Advertisements
Chapter 4 Reading Hukuncin Allah Book 1 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Hukuncin Allah Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 46

9K to 12K   out of 136.1K words

*HUKUNCIN ALLAH*

page 6⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*Assalamu alaikum, masoya na masoyan littafaina, ina mik'a sak'on gaisuwata a gareku tare dayi muku Al'bishir d'in gani na dawo gareku da sabon littafina mai suna HUKUNCIN ALLAH, wanda na shiga Nazari tunani bincike hangen nesa na zak'ulo matsalolinmu a yau tare da kuma samo Garkuwar da zata tsira damu da yaranmu k'annenmu daga fad'awa halin dana sani,*
*HUKUNCIN ALLAH*
littafine dake tafe da sak'onni masu tarin yawa. *tuna sarwa, tsorotarwa, jan hankali, fadakarwa, tare da zaburarwa da bada k'arfin guiwa da zamu had'u mu yak'i k'alubalen dake addabar al'ummar mutanen wannan k'arni da muke ciki. sannan akwai nishad'antawa tare da ban dariya hakan kuma* kunsan salo nane ban tausayi mai ratsa zuciyar ma abocin imani da tausayi, duk suna cikin wannan littafinawa mai suna *HUKUNCIN ALLAH,* domin samun damar karantashi zaku iya bibiyata a manhajar what's App a number wayata kamar haka 09097853276 kan farashi mai sauk'i yi register da naira d'ari biyu kacal damin samun damar karantashi daga forko har k'arshe littafin *HUKUNCIN ALLAH* ko katin waya na layin MTN wanda za'a turo shi ta wannan number 09097853276 ko tur'a d'ari biyun ta asusuna na 0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA,
kada ka/ki manta turo min shaidarki na tura kud'in a dai wannan number 09097853276 ina maraba daku masoyana tare da kuma yi muku al'bishir da yin posting a kai a kai kada ka/ki sake a baki labari, sai kunzo.......!!!

Dan Allah banda kira
*HUKUNCIN ALLAH


Free page








Kallonta yayi da idanuwansa da suka rine sukayi jajawur lokaci daya dan azabar dake ratsashi har cikin k'ahon zuciyarsa,
ita kuwa Zahra da hanzari tayi baya tana tsitstsillah idanu, tabbas wannan abin da Zarah tayi mishi dabadan gaba daya karfin shi da kuzarin shi sun gudu ba to da babu abinda zai hanashi babballata a wajennan.



Wani irin damk'a marar tashi tayi masa ritse ido yayi hadi dabin bango ya fara tafiya a sunkuye hannunsa d'aya dafe da marar shi daya hannun dafe da bango.



Ita kuwa Zarah ganin haka saita kyalkyale da dariyan dadi dayi mishi gwalo, ta fita waje a guje dan sosai kidan gurin Idi mai chaji ke tsumata.



Haka ya karasa part din Aunty Amarya a daddafe kan doguwar kujera ya karasa ya kwanta yana murkususu dan jinshi yake tamkar zai mutu saboda azaba da radadin da mararshi take masa, dan ba karamin buga mishi katon kanta Zarah tayi ba, yana cikin halinnan Aunty Amarya tazo ta taddashi nanta rikice da tambayar shi.
"Yusuf lafiya Kuwa?".
kai ya rink'a juyawa tare da rumtse idonshi, Zeenat dake gefeshi ya kalla cikin rawan murya dakyar ya hado kalmomi ya yace mata.
"Kije shagon Idi ki cewa Zahra maza ta dawo".
K'ara matsoshi Anty Amarya tayi tare da cewa.
"Ana maganar lafiyarka kana batun shirmen Zahra, meke damunka? ka gaya min ko in in kira Daddynku mu tafi hospital yanzu."
cikin rumtse ido yace.
"Maaaa-raaaa-taah". shima dan ganin yadda ta tada hankalin tane dan sosai suke shiri da Aunty Amarya, ita kam da hanzari tajuya ta shiga kitchen ta zuba ruwan Lipton a cup ta matsa lemon tsami da yawa, fitowa tayi da sauri ta kamashi ta dago kanshi, saboda zuwa lokacin jikin shi har rawa yakeyi, a sannu ta saka mishi cup din a baki ya farashan tea din a hankali yasha da yawa sannan ya ture hannunta.
Yana gama shan tea din yaji marar shi tayi wani irin kullewa zabura yayi gami da damke marar ya rumtse ido tare da cije lips enshi, a sannu yaji wani sanyi da sauki lokaci daya ya nemi ciwon ya rasa tamkar an zare gashi daga cikin nono gumi ne ya fara karyo mishi tako ina a sannu ya koma ya kwanta yana sauke numfashi, yana jin damshi a jikin cinyoyinshi, ido ya lumshe dan sai yaji kunya ta rufeshi, gani yaje kamar Aunty Amarya tasan abinda ke sashi ciwon da kuma abinda yaji na fita daga jikinshi.
ita kuwa Anty Amarya in banda sannu babu abinda take jera mishi,
zumbur ya mike tamkar wanda aka aka mintsina da sauri Aunty Amarya tace.
"Menene, Yusuf lafiya kuwa?"
Ina ko sauraronta baiyi ba ko takalmi babu a kafarshi da gudu-gudu sauri-sauri yayi waje Aunty Amarya na binshi a baya dan ita ta dauka wani abinne ko ciwon ne ya gigitashi.



