Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Complete Novels
ido dan jiyo sautin sheshshek'ar kukan da takeyi k'asa-k'asa sannan yana jin sautin marin da ya tabbatar mishi Abba ne keyi mata shi.
Shiru ya tsaya a wurin sai jikin shi dake rawa lips inshi ya kamo ya cija ta ciki lokaci d'aya
ida nunshi sukayi jazir gaba d'aya jijiyan dake goshinsa ya taso sama,
ya kasa yin gaba ya kasa yin baya
sai Zahra dake kan kafad'arsa ya k'ara tallab'e kanta,
yana tsaye a wurin har Abban ya fito yana tafe kamar zai bugi babu fuskarnan a murtuk'e, yana ficewa shiko ya nufi part din Maman.
A parlour ya sameta zaune bisa kujera ta kife kanta kan cinyoyinta tana kuka mai cike da cin rai,
da sauri ya kontar da Zahra kan 2 str,
idon shi cike da k'ollah ya durk'usa gabanta sannan yasa hannun shi kan guiwowinta cikin cushewar murya yace.
"Mama yauma dukanki Abba yayi ko?
Mama me kikayi mishi? ."
Da sauri ta d'ago kanta dan bata san da shigowarshi ba hannu tasa ta share hawayen ta ajiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Kai Yusuf duka kuma?."
"Eh mana Mama inba haka ba meya saki kuka?".
kauda fuska tayi cikin son b'oye abinda yaron nasu ke son ganowa tace.
"Har yaushe zanci gaba da cema Miji baya dukan matarsa, domin hakan ba halin mutanen k'warai dana kirki bane,
Abban ka kuma kai shaidane mutun ne managarci mai daraja da mutunci ko mak'otanshi da mutanen gari zasuyi shaidar dottakun sa da mutuncinsa,
a kullum ina shaida ma ni Abban ka bai tab'a koda muntsili na ba,
Kukan da kaga inayi,
rasuwa akayi mana, shine daya gaya min na kasa tsaida hawaye na."
girgiza kai yayi cikin rashin gamsuwa da zancen mahaifiyar tashi
ya dad'e da sanin boyemai laifin mahaifinshi takeyi,
a fili kuma sai tsura mata ido yayi yana kallon fuskarta da tayi jazir alamun marukan da aka yayyarfa mata,
idon shi ya rumtse da k'arfi cikin rawan murya yace.
"Kiyi hak'uri Mama komai yayi tsanani zaiyi sauk'i komai yanada iyaka watarana sai labari,
insha Allah Mama zakibar kukan wannan rasuwan da akeyi miki lokuta da dama duk da bansan wad'anda suke rasuwan ba,
amman kiyi hak'uri domin Mahak'urci mawadaci."
hannu yasa ya share mata hawayen nata cikin sauk'e numfashi mai nauyi yace.
"Mama insha Allah hawayenki zasubar zuba zan saki dariya a madadin wannan kukan, zan cire k'unci a ranki zan samar miki farin ciki."
Murmushi tayi cikin jin sanyi a ranta kanshi ta dafa tare da cewa.
"Allah yayima Al'barka Allah ya shirya minkai shiryar musulunci Allah ya tsaremin imanin ka da gabban ka."
"Amin Amin Maman Yusuf."
Murmushi sukayi dukan su dan jin yadda ya wanice Maman Yusuf kamar wanine Yusuf d'in ba shiba,
daga nan sukaci gaba da hirarsu sannan ta hadamai tea yana sha suna hira,
duk da shi kam Yusuf gaba d'aya ranshi cike yake da k'una da k'uncin yadda mahaifinshi ya maida mahaifiyarshi abin huce haushinsa,
ko a woje aka bata mai rai sai yazo gida ya huce haushin sa a kanta,
da kyer ya d'an sha tea d'in sannan ya fice ya koma d'akin su.
Kan gado ya konta tare da rumtse ida nunshi,
a hankali ya nisa cikin tunanin yanayin tsari da tarbiyar gidan nasu......!
*By*
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*HUKUNCIN ALLAH*
Page 3⃣
*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Free page
*Asalin zuriyar su Yusuf*
*M*arigayi Malam Usman shine kakan su Yusuf,
maifin uba gasu Yusuf da Zahra,
Malam Usman Asalin haifeffen garin Adamawa ne acikin yankin Girei shi asalin bafula tanin Girei ne,
wanda ba sai anyi bayanin kyawun su ba,
domin duk wanda yasan fulanin Girei to tabbas yasan kyawawan fulanine masu cikar haiba bugu da k'ari Fulani ne masu fafatawa wurin neman ilimin Arabic da boko shiyasa sunkayi fice da zarrah a cikin jihar Adamawa.
