Author : Hafsat Bature Category : Action Novels
har Malamai duk wanda yazo wucewa yaga Calendar d'in ko wani abu mai hotonsu sai ya tsaya ya tanka har discipline master d'insu da ya gani yace yana so shima aka bashi Calendar dasu jotter, basu koma gida ba a Cikin Makarantar suka ci Abinci har Abbas ya kirata yay mata ya Exams haka gwaggo ma da Kawu Amadu, k'arfe 3:00 suka shiga next paper ta IRS wannan ai ko awa ba'ayi ba ta gama ana fara amsa duk suka bada don itama Haulat d'in ta gama cike da farinciki suka koma gida.
After 2 Months,
A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji, a yau su Fatuu na cikin tsananin farincikin da Allah ya nuna masu gama jarabawar su lafiya sai murna suke suna celebration don har anko sukae dogon skirt da yar top sai coat mai d'auke da year d'in da sukae graduation da department d'in da Mutum yay wasu sun sa himar wasu hula facing cap wasu kuma gyale sukae rolling sai d'aukar hotuna suke harda Malamai sukae d'an party, Fatuu ba tayi komae ba ta raba kaman da Jsce, gwaggo ta so yi mata abubuwa don har kud'i Haisam ma ya turo mata yace tay hidiman graduation d'in amman tace ma gwaggo duk asara ne ayi wani abun dasu kawae, tun wurin Azahar suka gama amman basu fita daga Makarantar ba sai wuraren La'asar a k'asa suka taho suna ta nishad'i ganin suna ta tafiya haulat tace mata ita dae gaskiya ta gaji amman Fatun tace aikuwa yau k'asa zasu je gida, suka ci gaba da tafiya har suka fara yin nisa sosae, suna cikin tafiya wata galleliyar Mota ta tsaya a gefensu da yake a gefen titin suke tafiya juyawa sukae a tare suka kalli Motar kafin suka juya don cigaba da tafiya kawae sai gani sukae glass d'in Motar ya fara sauka nan take sukae arba da mai tuk'a Motar wanda matashi ne zai iya kaiwa shekaru 28 haka wankan tarwad'a ne yana sanye da kananan kaya kuma da gani Hutu ya zauna mashi sosae, lek'o da fuskar shi yay da d'an murmushi yace "Barka dae yan graduation" Haulat ce ta tsaya ita kuwa Fatuu gaba tay abunta itama d'an murmushin tay tace mashi yauwa yace "I just passed sai na gan ku shine nace bari mu gaisa" tana murmushi tace sun gode d'an juya kanshi yay ya kalli Fatuu da tay gaba yace "ita friend en naki bata gaisawa da wanda bata sani bane" juyawa tay itama ta kalli Fatuu dake ta tafiyarta kafin ta maido idon kanshi tace "kusan hakane kasan ba kowa ake yadda dashi ba yanzu" yar dariya yay yace "hakane nima bai kamata in tare ku a bakin titi ba, in ba damuwa ki bani no d'in ita friend d'in taki sai in zo gida mu gaisa da ita" d'an jimm Haulat tay sai kuma ta juya ta k'ara kallon Fatun tunani ta shiga yi tasan ko ta bashi no d'in Fatuu aikin banza ne don ko ya kira ma ba saurararshi zatai ba don sam ta haramtawa kanta yin saurayi, dubara ce ta fad'o mata ta juya tace mashi "kayi hakuri ko na baka no d'in ba zatai maka wani amfani ba don ita d'in akwae sa rana a kanta dama da mun gama Makaranta za'ai bakin ta kuma gashi mun gama d'in to ba lalle ta saurare ka ba" d'an buda ido yay sai kuma yayi murmushi yace "Ok bansani ba ne amman ba wani abu Nagode sosae" tana murmushi tace to har zata juya yace su zo ya kai su subar tafiya cikin rana, juyawa tay da niyyar yi ma Fatun Magana kawai sai ta ga har ta tsaida masu Keke Napep kallon shi tay tace yayi hakuri ta riga ta tsaida masu abun hawa yace to ba matsala tace mata yana mata fatan Alkhairi Haulat d'in ta amsa da to daga haka glass din ya d'aga ita kuma ta tafi, lokacin da ta k'arasa Fatun har ta shige cikin Napep d'in itama sai ta shiga dama ita suke jira mai Napep d'in ya