Tun daga nesa ya hangota tana kada kugu da siket dinta tayani tsalle duk inda ta juya yana bita bata damuwa sai dirkar rawa take gun-gun samarin dake zaune kan benci kofar shagon idi mai caji kuwa sai ihu suke suna dada zaburar ta.
Yana isa kunnenta yaja,
ita Kuwa jin anja kunnenta kiiiii, a firgice tayi baya k'ara ta kwallah tana.
"Ayyo kunne a ciye sh............" ganin Yusuf ne ya janyota saita had'iye ragowar maganar bakin ta, hadi da kifkifta idanu,
Yusuf kuwa wani mugun kallo ya jefi gun-gun samarin irinna ku shiga taitayin ku suka juya shida zarah sukayi gida hannun shi rike da kunnenta yanayi yana murza mata shi ita kuma saita saka tsalle kan sukai gida har tayi fitsari a wando fuskarta duk ruwan hawaye da majina.




Aunty Amarya data ganshi rike da kunnen zarah dariya tayi tace.
"Oh ni Maryam wataran dai Yusuf saika cire kunnen zarah zakaji dadi ko? ni kuwa haka zanta maka ajiyarta da cirarren kunne sai dai kaika aureta, dan babu wanda za'a bawa ita da kunne daya yanayi mata gori".
Siririn tsaki yaja hadi da sakin kunnen Zarah yayi cikin gida fuuuuu.



Zarah kuwa da gudu taje ta rungume Aunty Amarya kukan da bata samu damar yiba sai yanxu take baje kolinsa tuni ta fito da matan gidan Mama da Hajja Inna Mommy saboda kukan Zarah shegen kara gareshi kamar jiniya data baci, tambayar meya faru sukayi nan Aunty Amarya tace.
"Inaga kofar shagon Idi mai chaji Yusuf ya ganota tana sana'ar tata, dan wanka nake shirin mata tanajin ya saki kida ta fito a guje".
ta karashe maganar da dariya alamun abin baya damunta tsaki Hajja inna tayi tace.
"Kai wannan yaro anyi tantiri tak'adiri duk ya maida mana unguwa kamar wani gidan gala yana shirin maida min jika iyalin dujal".
harara ta bankawa Zarah ta koma bangaren ta, Mommy uwar gidan Anty Amarya kenan karasawa tayi ta dafa kafadar Aunty Amarya tace "Wlh Auntyn su gata Yusuf yakewa Zarah ba zaki gane illar sangarcin da kike mata ba sai nan gaba shi duk wani gata da zaka yiwa danka inba na ilimi bane shirme ne" daukar Zahrah Aunty Amarya tayi hadi da dariya tace.
"kai Mommy kuruciya cefa wataran da kudi akace zarah tayi ba zatayi ba".
hadi da kallon zarah tace.
"ko Tinana na".
dariya Zarah tayi hadi da gyada kai dan bata gane me Auntyn take cewa ba,
ita kuwa Maman Yusuf kanta ta girgiza a ranta tana fatan Aunty Amarya ta gane tun kafin duniya ta ganar da ita itama ta juya ta tafi part dinta.




Aunty Amarya ma part dinta suka shiga dakyar da wayo da dabara ta samu tayiwa zarah wanka anayi tana zillewa a haka dai aka gama.



Yusuf kuwa cikin kunar zuci ya k'arasa d'akin sa da yake part din Kaka amma shi a upstairs dakinshi yake kullum burinshi k'annenshi su zamo nagari abin koyi ga kowa amma ina a komai sai an fidda zakka ga Zarah nan da tata kalar kuruciyar,
ya yarda da kuruciya amma yana tsoro saboda ance icce tun yana d'anye ake tankwara shi kada ya barta yanxu yana ganin yarinya ce saita girma kuma ta gagaresu a haka yana tunanin yadda zaiyi da Idi mai chaji ya cire kayansa ya shiga toilet dan yayi wanka ya tsarkake jikin shi.



