Advertisements
Chapter 3 Reading Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 41

6K to 9K   out of 121.6K words

zazzaSin, suka yi sallama, saboda ba ya son jan magana.

Suna gama wayar ta tuna jiya Alhaji ya ce da kuWi a ledar nan da ya ba ta, sai ta Wakko ta dudduba, ba ta ga alamar kuWi ba, sai ta raya ko mantawa ya yi bai saka ba, ta san halin gidansu da sata, amma yanzun ba ta kawo wata ce ta Wauka ba, to idan ma Waukar aka yi, ita yanzu ba ta su take yi ba, ta koma ta kwanta.


Wajen azhar tana zaune tana cin abincin da ?anwar Mama ta kawo mata, sai ga Isa ya zo da leda har da ruwa wai zai saka mata, Baba yana ?ofar gida Isa ya gaishe su, ya shige, don haka ya biyo bayansa, daidai sanda Nuratu ta fito tsakar gida.

Baba ya ce"Kai yaro lafiya wajen wa ka zo?"

Ya ce"Baba aiko ni aka yi zan duba Nuratu".

Baba ya ce"Ikon Allah! Kai kuwa yaro wane hamsha?in ne?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ya aiko ka?"

Ya ce"Abdul ne saurayinta".

Baba ya ce"Ka ce dai tsohon saurayinta, to wuce ba ta bu?ata, sannan ka faWa masa kar ma ya sake asarar kuWinsa a kan matar da ba ta shi ba, ni na riga na ba da ?ata ga wanda ya dace, lokaci kawai muke jira, ba don mutuwar nan ba ma, da a cikin satin nan za a tsayar da rana".

"Ok" Isa ya faWa yana juyawa ya fice daga gidan.

Nuratu da duk ranta ya gama Saci, ta ce"Haba Baba..."

Ya ce"Buhun ubanki! Ba ki da lafiya shi ne ba ki faWa mini ba? Duk duniya yanzu kina da wanda ya fi ni ne?"

Ya ja tsaki, ya ciro waya, ya yi danne-danne ya kara a kunne, can ya washe baki ya ce"Wa alaikumus sallam, Alhaji ina kwana?"

Alhaji dake zaune tare da matarsa tana zuba masa abinci ya amsa da"Lafiya lau Baba, ya ?arin ha?uri?"

Baba ya ce"Da godiya. Wallahi Alhaji dama mutumiyar taka ce dama babu lafiya, wallahi zazzaSi jiya ba mu yi bacci ba, shi ne na ce to bari a sanar maka..."

Alhaji ya ce"Subhanallah! Bari yanzu zan aiko sai a Wauke ta a kai ta asibiti".

Daga nan sai Baba ya dinga jera godiya, har yana rusunawa kamar yana gabansa.

Ya kalli Nuratu ya ce"Tafi ki shirya, zai aiko a kai ki asibiti yanzu, ai ke dai Allah Ya dubi maraicinki da ya kawo miki wannan bawan Allah mai karamci".

Nuratu da ta shiga tashin hankali, ta marairaice ta ce"Baba Wan zazzaSi ne fa, ni ba sai mun je asibiti ba".

Baba ya ce"Ai ke shashasha ce, har ki samu mau jiSantar lamarinki amma ki tsaya shashanci, maza shirya".

Ta shiga Waki, ta zauna, sai ta fara hawaye, ta san manyan asibitocin nan da ?ir?ire-?ir?ire, tsoronta Waya kar a ce za a yi mata wani gwajin da zai fallasa sirrinta.

Babu jimawa Baba ya shigo ya ce ta fito su tafi, yayarta Rahma ?ar Mama Karime tana tsakar gida Baba ya ce"Ke Ramatu wuce ki raka su".

Har da saurinta ta sako hijjabi, suka fita, Nuratu tana jin kamar ta ce ba za ta je ba.

Har da buWe mata murfin motar, ta shiga ya ja suka Wauki hanya. Dab da asibitin ta ga wani babban chamest, ta ce"Bawan Allah kawai ka tsaya ka siya mini magani a nan, ba dole sai an je asibiti ba".

Ya Wan yi jim, sannan ya ce"To Hajiya ai ni umarni nake bi, sai dai na tambayi Alhajin, duk yadda ya ce".

