Author : Hafsat Bature Category : Action Novels
ta kira sunan shi ya kalleta kaman zata sa kuka ta mik'a mashi wayarta tace " gata kaci gaba da amfani da ita sai ka bani taka" waro ido yay baki bud'e alamar mamaki kafin yace "a'a ki bar abun ki can ma ai zaki iya amfani da ita" da sauri tace "ai shiyasa nace ka bani taka kaga can bama wani Network ke da akwae ba mai kyau ko naje da ita bazata yi man amfani ba sosae kaman yadda kai zata maka don Allah ka amsa" ta k'arasa hawaye na zubo mata hannu ya kai yana goge mata yana cewa tayi shiru zai amsa, dama ta goge abunda zata goge tace ya tura mata abubuwan da ta bari kafin su tafi yace to ya amshi wayar ya d'auki d'ayar jakar da yazo d'auka ya fita, gari na fara wayewa suka fito don tafiya har lokacin Fatuu bata ga fuskar gwaggo ba lokacin da ta shiga don yi mata sallama a zaune kan abun salla ta isketa ta d'ukar da kanta k'asa, duk'awa tay gefenta ta gaishe da ita ta d'aga mata kai kawae shiru Fatun tayi can kuma tay k'arfin halin cewa "G...gwaggo zamu tafi" farko shiru tay sai kuma murya a disashe taji tace "Allah ya tsare hanya yasa Alkhairi Amadu zai kawo maki sak'o" daga haka tay shiru sosae gaban Fatuu ya fad'i don daga jin muryarta kuka tayi cikin rawar murya Fatun tace "to gwaggo ke bazaki zo ba?"shiru tay mata ta k'ara tambayarta nan ma tay mata shiru kawae sai tasa mata kuka tana fad'in "Don Allah gwaggo ki yi hakuri ki yafe man kar ki ce bazaki zo ba, kowa in za'a mata aure Mahaifiyarta na mata fad'a da nasiha ni waye zai man in kika k'i zuwa??" sai lokacin ta d'ago idanunta sun yi jawur cike tabb da k'walla tay d'an guntun murmushin takaici kafin tace "ga yadikkon ki ga kuma wasu iyayen naki cike da gida Fatuu" sosae take kuka tana rok'onta ita dae don Allah ta zo suna cikin haka Hajiya ta shigo gidan da sallama jiyo kukan Fatun yasa ta nufi d'akin gwaggon tana fad'in "koke koken ne har yanzu ba'a gama ba an bar mutane nata jira a waje tafiya bata kusa ba" d'aga labulan kopar tayi ta shiga ganin yadda fatun ke kuka ta tambayeta abunda ya faru cikin kuka ta sanar mata, wani kallo tay ma gwaggon rai 6ace tace "haba Dije wai miyasa kike haka ne don Allah, yarinya zata tafi baza kuyi rabuwar Arziki ba ki faranta mata rai sai ki fad'a mata abunda zaki tada mata hankali haka" girgiza kai gwaggon tayi tace "nifa ban ce mata bazan je ba ita ta yanke hukunci" Hajiya ta kai hannu ta mik'ar da Fatun tsaye tana ce mata tayi shiru tama isa tace bazata je bikin ba suna nan zuwa harda ita sai lokacin taji sanyi a ranta suka nufi hanyar fita tana ta waiwayen gwaggo da tayi zaune bata da niyyar mik'ewa bare ta rakata, waje suka fito dama ita kawae ake jira Hajiya ta kaita har bakin Motar tace ma Baffanta gata nan su tafi kar suyi dare a hanya cike da girmamawa ya amsa mata da to ya bud'e ma Fatuu kopar Motar ta baya ta haye ta lek'o da kanta tana kallon su Tk da Amadu da Saude harda wasu daga cikin makwabta da suka fito sai kuka take Amadu ma ya kasa jurewa saida ya yi kwalla da k'yar ya matsa ya mik'a mata wayar tashi cikin kuka tace "Kawu Amadu zaka zo ko?" Da sauri ya jinjina mata kai ya kamo hannunta guda yace "in sha Allahu tun kafin bikin ina nan zuwa ki yi hakuri don Allah ki kwantar da hankalin ki kin ji" kai ta d'aga mashi lokacin Baffanta yace ma Amadu ya rufe mata kopar yace to ya saki hannunta ta maida kan ta ciki ya rufe sannan ta sake lek'o da kan ta windown kopar, zagayowa Baffanta yay ya yi masu sallama ya k'ara ma Hajiya godiya duk suka yi masu Allah ya tsare ya kai su lafiya ya amsa masu daga haka ya juya ya nufi gaban Motar ya shige shima Abokin nashi wanda shine driver d'in da zai tuk'a Motar ya lek'o yay masu sallama daga haka ya maida kan nashi ya tashi Motar wani bugu gaban Fatuu yay ta d'aga hannu tana masu bye bye tana ta kuka suma duk suka d'aga mata Tk da Saude ma duk kasa jurewa su kai sai da suka zubar da kwalla Motar na fara tafiya kawae sai ganin fuskar gwaggo tay ta lek'o sosae ta d'aga mata hannu ta kira sunanta da k'arfi "Gwaggo!!!" hakan yasa duk aka waiga ana kallon gwaggon don ba wanda ya lura da ta fito da k'yar ta d'aga ma Fatun hannu guda itama tay mata bye bye..........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
