Advertisements
Chapter 7 Reading Hukuncin Allah Book 1 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Hukuncin Allah Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 46

18K to 21K   out of 136.1K words

tasa hannun ta tsinci sweets d'in,
cikin son jan ra'ayin yarinyar yace.
"Zahra yan mata ki rink'a zuwa d'akina zan rink'a baki minti."
kafad'a ta mak'e tare da cewa.
"Bazan zoba Hamma Yusuf yace kai tsohon Najadu ne". tana fad'in haka ta juya ta tafi tana shan sweet d'in tare da cewa.
"Gobema zanzo in karb'a".
har ya bud'i baki zai kira wota sai kuma yayi shiru sabida hango,
yarinyar da take kawowa mishi tallan zogale ce ta iso wurin, saida ta duba gabas da yamma kudu da arewa bataga kowa ba sai tayi wuf ta fada gidan, Baba mai gadi ne ya washe jajayen hakwaran sa yace.
"Inno kece a tafe".
saida tayi fari da idanuwanta tace.
"iyi nice kaga muyi maza-maza kayi ka gama ka bani kudina na tafi kaga innar mu harta fara ganewa, tace ina nake kai zogale ina fita bana dadewa na dawo mata da kudin nace na siyar".
bakin shi ya kara washewa hadi da mikewa yana kunce tazugen wando,
dama Inno tuni ta dade da shigewa dakin nanya mara mata baya anan suka fara shed'ancin su.



Dan dazon yara ne da suke buga kwallo a bakin titin, suna bugawa ball d'in ya fad'o gidan kai tsaye suka shiga dauko ball din tasu da yake baba mai gadi har mangwaro yake tsinkowa ya raba musu, dan haka kai tsaye dakin shi suka tafi suna "Baba Ball dinmu ta fad'o munxo dauka".
ganin Baba turmi da tab'arya shida Inno ai sai suka saka ihu Baba mai gadi kuwa zabura yayi ya daga Inno yana kokarin maida tazugen shi.



Yara kuwa yadda suka fita da ihu shiya janyo hankalin samarin dake zaune akan wani dandamali tambayar su sukayi meya faru nan sukace Baba mai gadi suka gani yana yiwa wata yarinya wani abu ai a 100 suka shiga gidan Baba mai gadi da fitowarshi kenan daga dakin shi jikin shi sai rawa yake ganin gungun samari sun shigo a guje yayi ainahin cikin gidan senator wasu samarinne suka mara mishi baya wasu kuma sukayi cikin dakin shi wadanda suka shiga dakin nashi Inno suka gani a rakube jikinta sai rawa yake wasu ne suka fara dukanta inda wasu sukace su kyaleta aje a kamo Baba mai gadi a hadasu a mikawa hukuma.




Tofa akace ana wata ga wata wani babban tashin hankalin lokacin da Baba mai gadi yayi cikin gidan samarinnan suka mara mishi baya ai sai sukayi turus tarar da senator da wani matashin saurayi suna aikata masha'a a parlour tsirara haihuwar uwarsu (wa'iyazu billah) ai nan samarinnan sukayi kansu da duka baji ba gani ai jin duka shiya dawo da senator da saurayinnan daga duniyar shed'ancin da suka lula ihu suka fara da kokarin kwace kansu da gudu saurayin da senator sukayi daki suka saka sakata inda samarin suka mara musu baya sai dukan k'ofar suke suna saisun ballah, baba mai gadi ganin haka ya sulale da niyyar guduwa yana fita samarin dake waje suka cafke shi suka turashi dakinsa suka hada da inno suka kulle.



Senator na shiga daki yayi hanzarin daukar wayarshi ya kira commissioner of police yace ya turo mishi yan sanda matasa sun shigo har gidansa sun tayar mishi da hatsaniya.



