Advertisements
Chapter 40 Reading Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   40 / 41

117K to 120K   out of 121.6K words

kawai yake nema, ta ishe shi kariya a duk inda yake, sannan yara nawa ne suka zama ababen alfahari ba tare da sun rayu da mahaifiyarsu ba, haka kuma yara da dama sun zama baragurbi a ?ar?ashin kulawar mahaifiyarsu, don haka addu'a ita ce kawai.

Kabir ya ce"Nuratu me kika yanke? Kar ki matsawa kanki, idan soyayyar kika zaSa ki sanar da ni, don na fara laluben uwar da zan samawa Wana, na saki Nawwara kuma ba zan dawo da ita ba har abada, ke kuwa za ki yi auren soyayya da saurayi ki yi ?ara'i, kin ga dole na samarwa Wana makoma".

Ta ce"Ka yi ha?uri Yaya Kabir..."

Ya katse ta da faWin"Ba sai kin ba ni ha?uri ba, ki tafi kai tsaye, sannan ha?urin da kika saka a farko ya bayyana mini abin da zai zo a ?arshe, kin zaSi wannan saurayin ko?"

Ta ce"Hakane, amma..."

Ya sake katse ta da faWin"Nuratu babu wani amma, ai ba laifi kika yi ba, Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi, idan kin riga ni yin aure zan Wauki Wana na kai shi gidanmu a ri?e kafin na samu wacce zan aura, idan kuma na riga ki zan karSe shi na ri?e, na gode Nuratu Allah Ya ba ku zaman lafiya da zuri'a Wayyiba".

Ya ajiye mata kuWin da ya saba bata a cinyarta, ya ce"Ki je gida zan wuce".

Ta share hawayen rashin dalili da ya sakko mata, ta ce"Na gode".

Ta fita, ya bi bayanta da kallo har ta shige gidan, ya zaro tissue ya share nasa hawayen, sannan ya rungume Wansa, yana jin tausayin shi tare da tausayawa kansa shi ka, ya yi kamar minti biyu a haka sannan ya ja motar ya tafi gidan iyayensa, yana jin zafi a zuciyarsa, tabbas akwai ciwo ka nemi abin da kake so ka rasa, amma dole zai jure saboda ba ya fatan ya sake aurenta ba tare da son zuciyarta ba a karo na biyu.


ABDUL

Zuwa yanzu zai iya cewa shi bai ma san ta?amaiman halin da yake ciki ba, amma dai duk wani taurin kansa da na zuciya ya sauke yanzu ya yardarwa kansa tabbas yana son Nuratu har yanzu, kuma ita ce zaSinsa ba Asma'u ba, ba shi da wani tunani sai nata, kuma yanzu ya fara jin nadamar abin da ya yi mata, ya gane tabbas so ne da zuciyar mace mai cike da tausayi da sadaukarwa ya sa ta aikata abin da ya kalle shi a matsayin cin amana, ya fara tuna soyayyarsu sahihiyar nan tun ta ?uruciya, son ta ya dawo sabo dal a zuciyarsa ba tare da ya ankara ba, sai dai da wane idon zai kalle ta? Ta ya zai sake cewa yana sonta a karo na biyu ta yarda kuma ta manta da duka zafafan kalaman da ya jefe ta da shi a ranar da ya kai mata katin aurensa da wata? Gaskiya abu ne mai wuya Nuratu ta sake yarda da shi, duk da ya san zuciyar mace tana da saurin mantuwa da yafiya, amma fa wani butulcin ya fi ?arfin a manta da shi, wani Wacin ya wuce a sha alawa ya wuce, madawwami ne ga wanda aka WanWanawa shi har ?arshen numfashi.

Tun yana Soyewa har Asma'u ta gane ba ta gamsar da shi, sau biyu yana ambatar sunan Nuratu a yayin da yake tare da ita, Asma'u tana da matu?ar kishi, don haka daga ranar ba ta sake yarda ya taSa ta ba, kuma ta rasa wanda za ta kai wa ?arar shi, ta dai tambayi ?anwarsa ko Abdul ya taSa yin wata buduruwa mai suna Nuratu ta ce mata e ita ce wacce ya aure ta ya sake ta kafin su tare, har ma ta turo mata hotonta, don haka ta saka a ranta za ta binciki wayarsa ta gani ko bai daina kula ta ba.