tambayi inda zai kaisu Haulat tace mashi Barhim sabuwar Abuja ya ja suka tafi, kallon Fatuu tay da yake mai Napep d'in ya kunna Wak'a tasan ba jin su zai ba tace "Wannan Mutumin fa don ke ya tsaya har cewa yay na bashi no d'in wayar ki sai ya kira tunda baki tsaya ba amman nasan ba lalle ki saurare shi ba shiyasa nay mashi k'aryar an kusa bikin ki" d'an ta6e baki Fatun tay tace "gwara da kika ce mashi hakan ya kama gabanshi don kuwa ba sauraran nashi zan yi ba" idon Haulat a kanta ta d'an girgiza kai tace "Wai Fatuu miyasa kike korar samari ne, da wuya mu fito ba'a samu wanda ya nuna yana son ki ba Amman sam kin k'i ki fara saurarar kowa komi kice karatu to karatu yana hana ayi saurayi ne ko kuwa zaki ta karatun ne ba ranar da zaki aure??" wani kallon gefe tay ma Haulat d'in ba tare da ta ce mata komae ba Haulat taci gaba "nasan duk Saboda Ya Haisam ne baki saurarar kowa ba wani abu ba, zuwa yanzu yakamata ki cire son shi kwata kwata a ranki kema ki tsaya ki samu wanda zaki rayu tare dashi kada kita korar Mutanen kirki ba tare da kin sani ba, ki yi hakuri in na 6ata maki rai amman gaskiya nike fad'i maki kaman yadda ya samu abokiyar rayuwa wadda yanzu na tabbatar bata rasa juna biyu kema ki fara tunanin sama ma kan ki wanda zaku rayu tare ki hak'ura da ya Haisam don matuk'ar yana ranki to fa bazaki ma kanki abunda ya dace ba shawara ce nake baki a matsayina na mai son cigaban rayuwarki" a hankali tace mata ta gode kawae don kuwa son Ya Haisam na nan a cikin ranta ta rasa ta yadda zata cire shi, suna haka wak'ar da mai Keke Napep d'in ya kunna ta k'are wata ta shiga ta Labarina baitikan wak'ar suka fara kaman haka
๐ถ๐ถDawo bamu gama zama ba, dama ba mu raba jini ba, wai nikam mai naiwa kauna bata mi ni wuri ba labari da kai ne dawo bamu gama zama_๐ถ๐ถ
_๐ถ๐ถBan gani duhu haka na kwana, yanzu ma hakan na ishi rana, damuwa ta damu da gani na gashi ta raba ni da wani na, mi nai wa kauna ne guna bata iya zama ba, yafe man in na mutu so ne bai gama salo ba...๐ถ๐ถ_
Natsuwa sukae suna sauraran wak'ar dama Fatun kusan kullum sai ta saurareta ji take tamkar ita a kai ma wak'ar lokaci guda kwalla suka fara zubo mata sharrr da sauri Haulat tace ma mai Napep d'in "Malam don Allah in ba damuwa ka canja wata wak'ar" yace "yanzu kuwa Hajiya ai dama don jin dad'in ku muke sawa bari a canja maku" ya kai hannu yana yana k'ok'arin canzawa ana fara taken wak'ar Fatun ta saki d'an murmushin takaici don kuwa itama wak'ar kamar dae waccan ita wannan ma jinta take kaman ita ta raira ma kanta ita ta hamisu breaker ce mai taken ' _so gaskiya ne yadda yay min ni na gane, in dai amo ne kanshi ban daina shi zancen gaskiya_๐ถ๐ถ da sauri Haulat tace "Don Allah malam ka kashe wak'ar duka ta cika mana kunne" wannan karon juyowa yay yana niyyar yi mata Magana idonshi ya sauka kan fuskar Fatuu yana ganin kwalla yay d'an murmushi had'i da girgiza kai ya juya ba tare da ya ce komae ba a cikin ranshi ya ayyana ta Kamu da mugun ciwo ya kai hannu ya kashe gaba d'aya kaman yadda Haulat d'in ta buk'ata, suna gab da isa gwaggo ta kira Fatuu bayan ta d'aga ta tambayeta har yanzu basu taho bane don d'azun sun yi waya lokacin da suka gama Exams, ce mata tay gasu nan sun kusa isowa tace to ta taho harda Haulat ta amsa da to, dai dai gefen shagon Amadu dake a rufe mai Napep d'in ya tsaya suka fito bayan sun biya shi suka nufi cikin gidan mai Napep d'in ya bisu da ido a ranshi yake ayyana "Gata dae tubarkallah ko wani ya yaudareta ko kuwa wani take so ta rasa shi Allah kadae ya sani" daga haka yaja ya