Matasan nanne na cikin gidan suka fito suka bawa na waje labari nanfa wasu sukace kawai a kona gidan wasu sukace su kira hukuma cikin tsananin zafin rai da bak'in ciki Yusuf yace.
"Haba kamar bakusan hukuncin Nigeria ba ai yanxu ana kiran yan sanda ayau za'a sakesu ba zasu kai gobe ba kawai mu kona gidan komai zai faru sai dai ya faru, mu dai munsan mun rege mugun iri!".
da wannan shawarar suka fita wasu suka tsaya jira wasu suka tafi siyo fetir.



Dawowar samarin yayi dai-dai da isowar yan sanda ganin abinda samarin suke shirin yi da hanzari yan sandan suka tare gidan suka koro na ciki ganin da gaske samarin keson kona gidan senator sai suka sakar musu tiyagas har kofar part din senator yan sanda suka kai mota senator da saurayin nan suka fito suka shiga motar yan sanda suka hada da Baba mai gadi da yarinyar suka fita dasu ganin haka samarin da duk da tiyagas din da ake buga musu baisa sun gudu ba suka marawa motar baya da tofin Allah tsine.



Koda Yusuf ya dawo gida ji yake kamar ya mutu dan takaici da ba'a hadu an k'ona gidan ba an rage mugun iri, partrool aka saka a unguwar su Yusuf na kwana 3 babu shiga babu fita zuwa tsakankaninnan senator ya gama tattara inashi-inashi yabar garin. (Ya ubangiji dan girmanka dan zatinka ka kawo mana dauki da sauki a cikin al'ummar mu da kasar mu Nigeria me kudi zai iya komai ya kwana lfy ya taka wanda yaga dama ya cuci wanda yaga dama amma ba za'a iya kwatarwa wanda aka zalunta ba saboda ana ganin wannan mutumin mai fada ajine a gari Allah ya kyauta).



Tun faruwar abinnan senator bai k'ara dawowa gidanshi ba saboda tabbas yasan duk randa yazo sai dai uwarshi ta haifi wani dan labarin ya gama karade ADAMAWA gaba daya.

***********


A sannu tafiyar su Yusuf ke gabatowa dan baifi saura wata 1 ba inda harsun kammala Neco dinsu inda dama tuni sun zana jamb.


Bayan an idar da sallan asuba Abba, Daddy, Sulaiman, Yusuf, Ibrahim, Sadik, suka shigo gida kai tsaya suka nufi parlour Hajja Inna dan ak'adar su Abba kenan, suna dawowa sallan asuba sai sun shiga sun duba lfyar mahaifiyarsu,
zaune suka sameta bisa sallaya, cikin tsananin so da kulawa Abba ya zauna gabanta tare da karb'ar maganin dake hannunta tare da fara shafa mata, cikin tsananin kula da lalla fatar, shafa mata maganin yake kamar yana tsoron fameta.
"Sannu Hajja ya k'afafun naki?."

"Alhamdulillah da sauk'i. "

"Da sauk'i sosai ko, in fa kina jin ciwo duk k'ank'antarsa ki gaya mana. "

Daddy ne ya katsesu tare da cewa.
"Abba yadda kake shafa mata maganin namfa baiyiba so ake a murza maganin da kyau."

"A a haka ma yayi in an murza ai sai taji zafi."
sulaiman ne yayi dariya tare da cewa.
"Kai Abba kana ji da wannan tsohuwar ji yadda kake lalla b'ata kamar k'wai".

"ai tafi k'waima wannan".
Yusuf ya fad'a tare da ficewa, ya nufi part d'in mamanshi ya gaidata daga nan yaje part d'in Anty Amarya suka gaisa sannan ya tada Zahra daga baccin da take tana mak'ale da babynta saida tayi salla sannan ya fita.

A parlour Hajja inna kuwa Abba da kanshi ya had'a mad'a tea tasha, sanna Daddy ya bata maganinta tasha, hira suka yi sosai har gari ya k'ara washewa sannan suka fita kowa yayi part d'inshi, ita kuwa Hajja inna sai samusu albarka takeyi, suna tafiya matansu kuma duk suka zo suka gaidata.