*ASM Bk2027*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
...........Saida Motar ta bar layin sannan duk suka juya Hajiya ta kalli Gwaggo ganin hawaye a fuskarta ta shiga bata baki kafin suka wuce gida ita dasu Saude Amadu kuwa tsaye yay duk jin jikin shi yake ba dad'i yana ganin gwaggo ta koma ciki shima ya shige gidan ya nufi d'akin shi ya kwanta, akai akai yake kai hannu yana share kwallan dake gangaro ma shi, gwaggo na shiga d'aki ta haye gado tasa kuka mai cin rae taci guri in Allah ya nuna mata auren Fatuu sai gashi komae ya juye zata yi aure ba tare da tana farin ciki da hakan ba, sosae ta sha kuka daga baya ta lallashi kanta ta yi shiru. Tun da suka hau hanya take ta kuka Baffanta da Abokin nashi nata bata Hak'uri har dae ta yi shiru sai dae kwalla basu daina zubo mata ba tana kai gefen gyalen ta tana gogewa daga baya bacci ya kwashe ta, sosae Baffanta yaji dad'in hakan don ba k'aramin ta6a mashi zuciya kukan da take ke yi ba, sai da suka tsaya Kano sannan ta farka suka siya abunda zasu ci aka mik'a mata nata kamar bazata ci ba baffanta yace tayi hak'uri ta ci idanunta duk suyi luhu luhu ba yadda ta iya dole taci don tana jin yunwa Bayan sun d'an huta suka sake d'aukar hanya duk garin da suka tsaya sai Baffanta ya siya mata abu wani ta ci wani ta k'i ci, Alhamdulillah sai Bayan la'asar wuraren karfe biyar na yamma suka isa tunda suka iso jumeta Fatuu ke jin tamkar za'a kaita kurkuku sai ma da suka isa rugar kukan zuci kawae take, Motar na tsayawa gaban gidan Kamalu da su Mino dake ta dakon isowar su suka nufo Motar cike da farinciki Baffan Fatun ya zagaya ya bud'e mata kopar ta fito sai murnar ganinta ake ita kam ta kasa yin ko murmushi ganin yanayinta yasa Kamalu da Mino suma d'an shiga damuwa baffanta yace su shiga daga ciki Mino ta kama hannunta shi kuma kamalun yace ya tsaya su sauke kaya, bin Mutane da ido kawae ta rink'a yi ana mata sannu da zuwa kan kace mi labarin zuwanta ya isa ko ina a cikin gidan harda uban kayan da aka zo dasu yan gidan duk aka fito wasu suka lek'o ta Katanga ganin kwakwaf ita dae kallon su kawae take tamkar yau ta fara ganin su, kafin su isa sashen su sai ga yadikko ta fito cike da farinciki ta zo ta rungume Fatun tana mata sannu da zuwa lokacin da ta d'agota suka had'a ido kawae sai ganin kwalla tay ta zubo mata da sauri ta Sunna kai k'asa sosae jikin yadikko yay sanyi ta kama hannunta suka nufi ciki, an gyara sashen na su sosae har da su fenti haka d'akin yadikkon an maida shi ciki da falo har da bathroom a cikin uwar d'akan, zaunar da ita yadikko tay kan kujera ta zauna gefenta haka su Mino ma duk suka zazzauna suna kallon ta ta sadda kai k'asa, kan kace mi d'akin ya cika da yara harda wasu daga cikin Matan gidan suka shigo yi mata sannu da zuwa suna ce ma yadikko ashe Amarya ta iso ita kuma tana bin su da eh kawae don tasan yawanci duk gulma ce ta kawo su, sai Bayan wani lokaci mutanen suka lafa yadikko tace ma sauran yara suje su k'yaleta ta huta bayan duk sun fita ya rage saura yan'uwan Fatun kawae cike da nuna damuwa yadikkon tace "Fatuu ki yi hakuri kin ji, kowa yasan ba'a kyauta maki ba wllh duk bamu ji dad'in wannan abun ba ba yadda zamu yi ne da muka nuna bamu so baki ga halin da muka shiga ba akai ta mana wulak'anci da Maganganu duk aka tsangwame mu Baffan ki har ciwo yayi...." Dakatawa tay tana goge kwallan da suka taru haka ma su Mino duk kwalla suke zubar wa a hankali Fatun ta d'ago ta kalli yadikko cikin rawar murya tace "ba komae ki daina kuka ai gani na zo sai suyi man Auren" kamata tay ta rungume tana mata godiyar taimakon su da tayi ta amince da wuri wanda duk basu yi tunanin hakan ba ta tambayeta har yanzu gwaggo fushi take don baffanta ya sanar