Malam Usman shine babba a gidan su yana da k'annen shi 2 duk mata ne sai shine namiji
k'anwar shi mai binshi sunan ta Fatima Zahra irin matan nanne masu rakad'i da baki ga tsiwa kuma bata barin ta kwana,
sai mai binta itako Amina mace mai sanyi da al'kunya,
duk sunyi aure suna d'akunan su da 'yayen su da jikokin su.
Shiko Malam Usman a cikin Girei gidan shi yake inda Allah ya azurtashi da yara shida,
tare da matarsa Hajja Inna,
a cikin yaran nasu kuwa biyu ne rak maza duk saura hud'un mata ne,
Allah ya al'barkaci y'ayanshin da haihuwa mai yawa,
hakan yasa zuriyar tayi yad'o da al'ummah tsakanin 'yaya da jikoki da 'yayan jikoki duk cikin Adamawa Yola ko wanne sak'o da lungu akwai zuriyar Malam Usman,
d'anshi na fari namiji ne,
Al'k'ali Muhammad Usman Girei (Abba kenan mahaifin Yusuf da Zulaihat) sai Aisha, Fatima, Maimuna, sai Doctor Aliyu Usman Girei (Daddy kenan mahaifin Zahra) sai autarsu Madina,
Duk yaran shi matan nan sunyi aure suna d'akunan su da 'yayayen su da Jikokin su,
Mazan kuwa suma duk sunyi aure Abba da Daddy suna cikin gidan mahaifin nasu inda ya zama Babban Family house nasu ya zama jigon duk wani farin cikin zuriyar tasu matansu kuwa Alhamdulillah suna zaman lafiya Arzik'i kuwa Alhamdulillah sunada rufin asiri.
Malam Muhammad Abba kenan shi 'yar k'anwar Malam Usman aka Aura mai,
'yar Goggon shi kenan, wacce yara ke kiranta da Mama
ikon Allah Abba da Mama suko yara biyu rak Allah ya basu,
Zulaihat sai Yusuf wanda yanzu haka shekarun Yusuf 17 years
kuma bayan an haifi Yusuf da wata 9 Allah yayiwa kakanshi Malam Usman rasuwa,
ya rege sai Innarsu kawai,
Abba babban mutun ne mai kima da daraja a idon Al'ummah domin ya kasan ce mutun managarci mai halin gwarai,
shi babban *Al'k'aline a babban kotun musulunci dake cikin Yola mai suna HUKUNCIN ALLAH CORT*
duk halin nagarta Abba yana dashi,
sai dai cach ya kasance mai saurin hannu akan matarsa kuma k'anwarsa d'iyar Goggon shi,
sam zaman nasu abun takaici ne,
domin ya sawa kanshi d'abi'a da al'adar dukan mace,
duk k'ank'antar laifi sai ya ware yatsunshi ya yayyarfa mata maruka da ruwan masifa,
wannan abu shine babban abunda ke ciwa Yusuf tuwo a gwarai,
duk da Mama nab'oye mai abinda Abban nashi ke keyi amman yana ganewa,
yakan je gidan yayarshi Zulaihat su koka tare,
toh wannan d'abi'a ta Abba tasa Yusuf ya taso da wani irin murd'ed'd'en hali da miskilanci ko yaushe fuskarsa ba fara'a,
koda ko yayi fara'ar Abban shi ke kauda farin cikin nashi da dukan mahaifiyar tashi.
