Advertisements
Chapter 38 Reading Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Hafsat Bature Category :  Action Novels

Chapter   38 / 38

111K to 111.9K   out of 111.9K words

tana bacci hakanan ta ji kamar bata kyauta mata ba in ta tafi ba tare da ta sanar mata ba, a hankali ta jingine trolley d'in ta nufi gadon ta hau a hankali tasa hannu ta fara tashin ta da yake haulat bata da nauyin bacci a nutse ta bud'e idanunta tana ganin Fatuu a gabanta ta yunk'ura da sauri da alamar mamaki akan fuskarta tace "wai har Asuba tayi kin ma yi salla kenan" a hankali Fatuu ta girgiza mata kai murya k'asa k'asa tace "Asuba bata yi ba Haulat" ganin yadda tay Maganar yasa itama Haulat yin k'asa da murya ta tambaye ta miya faru, shiru ta d'an yi tana kikkafta ido kafin tace "Gida zan koma" cikin rashin fahimta Haulat ta sake tambayar ta wane Gidan tace mata Katsina waro ido Haulat tay baki bud'e jin abunda tace Fatuu taci gaba da cewa "Haulat ban son Auren nan, ban so gwara in gudu kawae in dae aka ga bana nan ai dole a fasa" a razane Haulat tace "Amman Fatuu baki ganin lokaci ya k'ure saura fa yan kwanaki a d'aura auran ki miyasa tun farko baki nuna baki so ba sai yanzu" kuka ta fara yi k'asa k'asa tace "Saboda Baffana ne Haulat Kawu Amadu baya fad'i maki ba" kai ta d'aga mata tace eh ya fad'i mata taci gaba da fad'in "Yanzu ban son auran nan Haulat....." Katse ta tay tace "amman Fatuu kina ganin abu ne mai sauk'i fasa auran nan don kin gudu, ni a ganina kawae zaki jawo wata matsalar ne ki k'ara jefa su Baffa cikin wani tashin hankalin" Fatun tace "ai dama gwaggo bata so dalilin hakan ne yasa take fushi da ni don na k'i goyon bayanta nace na amince aman auren yanzu in naje nasan zata yi wani abun a fasa" shiru Haulat tay tana kallonta kawae ta lura ganin hakan take abu mai sauk'i can ta dafata tace "Fatuu ni a ganina ki hak'ura kawae tunda har an zo nan....." Cikin kuka tace "Allah bazan Aure shi ba in ba haka ba mutuwa zanyi don baki san wanene za'a aura man bane yasa kike cewa in hak'ura, Mashayi ne fa mai neman mata kuma..." Nan ta kwashe komai harda gidan gona da ya kaita da Maganin bacci da ya saka mata a lemu harda abunda yay mata jiya da yamma da ta dawo ta isketa ta zo, hannu Haulat tasa ta rufe bakinta cike da Al'ajabi kafin ta cire a sanyaye tace "Shikenan Fatuu in dai kina ganin gwaggon zata iya yin wani abu da zai sa a fasan kije" da sauri ta goge kwallan fuskarta ta juya zata sauka daga gadon Haulat tace "Amman Fatuu ni fa?" juyowa tay ta kalleta tace "ba sai ku dawo da kawu Amadun ba" gyad'a kai Haulat tay sai kuma ta sake cewa "amman lafiya lau zaki iya tafiya dare fa ne" jinjina mata kai Fatuu tay tace zata iya lafiya lou ba abunda zai sameta in sha Allahu daga haka ta idasa sauka ta nufi hanyar fita idon Haulat a kanta tana kallon ta cike da tausayi har ta kai hannu zata d'auki trolley d'in taji muryar Haulat ta kira sunanta juyawa tay ta kalleta ta saukko ta nufo inda take tana zuwa tace "bari mu tafi tare" da mamaki tace "amman haulat jiya fa kuka zo ko hutawa sosae baki yi ba ki kwanciyar ki daga baya sai ku dawo" girgiza mata kai tay tace su tafi ba komae har cikin ran Fatuu taji dad'in hakan, Hijab Haulat ta d'aukko ta saka ta maida kayan da ta cire jiya cikin jakarta dama ita kadae ta zo da ita ta d'auka Fatuu ma ta d'auki trolley a hankali tasa k'afa cikin Falon ba kowa sai k'annenta dake ta bacci kan shimfid'a dama cikin d'akin daga ita sai Haulat Yadikko na d'akin Baffa, cikin sa'a suka fito daga cikin d'akin gaban Haulat nata bugawa gaba d'aya a tsorace take suna fitowa Fatuu tay ma Haulat nuni da hanyar bayan gidan a hankali cikin rad'a tace ta can zasu fita bata kopar waje ba...........

*Uhmmmm, shin su Fatuu zasu samu fita daga cikin gidan kuwa? In sun fita zasu samu komawa Katsina? Gwaggo zata saurari Fatuu in sun samu komawar? Za'a fasa auran ko baza'a fasa ba???*

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

********************** ⬇ **************************

********** Ai Hausa Novels ****************

*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.



Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************

*************** Ai Hausa Novels ****************

********************** ⬆ **************************

38 / 38