Author : Hafsat Bature Category : Action Novels
ta ta gaisa da wasu ne sannan ta rufe yaja suka tafi, Yar tafiya sukae suka k'araso bakin garin daidai k'aton gidan Gonar su ya karya kan Motar ya shige gate d'in farko dake a bud'e mai gadi na d'aga mashi hannu yay mashi horn ba tare da ya tsaya ba, wata tafiyar suka k'ara yi kafin suka sake isowa wani gate d'in na fence ya tsaida Motar ya fita ya bud'e Fatuu nata bin wurin da ido bayan ya dawo yaja suka kutsa ciki, wurin parking ya nufa ya parker Motar ya kalleta da Murmushi yace ta fito, a hankali ta kai hannu ta bud'e Motar bayan ta fita tay tsaye tana k'are ma wurin kallo shi kuma ya koma yaje ya rufe gate d'in tana cikin kallon wurin zuciyarta ta ayyana mata nan ai kaman gidan Gonar su ne dammm kirjinta ya buga sam ita da farko bata gane ba sai yanzu bayan ya dawo in da take tsaye yace mata su shiga yay Maganar yana nuna mata k'aton Flat d'in dake gaban su togewa tay tana bin shi da ido yace "Let go in wife" tana tura baki tace "Amman ai gidan kaman ba kowa" yana murmushi yace waya gaya mata ba kowa bata ga gida bane lafiya lou, shiru tay tana nazari lokacin Maganar yadikko da ta ce har Chairman d'in da Matan shi suna zuwa Hutu nan ta fad'o mata hakan yasa tay tunanin k'ilan da gasken akwae Mutane ganin ta d'aga k'afa yasa yay gaba yace su je tabi bayan shi suka nufi entry d'in, Babban falo ne mai d'auke da duk wani abu da zaka samu a falon yan gayu akwae corridors a 6angaren dama da hagu bin falon da kallo Fatuu tay Khalid d'in ya nuna mata ciki wajen da Sofas suke yace suje, zaunawa yay kan 3 seater ya nuna mata gefen shi yace ta zauna tay tsaye tana kallon shi kafin tace mashi ina wad'anda zasu gaisa d'in yace ta zauna mana ko zai cinye ta ne kaman bazata zaunan ba sai kuma ta d'an d'osana ta zauna a d'arare tana ta kallon shi, yana ganin ta zauna ya fad'ad'a murmushin shi had'i da d'an kwantar da kan shi yace ko ita fa, shiru tay ganin kallon da yake mata yasa fuska a d'aure tace "Wai ina Mutanen?" Hannu ya kai ya shafi sumar shi still da murmushi akan fuskar shi ya fara Magana "Wife ba fa wasu da zaku gaisa I just want us to spend time together yadda zamu k'ara fahimtar juna don naga kin k'i sakin jiki da ni gashi nan da few days zamu zama Couples" wani kallo ta bi shi da shi baki bud'e shi kuma sai faman lumshe mata ido yake can ya fara matsawa wurinta tay zumbur ta mik'e ta kumbura baki a fad'ace tace "shine duk gidan mu bai isa ba sai ka kawo ni nan harda yi man k'arya to ni dae ka tashi ka maida ni ko in tafiya ta tunda nasan hanya!" d'an ta6e baki yay kawae bai ce mata komae ba aikuwa a fusace ta juya ta nufi hanyar fita daga falon saidae tana kaiwa kopar taji ta a rufe gam wani bugu kirjinta yay kenan kulle kopar yay bayan sun shigo, juyawa tay ta kalle shi ko kallon ta bai yi ba hakan yasa jikinta mutuwa ta nufi cikin Falon gefen kujerar da yake ta tsaya idon ta a kan shi kamar zatayi kuka tace "Don girman Allah kai hak'uri ka maida ni gida" bai kalleta ba sai ma cigaba da latsa wayar shi da yake yay kwalla ne suka fara zubo mata taci gaba da yi mashi magiya saida ya mula yasha iska sannan ya d'aga ido ya kalleta cikin kashe murya yace "Don kin ga na damu da ke shiyasa kike taking advantage d'in hakan kina neman wahalar dani ko? Kuma ni kike ce ma makaryaci don kawae na buk'aci mu kasance tare dama ashe har yanzu baki daina rashin kunya ba?" d'an girgiza kai tay tace "a'a kai kace zamu gaisa da wasu ne ai da ka fad'i man gaskiya" kya6e baki yay ya d'age gira yace "in na fad'i maki gaskiya zaki zo ne?" shiru tay tana ci gaba da yamutsa fuska yaci gaba da cewa "Zuwa yanzu yakamata ki d'auke ni kaman yadda na d'auke ki just 6 days ya rage a d'aura mana aure what's there don na