Sannan wannan halayar tasa ta istimna'i tana ta ?ara gaba, ta taSa kama shi yana yi a Waki, ga kuma wayar a hannunsa yana kallo yana kiran sunan Nuratu, hankalinta ya tashi sosai, ta shiga banWaki ta ci kuka, amma ba ta yi masa maganar ba, sai da ya gama ya shiga wanka ta Wauki wayarsa ta duba, nan ta ga bidiyoyin Nuratu, ta gane ta duk da hotonta Waya ta gani, zuciyarta ta kumbura tana tunanin wannan wace irn shaiWaniya ce ya yi aure ma ba ta ?yale shi ba tana turo mata abubuwa, nan ta haWa su duka ta goge har hotunan ko da wanda ta saka hijjabi ba ta bari ba sai da goge komai, ta ajiye wayar ta tafi harkar gabanta.

Abdul bai tashi sanin ta goge ba sai tsakar dare da ya kasa bacci ya tashi don komawa falo ya biyawa kansa bu?ata kamar yadda ya saba, kawai ya ga wayam babu komai da ya danganci Nuratu, babu bidiyoyin da suke sama masa nutsuwa, hankalinsa ya tashi ya dinga shige-shige a wayar ya birkitata bai ga komai ba, tuni zuciyarsa ta kumburo ta fara azalzalarsa, ya san wayarsa babu key don haka ya fara tunanin Asma'u za ta iya Wauka ta goge masa, a birkice ya shiga Wakin gadon ya kunna globe ya fara tashin Asma'u, ta tashi zaune tana cewa"Lafiya?"

Kallo Waya ta yi masa ta gane ba ya cikin hayyacinsa, yana muzurai ya ce"Uban waye ya goge mini bidiyoyi a wayar nan!?"

Ta ce"Wasu bidiyoyi?"

Ya ce"Kar fa ki raina mini hankali, babu wanda na ba wa wayata, don haka na san ke ce kika Wauka kika yi mini bincike".

Ta sakko daga gadon cike da kishi ta ce"E ni ce, na goge Win! Kai idan kana da kunya har za ka aikata wannan mummunan abun don na goge ka zo ka titseye ni?"

Tass! Ya wanke ta da mari, ya ?ara fesa mata wani, yana huci cikin ?araji ya ce"Kin san me kika goge kuwa? To tamkar kin kashe ni ne! Wannan bidiyoyin su ne suke ba ni farinciki da kuma lasisin rayuwa, zan iya mutuwa saboda shirmen nan da kika aikata, gara ki ce na sake ki a kan ki goge su, kin cuce ni Asma'u, ba zan taSa yafe miki ba!".

Sai ya rufe ta da duka cikin fitar hayyaci, dukanta yake yi ta ko'ina kamar yana dukan sa'ansa namiji, sai da ya yi mata laga-laga sannan ya watsa ta waje, ya zauna yana ta huci, sai ya je kamar gara ma mutuwarsa da ganin wannan ranar, hakan yana nufin shi kenan ba shi da sauran abin da zai yi wa Nuratu barazana? Ba shi da wata dabara za ta ita yin aurenta da wanda take so yana kallo suna rayuwa mai inganci alhalin shi ta shi rayuwar ta shiga halin ni ?asu ta dalilinta? Bacci ya ?auracewa idonsa a wannan daren.

Ita kuwa Asma'u falo ta koma ta kwanta tana wani irin kuka mai cin raiz ga jikinta da yake ta karkarwa kamar an jona mata shokin, ta yi nadamar auren Abdul, ba ta tsinci komai a soyayyarsa da aurensa ba sai ba?inciki da nadama, ta rabu da tarin masoyanta ta zaSe shi da fatan samun rayuwa mai inganci ashe ba za ta samu ba sai tarin nadama, ba don tsoron sharri dare da kuma karnukan da suke haushi ba da babu abin da zai hana ta tafiya gidansu a daren nan, haka ta ha?ura sai da safe.

