Advertisements
Chapter 7 Reading Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Zuciyar Mace Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 41

18K to 21K   out of 121.6K words

Wan yi sanyi, amma ya danne bai nuna ba, ya ma tashi ya bar mata Wakin, shi dai bai ga wata matsala ba saboda yana kula mata, ai namiji mijin mace huWu ne, yana da ra'ayi da burin auren mata huWu idan har ya samu dama, saboda haka ba ta isa ta hana shi ba.

Daga baya ta yanke hukuncin jan hankalinsa don ta gane wace kalar mu'amula yake yi da mata a wayar? Sai ta saka Husainarta ta aiko mata d sabon layi, saboda akwai ?anin mijinta wanda yake siyarwa, ta saka a wayarta, ta saita sabon whatsApp da shi, ta nemi lambar Nura ta yi masa sallama, ya amsa suka gaisa, ya ce bai gane mai magana ba, a rubuce ta ce"E dama ba ka san ni ba ai, yanzu dai nake ganin lokaci ya yi da ya kamata ka san ni, saboda ka daWe kana azabtar da zuciyata da soyayyarka, burina ko yaya ne na samu matsuguni a zuciyarka, wanda za ka dinga tuna ni ko da sau Waya ne a sati".

Sai ya tura stikar murmushi, ya ce"Ikon Allah! Da farko dai ya sunanki?"

Ta ce"Sunana Suhaila, kuma a kasuwa nake ganinka, wallahi kana burge ni sosai, na daWe da samun lambarka, amma sai na yi ta jujjuya ta, na kasa yi maka magana, saboda a zotona za ka yi wula?anci duba da ganin yadda ka haWun nan kake da aji, na ji an ce ma mata ba sa gabanka, shi ne nake ta fargaba".

Nura ya yi murmushi ya ce"Wannan dalilin ai ba shi zai saka mutum ya yi wula?anci ba, sai dau idan dama can halinsa ne, ita mace ai ba abar wula?antawa ba ce, mace abar riritawa ce da tarairaya, kuna bu?atar kula ta kowane fanni, wannan shi ne burin da na ci a kan matar da zan aura har tsufanmu".

Ta ce"Kenan yanzu ba ka da aure? Zan so a ce ni ce zan samu wannan kulawar".

Ya ce"Ina da aure har da yara, sai dai wancen burin nawa yana neman zaSa tarihi, saboda wata kidahumar mace Allah Ya haWa ni da ita, wallahi sam ba ta san kanta ba, ballantana ta san mijinta".

Kalmar kidahuma ta daki zuciyar Hasana ba kaWan ba, nan take ranta ya yi ba?i, sai ta ji kamar ta yi voice ta faWa masa ita ce, sai dai kuma ba wannan gaSar take nema ba, don haka ta daure zuciyarta suka cigaba, ta ce"Ikon Allah! Yanzu duk wannan haWuwar taka ba ka yi dacen mace ba? Amma ai kai ya kamata ka canza ta, ka mayar da ita yadda kake so ku zauna".

Wannan karon voice ya yo, yana ?ar dariya ya ce"Malama Suhaila kenan, wato ba ki san wace ce matata ba, shiyasa kike zaton za ta canza hali, yanzu haka zancen da nake yi miki fa kin gan ni kwance a Wakina ni kaWai, na kasa bacci saboda tsananin bu?atarta nake, amma na kirata ta ?i zuwa, yanzu ya dace a ce mace ta dinga nisa da Wakin mijinta wai sai sanda ya kira ta?"

Hasana ta daskare da mamaki, sai ta kasa ri?e hawayenta, ashe dama haka Nura yake tona wa aurensu asiri? Kuma ma duk bin ta yake yi da sharri, indai har wacce ta fara yi masa magana yau bai santa ba, bai san inda take ba, zai saki jiki ya dinga tsara mata wannan ?aryar, to ina ga wacce ya saba da ita har ma yake zuwa gidansu? Yanzu haka yake faWawa Ramla ma? Tabbas dole ta raina ta.

Ta share hawaye ta Wauki wayar, sai ta ga ya turo mata stika, tana buWewa ta ga mace ce da namiji rungume da juna suna bacci, ta daure ta rubuta masa"To ko ni Win na zo na taya ka baccin?"