Ta ce"To ka faWa masa jikin da sau?i sosai, magani ma ya isa".

Ya faka motar, ya Wakko waya ya kira Alhaji, ya yi masa bayanin da Nuratu ta yi, Alhaji ya ce kawai ya wuce su tafi asibiti, idan ma maganin ne su ba ta a can".

Ba ta sake cewa komai ba, har suka ?arasa asibitin. Tun kafin zu je Alhaji ya yi magana da likita, don haka kai tsaye direban ya rakata inda ya kwatanta masa, ta zauna a kujera sai raba ido take yi, hannunta yana dafe da mararta ta cikin hijjabi, gani take kamar likitan yana kallonta zai gane tana da cikin. Ya tambaye ta me yake damunta? Ta ce"ZazzaSi ne kawai kuma ya riga ma ya sauka tun a hanya".

Ya ce"Ma sha Allah! Amma Alhaji ya ce ko abinci ba kya ci, ya ce a saka miki ruwa saboda ki samu ?arfin jikinki, sannan zazzaSin ?ila malaria ce, za mu yi miki gwaji mu gani".

?irjinta yana ta dukan uku-uku ta ce"Likita, ni fa ina jin ?arfin jikina, kawai ku ba ni magani ya isa".

Likita ya yi murmushi, don ya sabada mara lafiya mai gardama, ya ce"Ki yi ha?uri Hajiya, a yi miki yadda ya dace kawai".

Ya tura su wani Wakin, wajen wata nurse, ita ta Wibi jininta, sannan aka saka mata ruwa ta kwanta gabanta yana ta faWuwa, tana ayyana ?ila yau ce ranar ?arshe cikin ranakun farincikinta na gidan duniya.

A Sangaren likita bayan sun fita sai ga kiran Hajiya Laila, uwar gidan Alhaji, suka gaisa ta ce"Doctor yarinyar da aka kawo daga wajenmu me yake damunta?"

Ya ce"Yanzu dai za a duba, zazzaSi ne take yi, sai rashin ?arfin jiki, an tafi saka mata ruwa".

Ta ce"Ok, don Allah kar ka bari ta tafi, sai ka samu adireshinta ko lambar waya, ka ajiye mini account deteils Winka".

Ya ce"An gama Hajiya godiya nake". Suka ajiye waya.


08028966015
*ZUCIYAR MACE*



BY
SADIYA ABDULRAZA?


*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY


PAGE 4


Sakamako yana fitowa likitan Hajiya Kubra ya fara kira, ya sanar mata yarinyar ciki ne da ita na sati tara, sai kuma malaria. Hajiyar ta yi murmushi ta ce"Idan ka tashi sanar masa ka ?ara da cewar tana Wauke da cuta mai karya garkuwar jiki". Likita ya amsa, amma a zuciyarsa yana ta auna yiwuwar hakan, domin babban laifi ne, har a cikin aikinsu, sannan yana gudun Alhaji ya bincika ya gane ba haka ba ne.

Har allurar bacci Alhaji ya sa aka yi mata, don ta samu hutu, ba ta san tsayin lokacin da ta Wauka tana bacci ba, ta dai farka ne kawai ta ga Mama Karime zaune a kan sallaya, gefen gadon da take kwance, gabanta ya faWi, ta tashi zaune, har an cire ?arin ruwan, Mama Karime ta ce"Sannu Nuratu kin tashi?"

Sai ta kasa amsawa, kallonta dai take yi, tana son karantar fuskarta, don ta samu wani haske a kan zargin da take yi na fallasar sirrinta, sai dai ba ta ga komai a fuskar Mama ba, ta ce"Mama ba su sallame ni ba?"

Ta taSe baki ta ce"Jira suke ki tashi, amma ke wannan gadon asibitin ai a yanzu sai ya fi yi miki daWi fiye da gidanku".

Gabanta ya faWi, tana rabon ido ta ce"Mama saboda me?"

Ta ce"Saboda cikin jikinki, da ?yar aka fitar da babanki daga asibitin nan, don cewa ya yi sai ya kashe ki, da tuni sai dai ki farka ki ji ana man Rabbuka?"