Tana idar da sallar asuba ta shiga kitchen ta Wora ruwan wanka, sai da ya tafasa ta shiga Wakin gado don Wakko towel Win da za ta shiga wankan da shi, kwatsam ta ga Abdul kwance haihuwar uwarsa, yana ta ?o?arin biyawa kansa bu?ata yana kuka yana kiran sunan Nuratu, ba?inciki ya turnu?e ta, ba tare da zurfin tunani ba, ta koma kitchen ta je ta Wakko tukunyar ruwan zafin da yake ta tafasa ta shiga Wakin ta Waga ta she?a masa duka.

Wata irin azaba ta baibaye Abdul, nan take ya dawo hayyacinsa ya saki kururuwa yana ihu, kafin ka ce kwabo jikisa ya saluSe ya yi jawur, sai juyi yake yi a gadon cikin azaba yana ihun da har ma?ota suna jiyowa.

Sai a lokacin hankalin Asma'u ya dawo jikinta, ta lura da girman abin da ta aikata, ita ma kukan ta fara da nadama tare da tsoron kar ta yi kisan kai, ta saka hijjabi tana kuka ta fice daga gidan, kafin ta ?arasa gida ta sanar har ma?ota sun gaji da jin ihunsa sun shigo, suka same shi a wannan yanayin, aka kwashe shi a ka rufa masa zani sai asibiti.


08028966015
*ZUCIYAR MACE*



53

Idan ka ga yadda Abdul ya koma sai ka ?ara jin tsoron Allah, tun daga kan fuskarsa har ?afafunsa ya ?one abun ya yi muni, sai net da aka saka masa saboda babu damar saka kaya, ba kowa ma ake bari ya shiga ya gan shi ba, fata yake yi kawai Allah Ya Wauki rayuwarsa, bai taSa hasashen rayuwarsa za ta zama haka ba cikin ?an?anin lokaci, Nuratu ce ta tarwatsa masa rayuwa ko shi ya tarwatsawa kansa? Tambayar da yake ta yi wa kansa kenan, wata nadama mara kwatance ce take daskare a zuciyarsa, yana ta istigfari a zuciya, da fatan Allah ya yafe masa abin da ya yi wa Nuratu, hawayensa sun ?i tsayawa duk kuwa da nasihar yarda da ?addara da iyayensa suke ta yi masa.

Sanda Asma'u ta je gidan iyayenta, hankali tashe tare ta da tambayar abin da ya faru, saboda a birkice take sai haki take yi, don a ?afa ta je, gani ta yi tsayawa hawa adaidaita sahu ma Sata lokaci ne, ta fashe da kuka tana cewa"Na shiga uku Mama, na kashe Yaya Abdul, wallahi na san mutuwa zai yi!".

Mama ta jijjiga ta tana cewa"Ke ki nutsu! Me kika yi masa?"

Ta ce"Ruwan zafi na she?a masa, jikinsa duka ya saluSe ya yi ja, yana can, ni na san ma ya mutu".

Mama ta Wora hannu a ka ta rafka salatin da ya fito da mahaifin Asma'u, ta ce"Alhaji yau mun shiga uku, mun ga ba?ar rana, Asma'u ta ?ona mijinta".

Hankali tashe suke tambayarta abin da ya haWa su, ba ta Soye komai ba ta sanar da su, shi dai babanta gidan ya tafi don ceton shi, uwar kuwa ta rufe ta da duka tana kuka.

Wajen ?arfe tara mahaifiyar Asma'u ta je asibitin duba shi, yana ganinta ya tuna da ?arta ce silar faruwar komai, ya ce da babar shi "Umma na sake ta, na saki Asma'u, don Allah kar ta zo nan ba na son ganinta har abada".