***

Ranar wata Jumma'a da yamma,
Zulaihat ce zaune a parlour sai gurzar kuka take fuskarta duk a kumbure saboda dukan da Garzali ya samu dama ya lakad'a mata Mama sai fada take tamkar ta ari baki yau kome za'ayi sai anje an musu tsakani da Zulaihat da Garzali ko itama tayi hayar yan daba suje su daddatsa shi.
cikin takaici tace taje tayi wanka ta kwanta ta huta shigewarta kenan Abba ya dawo bayan Mama tayi masa sannu da zuwa ya shiga daki binsa tayi kayansa ya rage ta kai mishi abinci yaci saida ya koshi take fada mishi abinda ya faru.

A take Abba yace "Tom da izinin wa ta dawo gida".
cikin jin haushi Mama tace "Bangane da izinin wa ta dawo gida ba, ko so kakeyi ta tsaya ya kashemin yar tawa kodan bakai ka haifa min ita ba bakasan zafin nak'uda ba shiyasa".
abinda Mama bata sani ba yau Abba a sama ya shigo saboda shari'ar da yayi yau k'iri-k'iri ga gaskiya akasa ya murdeta dan d'an wani babba ne a kasar nan yayiwa wata yarinya fyade amma daga sama aka turo akace ya kori shari'ar tom da wannan bakin cikin ya dawo gida, toh kuma sai ga Mama tana farfad'a masa maganganu cikin zafin Zuciya dan zamu iya cewa a gurinshi Yusuf ya gado zafin rai, cikin fushi yace.
"Ni kike fadawa wadannan maganganun?".
Mama itama cikin zafi tace "Eh inba haka ba koso kakeyi ace naje na dauko gawar ta". zabura yayi da niyyar kai mata duka da gudu Mama ta tashi hadi dayin kara zata fita da tsautsayi ashe ruwa ya zube akan tile sai kafarta ta zame cikin kid'ima Abba yakai hannu zai tarota amma ina tsautsayi ya riga fata tuni takai k'asa ta gaba ta buga goshi hannunta da takai da nufin ta dogara kuma ta gurde shi a take ya goce kara ta saki had'i da sakin kuka saurin durgusawa Abba yayi danya taimaka mata amma sai tayi saurin janye jikinta bataso ya tab'ata tuni goshinta harya kumbura.



Rigarshi ya saka da sauri ya fita a masallaci ya samo mai gyaran targade saida yayi da gaske Mama ta yadda aka gyara mata gocewar kashin da tayi.



Abba na fita da mai gyaran targad'e Yusuf kuwa daya dauko Zarah daga makaranta suka iso bakin gate d'in da sauri Zahra ta sauka akan machine d'inparking yayi yabi bayanta,
a gajiye ya karasa shiga part d'in nasu, cikin jin wani irin yanayi, ya shiga parlour Mama bakinshi d'auke da sallama,
ganin goshin Mama a kumbure ga dauri a hannunta cikin tashin hankali ya karasa inda take yana.
"Lafiya Mama meya sameki?".
hawayen idonta ta share ganin yadda d'an nata ya shiga tashin hankali a zabure ya mike idonshi harya fara zubda hawaye murya na rawa cikin tsananin zafin zuciya da kuna yace.
"Nasan meya faru basai kin fad'amin ba, kuma wallahi yau sai na rama miki,".
juyawa yayi ya fice a guje jikinshi sai rawa yake kai tsaye part din Hajja Inna ya nufa Hajja Inna dake zaune akan carpet tanajin radio sai gani tayi Yusuf ya shigo yayo kanta gadan-gadan jikinshi sai rawa yake idonshi yayi jajawur da mamaki Hajja Inna ke tambayar Yusuf.
"Lafiya meya faru?" ai bai saurareta ba illah kokarin cire belt da yakeyi, ido ta zuba mishi cikin mamaki, shi kuwa yana gama zaro belt d'in, cikin zafin rai da iya k'arfinshi ya rink'a tsu..................!