Bugun zuciyarta ya tsananta, tuni tsoro ya dirar mata, ba ta sake shiga tashin hankali ba sai da Mama ta cigaba da faWin"Babban abun damuwar ma asirinki ya tonu, don na san zuwa yanzu maganar nan ta fantsama cikin gari, tun da a gaban Zainabu aka yi komai".

"Innalillahi! Me ya kawo ta?" Ta tambaya tana sakin kuka.

Mama ta ce"Ta je gida kai miki abinci, aka faWa mata kina asibiti, dama lokacin babanku ya ce gado aka ba ki, na ce ya kamata na bi ki, shi ne ta ce mu tafi tare, shigowarmu ke da wuya, muka samu ana kokowa da babanki. Nuratu kin ba mu mamaki, ba ki kyautawa Salamatu ba". Ta ?arasa a raunane.

Ta kifa kai a cinyarta ta rushe da kuka, shikenan asirinta ya tonu, abin da take ta Soyewa yau ya fito fili, tunani take yi yanzu ya za ta yi? Wane bayanin za ta yi musu su fahimce ta? Da wane idon za ta kalli Abdul? Sannan idan ta faWa masa dalilita zai yi mata uzuri kuwa?"

"Ina wayata?" Ta tambayi Mama.

Ta Wakko ta mi?a mata, ta danna ta ga ?arfe takwas da rabi na dare, ta sakko daga gadon, ta shiga banWaki ta yo alwala, ta fara jero salloli, lafin ta idar Mama ta zuba mata abinci, ta mi?a mata tana cewa"Wannan abincin duk Alhaji ne ya aiko miki, wallahi Nuratu kin yi asarar miji kamar shi, don kuwa shi ma zuwa yanzu ya samu labari, ai da mutunci ma, idan wani ne na tabbata korar kare zai sa a yi mana daga asibitin".

Nuratu ta fara cin abincin a hankali, tana hawaye.

Mama ta cigaba"Idan kuma Allah Ya tarfa wa garinmu nono sai ki ga duk da hakan bai janye ba, tun da wasu suna sane ma suke auren karuwa, saboda huce takaici ta wani Sangaren".

Sosai surutun Mama ya dame ta, saboda tana ruguza mata lissafin da take yi ta tafkawa a zuciyarta. Fatanta dai a ce yau a asibitin za ta kwana, indai lissafin da ta yi yanzu ya tafi daidai, to a tasha za ta kwana, washegari ta bar garin.

?arfe tara da ?an mintuna, sai ga direban Wazu da ya kawo su, ya shigo ya ce"Hajiya za mu tafi, in ji Alhaji".

Nuratu ta ce"Sun sallame ni?"

Ya ce"E". Ya kwashi kanukan abinci ya wuce gaba.

Mama ta ce"Sai ki tashi mu wuce, ?iyamarki ta tsaya cak yau".

Wani sabon kuka ya zo mata, duk nu?u-nu?un da ta tsaya yi don Mama ta yi gaba, abun bai yiwu ba, haka ta saka ta a gaba suka shiga mota, a ciki suka tarar da Alhaji Hashimu, sai kunyar duniya ta rufe Nuratu, duk da ba son shi take yi ba, amma ba ta so a ce zai yi mata kallon mara tarbiyya ba, haka motar ta yi tsit har suka ?arasa gidan.

Baba da abokansa biyu suna zaune a ?ofar gidan, ya taso da sauri ganin motar Alhajin, sai dai Nuratu tana fitowa ya gimtse fuska, yana huci.

Wani mugun haushinta yake ji, gabaWaya ta canza masa lissafi. Suka shiga daga ciki, a zaune Alhaji ya ce su tsaya, Nuratu za ta wuce ya ce ita ma ta tsaya, ta dawo ta tsugunna kanta a ?asa tana hawaye.

Baba ya ce"Don Allah Alhaji ka yi ha?uri, wallahi da na san da wannan bada?alar a jikinta da ban yi maka al?awari ba, Wan yau ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba!".

Alhaji ya ce"Na sani, kuma a yadda na samu labarin tarbiyyar Nuratu na san wannan ?addara ce, kar ku damu, ni tsakani da Allah nake son yarinyar nan, musamman yanzu da wannan ?addarar ta faru da ita, na san rayuwarta za ta iya shiga garari, saboda Baba ni na ji na gani, zan aure ta na kau da ido a kan komai, da an cire cikin shikenan".