Zuwa azhar labari ya karaWe gari, matar Abdul ta ?ona shi, sai ga shi har gidan rediyo ana labarin wata amarya ta ?ona angonta bayan watanni da auren nasu, don ma dai Abdul ya ?i yi wa ?an jarida ?arin bayani, amma dayake suna da ?wa?wa sai da suka nemo gidansu Asma'u suka je, ita kaWai ce a gidan lokacin sai ?annenta, don haka ta yi wa duniya ?arin bayani cewar wata buduruwarsa mai suna Nuratu ce take turo masa bidiyon banza yana kalla yana biyawa kansa bu?ata, shi yasa ta kasa jurewa har ta aikata masa haka. Duk yadda ?an sanda suka so tafiya da ita mahaifin Abdul ya hana ya ce matsala ce ta family, saboda tun da ala ji dalilin Asma'u sai kowa yake jin haushin Abdul Win, har da masu yi masa Allah Ya ?ara.

Sanda labari ya je kunnen Baba, hankali tashe ya tafi gida, ya samu Nuratu jikinsa har karkarwa yake yi ya ce"Nuratu! Da gaske ne abin da yake yawo a gari wai kina turawa wannan yaron Abdul bidiyon jikinki? Da gaske kin aikata?"

Nuratu ta fashe da kuka, don tun safe ?awayenta suke kiranta da zancen sai kashe wayarta ta yi, Asabe ta ce"Ba kuka za ki yi ba, bayani za ki yi? Amma fa Malam abun da kamar wuya gurguwa da auren nesa, anya Nuratu za ta yi haka?"

Baba ya ce"Nuratu za ki faWa mini ko sai na karaira ki!?"

Cikin kuka ta ce"E na tura masa amma wallahi a lokacin da aurenmu, kafin ya sake ni ne, yake cewa na tura masa, ni kuma na ga tun da mijina ne ai bai haramta ba, kuma bayan mun rabu sai da na ce ya goge".

Tana rufe baki Baba ya rufe ta da duka ta ko'ina yana cewa"Shikenan asirin gidan nan ya tonu, Nuratu kin cuce mu! Kin janyo mana abun kunya, yanzu fita ma sai ta gagare ni".

Da ?yar ?an gidan suka ?wace ta, aka rufar mata da faWan wannan gangancin sa ta yi, sai ta ji ina ma mutuwa ta Wauke ta ta huta? Nan take zazzaSi ya rufe ta, ta wuni a kwance, ba ta taSa nadama irin wacce take ciki a yanzu ba, ba ta taSa zaton don ta turawa mijin da ya biya sadakin aurenta bidiyon jikinta zai zama silar abubuwa marasa daWi a rayuwarta ba, tabbas Abdul ma?iyinta ne ba masoyi ba, kuma ba za ta taSa tafe masa ba.

Da daddare bayan sallar isha'i sai ga Suraj ya aiko yana sallama da ita, ta tashi da ?yar ta fito, idonta ya yi luhu-luhu, ga jiri da yake Waukarta saboda yunwa, Suraj ya ce"Nuratu meyasa kika kashe wayarki ne? Ina ta kiranki ba na samu".

Ta ce"Ba komai".

Ya ce"To dama sallama na zo na yi miki".

Ta ce"Sallama kuma? Na ga ka ce sai wani satin za ka tafi".

Ya ce"E tafiya tana nan sai wani satin, sallama na zo mu yi ta tabbacin mun rabu da ke salun-alun, ina nufin kamar dai yadda na zo ?ofar gidan nan muka ?ulla ala?ar soyayya, haka yanzu ma na zo mu kunce ta".

?irjinta ya yi wata irin bugawa, Suraj yana da barkwanci da tsokana, amma bai taSa yi mata irin wannan wasan ba, sannan babu alamun wasa a fuskarsa, ta ce"Suraj me yasa? Me na yi maka?"

Ya ce"Nuratu yau dai a eriyar nan da kewaye babu wanda zai samu labarin abin da ya faru ba, sunanki yana ta yawo a gari da cewar kina turawa tsohon mijinki bidiyon jikinki, Nuratu kin ba ni labarin soyayyarku da shi, da aurenku har zuwa rabuwarku, kin nuna mini kin manta da soyayyarsa har abada, amma me yasa haka ta faru?"