*BY*
*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣0⃣

*NA*

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*WANNAN SHAFIN GABA D'AYANSHI NA SAUDAKAR DASHINE GA DIJA CHIROMA ZAHRA DA YUSUF SUNCE A GAYA MIKI SUMA SUNA SONKI KAMAR YADDA KIKE SONKU, KI BAWA YAN TEAM SIR MOLY HARAFI GOMA-GOMA SABIDA YADDA SUKA NUWA SIR MOLY NAMU SO MUSAMMAN MOM SAYYID&NOOR ITA BATA HARUFA NOGAS DON TAFI KOWA SONSHI, HAUWA A USMAN MAI RASHIN SANI MASOYAN SIR MOLY SUNA YI MIKI FATAN ALKHAIRI*

FREE PAGE


```Hukuncin Allah Fans 2 sabida ku ne nayi posting da sanyin safiya dan naga haqurinku Hukuncin Allah fans 1 rakine garesu 😆shiyasama bazanma tura musuba sai dai su tsinceshi a gefe, ohoho su Sakina Yasir har an cillo min harara, kalli Kubura Sani yadda ta zumb'uro bakinta 😜 Amina lawan harda k'ollah to share hawayenki zan turo muku yanzu, sai daifa yaseen ni ba ruwana in Yusuf ya targad'a tsohuwa```



*Ga masu buk'atar sayan littafin hukuncin Allah zaku turo katin MTN na d'ari biyu kacal, ta wannan layin 09097853276, ko kuma ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, tabbatar ka/kin turo shaidar kin biya ta hanyar yin screenshort sannan in saki a group.Dan Allah masu yi min transfer ta layin etisalat kuyi hak'uri ku bari, katin Mtn zaku turo bana etisalat ba. Sai masu kira dan Allah kuyi hak'uri ku dena kira domin bani iya amsa yawan kiran da nake fuskanta, dama Sadik namiji one ya b'atamin layi ya badashi wa fans shiyasa bani da hutu ko yaushe amsa kira still ga kuma wadanda suketa son samun number sai yanzu suka samu dama shiyasa kiraye-kirayen yayi yawa,yafi k'arfin amsawata, gwara kimin mgn ta what's app zamufi fahimtar juna, sai kuma kunyi hak'uri dani especially fans d'ina na facebook kuyi hak'uri dan Allah da rashin ganin amsata, Wlh ni dai haka nan facebook baya min sam bana iya jurar mgn a can, don Allah kuyi hak'uri*


Belt d'in ya tsula mata da iya k'arfinshi,
kamar a mafarki Hajja Inna taji ya fara tsula mata, k'ara jin ya sake shimfid'a mata belt d'in a lafiyar fatarta yasa ta k'wallah ihu had'i da zabura tare da gantsarewa da yin mutsu-mutsu, cikin azaba da ihu da kururuwa tace.
"Wayyo Allah na! namutu Yusufa ya kasheni, waiyihuhuhuhuuu! jama ku kawo taimako."
ihu takeyi sosai dan ji take kamar da reza Yusuf ke tsarte mata jiki, domin kuwa rebonta da duka ya kai 75 years , sai gashi yau Yusuf na nad'a mata na jaki,
zillo tayi tare da dirowa k'asa kan carpet dan jin yana yi mata wani irin gigitaccen duka kai mata belt d'in yake tako ina, dukanta yakeyi yana kuka tare da yin magana cikin d'aga murya yake cewa.
"Ki hana d'anki dukarmin mahaifiyata, wallahi idan bai dena dukan Mama ba wallah! kullum a kanki zan ramawa mahaifiyata, shima yazo yaji irin k'unci da k'unan rai da nakeji duk randa ya daketa, ai ita ba baiwa bace."
sai kuma ya k'ara tsula mata belt d'in burburwa ta fara tare da sake fitsarin da tun dazu take jinsa,
son jin k'arshen tafsirin da akeyi a radio ya hanata tashi taje ta yisa, sai yanzu ta tsulashi tare da cewa.
"Wayyo Allah shike nan ya kasheni, ihuhuhuhuhuuuu wayyyyyyyyo Yusuf na tuba."