bukaci mu kasance tare, da wasu ne ma yanzu tuni sun d'auki kan su matsayin ma'aurata, kodae ban yi maki bane?" Wani wahalallan yawu ta had'iya a halin yanzu dole ta bi shi gudun kada yay mata wani abun ganin daga ita sai shi gashi ya kulle kopa, sake tambayarta yay bai yi mata bane a dabarbarce tace a'a yayi mata yace to ta kwantar da hankalin ta ba wani abu zai mata ba kuma nan gidan da take gani nan za'a kawo ta don haka gidan tane ya nuna mata gefe inda ta tashi yace ta zauna suyi hira tace to sai yaushe zasu tafi yace bada jimawa ba, bata da yadda zatayi dole ta koma ta zauna ya kai hannu kan c-table ya d'auki remote ya kunna masu kallo, bayan ya koma ya zauna yana murmushi yace mata miye labari a hankali tace mashi babu ya tambayi taga kaya akwae abunda babu tace mashi kawae akwae komae duk kuwa da bata ma ga kayan ba, tambayarta yay abubuwan da take so da wanda bata so ta kasa bashi amsa yace shi bari ya fad'i mata ya shiga lissafo mata tana dae ta kallon shi can ya tambayeta wai tana da saurayi farko shiru tay mashi don tsoron bashi amsa take ganin hakan yasa shi cewa in fa tana son ya maida ta gida ta bud'e baki ta rink'a mashi Magana ta girgiza mashi kai a hankali tace bata da shi yana dariya yace ta dai fad'a ne ya za'ai mace kaman ta ace bata da saurayi yace "Ni kin ga inada yan mata saidae ba wadda ta yi man matsayin Matar aure na don duk basu da qualities irin naki" sototo tay tana kallon shi haka ya ci gaba da bata mamaki ta hanyar yi mata kalamai masu d'aure kai har dae ta d'an fara sakewa sai gashi har tana yin d'an murmushi in ya kama can ya mik'e yace bari ya d'aukko masu lemu kishi yake ji itama tana bak'uwa ya barta ba ko ruwa duk da nan d'in gidanta ne, bada jimawa ba ya dawo ruk'e da babbar robar Fanta da glass cups guda biyu ya d'aura su akan c-table ya bud'e ya fara tsiyayawa cike da tsokana yake fad'in "nasan Fulani da son jan lemu" kallon shi kawae take sai kace shi ba bafullatanin bane, bayan ya zuba ko ina ya mik'a mata cup d'aya ta amsa ta ruk'e shima ya d'auki d'ayan ya koma ya zauna ya kai baki ya fara sha, ganin ta ruk'e wanda ya batan yasa shi ce mata ta sha mana ko tsoron sha take bata ga shima ya sha ba jin hakan yasa ta kai cup d'in ta fara sha......
***** *****
Bayan Wani Lokaci, A hankali ta fara motsa idanunta da sukae mata nauyi kafin da k'yar ta idasa waresu kan Pop ceiling d'in da take facing, k'ura ido tay tana kallo kaman mai nazarin wani abu can ta mik'e zaune zumbur da mamaki ta kai idonta saman gadon da take zaune kafin ta bi cikin d'akin da kallo with extreme surprise tunanin abunda ya kawo ta d'akin ta shiga yi da yadda akai har ta kwanta kan gadon, lokaci guda kwakwalwarta ta fara tariyo mata abubuwan da suka faru kafin yanzu, to miya faru da ita ne bayan ta sha lemun da ya bata? ta jefa ma kanta tambaya, wani irin bugu k'irjinta yay da sauri ta kai idonta jikinta ta fara bin kanta da kallo abun mamakin lafiya lou rigarta na a jikinta haka dogon skin tight d'in da ta sa a ciki shima yana nan hannu ta kai ta shafi kanta dake bud'e amman gashinta na a fake shima, kan ta ya gama d'aurewa tana cikin hakan taji an turo kopar da sauri ta kai idonta wurin Khalid ne ya shigo jikinshi sanye da singlet sai wandon jeans d'in da yazo da shi suna had'a ido ya sakar mata k'ayataccen murmushi ya tsaya a jikin kopar ya goya hannuwan shi a kirji yace mata ta tashi kenan, tabdijancan! ido waje take kallon shi murya na rawa tace "Ya akai nazo nan waya kawo ni??" d'an yamutsa baki yay yana lumshe ido yace "kin yi bacci ne and u'w not comfortable there har kina niyyar fad'owa shine na maido ki nan" k'ara zaro ido tay ta furta Kalmar ya maido tan nan da ya fad'i, a kidi'me tace "to ya akai nayi baccin ni bansani