tafi, suna shiga cikin gidan suka jiyo Wak'a na tashi ta happy graduation Fateema Zarah a cikin falo da sauri suka nufi falon suna shiga sukae turus a bakin kopar da tsananin mamaki akan fuskokinsu gaba d'aya an k'awata falon da flowers da balloons cards da sauransu kaman dae irin decoration d'in birthday a bangon dake kallon Mutum in ya shiga an had'a rubutun Happy Graduation Fateema Muhammad Ardo and Haulat is'haq a tsakiyar d'akin kuma k'aton cake ne saman table da sauran abubuwan ci, da gudu Fatuu ta nufi gwaggo dake tsaye tana masu dariya ta kankameta cike da farincikin surprise da suka mata sakin ta tay ta nufi Kawu Amadu dake gefe shima ta rungume shi sai kuma ta fashe da kuka duk suka sa dariya Amadu ya hau goge mata kwallan yana fad'in yau ranar Murna ce don daga yau ne ta hau matakin cikar burinta ta jinjina mashi kai yace yana mata fatan nasara cikin muryar kuka tace ta gode haka Haulat ma saida gwaggon ta rungumeta duk suka yi mata fatan sa'a tana ta dariya tay masu godiya, ci gaba da celebration d'insu sukai su hud'u gwanin burgewa Fatuu sai rawa take da wak'arta da aka yi mata ba tare da ta sani ba hakan aikin Amadu ne yaba wani abokin shi yay mata kuma tayi dad'i sosae daga baya Fatuu da haulat suka yanka cake Amadu na masu Videos da iPhone d'in wani abokin shi da ya aro Saboda hakan, sosae su kae hotuna kuma sunyi matuk'ar yin kyau sai bayan Magrib sannan Fatuu ta raka Haulat bayan an d'ibar mata komae cake d'in ma mai yawa aka bata tanata godiya, Fatuu na dawowa tasa Kawu Amadu ya tura mata pics d'in da videos ta shige d'aki ta fara aikin d'aura su a Status kan kace mi aka fara mata comments na taya murna wasu ma duk suka d'auka suma suka d'aura sai farinciki Fatuu ke yi jin yadda ake ta yabawa har wasu Friends d'insu na cewa shine ko a gayyace su, tana cikin duba wad'anda suka d'aurata kwatsam taci karo da na Haisam da mamaki ta bud'e hoton farko wanda akai mata ita kadae a gaban rubutun cikin falon tayi dariya duk dimples d'inta sun lotsa sosae a k'asan shi ya rubuta 'Wishing u success in ur Exams beloved sis Zarah' na gaba kuma wani d'an short video ne tana ta dariya had'i da yin Magana sam bata ma san anyi mata shi ba can kuma ta tura yankin cake a baki duk ya 6ata mata gefen baki kai da ganinta a Videon zaka fahimci tana cikin tsantsar farinciki sosae tasa Dariya da ta ga Videon wato tun kafin Amadu ya turo mata ya tura ma Haisam, tana cikin hakan kuma sai ga kiranshi ta d'auka ta gaishe dashi bayan ya amsa yace mata congratulations tace mashi thanks waya suka cigaba da yi wadda rabon da su jima suna yin waya har ta manta har ta tambaye shi Fanan yace tana wurin aiki da yake su can rana ce tace shi yana ina yace shima yana wurin aiki k'arshe ma cewa yay bari ya maida Video call tace to dama akwae haske d'akin koda ya maida tana ta sakin murmushi shima haka suka ci gaba da yin firan har yana nuna mata Office d'inshi na can ta yaba sosae da had'uwar shi don irin manya Office d'in da take gani ne a Fina finan turawa.
Bayan sati d'aya da yin candy d'in su Haulat tazo gidan ta sanar da ita zata tafi Nijar kuma bazata dawo ba har lokacin bakin ta dama a can za'ayi, Fatuu bata ji dad'i ba har tana ce mata ba sai bikin ya kusa ba sannan zata tafi tace itama tayi tunanin hakan to amman innarsu tace taje ta zaga dangi kafin bikin don ta dad'e bata je ba, Ranar Juma'a da zata tafi har tasha Fatuu da Kawu Amadu suka rakasu da yake da yayanta Usman zata tafi suna ta kuka suka rabu Fatuu tace mata sai sun zo biki, Allah sarki Haulat k'awar Arziki.