Baba ya fara jero godiya har da kukansa, Alhaji yana cewa "Babu komai".

Sannan ya yi wa Nuratu nasiha sosai, tamkar tsakanin uba da ?arsa, har ta ji a ranta wannan mutumin ?a?ansa sun yi sa'ar uba, ba kamar ita ba, ya ?ara da ro?on Baba kan kar ya ce zai dake ta, ko wani hukunci, addu'a ita ce kaWai mafita, daga haka ya tafi, ita ma ta shiga gida, ta saka sakata a Waki, duk bugun da Baba ya yi ba ta buWe masa ba.

Ba ta taSa zaton mutumin nan zai ce zai aure ta a hakan ba, ta san auren nasa rufin asirinta ne, amma ya za ta yi da soyayyar Abdul Winta? Sai ta Wakko wayarta, ta yi masa sallama ta whatsApp, yana online bai duba ba har tsawon mintuna, sai ta danna voice, sai dai ta kasa cewa komai, har tsawon sakan goma, sai ta sake shi a hakan ya tafi, wannan karon da wuri ya duba, bai ce mata komai ba, ta ajiye wayar ta kwanta.

Can tsakar dare kuma ta tashi ta fara haWa kayanta a wata tsohuwar akwatin Mama, wanda ta bar mata ita, kayanta ne dama a ciki, ta saka komai ta ajiye ta tsaf, sam ba ta runtsa ba, kiran sallar farko a kunnenta, ta fito a hankali, tana jan akwati ta fice daga gidan a hankali, ta karo ?ofar, ta fara sauri don gudun wani ya biyo bayanta, tafiya mai nisa ta kai ta tasha, ta tarar da tsirarun mutane, ta zauna ta fara hawaye tana fatan Allah Ya sa a karSe ta a inda za ta je, sannan ta samu buta, ta yi alwala ta yi sallar asuba wanda har an kusa idarwa. Ta faWawa kwandasta Kaduna za ta je, aka saka ta a motar, ta yi zaune tana jira ta cika, zuciyarta tana ta dukan uku-uku. A daidai lokacin ne kuma Mama Asabe ta le?a Wakinta, ta ga ba ta nan, nan ta hau cikiya a tsakar gida, kowa ya fito ana jajantawa.


********

Misalin ?arfe goma Nura ya kira Hasana a waya, tana Wagawa ya ce"Ke maza ki buWe wannan Wakin ki share shi tass! Gani nan zuwa".

Ta san dai Wakuna uku ne a gidan, ciki da falon da take ciki, sai kuma falle Waya, wanda take saukar ba?inta, da kuma keken Winkinta a ciki, ta san shi yake nufi, amma hakan bai hana ta tambayarsa ba"Wane Wakin?"

Ya ce"Wannan wace irin tambaya ce? ?ayan Wakin nan dai, da kike saka shirgi, ba na so na zo na tarar da komai a ciki".

Ta ce"To saboda me? Yanzu ina zan kai keken nawa?"

Ya ce"Wannan kuma ya rage naki, idan za ki kai shi bola zan taya ki". Ya kashe wayar.

Ta zauna tana mamakin me zai saka a cikin Wakin? Ta san halinsa yanzu sai ya zo ya fara yi mata hayaniya, don haka ta tashi, ta fito da komai, ta share kamar yadda ya ce, ta janyo ?ofar ta koma Wakinta, can anjima sai ga shi yana shigo da kaya, katifa ce madaidaiciya, da kayan kallo, har da ?aramin firji, ta cika da mamaki, tana tsaye ya fara shiga da kayan yana ?ar wa?arsa, da alama yana cike da nishaWi, ganin ko kallo ba ta ishe shi ba, sai ta shige Wakinta, tana jira ya gama ta ji bayanin da zai yi mata. Ai kuwa yana gamawa ya ?wala mata kira, ta fito tana amsawa, ya ce"Shigo mana".

Ta shiga tana ?arewa Wakin kallo, ya ce"To yanzu saurana sif, zan sa a yi mini sif mai biyu ?ar madaidaiciya haka, wacce zan zuba kayana a ciki, kin ga komai na zai zauna lafiya, idan zan fita na rufe Wakina shikenan".

