kaca, daga nan ya saka key a wayar yake kuma taka-tsan-tsan da ita, tun daga nan take zarginsa, ko don yawan son matansa dama dole ta kasa yarda da shi, ta san sarai bai daina chart Win banzan ba, ballantana yanzu da ya ware Wakinsa zai ci karensa babu babbaka, sai a ce mace ba ta jan mijinta a jiki, shiyasa yake yi da wasu matan ta waya, to idan da ba ta ja shi a jiki ba, yanzu ta yun?uro za ta gyara zaman, don kayan baccinta da ta daina sakawa duk ta fito da su, kuma ya ?i ya ba ta dama.

Ta jima tana wannan tunanin sannan ta tashi ta sake fita cikin sanWa, ta le?a shi ta windo, ta hango shi, zaune yana kallon waya yana magana fuskarsa Wauke da murmushi, ta koma Waki ta Wakko panadol da ruwa a kofi, ta je ta fara ?wan?wasawa. Nura yana jin daWin firarsa, ga iloka yana rakawa da ita kawai ya ji bugun ?ofa, sai da ya zabura, sannan ya ce wa Ramla yana zuwa.

Ya tashi ya je ya buWe yana cewa"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Hasana kaina fa ciwo yake yi, na samu bacci da ?yar kin tashe ni".

Ta ce"Dama magani na ga ya dace na kawo maka".

Ya karSa, ya mayar da ?ofar ya rufe, ta koma Waki ta yi addu'a ta kwanta, tana jin zafi a zuciyarta. Da asuba ta idar da sallah ta Wan kunna data, kamar an yi mata umarni ta shiga status Win Ramla, ta ga ta saka "Jama'a namiji ya ware turakarsa fa duniya ne, mace tana can sake da baki tana yawun bacci, shi yana caskalewa" Ta haWa da emojin dariya.

A na gaba kuma ta saka"Auren mijin wata akwai lada".

Nan take Hasana ta ji ta tsargu, kamar ta wuce sai kuma ta kasa, ta dawo ta ba ta amsa a kai, ta ce mata"?an'mata kenan, ku dai dinga tuna yadda ake caskalewar da ku, an caskale da na gidan fiye da haka, kuma kar lokacinku ya zo ku yi mamaki" Ta haWa mata da dariya.

A na biyun kuma da ta ce auren mijin wata da lada, ta ba ta amsa da "Musamman mai cefane da nama".

Wajen azhar da Ramla ta duba sa?on, ta ce mata"Ke dai ?awata ku ri?e mazajenku da kyau, amma tabbas duk wanda ya kawo kanshi wajena sai na tatike shi".

Hasana ta ce"Ku dai bi a hankali, wani sai bayan auren za ki san ko wane ne".

Daga haka suka taSa fira, aka bar wannan zancen.

Da rana yana cin abinci ta ce"Don Allah baban Salim kayan kwalliya nake so, hodata ta kusa ?arewa, ina son siyan humra ma, kuma underwears Wina duk sun tsufa".

Ya ce"Mata kenan, ku fa babu ruwanku da halin da ake ciki, a nemo a ba ku kawai, ana ta abinci ke kina ta wasu tarkacen da ba su zama dole ba".

Ta ce"Hmm! Ai tarkacen ne yake kwasarku ku je ku dinga rawar ?afa a wajen matan waje, waWanda ba kyau suka fi ni ba, na ji an ce ma an ce har wannan mai awarar ta bakin kasuwa ita ma son ta kake yi, wannan dai zubar da aji ne wallahi, ka rasa wa za ka so wannan kucakar? Wannan uban kurkur Win ne fa ya kwashe ka, amma ka faWo wallahi".

Ya ture abincin yana nuna ta da yatsa ya ce"Ke ya ishe ki haka! Saboda tsabar raini ni za ki saka a gaba da zancen banza sai ka ce wani Wanki? Ba mai awara kaWai ba har mai dankali ma son ta nake, wannan mai gurasar ma yau zan je wajenta, ko za ki hana?"

Ya tashi yana cewa"Kuturu da kuWinsa alkaki sai na ?asan langa, ina da kuWin auren, kuma Allah Ya ba ni damar ?arawa za ki hana ne? Idan na ga dama ma mai ?osai zan auro wallahi, ta zo kuma idan kika yi wasa ta fi fada a wajena!".

Ta ce"Au kai har wata fada ce da kai?"

Ya ce"Da babu da ba a biyo ni da ilokar toshiyar baki ba".Ya fice daga gidan, yana ayyana dole ma fa ya tattara ?aryar nan ya tsayar da mace Waya ya aura.


