Author : Aisha Aliyu Garkuwa Category : Complete Novels
yake yiba.
Yusuf dake durkushe kan kafafun sa kanshi a k'asa yanata ambaliyar kuka bai d'ago kanshi ba tuni ya farajin duka tako ina dan belt din da Mama ta k'wace ita Abba ya dauka ya fara dukan shi kuma da gurin karfen duka yake kai mishi tako ina yana had'a mishi da gula da k'afa dukan shi yakeyi amma Abba bayajin dukan da yake mishi ya wadatar dan haka yasa hannu ya shak'o wuyanshi tare da fara tattakashi,
Yusuf kuwa sarkin zuciya daman yau zuciyar shi ta gama hawa baya ji baya gani baya tsoro da shakkar komai yau ya yadda ya dauki duk wani hukunci daga mahaifin nashi dan ya gaji dacin kashin da yake yiwa mahaifiyar shi,
Ita kuwa Zahra cikin tsananin firgita ta saki ihu ganin irin dukan da Abba kewa Hamma Yusuf d'in nata, kuka takeyi tare da rik'o hannun Antyn ta tana janta zuwa gun da Yusuf din ke durk'ushe cikin kuka tace.
"Wayyo! Anty na Abba zai kashe Hamma Yusuf,
Anty, Ummee, ku hana Abba dukan Hamma."
sai ta kuma sakin ihu, ganin ta firgita yasa Antyn ta jawota ta rugumeta tare da sakin
ihu,
ihun su Aunty Amarya sukeyi ganin tuni jikin Yusuf ya farfashe yanata fidda jini amma hakan bai saka Yusuf yayi kokarin guduwa ba kuma hakan bai saka Abba ya tsaya da dukan shiba Mama ce tayi kukan kura had'i da tare gaban Abba cikin tsanani firgita da kuka tace. "Kasheshi kakeso kayi ne?
zaka kasheshi ne? ka kasheni ni dan dalilina yasa yayi haka, sau nawa nake fad'a maka ka guji randa Yusuf zaizo daukar mataki akan dukan da kakemin, amma kayi biris, shekara nawa na dauka ina shan duka daga gurin ka yanzu karfin d'ana ya kawo yanajin dai-dai yake da duk wanda ya dakar mishi mahaifiya!!".
tunkudeta Abba yayi had'i da jifanta da wani mugun kallo cikin haki yace.
"Ashe kece kika saka yazo ya illatamin mahaifiya ta? toh ki fad'awa d'an iskan d'an naki yayi maza-maza ya bar gidannan tun kan fushina ya sauka a kanshi ya tattara ya nasa ya nasa yabar min gida kuma duk randa ya yadda yazo gidana ko yaje gidan wani daga cikin k'annena naji labari kona gani ranar a bakin auren ki, kuma ko gawata ban yadda yazo kanta ba inhar yazo ban yafe masa ba".
cikin matsanaicin kuka Mama tace.
"Wallahi tun yanzu zamu bar maka gidan dani dashi, sai dai mubar maka gidan naka dukan mu amma ba zaka kori d'ana ba alhalin akan gaskiyar sa yake."
sai zuwa lokacin Yusuf yayi magana da wata irin murya ta tsantsar b'acin rai da k'una yace.
"A a Mama ba zamu tafi tare ba zanbar mishi gidanshi saboda dama kullum cikin bacin rai da bak'in ciki nake a zamana a gidannan saboda abinda akeyi miki, amma wallahi!!! ki sanar mishi duk randa ya k'ara dukan ki zan dawo na rama miki akan mahaifiyar shi!".
saroro Abba ya bishi da kallo haka ma Mama dasu aunty Amarya ba karamin mamaki da tsoro furucin Yusuf ya basu ba yadda yayi maganar da kwarin gwiwar shi babu wani tsoro ko danasani.