Da mamaki ta ce"Kamar ya Wakinka? Au wai nan turaka ce ka ware kenan?"

Ya ce"Ai ya wuce wai, ni na gaji da yadda nake bacci rabi da rabi, yara su hana ni bacci su hana ni sakat, tsakar dare a farka a yi ta kuka, don haka na ware Wakina".

Hasana ta ce"Baban Salim kenan! Kuma ban da abunka na ga dai yaran nan naka ne, sannan abu ba na farko ba, ba na biyu ba ai ya kamata zuwa yanzu a ce ka saba, kuma ma yanzu don ka yi hakan ai ba shi zai hana ka jin kukan Aiman ba, tun da dai ka san ba zan zo na kwana a nan na baro yaro ?arami mai shan nono ba, dole da shi zan dinga tahowa".

Nan take fara'ar fuskarsa ta gushe, ya ce"Ki taho ina? Wai kina nufin saboda na ware Waki sai ki kwaso jiki ki biyo ni? Kenan ma na gudu ban tsira ba! A'a ba zai yiwu ba, ki yi zamanki da yara, ni duk sanda na bu?ace ki zan kira ki, amma gaskiya ba don mu tare mu biyu na ware Wakina ba".

Ta ce"To shikenan!" Ta juya ta fice, ranta bai so ba, sam ba za ta samu nutsuwa ba, saboda zarginsa da take yi ne zai ?aru sosai, haka kawai ma tsakar dare farkawa take yi ta ga ba ya Wakin, sai ta ji shi a tsakar gida yana waya, ko ta gan shi a falo yana vedio call, sai ya ganta ya yi tsaki, ya koma ya kwanta, to ina ga kuma ya ware Wakinsa shi kaWai? Tabbas zai ci karensa babu babbaka kenan, ta san ba ta isa ta ja da shi ba, amma kuma za ta yi iya yinta ta saka masa ido, don ganin bai kauce hanya ba, don haka ta ayyana bacci da ido Waya ya kama ta.

Haka ya wuni yana shige da fice, ya saita kayan kallo tsaf, dama akwai babbar setilait a tsakar gidan, tun da risibarsu ta lalace take ajiye kawai, bai kai musu gyara ba, yanzu sai ya sa aka saita da sabuwar risibar da ya siyo, firji ma nasu ya lalace bai kai gyaran ba, don ya ce ya gaji da gyarawa suna lalatawa, ita kuma a ganinta tsufa ya yi, tun da tun na aurenta ne, shekararsa takwas kenan.

Ya Wakko yara daga makaranta, suna zaune suna cin abincin rana, yake cewa"Ma sha Allah! ?akina ya haWu, yanzu mun yi magana da wani kafinta, zuwa jibi sif Wina za ta zo, sai na samu Wan kafet, na saka a tsakiyar Wakin, ina ga ma sai na sayi senta tebur".

Hasana ko kallonsa ba ta yi ba, saboda takaici duk ya ishe ta.

Ya cigaba da cewa"Yadda tsarin gyaran Wakin zai kasance, da safe idan na gama shiryawa, ina zaune ina karyawa, ke kuma sai ki shiga ki gyara, idan zan fita na rufe abuna, salun-alun karatun yankan jaki".

Har yanzu dai ba ta ce komai ba. Sai ya ajiye kofin hannunsa yana haWe gira ya ce"Wai ni Hasana me kike nufi ne? Ya ina magana kina manna mini hauka? Ko hassada kike yi da Wakin nawa?"

Ta ce"Hmm! A kan me zan yi maka hassada? Kawai dai gani na yi tsarin kamar bai yi ba, a ce kana da mata ita tana Wakinta, kai kana naka, wai sai ranar da ka kira ta? Ka manta sai ka yi wata ba ka kira ni ba?"

Ya ce"To mene ne? Ke ba hutunki ba ne ba ma? Ki sake a Wakinki, na sake a Wakina".

Salim Ya ce"Abba wane Wakin?"

Gwab! Hasana ta buge bakin yaron, tana cewa"Ban hana ka saka mana baki a

3 / 41