Advertisements
Chapter 21 Reading Hukuncin Allah Book 1 Complete Hausa Novel Hausa Novels
Advertisements

Hukuncin Allah Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Aisha Aliyu Garkuwa Category :  Complete Novels

Chapter   21 / 46

60K to 63K   out of 136.1K words

bi jirgi suka tafi shi kuma Yusuf ya koma south Africa ya fara kara tunshi haik'an k'adaran.


Bayan wata biyu dayin gasar
shuwaga bannnin Ghantoot racing & polo club Dubai suka shirya taro na musammman dan karrama Yusuf sannnan da neman alfarman d'aukar hayanshi,
inda M Jabeer da wasu wakilan polo na Nigeria suka bak'unci taro, wonda sanadin wannan taro ya k'ara d'aga darajar Yusuf lokaci d'aya k'unguyoyin polo na duniya baki d'aya suka fara harin sayan Yusuf da kudade masu tarin yawa,
amman da yake shi d'an halak ne baya manta alkhari sam yak'I sauraronsu, har saida M Jabeer yayi ta mishi fada ya nuna mishi wannan ma nasarace kuma da haka zai iya gina kanshi har ya taimaki k'asarsa da ker dai ya amince sannan yace.
"Duk mai sonshi sai dai hayarshi Amman shi dan wasan Nigeria ne. "
aiko a take Argentina ta daukeshi da farashin da saida ya firgita Malam Jabeer ma domin miliyoyin kud'i ,
cikin ikon Allah yana bugawa Argentina da India sai gashi sun cinye India, bayan wani d'an lokaci kuma suma India suka nemashi da kudin daya ninka na Argentina.

Tuni rayuwa ta juya shi da kanshi Yusuf tsoron yadda nasarori ke riskar rayuwarsa yakeyi wani lokacin sai yayi ta tunanin ko mutuwa zaiyi nan kusa Allah keta tara mai k'addarorinshi a jere a Jere yayi kudin da shi kanshi bai san adadinsuba yayinda tuni ake mishi inkiya da mai nasara ko yaro da kud'i.

Anan south Africa ma shugaban makarantar su na Jurassic Park polo kwarya-kwaryar liyafa ya shirya masa saboda farin cikin nasarar da Yusuf ya samu ya dad'a kankarowa makarantar shi mutunci dan tun randa akayi gasar yake ta samun sababbin dalibai dan cotch na k'asashe suka dinga zuwa gurin shugaban makarantar akan ya saida musu Yusuf sai yace bashi da wannan hurumin yayinda su kansu South Africa din suke son seyeshi domin ya musu kazo garinsu ka fisu.


Bayan komai ya d'an lafa mishi Yusuf ya meda hankalinshi kan karatunshi yayinda U, C, T ya fara karatun shi yana karantar Business Administration shi da Aryan dinshi karatu suke babu kama hannnun yaro dan yanzu sun zama manyan k'wari duk makarantar ji akeyi dasu.




******************


Lokaci yaja kwanaki sun shud'e makkonni sun gifta watanni sun zarta har ya isa ga shekaru sun tafi.

Aryan ya gama karatun shi na degree na farko inda zai dawo Nigeria yayi NYSC d'inshi randa zai dawo Nigeria sunyi kukan rabuwa da Yusuf dan Yusuf yanaji tamkar sun rabu kenan ba zasu k'ara had'uwa ba haka Aryan ma ya dawo Nigeria cikin kewar d'an uwanshi.



Yusuf ya dad'e kafin ya ware ya dawo kamar yadda yake ada, Aryan kuwa ya fara da zaman camp kafin daga bisani ya fara service d'inshi.