Washe gari tsaye yake a bakin k'ofar Aunty Amarya 7:45am yana muzurai Zarah da ake sakawa socks sai matsar hawaye take dan ita a rayuwarta in anaso a kuntata mata a takura rayuwarta ace taje makaranta yau kuma gashi Hamma Yusuf da kanshi yazo yace a shiryata shine zai kaita makarantar da kanshi, haka aka gama shiryata da sauran yaran suka dauki launching box dinsu suka yiwa Aunty Amarya sallama suka tafi,
suna tafiya yau Zarah babu halin tsokana ko taki tafiya tace saisun goyata su kuwa duk dadi ya cikasu,
har cikin class ya rakasu sannan ya cewa
"Aunty dinsu dan Allah yau ko fitsari in Zarah ta tambaya a hadata da wani suje su dawo dan guduwa take".
tace "toh" sannan ya tafi.



Da aka tashi ma Yusuf shi yazo ya koma dasu gida saboda sun fara shirye2 fara WAEC yanxu ba kullum suke zuwa school ba, kuma yau a zaman da yayi a gida ya fita ya binciko wata islamiyya can nesa da gidansu dan sai an hau napep ko mota ma dan zaiyi tafiyar 25 to 30 minutes tsakanin suda makarantar 3:00pm ake shiga a taso 6:30pm nan yayi niyyar yakai zarah ya kwammace in bayanan ya saka a dauko masa ita gwanda ta daina wunin gidan gaba daya.



Hakance kuwa ta kasance 2:15pm suka dawo daga school da kanshi ya shigo ya cewa Aunty Amarya tayi mata wanka yana tsaye akayi mata wankan bayan an shiryata har Aunty Amarya ta dauko mata kayanta na sawa vest da siket dinta tayani tsalle saboda zafi da ake fama dashi saboda gabatowar damuna amma har yanxu ruwan bai sakko ba yace.
"Aunty Amarya ki saka mata kayan mutunci islamiyya zan kaita fa".
kuka Zarah zata saka Yusuf ya zare mata idanu Aunty Amarya kuwa dariya tayi dan ita tanada kawaici da kara koda zaka dakar mata yaronta a gabanta ba zata daga ido ta kalleka ba balle tayi magana, bayan ta gama saka mata kayan da kanshi ya bata abinci tayi tana gamawa ya saka mata hijab ya rike hannunta suka fita a gidan,
napep sukaje suka hau dama yaje yayi mata registration duk ya biya kudin komai interview akayi mata amma Zarah bata iya komai ba saboda yadda take gudun makarantar allon in an kaita, dama makarantar tahfiz ce daga dan shekara 3 suke fara daukar yara zarah kuma yanxu tana shekarunta sun zarta haka ta nan suka kaita aji biyu Yusuf yayi signing akan shine zaina zuwa daukarta in an tashi in kuma ba zaizo ba zaiyi waya ya fadi wanda zai dauko ta yayiwa head master sallama ya tafi.





Tun 6:00pm Yusuf yana cikin islamiyyar su Zarah har aka tashi yara ita ta fara fitowa daga aji a guje ganin Yusuf saita dan nutsu ta karaso tanata washe baki nan ta fara bashi labari "Hamma Yushuf Malam ayi mana kayatu shoshe, ayifun ta'un jimun Alhamdu lillahi labbli alamin" cikin farin ciki Yusuf ya dauke ta ya daurata akan cinya rabon da Yusuf yayiwa Zarah wannan daukar harya manta cikin sakin fuska yaja kumatun ta yace "Yauwa kanwata kinga kin fara zama good girl ko kiyi karatu sosai kinji".
dariya ta kyalkyale da ita tace "yauwa Hamma Yushuf inna jama gud jel jaka shiyamin alawa ko?".
Murmushi yayi hadi da sauke ta ya mike hannu ya saka ya d'auke ta yace.
"Eh in kika iya karatu kika zama good girl babu rawa babu tsokana da rashin ji har Baby zan siya miki".
cikin zumud'i tace.
"Hamma Yucuf baby mai gashi zaka sayamin ko sai in mata kitso."
"eh." yace mata a tak'aice
murna tayi-tayi har suka karasa titi suka sami napep ya kaisu gida.



Yaufa duk wanda ya shigo part dinsu sai Zarah ta biya mishi karatun da aka mata,
d'ad'i sosai Aunty Amarya taji har part din Ummi da Mama da Hajja Inna sai da Zarah taje ta biya musu karatun data koyo duk da batayi dai-dai amma sunji dadi haka Daddy da Abba ma da suka dawo saida Zarah ta biya musu karatun, Daddy kam yaji dad'in abin sosai, cewa yake.
" iyeh Goggon Daddy ta girma".

Tun daga ranar Zarah ta daina wunin gida dan tana dawowa daga boko Yusuf zai dauketa ya kaita Islamiyya in kuma bayanan zai barwa Aunty Amarya sallahu yace in Sulaiman ya dawo yaje ya dauko ta, har zuwa lokacin da suka fara rubuta exam dinsu ta WAEC.


