Author : Hafsat Bature Category : Action Novels
sauk'i sosae kaman ta saka ihu haka taji ba yadda zatai dole ta mik'e ta wuce ciki, gyale kawae ta yafa akan doguwar rigar material din jikinta tasa takalma ta fito, lokacin da suka fita kopar gidan ja tay ta tsaya ganin Motar Khalid sam bata yi tunanin shi ya kawo Sadeeyar ba daba abunda zai sa ta fito tay zaton driver ne kaman rannan ganin ta toge yasa Sadeeya ce mata suje mana da K'yar ta ja k'afa suka nufi Motar don bata son ta gane da wani abu duk Khalid d'in na kallon ta duk da Motar a rufe take ruff kuma glass d'in black tinted ne, Front seat Sadeeya ta bud'e mata ta shiga bayan ta rufe itama ta bud'e baya ta shiga, wani kalan d'aure fuska tay ba tare data kalle shi ba shi kam sai kallonta yake with smile on his face yace tana lafiya kafin ta bashi amsa Sadeeya tace "Big bro Bride en ka fa bata lafiya" d'an bud'e ido yay idon shi akan Fatuu ya tambayi Mike damunta da kyar ciki ciki tace mashi zazza6i, shiru ya d'an yi still idon shi na akanta ita kuma ta juyar da fuskarta can taji yace ko su wuce Asibiti ya duba ta ne, ba shiri tay mashi wani kallo ya d'age mata gira baki kumbure tace ta samu sauk'i yace Ok daga haka yaja Motar suka tafi, sai firar bikin suke shida Sadeeya tay masu banza tamkar ma bata acikin Motar sam Sadeeya bata kawo komae ba ta d'auka don bata jin dad'in jikinta yasa tay shiru kuma dama ta san bata Magana sai ta kama, lokacin da suka isa shagon Fatuu na niyyar fita taji ya kamo hannunta akan idon Sadeeya tay d'an murmushi kawae ta fita Fatuu na jin ta rufe kopar ta fara k'ok'arin fuzge hannunta amman ta kasa a fad'ace tace "Ka sakar man hannu!" d'an lumshe ido yay yana mata wani irin kallo ganin bai da niyyar sakin yasa idanunta suka cicciko da kwalla murya kaman zata yi kuka ta k'ara cewa ya sakar mata hannu ita ba yar iska bace da zai rink'a ta6a ta sai lokacin yay d'an murmushi cikin kashe murya yace "nima ba d'an iska bane wife......" A fusace ta katse shi da fad'in "wllh kai d'an iska ne in ba haka ba mi yasa zaka bud'e man jikina ka ta6a ni!" Daga yadda tay Maganar zaka fahimci ba k'aramin ciwo abun yay mata ba, d'an ta6e baki yay still da murmushi akan fuskar shi yace "Ok mu barshi a hakan na yadda ni d'an iska ne but nan da next 5 days zan assuring naki hakan" damm k'irjin ta ya buga ta bi shi da ido ya wani d'age mata gira, d'ayan hannunta ta sa tana goge kwallan dake zubo mata ya kai hannu ya bud'e glove box ya fiddo hanky ya mik'a mata don ta goge kwallan k'in amsa tay tabi hanky d'in da kallo ba komae ya tuna mata ba sai ranar da Ya Haisam zai tafi, ganin ta k'i amsa ne yasa shi ce mata in fa bata amsa ta goge su ba bazai bari ta fita ba sai dae suyi ta zama har sai sanda ta gogen, ba yadda ta iya cike da takaici don ita k'yamar hanky d'in take Saboda rannan a cikin wurin ya fiddo kwalin cigarettes, saida ya ga ta goge su tass sannan ya kyaleta ta fita lokacin Sadeeya tuni ta shige cikin wurin gyaran jikin.