Raihana yanzu har tayi candy dan tama fara university Modibbo Adama university kuma tana da kyawunta dai-dai gwargwado lokaci zuwa lokaci tana kaiwa Maman Yusuf ziyara.
kasancewar Zarah akwai rawar kai dason gayu duka-duka a lokacin tana s s 1 ne batafi shekaru 13 zuwa 14 ba amma yadda take da manyance da gayu saika dauka tayi 17 years kuma dama masha Allah tana da girman jiki amma har zuwa lokacin Zarah tana k'aunar English wears in kuwa an musu d'inki ne to ko dai-dai jikin tane saita d'auka ta kaiwa tela ya rage mata ya kama jikinta d'am-d'am ya zama tamkar a jikinta aka d'inkasu dan saika rantse da Allah ma in tayi tafiya kayan yagewa zasuyi ita kuwa babu ruwanta.

Sai da in Mama ta gani ko Ummi suyi mata fad'a Aunty Amarya kuwa sai tace k'uruciya ce zata dena wataran in ance tayi ma ba zatayi ba.



Saboda nacin Zarah nason kwalliya da gwalli da manyance a mak'otan su sabbin k'aurora ta Saba da Anty Shuwa matar da mijinta ya sayi gidan senator dinnan da matasan unguward suka tab'ayin yunk'urin k'onawa,
to daga nanfa ya saida gidan inda wani babarbare borno ya sayi gidan ya dawo da matarsa da yaranshi,

Zarah kuwa tun randa matar ta shigo gidansu ganin yadda take da gayu ga k'anshi ya sakata maida gidanta wajen zuwanta, dama matar sana'ar gyaran jiki da lalle takeyi dan da kolliyar amare
daga gari-gari ma zuwa akeyi daukarta dan ta k'ware sosai ganin sha'awar Zarah da abin ya sakata fara koya mata kuma Alhamdulillah kasancewar tanason abin yasa cikin k'ank'anin lokaci ta fara iyawa uwa uba dama Zarah ta iya kwalliya sosai dan intayi wa fuskarta kwalliya saika rantse da Allah zuwa tayi akayi mata ana haka ta damu Aunty Amarya ta siya mata kit, in anzo gyaran jiki gidan Hajiya Fadwa sai tace tana kwalliya haka kuma in ana biki dama ana zuwa a d'auke ta taje tayiwa Amarya da kawayenta kasancewar ta iya kwalliyar sosai tuni tayi suna duk wata Amarya dakeji da kanta fatanta in bikinta yayi tazo gidan Hajiya Fadwa gyaran jiki sannan Zarah tayi mata makeup har ya zama ana d'aukarsu suje har gidan bikin suyiwa Amarya da k'awayenta makeup.



Zarah kuwa nan gwalli da iyayi ya karu jin kanta take dai-dai da kowa duk abinda takeso siya takeyi da kudinta saiya zamana inba da gaske akayi mata ba bata saka manyan kanya tunda da kudinta sai taje ta siyo duk wanda takeso ga k'atuwar woya suturu duk sabon yayi a gunta ake gani.




Cikin Amincin Allah Aryan ya gama service d'inshi lfy nan uncle d'inshi ya karbi c.b d'inshi yace zai sama mishi aiki,
cikin ikon Allah kuwa wata d'aya da karbar c.b d'in nashi yazo mishi da upper ya sama mishi aiki a (criminal court) sannan ya bud'e mishi office a matsayin lowyer mai zaman kanshi ranar Aryan har kuka yayi dan farin cikin cikar burinshi yaso ace Yusuf yananan ya tayashi murna, yana gama murnar tashi ya d'auki waya ya kira Yusuf.