Hajja Inna data sandare ta sume shiya dawo da Abba hankalin sa yayi kanta yana jijjigata,
Allah sarki Maman ce ta tafi da gudu ta debo ruwa ta shafa mata a sannu numfashin ta ya dawo, Daddy da Aunty Amarya ta kira shine ya shigo a guje nan ya fara bawa Hajja Inna taimakon gaggawa a sannu numfashinta ya dai-daita bacci ya kwasheta.
Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.
"Toh yanzu ina Yusuf d'in?" Mama ce ta share hawayen daya zubo mata tace.
"Ya koreshi".
Cikin takaici yace.
"Haba-haba Yaya in rai ya b'aci ai hankali ke nemo shi ba'a yanke hukunci cikin fushi bai kamata ka kori Yusuf a wannan shekarun nasa ba ai yayi kankanta da yawa, yanzu kasan ina zai shiga? kasan wani hali zai fad'a? kasan irin rayuwar da zayyi? kasan irin matsalar da hakan zai iya jawowa nan gaba!!!? masalaha ya kamata a nema ba aiki da zafin raiba".
wani banzan kallo Abba yayiwa Daddy had'i da cewa "K'ank'anta! K'ank'anta fa kace!! inhar shid'in karamine mai zai saka yayiwa mahaifiyar mu irin wannan dukan, in tafiya tayi tafiya wataran ni zaice zai daka ai kanaga yaro ya zama dan daba d'an ta adda kace in barshi a cikinmu".
cikin jin takaici Daddy yace. "Toh shikenan nizan nemi Yusuf d'in ni nasan har abadan bazai dakeni ba yanzu zan nemoshi muyi magana".
a zabure Abba yace.
"Kul!!! kada ka sake inhar kayi gangancin aikata hakan ina mai tabbatar maka zaka hadu da fushina mai tsanani, wallahi matuk'ar ka nemoshi bani ba kai har abadan".
nan Abba ya tashi ya fice daga dakin cikin fushi, gaba d'ayansu da ido suka bishi Mama kuwa fashewa tayi da wani irin kuka mai tsuma zuciya,
a sannu Daddy ya dinga bata baki da ban hakuri yana nuna mata cewar insha Allah zai samu ya shawo kan Yaya harya yarda Yusuf din ya dawo gida,
anan yake tambayar ta mene sababin faruwar abin tiryan-tiryan ta fara bashi labari tun daga farko har karshe sosai yayi mamaki da al'ajabi a shekaru da ilimin da dottaku yayansa bai zaci zai iya dukan iyalin shiba ashe ba'a iya zafin zuciya ya tsaya ba harda duka hakan kuwa sam bai kamaci babban mutum mai shekaru irinsa ba , bai kamaci dukkan namiji mai cikar nagartaba. (kalubale a gareku iyaye maza kubar ganin kuna ware kwanji ku jibgi matan ku son ranku tom a sannu ranar biya zatazo dan da zarar yaranta sun tasa burinsu su kwaci mahaifiyar su su rama mata dukan da ake mata) kuma abin al'ajabi da mamaki duk wannan dukan da Abba ke yiwa Mama yan gidan babu wanda ya sani daga Zulaihat sai Yusuf kadai suka sani dan tana b'oye sirrinta suma su Yusuf bata tab'a ajiyesu ta gaya musuba gudun kar tasa musu tsanar mahaifinsu, sai Anty Amarya da Ummee wanda suna fahimtar dukan da Abba ke mata, musamman Anty Amarya da Yusuf ke koka mata matsalar.
Shi kuwa Yusuf yana fita d'akinshi yaje duk da jini na zuba a jikin shi hakan bai dameshi ba abubuwan da suke da amfani a rayuwarsa ta duniya da lahirarsa kama daga, Qur'an d'inshi takardun makarantarsa dana aikin Pollonsu da dai sauransu ya tattara a karamar jaka sannan ya fito daga d'akin,
part d'in Mama ya nufa cikin jan k'afa a parlour ya tadda ita, tana kuka kamar ranta zai fita, Anty Amarya da Ummee sun tasata gaba suma kukan suke tare da lallashinta,
gabanta yaje ya durk'usa tare da d'ora kanshi bisa cinyarta, cikin rawan murya yace.