ba?" d'an watsa hannuwa yay alamar bai sani ba ta k'ura mashi ido alamar bata yadda ba can murya kaman zata yi kuka tace "Daga shan lemu sai bacci..." dakatawa tay tana tunani can ta tuno da maganin bacci da Kawu Amadu ya ta6a amso mata a rud'e tace "k...ko dae maganin bacci kasa man kai man wani abun???" d'an ta6e baki yay yace "u can check ur body" daga haka ya juya ya fita, da sauri ta saukko daga kan gadon ta nufi gaban dressing mirror tana kallon kanta ko zata ga wani canji amman bata ga komae ba da sauri ta d'aga rigarta sama ta k'ura ma k'irjinta ido boobs d'inta na acikin bra lafiya lau sakin rigar tay ta gwada yin tafiya don tasan in dae yayi mata wani abun a gurin zata gane amman bata ji komae ba lafiya lou take tafiya kasa yadda tay ta nufi wata k'opa da take tunanin toilet ne ta tura sai gashi toilet d'in ne ta shige, sosae ta duba under d'inta lafiya lau bata ga wani canji ba tsaye tay sam ta kasa yarda da bai mata wani abu ba don zuciyarta na raya mata wani abu yasa a cikin lemun nan, hakanan bazata yi nauyin baccin da har zai maido ta d'aki ba ba tare da ta farka ba tana haka taji wani abu na yawo cikin rigarta da sauri ta zura hannu ta jawo sai ganin hannun bra d'inta tay wani irin bugu kirjin ta ya fara yi ta zazzaro ido waje da sauri ta k'arasa gaban mirror d'in dake cikin wurin ta k'ara d'age rigar sama sai lokacin ta lura da bra d'in bata kamata sosae ba kamar yadda ta sata, hannu na rawa ta fiddo breast d'inta guda tana dubawa koda ta kalli nipple d'in da sauri tasa hannu ta rufe bakinta ganin yadda yay jajir da shi gashi ya fito sosae, wani irin kuka Fatuu ta saka tana fad'in ta shiga ukku ta bani ta lalace sakin rigar tay a fusace ta juya ta fita ta nufi falo, lokacin da ta shiga yana zaune ya kishingid'a jikin kujera ta tsaya gaban shi kaman an jefota cike da Masifa tace "Ashe abunda zaka aikata man kenan yasa ka kawo ni nan, dama an ce kai d'in manemin mata ne d'an shaye shaye kuma dama ban yarda da duk abubuwan da kake fad'a man ba, ba wani so na da kake yaudarata kawae kake kana son ka cutar dani don in kana sona da gaske bazaka man haka ba nima kuma ban son ka ban kaunar ka na tsaneka kuma bazan Aure ka ba wllh!!!" d'age gira yay yana kallonta da d'an murmushi hakan yasa ta k'ara k'ulewa taci gaba da zazzaga mashi Masifa har tana kiran shi da Mazinaci aikuwa tana fad'in hakan ya daka mata tsawa ya mik'e har saida ta d'an ja baya fuska tamke ya fara Magana "Kar ki k'ara kirana da wannan sunan! Ke in ni Mazinaci ne kina tunanin yadda na samu dama akan ki zan kyaleki ne iya hakan??" Duk da ta tsorata tay k'arfin halin cewa "ai duk d'aya ne miyasa zaka bud'e man jiki har ka ta6a man jikina!" tay Maganar kwalla na zubo mata, sassauta murya yay cikin sigar rarrashi yace "it's just a romance wife and ba don na biya sadaki ba ba abunda zai sa in ta6a ki kuma duk laifin ki ne kin k'i ki saki jiki da ni, I truly love u shiyasa nike maki hakan kuma bai kamata ki tada hankalin ki ba komi nai maki ai ni zaki aura ko......." A fusace tace "Allah ya kyauta! wllh bazan Aure ka ba na tsane ka kuma sai Allah ya saka man abunda kai man tunda dai ba d'aura mana aure akai ba" yar dariya yay ya girgiza kai yace "Do u think is as simple as u said?" banza tay mashi tana huci kwalla naci gaba da zubo mata yace "Look Wife ki bar wannan a tsakanin mu ba wani abu bane muje in maida ki" wani kallo take bin shi da shi cike da takaici ranta na mata wani irin suya ya wuce Bedroom d'in bada jimawa ba ya dawo ya maida rigar shi ya mik'a mata veil d'inta kaman bazata amsa ba yace ta amsa su tafi Magrib ta kusa in kuma zata kwana ne anan to, amsa tay ta yafa yay mata alamar suje tayi gaba yana bin ta a baya suka fita ba yadda ta iya ba don ta so ba