Da yamma wurin k'arfe biyar ya dawo d'aukar su bayan da Sadeeya tay mashi waya ta sanar mashi sun gama, a gida ya fara sauke Sadeeya tana cewa Amarya bazata shiga su gaisa da Momy ba yace yamma yayi yana so yay dropping nata before Magrib tay ma Fatun sallama, tun da suka hau hanya jininta akan a kaifa yake har sukae nisa bai tanka mata ba yana ta sauraren music d'in da ya kunna yana bi a hankali, saida suka iso bakin gari wurin gidan Gonar su sannan ya kalleta ta juyar da fuskarta tana kallon gefe yace "Wife ko muje ki huta anjima sai in maida ki" tun kafin ya rufe baki ta juyo a harzuk'e tay mashi wani kallo, k'ok'arin juya kan Motar ya fara yi aikuwa a firgice har bata san ta kai hannu kan hannunshi dake ruk'e da steering murya na rawa ta fara mashi magiya ya kaita gida wani irin lumshe ido yay sakamakon shak'ar daddad'an k'amshin da jikinta ke fitarwa dama tunda ta shigo Motar yake d'an bugun hancinshi ba shiri ya taka burki, jin ya tsaida Motar yasa ta juya ta kalleshi tana ganin yadda idanuwan shi suka koma da sauri ta cire hannunta ta juya zata bud'e Motar da sauri ya kai hannu yay locking Kopar ido waje ta juya ta kalle shi yana ta bin ta da wani irin mayen kallo tana ganin haka ta fara yamutsa fuska nan da nan ta fara kuka tana had'a shi da Allah kan kada yay mata wani abu hakan bai da kyau ya bud'e mata ita zata tafi a k'asa ma, Still kallonta yake bai san miya sa ba komae yarinyar tay sha'awa yake bashi shi kad'ai yasan yadda yake ji ko jiya a gidan gona ba k'aramin yak'i yay da zuciyar shi ba har ya iya k'yaleta don ya fahimci bata san namiji ba daga yadda take tsoron ya ta6a ta shiyasa ma ko tunanin kaiwa can ma bai yi ba ko ba haka ba bai iya yin hakan tana a yanayin bacci don zai zama kaman yay raping nata ne shi kuma abunda ya tsana kenan shi yasa ko ada da yake kula mata wani abu bai shiga tsakanin shi da mace face da amincewar ta, Kuka sosae take mashi duk ta rud'e can ya sauke ajiyar zuciya cikin kasalalliyar murya yace mata tay shiru ba abunda zai mata in kuma bata yi shirun ba to zai wuce da ita gidan gonar ne ba Arziki tay tsit sai motsa baki take tana zare ido, idanu a lumshe yake kallonta sai kikkafta ido take taji yace tana so su tafi, da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh jinjina kai yay yace "I want a single kiss pls" k'ara zaro ido tay baki bud'e take kallon shi ta kasa cewa komae yaci gaba "in kikai man hakan zamu tafi in kuma kika k'i saidae muyi ta zama anan har dare yayi sai mu wuce gidan gona mu kwana can" k'ara rud'ewa tay ganin on a serious note yay Maganar murya na rawa tace "amman fa kasan babu kyau tunda ba'a d'aura mana Auren ba" still bin ta yake da kallo yay d'an guntun murmushi yace "But ai zamu yi auren ne ko, kuma miya rage abunda yake dole saida shi ake d'aura auren already an bada so ba wani abu bane" kuka ta fara k'ok'arin ci gaba da yi yace ko na jini zatai in dae bata yi mashi ba ba tafiya zasu yi ba kuma da gaske gidan gona zasu wuce, wani irin bak'in ciki ne ya turnuk'eta taji ta k'ara tsanar Auren shi ganin da gaske bazasu tafin ba don yama jingina da seat ya d'age kan shi yasa tace zata yi mashi jin hakan yasa ya d'ago yana murmushi ita kuma ta d'aure fuska tamkar bata ta6a yin dariya ba nuna mata lips d'in shi yay alamar anan zata yi mashi ta ce ita bazata yi mashi anan ba yace Ok bata shirya su tafi ba kenan ganin yana niyyar maida kan yasa tace to zata yi mashi amman kar ya ta6a ta yace ya yarda tana kukan zuci da har ya bayyana kan fuskarta ta fara matsawa shi kuma sai sakar mata murmushi yake, kasa yi mashi tay tana ta yamutsa fuska can dae ta daure ta cije ta rufe ido ta kai bakin ta saitin fuskar shi amfani yay damar daya samu ta rufe idon da tay ya kai hannu ya kamo kan nata ya