"Ki gafarceni Mama ki yafe min ki jik'aina kisamin albarka, ki dena zubda hawayenki a kaina."
cikin kuka tace.
"In banyi kukaba Yusuf me zanyi? yanzu ina kasan zaka shiga a fad'in duniyar nan tunda ya hanaka zuwa gun yan uwanshi, nima kuma yan uwanshin sune yan uwa, yau da ace ba zuriyarmu d'aya bane da Abbanku da nasan yan uwana zasu rik'emin kai gashi duk family shine babba babu wanda zai tonk'orashi, Yusuf me zanyi in banyi kukaba ina tsoron lalacewar tarbiyarka."
kai ya kuma kontarwa bisa cinyarta tare da rik'e tafin hannunta Yance.
"Mama Addu'a zaki min ba kukaba Mama nayi miki Al'k'awari zan zama d'a nagari zan kasan ce miki Al'waladul saliha insha Allah bazaki kunyata ba akan tarbiyar da kika bani, Mama duniya da fad'i zan tafi kuma duk inda nake muna tare."
Murya na rawa ta dafa tsakiyar kanshi tare da cewa.
"Allah yamaka Al'barka ya shirya min kai ya tsaremin gabanka da bayanka ya Allah ya tsare min imaninka da gabb'an ka daga aikata aikin ashsha Allah ya baka sa'a ya huci zuciyar haifihaifinka in samu ka dawo garemu."
"Amin Amin Ameeeeeeeeen ya rabbil izzati Ngd matuka Mama. "
yace tare da mik'ewa gaban Ummee yaje ya nemi gafararta sannan ya dawo gaban Anty Amarya da take kuka kamar ranta zai fita ta kasa magana sai jujjuya mishi kai takeyi kuka ta saki da k'arfi jin abinda yake fad'i mata.
"Dan Allah! Dan Allah!! Dan Allah!!! Anty ki kula da Zahra, Anty ki kula da amanar da Allah ya dank'a miki a matsayinki na mahaifiya Anty ki rufa mana asiri kar sakacin ki akan Zahra ya jazawa Familynmu zubewar mutunci da k'ask'anci, dan Allah Ummee, Anty, Mama ku kularmin da tarbiyar k'annena wallahi ina jin tsoron kar rayuwarsu ta cutu ina fargaba akan k'annena."
yana kaiwa nan ya fice da sauri yana mai zubda hawaye,
ita kuwa Anty Amarya da sauri tabi bayanshi tana kuka tare da cewa.
"Dan Allah Yusuf ka tafi gidanmu karkaje wani wuri kaje gidanmu wallahi nasan Mahaifiyata da yan uwana zasu rir'eka iya rai da mutuwa."
Yana jinta amman sai ya fice daga gidan da saurinshi,
ita kuwa komawa tayi part d'in Mama sukayi ta kuka.
Tafiya yayi mai nisa har ya fice daga yankin Girei , da k'afa ya shigo har cikin Jimeta.
Kai tsaye bayan P, Z ya nufa dai-dai k'ofar gidansu Aryan jiri ya fara d'ibanshi saboda jinin daya zubar sai kuma ya tafi luuuuuuu...............
*BY*
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*HUKUNCIN ALLAH*
Page 1⃣1⃣
*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*GA masu buk'atar sayan littafin Hukuncin Allah zaku turo katin Mtn na 200 kacal ta layin nan 09097853276 ko kuma ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, tabbatar ka/kin turo shaidar biyanki*
*Free page*
Aryan ne ya fito daga gida da niyyar zaije aski ganin mutum a kwance a kofar gidan su kamar bashi da rai shiya saka shi yin baya da sauri,
komawa gida yayi da gudu yana kwalawa Baba mai gadi kira tare da karasa shiga cikin gidan a gigice, Baba mai gadi da fitowar shi daga bandaki kenan shine ya saka shi fitowa a daki shima a tsorace yace.