ta shiga Motar don kuwa akwae tafiya ga Magrib tayi, tunda suka hau hanya take sheshsheka yana bata hak'uri had'i da nuna mata ba fa wani abu bane shi yanzu ma ji yay ya k'ara sonta don gaba d'aya yadda yake son Matar shi ta kasance haka take, suna isowa ta bud'e Motar ko rufewa ba tayi ba tay gaba, Lokacin da ta shiga falon iske Yadikko tay tana salla ta wuce uwar d'akan ta fad'a kan gado tasa kuka mai cin rae yadikko na sallame sallar ta shigo d'akin da sauri don tun tana sallar take jiyo sauti kukanta, hayewa tay Saman gadon ta d'ago Fatun tana tambayarta abunda ya faru cikin kuka ta kwashe komae ta fad'a mata tace "ban son shi yadikko don Allah ki fad'a ma Baffana kada a Aura man shi mutuwa zanyi in na aure shi, wllh da gaske d'an iska ne kuma yana shaye shaye" Ajiyar zuciya kawae yadikko ke saukewa tasan hakan ba mai yuwuwa bane ba kamar yanzu da ya rage saura yan kwanaki bikin, sosae ta shiga rarrashinta tana nuna mata lokaci ya k'ure kuma ita a tunaninta da gaske don ya biya sadakin yasa yay mata hakan tunda yana ganin saura yan kwanaki ta zama Matar shi ta daina damuwa tunda ma shi d'in da yay mata hakan zata Aura kuma da bai son ta abunda yafi hakan zai aikata mata ya dawo yace kuma bazai Aure ta ba, ita kanta yadikkon hankalinta ya tashi sosae da jin abunda ya faru hakanan ta danne don kar ta k'ara tada ma Fatun hankali da k'yar ta shawo kanta ta d'an saukko har taje tayo wanka ta dauro Alwala bayan ta gama sallar ta d'aga hannu tana kuka tana rokon Allah kan ya kawo mata Mafita, kasa cin Abinci tay duk da tana jin yunwa ta sha yar fura kawae, koda ta kwanta sak'e sak'e taci gaba da yi a ranta da ta tuna wani ya gane mata jiki har ya ta6ata sai wani kunci ya k'ara lullu6e ranta lokaci guda ta fara tunanin yadda zata guje ma Auran Khalid abunda bata ta6a tunanin yi ba tunda aka fara Maganar Auran sai yanzu...........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
*ASM Bk2031*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
..........Tana cikin tunanin neman mafita wayarta ta fara ringing da k'yar ta kai hannu ta d'aukko ta duba screen d'in ganin Number yasa ta gane Khalid ne ta kife wayar kawai ba tare da tayi picking ba, sake kira yay sai kawae ta kashe wayar ma gaba d'aya ta cillar da ita taci gaba da tunaninta da k'yar bacci ya dauketa, Washe gari da zazza6i ta tashi da k'yar tayi sallar Asuba ta koma ta kwanta sai da yadikko ta zo tashin ta don tayi karin kumallo tasan bata lafiya da k'yar ta lalla6ata ta tashi ta yi breakfast d'in ta bata Magani ta sha kafin ta koma gado, sai wurin sallar Azahar ta farka ba laifi ta samu sauki sosae hakan yasa ta wuce bathroom tayo wanka ta d'auro alwala, bayan ta gama sallar ta zura doguwar riga ta fita falo anan ta iske Yadikko itama ta gama salla da murmushi tay mata ya jikin tace ta samu sauki ta samu wuri kan kujera ta zauna, ganin yanayin damuwa tattare da ita yasa yadikko ta shiga rarrashin ta kan ta kwantar da hankalin ta da k'yar ta lalla6a ta ta zubo mata Abinci tana cikin ci sai ga Sadeeya tazo tana sanye da jallabiya tay rolling veil da fara'a yadikko ta tarbeta ta nuna mata wurin zama kafin suka shiga gaisawa daga baya ta kalli Fatuu da fara'a ta gaishe da ita anan take sanar ma yadikko tazo ne zasu je wurin gyaran jiki lokaci guda yanayin fuskar Fatun ya canza yadikko ta lura da hakan ita kanta Sadeeyar ta ga canji a Fuskar ta nan yadikko ke sanar mata yau ta tashi bata jin dad'in jikinta ne amman ta samu sauki da ta sha Magani cike da nuna damuwa Sadeeya ta shiga yi mata sannu har tana cewa amman dae Ya Khalid bai sani ba ko tunda bai fad'a masu ba yadikko tace eh ai yau ne ta tashi da ciwon, kallon Fatuu tay da bata da niyyar tashi tace taje ta shirya su je tunda da