Satin Haulat d'aya da tafiya lokacin ya kama satinsu biyu da gama Makaranta ran Asabar Fatuu ta dawo daga islamiyyar safe tana tafe tana ta tunane tunanenta da suka zame mata jiki don yanzu wani irin kad'aici ne ke damunta, ba Haisam ba Haulat gashi Hajiya har yanzu bata dawo ba balle ta d'an rink'a zuwa can a haka har ta k'araso gida tana shiga tun a zaure ta jiyo Muryar gwaggo cikin harshen fulatanci tana ta fad'a, lokacin da ta k'arasa a tsaye ta ganta gaban kitchen sai kai da kawowa take ga wayar Amadu kange a kunnanta tana yin waya, tsayawa tay tana bin ta da ido hakan ya bata damar jin Maganar da take a lokacin kamar haka "Sam bazan yarda ba wllh! Lokacin da aka bani ita ai ba ace man za'a rabani da ita ba hasali ma kowa ba son ta yake ba anata muzguna mata sai yanzu da aka ga ta zama Mutum shine za'a nuna man iko da ita, to bari kaji bazan ta6a yarda ta dawo ba sai dai komae zai faru ya faru na shirya ma hakan!!!" daga haka ta katse kiran ta juyo a fusace ta mik'a ma Amadu wayar kafin ta wuce d'akinta fuu tana ta kwafa, juyawa Amadu yay ya shige d'akinshi yayin da Fatun tay tsaye jikinta duk yayi sanyi yaushe rabon data ga gwaggo na fad'a haka sam ta kasa fahimtar inda zancen da ta ji tana yi ya dosa, har zata nufi d'akinta sai kuma ta juya ta nufi d'akin Amadu lokacin data shiga yana zaune a gefen katifa yayi jigum da alama shima abun ya dameshi sosae, d'aga kai yay ya kalleta ganin hakan yasa ta duk'a tana kallonshi itama, a sanyaye ta tambayeshi abunda ke faruwa, farko shiru yay mata yana dai ta kallonta saida ta marairaice mashi kaman zata sa kuka tana had'ashi da Allah sannan ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi yama rasa ta ina zai fara ganin dae ta zuba mashi ido ne yasa yay k'arfin halin cewa "Dama Baffan ki ne ya kira yace zai zo ya tafi dake wai Ard'o ya bada auren ki" wani bugu k'irjinta yay ta zaro ido tana kallonshi kafin cikin sark'ewar murya tace "y...ya bada au..aurena, ni...d'in???" Kai ya d'aga mata alamar eh, a razane tace "Waye ya ba aurena??" Shiru ya d'anyi shima duk damuwa ta bayyana akan fuskarshi can yace "Chairman Alhaji Lawal ya nema ma d'an shi wai Dr Khalid Auren ki tun lokacin da muka je shekara ukku da ta wuce shine ma yace a barki sai kin gama Secondary don da tun lokacin Ard'on yace ya bashi................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._
*ASM Bk2023*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........bin Kawu Amadu kawai take da ido da alama tayi mutuwar zaune abun kaman a mafarki take jin shi wai ita za'a ma Aure kuma ma a garinsu, shima Kawu Amadun zugudum yay yana kallonta can ta yunk'ura da k'yar ta mik'e hannunta ruk'e da jakarta ta fita daga d'akin ta nufi d'akinta har wani Jiri Jiri take ji a haka ta isa tana shiga ta aje jakarta a gefe ta nufi bakin gado ta zauna sai zare ido take sam tama rasa tunanin da zata yi can zuciyarta ta fara tunano mata da Mutumin wato wanda ta iske a fadar Ard'o har ya rink'a mata tambayoyi da turanci ashe da biyu yayi mata hakan kenan,wai d'anshi Dr Khalid za'a aura mata! haka ta dingi maimaita sunan a cikin ranta tana haka wayarta dake cikin jakar islamiyya ta fara ringing da k'yar ta yunk'ura ta nufi jakar ta fiddo wayar kafin ta koma bakin gadon sai lokacin ta kalli screen d'in taga mai kiran nata, My Lovely Dad shine sunan da ta gani wato Baffan ta ne kenan, d'an jimm tayi cike da fargaba kafin hannu na rawa ta d'aga kiran ta kara a kunne kafin tayi Magana daga can yace "Inna wuro" har saida gabanta ya d'an fad'i kafin a hankali tace "ah Baffa",
"Kin dawo daga Makarantar kenan Amadu ya fad'a man kina can" wani abu ta had'iya jin muryar shi ta canza sosae a hankali tace mashi eh ta dawo ta gaida shi ya amsa, shiru ya biyo baya daga ji yana son mata magana ne amman ya kasa, can tay k'arfin halin cewa "Baffa wai da gaske an bada ni za'a man Aure?" D'an jimm yay kafin ya fara Magana "Wallahi tallahi inna wuro wannan duk aikin Ard'o ne ni sam bansan da Maganar wai ya bada ki ba sai wata guda da ya wuce lokacin kuna cikin yin jarabawa shine ya kira ni yake sanar dani wai in fad'a maku ya bada ke ga yaron chairman kuma ya sanar mashi kun kusa k'are karatun naki don haka kuna gamawa in zo in d'aukko ki, Wllh inna wuro ranar banyi bacci ba Saboda tashin hankali ban k'ara shiga damuwa ba sai bayan da kuka gaman ya kira ni yace ai Chairman ya fad'a mashi kun k'are don haka in zo in d'aukko ki ranar gwuiwa na a k'asa na rokeshi da a kyale ki karatu kike son yi in kika yi za'a amfana sosae amman da bud'ar bakin shi sai cewa yay ina kokarin nuna mashi iko da ke abunda wani bai ta6a yi mashi ba, duk yadda na so in fahimtar