"Aryan lafiya ka shigo gida a gigice haka meke faruwa?". da hannu yake masa nunin waje yama kasa magana, a hankali cikin sand'a da tsoro Baba mai gadin yake tafiya har ya isa bakin gate d'in sannan ya lek'a da ido d'aya dan Baba isa ba k'aramin matsoraci bane, ganin mutum kwance ya sakashi fitowa da sauri yana. "Subhanallahi ai mutum ne a kwance".
juya shi, ido ya zaro da mamaki ganin Yusuf ne ya fara kwalawa Aryan da yake cikin gida kira.
"Aryan! Aryan!! Aryan..!!! zoka gani ai abokin kane Yusuf".
da gudu Aryan ya fito daga gida ganin Yusuf cikin halin ciwo alamar ya sume shine ya kara rikita Aryan da gudu ya kuma shiga cikin gida.
Kakar su data fito lullube da mayafi tana rike da hannun Rayhana dan zasu fita unguwa,
driver dazai kaisu kuma yana cikin mota yana jiransu da sauri yake kiran Hajiya kakar su yace.
"Hajiya Yusuf a waje ya suma jikin shi duk a farfashe".
da mamakin zancen Aryan Hajiya tace.
"kamar yaya Aryan suma kuma?".
Mai gadi ne ya shigo ya nemi temakon driver dan su d'auko Yusuf sai lokacin Hajiya ta gane abinda Aryan yake nufi cewa tayi.
"kuje ku kamoshi ku saka shi a mota mu kaishi asibitin saimu kira gidansu muji kosun sani?".
Da "toh" suka amsa mata sannan d'aukoshi suka saka shi a motar da Aryan da Kaka da Rayhana suka shiga motar Mai gadi ya wangale musu gate yana addu'ar Allah ya kiyaye hanya.
A gidan Yusuf kuwa Aunty Amarya ce dake rungume da Zarah a cinyar ta tayi bacci saboda kukan da tasha, cikin muryar kuka Anty tace.
"Maman Yusuf ina Zulaihat d'inne naga duk abinnan da ake ban ganta ba?".
Ajiyar zuciya Mama taja had'i da goge ruwan hawayen daya kasa daina zuba daga idanuwan ta cikin kuka tace.
"Kinsan Zulaihat bata son rikici da tashin hankali, duk abinnan daya faru babu wanda ta sani, tana farajin Abbansu yana fada ta tattara kayanta ta koma gidanta nima d'in ban sani ba kirana tayi a waya ta fadamin".
shiru Aunty Amarya tayi tana jaddada hakurin Zulaihat dan tana da hakuri nesa ba kusa ba.
Zarah ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi.
"Ancy ina Hamma Yucuf na Abba a kasheshi ko?".
saita kuma fashewa da kuka rarrashin ta Aunty Amarya ta dingayi saboda kukan da Zarah tayi tuni zazzabi ya rufeta ta fara rawar sanyi, cikin tausayawa Ummee tace.
"Kije ki bata paracetamol tasha kafin zazzabin ya kamata da yawa".
A can gunsu Yusuf kuma Kai tsaye F, M,C YOLA su Aryan suka nufa da Yusuf emergency amma firr likitoci sukaki karb'ar shi sukace ai accident ne saida police ana cikin haka Daddy ya dawo dama bai tashi aiki ba kiran da Aunty Amarya tayi masa shine ya saka shi komawa gida.
Aryan daya fito yanata kokarin kiran number d'in Abba tak'i shiga saboda matsalar network danshi shaf yama manta Daddy a asibitin yake aiki,
har ya juya zai koma gun kaka dan shaida mata wayar bata shiga,
sai kuma ya juyo da sauri ganin Daddy da yayi da gudu ya karasa wajen shi nan yake fada mishi da sassarfa Daddy ya shiga da kanshi ya karbi Yusuf shi yayi masa duk wasu taimako daya kamata aka bashi gado,
drip aka saka mishi Bayamon ya farfado daga suman da yayi amma anyi mishi allurar bacci danya samu hutu.