da ita ta d'au ki zafi sosae Fatun tace mata a'a ta hak'ura tana nan zuwa sosae yadikko taji dad'in hakan, d'agota tay tace bari ta zubo mata Abinci ta barta da yunwa ga gajiyar hanya Fatun ta mik'e tace band'aki zata shiga da sauri Mino ta mik'e tana nuna Mata cikin d'aki tace an yi sabo a ciki suka nufi cikin tare, harda Alwala tayo Bayan ta fito ta kabbara salla a cikin uwar d'akin lokacin Baffanta da Kamalu suka shigo d'akin a Falo suka tsaya baffan ya tambayi Mino inna wuron ta kwanta ne tace mashi tana salla ne ya nemi wuri ya zauna Kamalu ma ya zauna lokacin yadikko ta shigo ta jere ma Fatun kayan Abinci kafin ta zauna a gefe tana ma Baffan ya gajiyar hanya Kamalu ya shiga basu labarin uban kayan da Fatuu tazo da su yace yawanci ma shi duk bai san mi ake dasu ba wasu dae ya san su a cikin film harda wanda ake gasa kaji duk su kae yar dariya kafin kuma shiru ta biyo baya can kuma Baffan yace ma yadikkon kayan na a d'akin shi aka kai su da d'akin Kamalu za'a sa to kuma kar a lalata wani abun tunda bashi kadae bane a ciki tace hakan yayi suna haka Fatuu ta fito duk suka d'aga ido suna kallonta ta k'araso da d'an murmushi zata zauna a k'asa kan leda Baffan yace tazo ta zauna kusa dashi yadikko tace ai Abinci zata ci yace to, saida ta tambaye ta abunda zata ci tace duk wanda ta zuba mata tasa mata burabusko tace in ta cinye sai a k'ara mata wani Abincin ita dae shiru kawae tay, Sam ta kasa sakin jiki ta ci Abincin sai dae tai ta juya cokali baffanta ne da ya kula da hakan yace ta daure ta samu ta ci tace to ta d'an k'ara tsakura kafin ta ture tace ta k'oshi, yadikko tace ai bata ci komae ba tace bata jin dad'in bakinta ne, fura ta zuba mata tace ta daure ta sha zata ji k'arfin jikin tace to, ba laifi ta sha da d'an yawa suna son suyi fira da ita saidae kowa bai cikin yanayi mai dad'i ba kamar ganin yanayin Fatun duk sunyi jigum jigum sai jefi jefi suke Magana daga baya Baffanta da Kamalu suka tafi yin salla suma suka Mik'e don su yi, Bayan sun gama sallar ne su Aysha suka matsa ma yadikko kan tazo ta ga kayan da aka zo dasu har saida ta mik'e ta bisu, koda taga kayan kitchen d'in tsananin mamaki ne ya kamata don ta san ba kananun kud'i aka kashe ba don kuwa ta ta6a yin aikatau a gidan wasu yan gayu a Abuja duk ta san amfanin kayayyakin yan gidan ma duk suna ta zuwa suna gani tuni labarin irin kayan da aka zo da su ya kai ma su Yaya, Bayan yadikkon ta koma d'aki ne ta zauna a gefen gado da d'an murmushi tace ma Fatuu dake zaune kan sallaya "ko zaki je ki gaisa da su Yaya nasan sun san da kun iso tuni" tura baki Fatuu tay ta juyar da kanta wani irin haushin Yayar take ji don ta san harda ita aka had'a komae, ganin bata ce komae ba yasa yadikkon k'ara mata Magana a hankali ta juyo tace mata ta gaji ba yanzu ba sai ta huta, d'aga mata kai kawae tayi itama gudun Magana ne yasa tace taje su gaisan don tasan sai anyi tsegumin rashin zuwan nata ta gaishe dasu, shiru suka d'an yi kafin yadikkon tace "naga uban kayan kicin gaskia gwaggo ta kashe kud'i ba kad'an ba, ni baffan ki ce man yay dubu d'ari ya tura har ina cewa sun yi kad'an don jere ake ma kicin sosae a birni kuma kayan suna da kud'i to sai yace man bai gama biyan kud'in kayan gado da kujeru ba don shi kad'ai aka bari da hidimar Ard'o ne kawae ya bashi shanu guda d'aya ya siyar yayi maki kayan d'aki sai kuma kud'in sadakin ki dubu 100, shi kuma so yake yayi maki kaya irin na yan birni shiyasa duk ya tattara kud'in shi ya biya don kayan fin rabin miliyan ne za'a maki" shiru Fatun tay yayin da tausayin mahaifin nata ya k'ara kamata,
"Wai nikam Fatuu ina Ya Handsome d'in ki??" Har saida kirjin Fatuu ya d'an buga damm jin tambayar da yadikkon tayi mata, shiru ta d'an yi sai kuma a hankali ta kalleta ganin tana kallon ta alamar jiran amsa yasa tace "Ya yi aure" dan bud'a ido yadikko tay kafin tace "Allah sarki yaushe?" tace "kusan wata ukku yanzu" rausayar da kai yadikko tay kafin ta sake cewa "a nan Katsina?"