Dr Aliyu Usman Girei kuwa matan shi biyu uwar gida Ummi sai Amariya Aunty,
Ummi nada yara 5 sai Aunty yaranta 3,
Ibrahim sai Mami sai Zahra,
wacce takwarace ga Goggon mahaifinta Fatima Zahra k'anwar Malam Usman Kenan, yanzu haka Zahra yar 7 years ne going to 8
Zahra kam kab ta kwaso halin tokwararta harda k'ari,
yarin 'yar k'arama amman Al'amarinta ya girmama,
duk wani irin neman tsokana da rigima Zahra ta iyashi ga tsiwa da rashin ta ido ga kaud'i da rakad'i
ko yaushe kaganta tana cikin gudu,
tsabar guje-guje har ya zama ko yaushe dunduniyar k'afarta yana d'ane a sama,
bata tsoron kowa
ga son rawa kamar mazari,
Zahra ba bak'a bace kuma ba mummuna bace amman kasan cewar kab zuruyarsu kyawawan mutanene farare k'al-k'al ne ,
sai ake ganin Zahra bak'ace dan farinta bai kai na 'yan uwanta ba kuma kyawunta bai kai nasuba,
Yusuf kuwa duk ya fisu kyau,
kuma shine wanda Zahra ke tsoro,
dan Anuty kam sam bata damu da lura da yanayin d'iyar tataba,
Ummi Kuwa uwar gidan Antyn Babbar yarta mace ce,
Amira sai Sulaiman sai Jafar sai Nana da Auta Zeenat,
Suleiman da Yusuf sa'anni ne kuma sune manya a mazan Amira ce kawai ta fisu.
Rayuwar gidan abun shawa'a ne domin gida ne,
na mu samman zama suke cikin aminci da fahimtar juna,
duk da tsaurin hali da ra'ayi irin na Abba k'annenshi na girmamashi suna bin umurnin shi,
baya fad'a su musa bare suk'i bin dokarsa,
kan komai in ya yanke hukunci to dolene ma kawai subi maganarsa,
musamman Daddy da yake kallon shi tamkar mahaifinsu.
Aunty Amarya kuwa mahaifiyar Zahra macece mai son yara da sauk'in mu'amala kab yaran gidan d'akin ta suke tarewa,
ita da Yusuf kuwa tamkar ya da k'ani suke,
bata da yarjejjen d'an aike kamar Yusuf komai shi yake mata duk aikenta shi yake zuwa mata,
hakan yasa kab degginta sun san Yusuf,
Mamar ta kuwa tamkar jikokin ta su Zahra take kallon Yusuf.
In an aikeshi yaje gidan su Aunty kuwa yana ganin gata da so a gun Tatti mamar Anty da Uncle Gambo da Uncle Sani,
Gambo shine babba a kan Aunty,
Sani kuwa k'anin tane,
Baban su baya raye komai na duniya Gombo keyi musu duk da k'aramin k'arfi gareshi,
ga fama da karatun Sani,
gidan nasu yana cikin Girein suna lallab'a rayuwarsu a hankali,
duk da talaucin su ba'a fiye ganewa sabida tsananin tsaftar da Tatti keda shi.
***********
Yana cikin wannan dogon nazarin da tunanin yaji Muryar Daddy yana cewa.
"Yusuf bacci kakeyi ne?."
da sauri ya diro daga kan gadon, gamida murza idanunshi da sukayi jazir,
da sauri ya fito,
cikin girmamawa yace.
"Na'am Daddy gani."
ido ya d'an zuba mai tare da nazartan yanayin shi,
sai kuma ya matso kusa dashi goshin sa ya d'an dafa tare da cewa.
"Baka da lafiya ne?."
Kai ya gyada'a mai alamar a,a,
"ka tabbatar lafiyar ka lau?. "
"Eh Daddy bacci nakeyi shiyasa."
Juyawa yayi yana taka step d'in sauk'a tare da cemi shi.
"Ka kira Sulaiman kuzo k'ofar gida, akwai aikin masallaci,
zaku firfitar da carpet d'in masallacin,
za'asa tayis da kuma yin fenti."
biyo bayan shi yayi tare da cewa.
"Toh Daddy, bari inje in fara,
kafin Sulaiman ya dawo ya tafi kaiwa su Mami Abinci".
Tare suka fito sannan suka nufi cikin masallacin,
Manyan Dottab'an unguwar suna tsaye a gefe,
suko 'yan matasan kamarsu Yusuf dama wadanda suka fisu da wadanda basu kaisu ba sunata fito da abubuwan cikin massalanci,
ganin duk wurin ya hargitse yasa Abba yace suje su shimfida taburman da carpet din a dai-dai bakin gate d'in gidan nasu in yaso ayi sallan yau da goben a wurin kafin a gama gyaran,
haka kuwa akayi Yusuf da Abokin shi Aryan da sauran mutanen sune suka gama kimtsa wurin sannan suka kafa rumfar kanofi a wurin,
suna gamawa azahar nayi,
anan sukayi sallan cikin jam'i.