Bini-bini Daddy zaizo ya dubashi har zuwa lokacin da ruwan ya kare yana cikin cire mishi ruwan Yusuf ya farka, a hankali ya fara bude idanuwan sa wani irin sarawa kanshi yake mishi saboda ba karamin ciwo yake masa ba, fess kuwa ya ware idanuwan nashi akan Daddy da tun dazu yake kula da alamun sa ya farka.
Ganin Daddy a gaban shi sai yayi hanzarin maida idon shi ya lumshe hawaye na bin gefen fuskarsa, murmushin gefen baki Daddy yayi hadi da cewa.
"Bud'e idanun ka mana".
jin kunya yasa Yusuf ya kasa bud'e idanuwan shi,shiko Daddy daurewa yake ya gimtse dariyarsa, dan in ya tuna abinda Yusuf yayi dariya ke kamashi ja'irin yaro wato ya ramawa uwarsa abinda ake mata a kan tsohuwarsu, gashi dama yasan Hajja Inna da d'an banzan raki,
murmushi ya kumayi sannan yasa hannun ya tallaboshi ya taimaka mishi ya mike ya jingina shi da pillow amma har zuwa lokacin Yusuf ya kasa hada ido da Daddy dan wani matsanancin kunyar shi yakeji kuma sai yaji danasani ya kamashi.
Daddy ne ya kalli Aryan yace.
"Ka taimaka mishi ya wanke bakin shi ka hada mishi tea yasha ka bashi maganin shi yadda na nuna maka saiya rama sallolin da ake binshi nizan tafi gida dare yayi sai gobe in Allah ya kaimu".
da "toh" Aryan ya amsa saida Yusuf yaji fitar Daddy ya iya d'ago kanshi.
A gida kuwa lokacin da yaran gidan suka dawo Zarah itace ta basu labarin abinda ya faru dan zuwa lokacin zazzabin ya sauka dukkansu basuji dadin abinba musamman Sulaiman daya tambayi Ummi take fada mishi yadda abin ya faru da korar da Abba yayiwaYusuf ranar sukuku aka wuni a gidan saboda babu walwala a fuskar kowa.
A asibiti kuwa cikin tausayawa Aryan ya taimakawa Yusuf ya wanke bakin shi.
tea ya hada mishi ya zuba mishi pepper soup din kayan ciki daya koma gida ya karbo a hankali Yusuf yake cin pepper soup din sam bayajin dandanon komai a bakin shi salam haka dai ya tuttura dan matsamishi da Aryan yayi da k'er yasha tea din, mikewa yayi yaji kamar iska zata kadashi Aryan ne ya taimaka mishi ya kaishi har bakin bandaki sannan ya juyo,
saida Yusuf ya watsa ruwa jallabiyar da Aryan ya dauko mishi ya mika masa da gajeren wando ya sako ya fito, lokacin Aryan ya shimfida mishi sallaya tambayar Aryan yayi wacce sallah zaiyi dan baisan tsawon lokacin dayayi a sume ba ,
cikin kula Aryan yace.
"In bakayi magriba ba tom magriba da isha'i zakayi". "ok". a zaune Yusuf yayi duka sallolin harda shafa'i da wutiri sannan ya koma gadon shi ya kwanta ya jingina da pillow lumshe idanuwan sa yayi a sannu ya fara tariyo abubuwan da suka faru acikin rayuwar shi a yau wanda ya jingina hakan a matsayin tashi kalar kaddarar.
Baiyi kokarin hana hawayen zuba ba,
shiko Aryan ganin yana hawaye sai ya matso gareshi tare da fuskantarshi cikin amincin aminai yace.
"Yusuf!!! me yake faruwa ne? hankalina ya tashi dan dazu bayan Daddy ya saka an baka gado