"A'a basu nan k'asar suna America" da k'yar ta bata amsar ta d'ukar da kanta k'asa jin kwalla na niyyar zubo mata girgiza kai yadikko tay tace "Allah bai k'addara mijin ki bane don ni da nayi tunanin son ki yake wllh koda kika ce man ba haka bane wancan lokacin kawae na jiki ne na zata yana son ki ne ya bari sai kin k'ara girma don hidimar da yake tayi yawa yawanci zaki ga irin hakan ba hakanan mutum ke yi ba da dalili ashe shi don Allah yake yi" a sanyaye Fatun ta d'ago tace "shine ma ai ya turo kud'i aka siya wancan kayan" hannu yadikko tasa ta ruk'e ha6a tace kai don Allah Fatun ta d'aga mata kai alamar eh,
"Kai amman dae wannan mutumin d'an Arziki ne wllh ni bamma ta6a jin mutum mai Alkhairi irin nashi ba, ace daga makwabta ka ya dinga hidima haka ni fa wllh nayi mamakin kayan can don ko banza sai sun yi miliyan ko ma fi" dakatawa tay tana maida numfashi kafin da d'an murmushi ta dafa kafad'ar Fatun tace "amman da gaske bai son ki kuwa?" D'agowa Fatuu tay ta kalleta idanunta sun k'ara sauyawa a hankali tay shaking kanta tace "bai ta6a so na ba, dama yana tare da wadda ya auran yar uwarshi ce" cike da zolaya yadikko tace "to amman ke nasan ai kina son shi ko?" bin ta da ido Fatuu tay ta kasa ce mata komae kawae sai ganin kwalla yadikko tayi tana zubo mata zaro ido tay Fatun ta kifa kanta a jikin kafafun yadikkon ta sa kuka, wani irin sanyi jikin yadikkon yay ta kai hannu ta d'ago ta ta zaunar da ita gefenta ta rungumo ta ta gefe cikin kuka Fatun ke fad'in "ina son shi sosae yadikko nayi tunanin shima yana sona ne ashe ba haka bane bai ta6a so na ba ina ji ina gani yayi auren shi ya tafi ya barni" har idanun yadikko sun ciko da k'walla ita dama tayi mamakin saurin amincewa da Fatun tay ai mata auren ashe ashe ciwo ne da ita a zuciya sosae ta bata tausayi ta shiga rarrashinta tana bubbuga bayanta tace "kiyi hakuri Fatuu na fahimci yadda kike ji ki bar ma Allah komae in har shi rabon ki ne Allah ya k'addaro zaku rayu matsayin mata da miji ko ba dad'e ko ba jima hakan sai ta faru don in dae abu rabon ka ne kana zaune zai iske ka har inda kake har kai ta mamakin yadda hakan ya kasance wannan kad'an daga ikon Allah ne don ni kaina shaida ce na so Mahaifin ki kamar mi muna cikin soyayya aka ce an bayar dani ga wani abokin mahaifina ina ji ina gani aka man Auren dole kaman zan yi hauka naje gidan shi sam ba kwanciyar hankali ga wulak'anci dama shi bai d'auki mace a bakin komae ba tamkar riga haka yake canja mata shima Baffana harda kwad'ayi yasa ya bashi aure na k'arshe ya yi man sakin wulakanci lokacin yunwa duk ta k'arar dani abun bak'in cikin lokacin Mahaifin ku har yayi auren shi koda na tuntu6e shi Bayan na gama idda sai ya bani hak'uri ya nuna man bai da ra'ayin mata biyu, ya dae fad'a man haka ne kawae amman nasan kawae ya daina so na ne dama na samu labarin irin son da yake ma matarshi wato mahaifiyar ki gata yar birni mai ilimin boko a lokacin ne na samu aka man hanya na tafi aikatau Abuja nayi nisa da garin to ashe Allah bai kaddaro zasu rayu tare tsawon lokaci ba wllh lokacin na girgiza da jin labarin mutuwarta don lokacin ni nama fidda ran auren nashi