Idi mai chaji kuwa tun yana zuba idon ganin Zarah dan har tambayar yaran gidansu yake in zasu wuce makarantar Allo sai suce Hamma Yusuf ya kaita Islamiyya kullum zuba ido yake yaganta amma babu hali dan ya kulla mugun nufi a ranshi game da Zarah ko ta halin ya sai ya maida ruwa maganin k'inshi.




Zarah kuwa sosai take daukar karatun dama shegen wasa ne dayayi mata yawa yasa sam bata gane karatu amma yanxu sosai kanta keja dan Friday da Thursday da yamma in sun dawo daga boko Hamma Yusuf da kanshi yake musu lesson week end kuwa tun 8:00am ake kaita makaranta sai 6:30pm aje a dauko ta aikuwa Zarah har ramewa tayi.



Zuwa yanxu Yusuf sun gama WAEC sai dai sunata shirye-shiryen gasar tseren doki da za'ayi da yayan sarakunan sassan jihar Adamawa, kamarsu Mubi, Guyuk, Numan, Maiha, Fufore, Madagali, Mabalwa, Shelem, Ankara, gora, Som, Gire,
da dai sauransu, dan zab'an fidda goni d'aya da zai wakilci jihar a gasar da za'ayi na sauran jihohin Nigeria, shi Yusuf ya zauna matsayin Aryan ne dan yafi Aryan din iyawa da ra'ayin abun, kullum in yakai Zarah islamiyya saiya wuce gidansu Aryan acan zasu dauki doki suyi cikin airport da yake babu nisa da gidansu Aryan din acan zasuyi ta gwada tsere koda yaushe dai Yusuf shike cinye duk taron yayan masu anguwanni da suke haduwa awurin.
suna dawowa kuma sai yaje ya dauko Zarah suke wucewa gida gaba d'aya.


Ana haka aka yiwa su Zarah hutu bayan exam da akayi musu acikin yara 20 zarah tayi ta 6.




Yau ta kama Asabar kuma ranar ne ya zama ranar gasar tseren dokin dasu Yusuf zasuyi, wanda mai Martaba Sarkin Adamawa da Gwomnansu jihar zasu hallarta wojen taron da sauran manyan jihar,
Sai dai tun bayan sallar Asuba har zuwa 7:39 Am, hadari ya hado mai duhu, amma bai saukar da ruwa ba sai tsawa da walk'iya ake da iska mai dadi garin yayi luf-luf ko ina yayi duhu kamar dere gari yayi sit kamar babu mutane kowa yayi cikin gidansa da gujewa jik'ewa dim garin yayi alamar koda yaushe ruwa zai iya saukowa.



8:00am Zarah ce tayo sadaf-sadaf ta fito daga part dinsu a hankali take tafiya tana waige-waige har saida taje get ta bude a hankali ta nufi shagon idi daya cika illahirin unguwar da kid'i inda shi kuma yake konce yana kallon BF a woyarshi.
tana fita karar jan get d'in da tayi da karfi shine ya ankarar da Yusuf da fitowar shi wanka kenan,
sauri-sauri ya shafa mai ya saka kaya dan jikin shi ya bashi fita akayi.



Zarah kuwa tana fita a 100 tayi shagon Idi daya kure kida karar shi duk ya cika unguwar,
Shi kuwa Idi dake kwance kan benji a cikin shago ya shagala da aikata Masha'ar daya saba,
kamar daga sama yaji muryar Zarah dan karfi tace "Idi a bani ayawa 🗣".
firgigit ya farka saura kiris ya fado daga kan bencin ganin Zarah sanye da dogon wando da riga alamar daga bacci ta tashi shine ya saka shi mutstsike idanuwan shi,
da hanzarin ya mike yayi woje ya fara leka wajen shiru yaga layin alamun babu kowa dariya yayi hadi da dawowa cikin shagon ya tura kofar, bel d'in k'ugunshi ya fara zarewa tare da cillashi gefe.



Yusuf kuwa da gudu-gudu sauri-sauri ya gama shiryawa ya sakko kai tsaye part din Mama ya wuce, bayan sun gaisa ya nufi part d'in Aunty Amarya yana shiga dakin yaran gidan ya nufa, bacci ya tarar sunayi har ya juya sai kuma yaji b'uruntu a kitchen da sauri ya leka Aunty Amarya ya gani tana kokarin hada break fast ko gaisheta baiyi ba yace.
"Ina Zarah na duba dakin su bata ciki?".
Murmushi Aunty Amarya tayi had'i da cewa.
"Zarah uwar rigima, ai jiya daru ta saka akan ita a d'akina zata kwana tanacan tana bacci na barta na taho kitchen hada break fast". ajiyar zuciya

4 / 46