Kwance Yusuf yake akan gado kanannad'e cikin bargo yana ta rawar sanyi kasancewar ciwon marar shi ya tasar masa yanzu ya zama koda yaushe cikin ciwon yake kasancewar k'ara girma da yakeyi sai yawan sha'awar shi ya k'aru koya akayi sanyi toh ranar baya iya bacci gashi sam duk wasu tablet's sun daina masa aiki shi tunanin shima duka-duka yanzu shekarun shi nawa ne 24 years nefa baya mantawa last ciwon daya tashi yana class ana lecture ashe suma yayi ma sai d'aukar shi akayi aka kaishi asibitin makaranta shine likitan ke bashi shawara tunda addinin su bai yadda da neman mata ba toh yayi aure kawai shine mafita , dan gaba kad'an zai kasa yin control din kanshi kuma komai na iya faruwa da lafiyarshi.
Bugu da k'ari ga matan garin suna bada gudun mawa wajen zuzuzuta wutar ciwon shi kasancewar yadda suke kawo mishi kansu da shigar banza sunaso yayi lalata dasu shi kuwa ina yadda ya kyamaci zina ya rasa da wadanda zaiyi fasikanci sai turawa ina yana cikin wannan halin wani lokacin ji yake kamar ya dannne gini dan azabar sha'awar dake azalzalarsa.
mik'a yayi da k'arfi ido ya dan zaro ganin yadda Yusuf d'inshi yake mik'e da harbawa juyawa yayi cikin nama yayi rubda ciki wai ko zai samu sauk'en harbawar da yakeyi ido ya rumtse da k'arfi tare da sa hannunshi duka biyu ya matse pillow a jikinshi, lokaci d'aya zufa ta fara tsatstsafowa kan goshinshi ji yake kamar ya dandatse kanshi ko zai rabu da wannan fitinenniyar sha'awar.
yana cikin wannan azabar yaji wayar shi dake kan bedside cabinet ta d'auki k'ara.





*BY*
*GARKUWAR FUNANI*

[11/26, 7:41 PM] Garkuwar FulaniπŸ„πŸ«πŸ§•πŸ»: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 2⃣2⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*




πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡



Har wayar ta katse bai iya fitar da hannunshi daga cikin bargon ya d'auko ta ba, wani kiranne ya k'ara shigowa cikin zafin ciwon ya rumtse idonshi tare datse lips enshi na k'asa dan k'arfi, a hankali ya fidda hannunshi da shima rawar yake bai samu d'amar duba wanda ya kirashi ba kawai ya d'aga wayar ya manna a kunne.



Cikin tsantsar farin ciki Aryan yace .
"Albishirin ka bro".
bai jira amsar Yusuf ba yaci gaba da cewa.
"Burina ya cika yau na fito a matsayin cikakken lawyer mai zaman kanshi sannan kuma".
ihu ya saka cikin wayar da kyalkyalewa da dariyar farin ciki wadda har saida Yusuf ya zare wayar daga kunnenshi jin kamar k'arar zata tarwatsa mishi k'wak'walwa, sai da yaji alamun Aryan ya tsagaita da dariyar sannan ya maida wayar kunnen shi a hankali ya fara magana cikin sanyi da k'arfin hali tare da fidda numfashi irinna wanda yake cikin tsantsar rashin lafiya yace.
"Alhamdulillah nayi farin ciki sosai da samun cikar burinka Allah sanya al'khairi aikin nan naka Allah yayi jagora ya bada nasara,
amma naso ace a shari'a court zakayi aiki saboda kana fidda zunzurutun gaskiya irinna shari'ar musulunci kana kwatarwa wadanda aka zalinta hakkin su danni nafison komai a yishi cikin tsarin addinin musulunci".
duk cikin hankali da numfarfashi yayi maganar a maimakon Aryan ya bashi amsa saiya rikice yace. "Subhanallah bro ya naji muryar ka tana rawa alamun ciwo? meke damun ka?". runtse ido Yusuf yayi had'i da cije labbanshi duka biyu da hak'ora ta ciki sannan ya bude bakin shi da furzar da wata zazzafar iska yace "Ciwon mara tane ya matsamin tun jiya".
cikin tausayawa da kula Aryan yace.
"Innalillahi! wai wannan wanne irin ciwo ne da bayajin magani,
oh ya Allah ka bawa dan uwana lafiya ka kawo masa sassauci da mafita ya Allah ka fimu sanin dalilin dayasa ka halicceshi a haka ya Allah ka sassauta mishi yawan sha'awarsa da take zame mishi cuta."
Cikin lumshe ido Yusuf yace.
"Amin ya Allah."
shi kuwa Aryan ci gaba yayi da cewa.
"Amma kaje asibiti kuwa?". mik'a Yusuf d'in yayi tare da cewa.
"Eh ina kan magani da allurai ma duk da sun daina min tasiri na rasa wannan wanne iriyar sha'awa gareni me k'arfi wlh ni kaina tsoron kaina nakeji da irin halittata dan ni tsoro ma nakeji kar inyi aurenma matar ta gujeni ta gaza zama dani".
ajiyar zuciya yaja sannan yaci gaba da cewa.
"Kuma gashi Dr yace yanzu aure ne kawai zanyi ya samar min lafiya ni yanzu wlh na rasa inda zan saka kaina". saiya karasa maganar da alamu na karaya tattare dashi,
tausayin shine ya kama Aryar har yanajin tamkar xai zubar mishi da k'wallah yace "Addu'a bro kaci gaba da addu'a kuma nasan ka dama azumin litinin da alhamis baya wuce ka kaci gaba insha Allah, Allah yana tare da kai kuma zai kawo mana mafita".
cikin furzar da zazzafan numfashi yace.
"Allah ya yarda".
Aryan yace.
"Bari na barka haka ka samu ka huta kada na dameka da surutu".
cikin sanyi Yusuf yace.
"toh sai anjima in sha Allah zan kiraka,
Ka gaida min kaka da Raihana tawa".
"in sha Allah zasuji ".
cewar Aryan
had'i da kashe wayar.