Ya tura mata dariya ya ce"Da gaske ba za ki ji tsorona ba?"

Ta ce"To tsoron me?"

Ya ce"Ai za ki zo ne matsayin mai Webe mini kewa".

Ta ce"Hmm, za ka same ni fiye da matarka, kwatanta mini gidan naka yanzu zan zo".

Ya ce"Ki dai gwada ta waya don na yarda idan kin zo Win za ki iya taSuka abun arzi?i".

Sai ya turo mata wani vedio, tana buWewa, ta yi saurin kifa wayar, ganin blue film ne ?arara, ta dinfa maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!", ta kashe wayar duka ba tare da ta ba shi amsa ba, sai ta samu kanta da fashewa da kuka, ashe irin mijin da take aure kenan?

A daren nan da ?yar bacci ya Wauke ta, da safe har ta makara, sai da ya tashe ta, har da faWansa yana cewa"Wannan wani sabon salon ne kuma salon yara su makara?"

"Ba ni da lafiya ne" Abin da ta ce kenan kawai, wani irin mugun haushinsa take ji, ji take kamar ta kama shi ta sha?e, ta tambaye shi me yasa yake zaune da ita ba zai sake ta ba? Ta je ta kunna wuta, sai dai tunawa da kalmar kidahuma ya sa ta fara hawaye, idan ya tashi wula?ancinsa har jaka yana ce mata, amma a jiya fa wata yake faWawa ita kidahuma ce, tabbas ta san duk wacce zai auro nan gaba ba za ta kalle ta da mutunci ba.

"Kukan me kike yi?" Ya tambaye ta yana yamutsa fuska.

Ta ce"Na ce maka ba ni da lafiya".

Ya ce"To Allah Ya sawa?e, sai ki yi ?o?ari ki dafa shayi, bari na siyo biredi".

Ya fita, ta bi bayansa da kallo, tana tuna wannan ?azamin vedion, wa ya san adadin matan da ya turawa shi? Wa ya san adadin yawansu a wayarsu, lallai wata wayar za ta iya yi wa mutum jagora zuwa jahannama, haka ta dafa shayin, suka karya, ta shirya yara, tana yin komai a sanyaye, yana taSa aljihunsa ya ce"Ga shi ba ni da kuWi da kin tafi asibiti".

Ta ce"Ciwon kai ne, zan sha magani yanzu".

Ya ce"Allah Ya sawa?e ya fice".

Wajen ?arfe goma ta kunna data, ta gan shi online, zuciyarta tana ba ta shawarar ta ajiye layin nan, tun da har ta san wane ne mijinta, ta samu abin da take so, wani Sangare na zuciyar kuw??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a zugata yake yi, a kan ta cigaba don ta gano iya waya abun nashi ya tsaya ko zai yarda su haWu a zahiri? Ta fi yarda da wannan don haka ta yi masa sallama, sai da ma ya duba chart Win baya har farko, sannan ya tuna ta, saboda yawan matan da yake chart da su, ya amsa ya ce"Matsoraciya jiya sai kika gudu ko?"

Ta ce"La ba fa guduwa na yi ba, wayar ce ta mutu, caji ya ?are, ban ma kai ga ganin me ka turo ba".

Ya ce"Kin bar ni da kewarki, har da mafarkinki na yi".

Ta ce"Daga haWuwa?"

Ya ce"Ai haWuwar ce ta yi daWi shiyasa, yau za ki rage mini dar ko?"

Ta ce"Me zai hana? Ni fa da gaske nake, ka ga ni ban saba ta waya ba, a ina za mu haWu?"

Sai ya tura mata dariya ya ce"Kamar gaske".

Ta ce"Tun da ba ka shirya ba shikenan mu bar zancen".

Ya ce"Wai ke ba kya yin voice note?"

Ta ce"Ai ni kurma ce, ba na magana kuma ba na jin komai".

Ya tura stikar dariya ya ce"Ban yarda ba, sai ranar da na ganki a zahiri".

Ta ce"To yaushe zan zo taya ka kwana?"

Ya ce"Yau".

Ta ce"Za kuwa ka gan ni, da gaske fa".

Ya yi dariya.

Ta ce"Zan zo ?arfe sha Waya daidai, saboda haka ka koma gidanka da wuri yau".

Ya ce"Allah Ya kawo ki, zan shirya miki abubuwan mamaki kuwa".