haka Yusuf ya rink'a zaneta ciki da woje bai duba girma da tsufanta ba bare kasancewar ta kakarshi ya zage ya dinga tsula mata belt dinnan, kamar Allah ya aikoshi.


Mama kuwa ganin yadda ya fito tasan Tabbas wani abin zai aikata, dan haka ta biyoshi amma kafin ta fitoma yayi nisa, sai shigar shi bangaren Hajja Inna ta gani, da sauri ta da kai zata shiga kenan taji ihun Hajja Inna,
ai daskarewa tayi ganin Yusuf ya zage sai dukan Hajja Inna yake, ganin bazai tsaya ba da gudu taje ta wafce belt din hadi da zabga mishi mari da hannunta mai lafiya,
duk da haka Yusuf bai tsaya ba sai nannad'e hannun rigarshi yayi tare bin Hajja Inna ya yaci gaba da dukan ta da hannu, cikin kid'ima da tsananin tsoro da sauri Mama ta tare gaban shi hadi da sa hannunta duka biyu harda mai ciwon ta rink'a jijjigashi tana cewa.
"Kai.! Yusuf! ka dawo hankalin! kasan me kake aikatawa kuwa ? nashiga uku Yusuf koka fara shaye-shaye ne irinna yaran zamani kwakwalwarka ta tab'u ne? !!!".
duk da haka cikin fushi k'ara nufar Hajja inna yakeyi da nufin zaici gaba da dukan, ganin haka cikin d'aga murya Mama tace.
"Yusuf wallahi in ka kuskura ka k'ara tab'ata zan jamaka Allah ya isa!."
yana jin haka sai ya fara yin baya-baya ya koma gaban Mama sai kuma ya rushe da kuka had'i da durkushewa akan kafafuwan sa,
Mama ma kuka ta saka.

Hajja Inna kuwa a gurin ta zube tana makyarkyata tuni zazzabi ya rufeta jikinta duk ya kumbura saboda ba karamin duka Yusuf yayi mata ba,
kuma gashi ya hadu da tsufa.
A part d'in su Zahra kuwa jin Ihunta shiya fito da Aunty Amarya da Ummi daga nasu bangaren, a guje suka shiga b'angaren surkar tasu, lokacin kuma yayi dai-dai da dawowar Abba daga raka mai gyaran targade shima a guje yayi bangaren mahaifiyar tashi jin ihunta da yakeji,
Zahra kuma dake biye da bayan Antynta ganin yadda Hamma Yusuf d'insu ke jibgaar kakar tasu sai ta koma gefe ta tsaya tare da fashewa da dariyar mugunta, dariya takeyi sosai harda rik'e cikinta, cikin tsananin dariya da jindad'i tace.
"Allah shi k'ara hegiya Hajja Inna a dakaki dai, ke ba kullum kin iya kai gulmataba, in kinga ana dukana har dariya kikeyi kina cewa a zaneni da kyau ko? to kema yau zagaye ya isa kanki."
sai ta kuma kalli yadda tsohuwar keyin burburwa da ihu da kururuwa tana gaggantsarewa, sai ta kuma kecewa da dariya harda buga tsalle, tana.
"Yauwa Hamma Yusuf zaneta dai sai itama tayi fitsari a wondo."
lokacin kuma yayi dai-dai kwace belt din da Mama tayi a gurin Yusuf da marinshi amma bai tsaya ba yaci gaba da dukanta da hannu mutuwar tsaye Abba yayi sai jikinshi da yaketa b'ari kamar mazari har zuwa lokacin da Mama ta tare Yusuf, abin yake gani kamar a mafarki wai,
Yusuf ne yayiwa mahaifiyar shi haka.
Cikin tsananin fushi da tafasan zuciya yayi kukan kura tare da sakin tsawa mai firgitarwa,
sai lokacin hankalin Mama dasu Aunty Amarya yayi kanshi dan basu san yazo gurin ba, cikin firgici da tsoro sukayi baya dan sunsan tsauri da zafin zuciya irinna Abba tabbas yau zai iya illata Yusuf koya kasheshi dan ba karamin tattalin lafiyar mahaifiyarshi

7 / 46