Gabanin magrib,
kamar yadda ta saba,
ta faki idon su Mama dake tsakiyar gidan cikin rawa-rawa tsalle-tsalle ta fice,
a guje ta nufi shagon Idi inda ya saki kid'a kamar ba kiraye-kirayen sallan magrib aka farayi ba,
tana zuwa ta fara rawa tana.
" Idi a bani sweet."
jawota yayi cikin yin tsilli-tsilli da ido ya d'orata kan cinyarshi ya rink'a lallatsa cinyoyinta yana magana k'asa-k'asa.
"Fatima Zahra bintu sai na more kud'in sweet na fa,
domin adashe nake zubawa,
dole wata rana na kwashi gara."
ita ko sai dariya take tana tsalle kan cinyoyin shi
shiko sai k'ara mimmik'e k'afa yakeyi yana shafa fuskarta,
a gida kuwa duk abinda suke Yusuf na ganin su da yake a saman yake yana al'wala a 'yar barandar dake fuskantar shagon Idin,
sauri-sauri yayi al'wala,
ya fito kai tsaye bakin shagon ya nufa,
yana zuwa ya zaro igiyan charge ya fara shaud'a mata shi a cinyoyin ta,
da gudu ta sauk'a,
a guje ta nufi gida shiko yana binta a baya,
har cikin gida ya rakata sai ihu take da tsalle,
kan Mama ta fad'a,
tana kare cinyoyin nata,
cikin zaro ido yace.
"Wallahi in kika kuma fita sai na kumbura miki jiki."
sannan ya kalli Aunty cikin murtuk'e fuska yace.
"Allah ko Aunty wallahi zan gayawa Daddy irin goyawa Zahra baya da kikeyi,
kuma zan kai k'aran Idi gun Daddy da Abba insha Allah zai bar kan titin nan,
duk ya meda mana unguwa gurin kid'e-kid'e da tara 'yan iska."
Dariya tayi cikin rashin kulawa,
ganin hakan yasashi ficewa yana ta fad'a,
itako Zahra sai kuka take.
yana fita ana tada ik'ama,
suka fara sallan magrib.
itako Zahra a cikin gida yana fita ta fara tsallenta
tana ganin duk su Mama sunyi cikin d'akunan su dan yin sallan,
maza ta ruga a guje sai k'ofar gida,
tana bud'e gate d'in zata fita,
taga taron mutane anyi layi duk sunyi sujadda,
gaban Liman tazo har kamar zata wuce,
sai ta kuma juyowa, kawai sai ta d'aga k'afarta ta d'aura kan......!
*By*
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*HUKUNCIN ALLAH*
Page 4⃣
*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Hannunshi ta taka mashi yatsun hanunshi,
bai kulaba yaci gaba da ibadarshi,
saida suka taso,
bayan sunyi sallama,
ya juyo gefen shi kad'an dan ganin wanda ya takashin,
cikin mamaki ya zaro wayar shi tare da haska fuskar ta,
wik'i-wik'i tayi da ido tana murmushi,
ta wani a zauna a gefenshi,
a dole itama sallah takeyi,
sai wani motsa baki take tana.
"wisih-wisih."
kai Kawai ya jinjina tare da yi mata addu'ar shirya a zuciyar shi,
itako tana ganin duk an mimmik'e sai gyara zama tayi,
Yayan ta Sulaiman ne ya haggota har zai fice sai kuma ya yafitota tare da cewa.
"Taho mu tafi gida."
kai ta juya mai tare da cewa.
"Ban gamaba yaya Culaiman."
sanin halinta ba tsoron shi take ba yasashi komawa gefen Yusuf dake karatun azkar yace.
"Yusuf ga can Zahra kusa da liman,
na kirata tak'i,
dan Allah korata gida."
shafa addu'an yayi tare da mik'ewa ya nufu inda take ta dungura goshi a kasa,
ta d'ago kenan ta hangoshi yayi kanta da sauri ta mik'e tare da had'a tafin hannunta tana kad'ewa,
kai ta karya cikin tsoro tace.
"Hamma Yucuf a gama salla an tafi gida yanzu."
Tsuke fuska yayi tare da watsa mata mugun kallo,
da gudu ta fece sai gida.
Tana shiga cikin gidan kuma,
da tsalle tayi parlour Ummee,
ba kowa a ciki sai Zeenat
itako Umme tana salla a cikin bedroom,
gaban Zeenat ta tsaya tare dasa hannu ta fizge bobon dake hannunta sannan ta fice ta nufi d'akin Mama,
k'ara Zeenat ta saki tare da binta a bayan ta,
Itako tana zuwa d'akin ta b'uya ta zuk'e bobon sannan ta fito,
tana dariya da tsalle tare da kama hannun Zeenat suka nufi d'akin Ummi,
suna shiga Ummi ta kamo y'arta tare da cewa.