Daga haka ta kashe data, ta tashi ta Wora girki, a ranta tana ayyana tabbas yau Win kuwa za ta je, ta fito masa a mutum, don ya san ta gane bada?alar da yake yi a wayarsa. Da ya zo cin abincin rana ba ta nuna komai ba, sai dai sam ba ta da walwala, da daddare yana dawowa ya gama komai ya shiga Wakinsa, ta kunna data, ta ga sa?onsa ya shigo, yana ce mata"Kyaun al?awari dai a cika, yana jiranta".

Ta ce"Ka tashi ka buWe ?ofa yanzu za ka ji na turo na shigo".

Ya ce"Na buWe".

Ta ce"Ba ka buWe ba, ina kallonka fa, kana kwance a katifa da gajeren wando bulu".

Ya yi ?ar dariya ce"Kuma wallahi kin canka".

Ta ce"Na ce fa ina kallonka, yanzu na ?araso ?ofar Wakin zan ?wan?wasa, ka buWe, amma don Allah ko a yaya ka gan ni kar ka ji tsorona, wallahi ni mai sonka ce".

Ya ce"Kai Suhaila kenan".

Hasana ta buWe ?ofarta a hankali, ta fito, ta fara ?wan?wasa ?ofar Wakin Nura da ?arfi, gabansa ya faWi rass, ya ce"Wane ne?"

Ta tsaya da bugun ta rubuta masa cewar"Ni ce mana, ya kake haka, ko na shigo ta saman Wakin?" Sannan ta cigaba da bugawa.

Nura bai san sanda ya yi wulli da wayar ba, ya fara karanto duk addu'ar da ta zo bakinsa, ya yaye zanin gadon da aka shimfiWa a katifa ya lulluSa, yana ta addu'o'i.


LITTAFIN NAN NA KU?I NE A KAN NAIRA 500 KACAL! ZA KU IYA FARA BIYAN KU?INKU TUN YANZU TA NAN

8028966015
Sadiya Abdulrazak opay bank

Sahaidar biya ta nan
08028966015

*ZUCIYAR MACE*



BY
SADIYA ABDULRAZA?


*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 10


Jin shiru ya sa Hasana ta le?a shi ta windo, nan ta hango shi ya nani?e bango kamar ?adangare, dariya ta zo mata, amma ta daure ta ri?e ta, ta matse murya tare da dakushe ta tamkar ta tsohuwar da ta gaji da duniya ta ce"Kai yaro kai fa ka ce kyaun al?awari a cika, mu ba ma karya al?wari, kai yaro yanzu za mu Wage ka, kai da katifar mun kai ka tsakiyar sansanin karuwan aljanu, zan nuna musu masoyina, a can za mu rage dare na zo maka a matsayin matarka kamar yadda ka ce".

Wani irin hautsinawa kayan cikinsa suka fara yi, ya yi adungure ya diro daga katifar, ya buWe sif Winsa ya shige lokar ?asa yana tsananta addu'arsa.

Hasana ta sake cewa"Sakan Waya na ba ka, ka fito daga sif Win nan idan ba haka ba, zan rufe ta da mukullin gar?am na kakana na goma sha tara, babu wanda ya isa ya buWe sai bayan shekara Wari da saba'in".

Kafin ta rufe baki, sai ga shi ya faWo daga ciki kamar an jefo shi, ya kalli gabas da yamma, ya fashe da kuka yana cewa"Na tuba, wallahi na tuba don Allah ki yi ha?uri?"

Ta ce"Me ka yi kake tuba?"

Ya ce"Ni Wan iska ne wallahi, amma daga yau na daina ba zan ?ara ba".

Ta saki wata muguwar dariya ta ce"Yanzu kana nufin ka ha?ura da rage daren?"

Da sauri ya ce"E wallahi, dama ?arya nake yi, ban san ma yanda ake rage daren ba, ki yafe ni".

Ta ce"Ni sunana Aljana Salsabilatul-silsilatul-sakafilatul-salwaisus, ya na ce sunana?"

Nan Nura ya ruWe ya fara jero baragada, S kawai kake ji tana tashi, ga shi kuma yana kuka".