********

Ta yi wa Abdul sa?o ya kai biyar bai ba ta amsa ba, amma ya saurara, duka ha?uri take ba shi, tare da al?warin za ta jira shi ko shekara nawa ne. Da daddare Alhaji Hashimu ya zo, Baba yana rawar jiki ya zo ya kira Nuratu, tana jin haushi a ce wai mahaifinta ne Wan aiken saurayinta, ta fito suka gaisa, ta sunkuyar da kai, ya ce"Ya ?arin ha?uri?"

Ya ce"Da godiya".

Ya ce"Ya jikin naki?"

Ta ce"Na warware".

Ya ce"To ma sha Allah!Mun yi magana da Baba, gobe za a kai ki asibiti sai a cire cikin, bayan sadakar arba'in sai a saka rana ko wata biyu ne, zuwa lokacin na kamalla ginin inda zan saka ki".

Ta ce"Amma Alhaji Baba bai yi maka bayani ba?"

Ya ce"Na me?"

Ta ce"Shi saurayin nawa da abun ya faru sanadinsa, ya ce zai aure ni, kuma har an gama magana da Baba".

Ya yi shiru na Wan lokaci sannan ya ce"Amma bai faWa mini ba".

Ta ce"To zai faWa maka".

Suka yi shiru na ?an sakanni, sannan ta cigaba"Alhaji na gode da ?aunarka gare ni, sai dai ina so na faWa maka ni Abdul shi kaWai nake so, gaskiya duk wanda ya aure ni ba shi ba, zai iya yin nadama a gaba, saboda ba zai taba samun nutsuwa da ni ba, kai babban mutum ne mai mutunci, kuma kana da ?ima a idona, ba zan so yi maka abin da na tanadarwa namijin da ya yi gangancin aurena ba, saboda haka don Allah Baba ka kama girmanka, kai baban wasu ne, ba zan so yi maka ba daidai ba, tun da ba zan so a yi wa nawa uban ba, na gode sosai Alhaji".

Daga haka ta juya za ta shiga gida, ya ce"?an tsaya Nuratu".

Ta dawo, ya ce"Na ji duk bayaninki, kuma na fahimce ki, ita rayuwar aure ba a yin ta da tilas, kamar yadda kika ce na kama girmana, na kama in sha Allah, dama ni na zo da ?auna ne, da kuma niyyar taimako duba da ?addarar da ta same ki, yanzu zan janye batun soyayya, zan kuma yi wa Baba bayanin da zai fahimta, idan har kina bu?atar wani taimako ?ofa a buWe take za ki iya tambayata, a matsayina na mai tallafawa marayu. Sannan goben za a je cire cikin" Daga haka ya juya ya fita, ta shiga gida jiki a mace, amma sai ya kasa faWawa Baba yadda suka yi, saboda ba ya son haWa ta da mahaifinta.

Washegari da safe direba ya zo ya Wauke ta, tare da wata yayarta, suka tafi asibiti, gabanta yana ta faWuwa, tana jin kamar ta gudu, a hannun likitan farko dai ya dam?a ta, da alama shi Win amintaccensa ne, shi da kansa ya yi mata allurar zubar da cikin, sannan ya ba ta gado. Bayan ya kammala ya kira Hajiya Kubra a waya ya sanar mata.

Zuwa yamma komai ya kammala, cikin ya fita duka, aka sallame su direba ya mayar da su gida. Tun kafin su ?arasa likita ya kira Alhaji suka gaisa ya ce"An kammala aikin cikin nasara".

Ya ce"To Alhamdulillah!".

Likita ya ce"Sai dai fa akwai wata matsala".

Ya ce"Ta mene ne?"

Likita ya ce"To ban sani ba ko ka san yarinyar tana Wauke da cuta mai karya garkuwar jiki".

Gaban Alhaji ya faWi, ya kaWu sosai da jin kalmar nan, ya ce"Ok babu damuwa, na gode".

Ya katse kiran, nan tausayinta ya ?ara kama shi, ya kuma raya a zuciyarsa lallai yaron nan ya cuci Nuratu, ko ta san tana da cutar a jikint? Da ya yi tunanin sanarwa Baba, sai kuma ya ga tun da yaron ne zai aure ta gara ma ya bar zancen don kar abun ya yi wa Baba yawa, ya tausaya musu sosai, ya kuma gode Allah da aka gano hakan, bai aure ta ba ya sakawa

5 / 41