"Zeenat waya tab'aki?. "
Da sauri Zahra tayi tsagal tare da cewa.
"Ummi ni na k'wace boron inta kuma na shaye."
ta k'arishe maganar tana bud'e baki tare da kad'a harshenta,
da sauri Ummi tasa hannu zata kamota,
aiko tuni ta fece a guje tana dariya,
ita kam Ummi shiru tayi tana mamakin hali irin na Zahra wato sam ita bata b'oye laifinta ko wani yayi b'arna in ana cekiyar waye b'ata abu kaza,
sai tayi tsagal tace itace,
bare kuma in itace tayi laifin,
to sai ma tayi bayanin yadda tayi shi,
kai ta juya tare da cewa.
"Allah ya shirya mana ku."
Ita ko Hajia tsagal tana fita d'akin Ummi parlour Auntyn ta nufa
inda ta tadda Auntyn nata da su Yusuf da Sulaiman sai Mami da su Nana
tana shiga duk suka juyo kanta dan yanzu zata iya sa su Mami da Nana kuka,
itako ganin Yusuf na wurin sai ta rab'e gefen Auntyn ta
ta zauna shiru ta nitsu kamar shinkafar walima,
ganin bata kula kowaba yasa sukaci gaba da hirarsu,
can Yusuf ya kalli Mami tare da cewa.
"Mami karb'o min ayon a gun Mama."
shiru Mami uwar mannin hauka tayi kamar bata jishiba,
itako Zahra da tsallenta ta mik'e tare da cewa.
"Hamma Yucut ni an karb'o maka."
Harararta yayi yace.
"Tafi daga nan mara kunya ke me kika iya in banda fitsara."
jawota Aunty tayi cikin dariya tace.
"Ayyah Tinana ke dai komai kikayi sai anga laifinki."
sai kuma ta juyo ta kalli Yusuf d'in tare da cewa.
"Wallahi kai kanka kasan kab yaran gidan nan ba mai son aike kamar Zahra ita bata k'in aike ko kad'an,
Mami da Nana da kuke son sune iyayen k'iwuya da mannin hauka."
ido ya zarowa Mami tare da buga mata tsawa.
"Maza tashi ki karb'o min banza uwar mannin hauka."
simi-simi ta mik'e taje ta karb'o mashi,
tana kawo mai ya karb'a zai fara gugar kenan akayi kiran sallan ishah,
jin kiran sallan yasa suka fice shida Sulaiman.
Bayan an idar da salla,
suka shigo gida parlour Aunty suka shiga tare da abo kinshi Aryan da Sulaiman d'in
suna shiga suka samu tuni Zahra ta b'ingire tayi bacci sai numfashi take sauk'ewa,
Murmushi Aryan yayi tare da cewa.
"Aunty har Goggon Daddy tayi bacci kenan?."
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ba doleba,
sam bata da hutu sai dere asuban fari Idi zai tayar da ita da kid'e-kid'en shin nan,
gashi ita ba kasafai take baccin rana ba ga gajiyan dukan da Yusuf ke mata."
Tab'e baki Yusuf yayi sannan ya fara gugan yana cewa.
"In sha Allah next week zan canza mata school in taga dama tayi ta kuka har ta fashe, kuma na Arabic da bokone ga hadda ba k'ak'k'autawa zan kaita inda zata wuni tun safe sai shida na yamma,
wala Allah in taga ita d'aya ne ba yayunta ta rege masifa da dukan 'yayan mutane,
amman zata bar zaman banzan nan kam da kwad'ayin tsiya."
Sulaiman ne yayi dariya cikin jin dad'in shawarar Yusuf yace.
"wallahi kuwa irin makarantar ce kawai maganin ta."
itako Aunty ido ta zuba musu tana musu kallon, to mugaye,
cikin dariya Aryan yace.
"Ni kam Anty aji nawa Zahra take ne?."
cikin dariya tace.
"Kaga Aryan k'yalesu mugun baki suke mata,
kuma in sha Allah shekarar da zasu gama digiri d'insu na forko a shekarar zatayi candy."
tsaki Yusuf yaja tare da cewa.
"A