Hasana ta kasa daurewa ta yi nesa da Wakin, ta yi dariya a ciki-ciki, sannan ta daidaita kanta ta dawo ta sake buga ?ofar, ya zabura, yana ba da ha?uri, ta ce"Yi min shiru, munafukin banza!" Daidai nan kuma ta fara jiyo kukan Aiman.

Ta ce"Ka ci sa'a, yau muna da mitin namu na ?ungiyar karuwai, amma ka sani zan dawo gobe domin mu tattauna game da ?untatawar da kake yi wa matarka, da sharrin da kake yi mata, sannan duk chart Win cikin wayarka ka tabbata ka goge su, ka goge whatsApp Win duka mun haramta maka shi har abada, tun da tarbiyyar yaran mutane kake Satawa".

Ya ce"To zan goge, na ma goge wallahi, ni da charting har abada Kaka".

Ta ce"Kai yaro, bar ganin muryata haka kake ce mini Kaka, ni matashiyar aljana ce, shekaruna Wari uku da ashirin da uku, kawai ina yi maka kalar muryar da kunnenka zai iya Wauka ne".

Ya ce"To na gode, na gode".

Ta ce"Gobe zan dawo mu tattauna, sannan duk wanda ka ba wa labari, to ka tabbata ka furta kalamanka na ?arshe kenan, domin daga ranar zan fansar da harshenka ga saurayina, ba za ka sake magana da bakinka ba. Yanzu ka tashi ka yi ta tsallen kwaWo har sai gari ya waye, idan ka fito kafin kiran sallar asuba, sai dai ka ga kanka a tsakiyar barikin aljanu".

Ta le?a ta windo ta gan shi yana ta tsallen kwaWon har da kama kunnensa kamar a makaranta, ta buga ?ofar Wakin da ?arfi, Nura don tsoro har sai da ya faWi, sannan ya tashi ya cigaba da yi, ta yi wani irin abu da muryarta, sannan ta tafi cikin sanWa ta buWe ?ofar Wakinta, ta shiga, ta hau gadon ta Wauki Aiman, ta fashe da dariya, ashe ita tana da maganin Nura ta tsaya take ta sha?ar takaici? Har ta fara hasashen azabar da za ta ba shi gobe, tabbas sai ta huce takaicinta. Haka ta kwanta bacci ranta fes.

A Sangaren Nura kuwa, ya kai awa biyu yana ta tsallen kwaWo, yana yi yana addu'a, ya gaji matu?a, amma tsoro ya hana shi tsayawa, ?arshe dai da abun ya ishe shi, sai ya yi shahada ya daina yi, ya rarrafa ya kunna kayan kallo, ya nemo tashar da ake yin karatun Qur'ani, ya manta rabon da ya saurari Qur'ani sai yanzu da yake neman tsira, ya zauna yana bin karatun duk da ma bai iya surar ba, a haka har asuba ta yi, bai runtsa ba. Yana jin fitowar Hasana za ta yi alwala, amma tsoro ya hana shi fitowa, ya ce"Hasana!"

Ta amsa tana tahowa Wakin.

Ya ce"Don Allah samo mini buta da roba mai faWi haka, alwala zan yi, ki haWo da fo ma".

Ta ce"Subhanallah! Baban Salim karyewa ka yi ne?"

Ya ce"Dalla idan ba za ki kawo mini ba ki faWa mini!".

Ta ce"A'a ni ba ni da fon da ?ato zai hau, ga dai buta nan" Ta mi?a masa butar hannunta da roba ta fice.

Can dai ya yi shahada ya fito, ya yi alwala ya tafi masallaci, sai da gari ya waye sosai sannan ya dawo, yanzu tsoron Wakin yake ji, wayarsa kuwa bai kula ta ba, sai da suka gama cin abinci, gabansa yana faWuwa ya Wauka, ya goge whatsApp Win duka, ya saka a aljihu ya fita, a kasuwa ma jikinsa duk a sanyeye, haka ya dawo cin abincin rana Hasana tana lura da yanayinsa, da zai fita ya ce"Yau kar ki rufe ?ofar nan, a nan zan kwana".

Ta ce"A nan za ka kwana kuma? Kai kuwa me ya yi zafi?"

Ya Sata rai ya ce"Ban sani ba! Ko ni da gida za ki yi mini iyaka ne?"