Yusuf kuwa bayan kamar minti 5 da gama wayar tasu wani wahalallen bacci ya kwasheshi.



Bai farkaba sai bayan sallan magrib yana tashi bathroom ya shiga tare da yin wonka sanna ya fito mai ya shafa tare da fesa turare sannan ya zira farar jallabiya tare dasa yar k'aramar hularnan da ake cewa tab'a kaji hadisi,
sallar magrib din yayi bayan ya idar ya d'auki k'ura'aninshi yayi ta karatu har saida lokacin isha'eh yayi sannan yayi sallar,
yana idarwa kiran Abdul-Kareem na shiga woyarsa cikin kewar juna suka gaisa bayan sun gaisa ne Abduk-kareem din yayi gyaran murya tare da cewa.
"Yusuf naga k'ungiyar polo ta k'asar England sunata fafutukar sayanka ko?."
dariya Yusuf yayi tare da cewa.
"Ka jika fa su sayeni kamar wani kayan gonjo."
Shima dariyar yayi yace.
"Ato naga sunata zuzuta biliyoyin da suka ware dominka sannan kuma nasan mutanenku ne tunda iyayen gidanku ne su suka yaye Nigeria."
sajenshi ya shafa tare da cewa.
"Kai ina..! ina..! aini babu k'asar da zasu seyeni, kuma kud'insu bazai rud'ani ba dan Alhamdulillah wanda nike da shima har tsoro yake bani, ina gama karatuna zan koma k'asata in tallafi rayuwar al'ummarmu da basu da k'arfi."

Kai Abdul-kareem ya jinjina tare da cewa.
"To yanzu wacce k'asace take neman hayanka?."

"Eh to k'asa d'aya ce amman team uku ne na cikin k'asar suke neman inje in buga musu."

"Wacce k'asarce kam".

"Argentina. "

cikin jin haushi Abdul-kareem yace.
"wai su kam wadanne irin mayune? to gskya baza je musuba, muma k'asata muna buk'atarka a wasan da za'ayi next year shiyasa nace to bari in gaya maka tun yanzu, zamu bada miliyon 50 tunda su wadancan sunce 40 zasu bada."
Murmushi Yusuf yayi cikin jin dadin yadda Abdul-kareem ya nuna shi nashi ne kuma yana da dama a gunshi, hello yaji mgnar Abdul-kareem din ta katse mishi tunani,
gyaran murya yayi tare da cewa.
"Allah ya kaimu lokacin ya kuma bamu sa'a sannan batun kud'in barshi kawai, kudai nemi izin Malam Jabeer kawai in dai ya amince to babu wata matsala."
murmushin jin dad'i Abdul-kareem yayi tare da cewa,
"Ai last month naje Nigeria nayi kwana biyar tuni shugaban k'ungiyarmu ya samu corch dinku sun gama mgna yace in dai ka amince ba matsala, to Alhamdulillah kuwa dama ya bamu form mun cika saura sa hannunka shima baisa hannunba yace sai kasa hannu sannan ya saka."
Murmushi ya d'anyi yace.
"Allah sarki Alhamdulillah Allah ngd maka da ka bani adalin sugaba,
toh yanzu sai munyi mgna duk yadda muka zakuji, Argentina kuwa zan meda musu form' d'insu na gayyata."