Kukanta ya tsananta, sai da ta tsagaita sannan ta faWa masa komai da ya jawo hakan, ya ce"Allah Ya kyauta, amma dai kin yi wauta, ta ya za ki tura masa jikinki don yana mijinki? Wannan ba ?aramin abu ba ne, darajar mace ya wuce ta aikata wannan, mata kuna kuskure sosai, yanzu za ki bi duk mutanen gari ne ki faWa musu gaskiya ko kuwa gidan reriyo za ki je ki yi bayani? Ko kin yi hakan wani ba zai taSa yarda da ke ba har abada, zancen da nake yi miki wannan labarin har Sokoto ya je, wasu ma har sun samu hoton shi ana sakawa a media tare da ?arin bayani, ?ila nan gaba kema a nemo naki, ko ma a nemo ainahin bidiyon".

Ya nisa kafin ya ce"Ki yi ha?uri Nuratu, zan iya auren wacce ta yi aure goma, amma ba zan iya auren wacce bidiyon jikinta ya shiga duniya ba, ko na aure ki zan yi ta kallon ki da wannan, saboda haka daga yau ki manta kin yi soyayya da wani mai suna Suraj, ni ma zan manta da ke, Allah Ya haWa kowa da rabonsa na alkhairi".

Daga haka ya juya ya tafi, wani irin yanayi Nuratu ta shiga mara misali a daidai wannan lokacin, tana matu?ar ?aunar Suraj, tsaf ta gama tsara rayuwar auren da yadda za ta kasance, ashe Wan hakin da ta raina zan tsole mata ido har ma ya kashe mata buruka? Ba ta taSa hasashen turawa miji bidiyo zai saka rayuwarta a wannan ?adamin ba, lallai ya kamata a dinga zurfafa tunani da shawartar sha?i?an ?an'uwa kafin aiwatar da komai.

Tun daga ranar ta kwanta jinya, tun ana banza da ita har aka fara damuwa, sai da ta kwanta a asibiti. Abdul ya fara samun sau?i a yanzu babu abin da yake bu?ata kamar neman yafiyar daga Nuratu, kullum zancensa kenan a kira Nuratu ya ro?i yafiyarta, sau biyu iyayen Abdul Win suna zuwa wajen Baba, amma sam ba ya sauraron su, ita kuma tana asibiti, ?arshe dai sun samu zuwa asibitin suka ro?e ta, tana kuka ta ce ba za ta yafe masa ba.

Satinta Waya aka sallame ta ba don zuciyarta ta ji sau?i ba, sai dai sau?in gangar jiki. Duk abin da ake yi Kabir yana sane da komai, don shi ne ya turo kuWi aka kai ta asibitin da duk wani abin da ake bu?ata, amma bai zo ba, Nuratu ba ta yi mamakin rashin zuwansa ba tun ta nuna masa ba shi da wani tasiri a rayuwarta, ta zaSi Suraj a kansa, ba tare da sanin saki reshe kama ganye ta yi ba, sai yanzu ta fahimci Kabir ne masoyinta na ha?i?a, tun da shi ya san da sanin bidiyon nan amma ya ce ya ji ya gani, don haka dole za ta aure shi don yanzu ba ta da mafitar da ta fi tashi, ko da kuwa ya samu wacce ya ce zai laluba sai dai ya fasa ko kuma ya haWa su duka ya aura.

Kusan kullum sai sun yi waya da Hajiya kafin a sallame ta daga asibitin nan, kwana biyu da sallamarta sai ga Hajiya ta zo dubiya, ta zaunar da Nuratu ta yi mata nasiha sosai kan ta kiyaye gaba domin kuskure ta riga ta yi shi, ta ?ara da faWin"Nuratu na ji takaicin yadda sunanki ya karaWe duniya da abin da kika yi, wannan zai iya taSa rayuwarki a gaba, don haka na yanke shawarar haWa ki aure da Wana..."

Nuratu ta Wago da sauri ta kalle ta, Hajiya ta ce"E mijin Zahra nake nufi, ya sake ta wata Waya da ya wuce, saboda ya kamata tana lalata da Safiyya, shi ne na yanke shawarar aura masa ke, domin ni na san wace ce ke, na san ba da ganagan kika aikata abin da ake ta yamaWiWi da ke ba".

Nuratu ta ce"Amma Hajiya shi ba lallai ya yarda da ni ba, ?ila ya aure ni saboda ya yi miki biyayya, ba don

40 / 41