Ta ce"A'a, amma dai da mamaki, a ce wai kai da kake kora ta kuma yanzu za ka baro lafiyayyen Wakinka ka zo nawa, gaskiya da wata a ?asa".

Ya yi banza da ita, ya fice.

Ana yin sallar isha'i, Hasana ta gar?ama sakata a ?ofarta, ?arfe takwas sai ga shi ya dawo gidan, gabansa yana ta faWuwa, ya ga abincinsa a ?ofar Wakinsa, ya je ya fara ?wan?wasa Wakin Hasana tare da kiran sunanta, tana ji ta yi banza da shi, ya dinga bugawa, ?arshe har Salim da Amir yake kira, ya ji shiru, sai ya kira ta a waya ta ?i Wagawa, abun duniya ya ishe shi, shi bai taSa jin haushin wannan nauyin baccin nata ba kamar yau, ya zauna a tsakar gida duk da gabaWaya gidan ma tsoro yake ba shi, Hasana ta Wakko wayarta ta rubuta mata sa?o, ta ce"Ko ka tashi ka shiga Wakinka mu tattaunawa ko kuma mu yi sama da ?o?on kanka yanzu".

Sai da gabansa ya faWi da ya ji shigowar sa?on, ai kuwa yana karantawa ya tashi a guje ya nufi Wakin Hasanar yana ta bugawa haWi da addu'a, Hasana da take ta dariya, ta sake rubuta masa"Muna kallonka kana buga Wakin baiwar Allah, nan muka aike ka?"

A guje ya je ya buWe Wakin nasa ya shiga, yana ta addu'a. Ya tsugunna kamar Walibi a gaban Malami, ki mai laifi a gaban jami'an tsaro, ya fara cewa"Don Allah ki yi ha?uri ki yafe ni, wallahi na tuba".

Hasana ta buWe Waki ta fito, karaf a kunnensa, sai kuwa ya daddage yana ?wala mata kira cikin kuka, "Hasana! Hasana don Allah zo ki cece ni".

Maganarsa ta guntse jin an buga ?ofar Wakin da mugun ?arfi, ya yi tsalle ya haye katifa yana "Wa innahu Sulaimanu".

Hasana ta fara irin muryar jiya ta ce"Wato matar taka da kake cuta ita za ta zo ta cece ka ko? To fitsari ta fito, kuma mun juya mata ?wa?walwarta mun mai da ita Waki, sai kuma wa za ka kira?"

Da sauri ya ce"Babu, wallahi babu wanda zan kira".

Ta ce"Me yasa kake chart Win banza da ?a?an mutane?"

Ya ce"?addara ce, amma na daina wallahi, har abada".

Ta ce"Mun gama da wannan shafin, to me yasa kake ?untatawa matarka? Kake zaginta idan ka je zance wajen ?an'matanka?"

Ya ce"Babu komai wallahi, na daina".

Ta ce"Bayan ?ungiyar karuwan aljanu, ina cikin ?ungiyar masu ladabta bil-adaman da suke ?untatawa matansu, saboda haka zan Wauke ka na kai ka can ofishinmu na aljanu masu kare ha??in matan bil-adama! A tarihin sama da shekara dubu, babu bil-adaman da ya shiga ofishinmu ya fito da rai"

Cikin tashin hankali Nura ya fara"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Don girman Allah ku yi ha?uri, wallahi na daina, daga yau ba zan sake yi mata komai ba, zancen ma na daina zuwa".

Ta yi wata dariya ta ce"Muna sane da abubuwan da kake yi mata, ba ka ba ta kayan kwalliya, amma kana ba wa matan waje, kwanaki ta tambaye ka me kake so ta dinga yi don ku zauna lafiya, ka ?i faWa mata, ta ce ka ba ta kuWi ta sayi ?ananun kaya nan ma ka ?i, haka kawai sai ka fara yi mata masifa, sannan kuma ba ka ba ta Wan kuWin kashewa, kuma duk ba?in da ta yi sai ka ce kana son su, hakane? Ka raba Waki, ka hana ta dinga biyoka"

Da sauri ya ce"Hakane, hakane wallahi wannnan duk halina ne, amma na tuba yanzu".

Ta ce"Sannan sai ka yi wata ba ka kira ta ba, to idan ba ka bu?atar mace mu za mu turo maka aljana shafumuleratu, ta shafeka".

Da sauri

7 / 41