Godiya Abdul-kareem yayi ta mishi tare da yin sallama,

shi kuwa ya kira Malam Jabeer ya shaida mishi yadda suka, inda yace yanan tafema zai kawowa Yusuf din ziyara sai sun gama komai anan tunda shima ya kusa gama karatunshi yabar k'asar baki d'aya..



Haka rayuwar taci gaba da tafiya duk hanyar da Yusuf yasan zata iya tado mishi da ciwon shi ya daina bi dan yanzu kwata-kwata ya daina zaman wajen makarantar ana gama lecture in bashi da gurin zuwa zai tafi hostel saboda zaman shi a waje kamar farmaki ne a cikin rayuwar shi bayan yan matan turawa dake kawo mishi farmaki kuma babu wani suturar mutunci da matansu suke yawo dashi dan a bakin tafkin makarantar haka za yan matan zasuna yawo daga su sai pant da bra.



Inda Aryan kuma ya kama aiki kuma Alhamdullah ya shiga a sa'a saboda,
da wuya ya jagoranci case baiyi nasara ba shiyasa a lokaci k'ank'ani yayi suna a aikin shi gadai shi matashin saurayi amma yasan k'a'idar aikin shi yana yinshi yadda ya kamata ya jagoranci case a court iri daban daban kuma nasara ta zama rigarsa.




Zarah kuwa ganin yanzu kud'i na shigo mata ya saka idanuwanta k'ara bud'ewa dama kunsan Zarah da rawar kai sai takejin kanta take abubuwa irinna manyan mata dan harta maganarta ta canja in zatayi magana cikin yauk'i da yanga tanayi tana fari da ido da tab'e baki gata dason gayu da kwalliya hakan saiya janyo mata farin jini ga kuma tarin k'awaye age mate d'inta harda wadanda suka girmeta ma, kananun kaya kuwa bata kunyar sakasu ta fita duk inda taso amma duk abinnan da takeyi Daddy ko Abba babu wanda ya sani gata dason taji za'ayi biki a gayyaceta akwai dan taje tayi rawa .



Misalin 7:00am Raihana ce ta fito da alamun sauri take dan text gareta yau a school nan driver yayi sauri ya shiga mota itama ta shiga amma abinka da k'arfen nasara akayi-akayi mota ta tashi amma taki gashi Aryan ya tafi office ganin zata makara ya sakata fitowa da niyyar taje tahau napep kada ta rasa text d'in,da yake gidansu babu nisa da titi, koda ta k'arasa bakin titi nanma babu napep ko duk wanda yazo zai wuce akwai mutane a ciki gashi tana tsoron ta makara dan minti kadan zata duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta sai kuma tayi tsaki.
da sauri ta dan dago kanta dan wani sauti da taji,
shuuu wata mota ta wuce ta a sannu kuma motar ta tsaya tad'an fara yo ribas baya dai-dai inda Raihana take motar tayi parking inda mamallakin cikin motar ya zuge glass d'in motar shi sanyin A.C had'e da k'amshi air conditoner din dake cikin motar ne ya buso hancin Raihana inda wani kyakykyawan d'an Fulani black beauty dake cikin motar yace.
"Yan mata ina zuwa ne da sanyin safiyar nan?".
Ko kallon inda yake Raihana batayi ba illah k'ok'arinta nata tsaida wani empty napep da yake k'ok'arin wucewa ganin haka ya saka saurayin nan kashe motar shi ya fito.
"Yana haba yan mata tom in ba zaki

21 / 46