had'e bakin su, irin yadda yay mata ranar da ya maido ta daga gidan su yau ma yay mata, lokacin da ya saketa wani irin kukan bak'in ciki Fatuu ta saki tana yi mashi Allah ya isa kuma Allah sai ya saka mata in sha Allahu bazata Aure shi ba, bai ce mata uffan ba don shi kadae yasan abun da yake ji da k'yar ya tashi Motar suka tafi, suna isowa tun kafin ya idasa tsayawa ta kai hannu zata bud'e kopar Allah yasa a rufe take har saida ya tsaya sannan ya bud'e kopar a fusace ta fice ya bita da ido ta cikin glass har ta shige cikin gida, sai da ya d'au d'an lokaci kafin da k'yar ya ja Motar ya tafi, Tana shiga saida ta tsaya a soro ta goge fuskar ta sosae sannan ta shiga ciki lokacin da ta shiga falon su da yar sallama cak ta tsaya ta kasa k'arasa sallamar sakamakon wadda ta gani a zaune ta d'an kishingid'a kan kujera suna had'a ido ta fara sakar mata murmushi da tsananin mamaki Fatuu ta furta "HAULAT.....!" tashi zaune sosae Haulat tay tana dariya tace "Na'am k'awata Amarya" aikuwa da gudu Fatuu ta nufeta ta fad'a jikinta cike da farinciki haulat sai dariya take yi, d'agowa Fatuu tay fuskarta d'auke da tsantsar farin ciki tace "yaushe kuka zo ne?" Haulat tace "bamu dad'e ba salla kawae nayi ko Abinci kin ganshi ban ci ba nace sai na gan ki tukunna na dae sha fura, ance gyaran jiki kika je gaki nan ai sai annuri kike kin fito sak Amarya" ta k'arasa tana murmushi Fatuu ta tura mata baki kafin tace "keda wa kuka zo" tace "da kawu Amadu ne" da d'an mamaki tace "shine bai sanar da ni ba,to Gwaggo fa?" Haulat tace "gaskiya mu biyu muka zo sai kaya k'ilan ko ita sai daga baya ina jin" shiru Fatuu tay sai kuma ta mik'e da sauri tace mata tana zuwa tay hanyar fita Haulat ta bita da kallo tana ta murmushi, d'akin su Kamalu dake a soro ta nufa tana zuwa ko sallama bata yi ba ta kutsa kai tana shiga ta iske Kawu Amadu kwance yana latsa waya ta nufe shi tana kiran sunan shi ya d'ago ido yana ganinta ya saki murmushi yana kokarin tashi zaune, a gefen shi ta zauna tana kallon shi tace "Kawu Amadu ashe kun zo" yana murmushi yace "Eh Amaryarmu bamu dad'e da zuwa ba na tambaye ki aka ce kun fita" a sanyaye tace "Gwaggo fa, haulat tace ku biyu kuka zo" shiru ya d'an yi sai kuma yace "Eh amman tace zata zo ta bada kaya ma akawo" kafe shi da ido Fatuu tay kaman bata yarda ba tace "to yaushe zata zo?" Shiru yay baisan ranar da zai ce mata ba don in ma yayi mata k'arya yasan ranar zata zo kuma ba zuwa gwaggon zatai ba, ganin haka yasa fuskarta canzawa tamkar zata sa kuka tace mashi bazata zo ba ko, farko shiru yay ganin ta kafe shi da ido yasa ya d'aga mata kai alamar eh, kuka ta fashe mashi da shi tana fad'in ashe bata hak'ura ba har yanzu fushi take da ita, side hug Amadu yay mata ya shiga rarrashin ta yana tayi hakuri a hankali komae zai wuce yasan dole zata zo ne koda bayan anyi auren ne can ta d'ago tace mashi Hajiyar Sanata fa itama bazata zo ba, da yar damuwa yace mata Hajiya bata lafiya ciwon kafafu take yanzu ko wurin aiki ma ba zuwa take ba amman taso ta zo koda taji gwaggo bazata zo ba har fushi tay da ita, sosae ya rarrasheta ya nuna mata tayi hak'uri wannan jarabawa ce daga Allah, kiran sallar Magrib yasa shi tashi yace mata ta koma ciki zai je yay salla ya dawo, zaune tay a cikin d'akin tana cigaba da matsar k'walla sai daga baya ta tashi ta nufi cikin gidan lokacin da taje d'akin su a k'urya ta iske Haulat na yin salla itama taje tayo Alwala tazo gefenta ta kabbara salla, bayan sun gama Haulat ta kalleta da Murmushi tana ganin yanayin fuskar Fatun tace "K'awata lafiya dai ko, idanun ki naga sun canja kuma dama naga har rama kin yi" kaman zata sa kuka tace "Haulat baki ji Auren dole za'a man bane?" da yar damuwa Haulat tace "naji Fatuu lokacin da innata ta kira waya can Nijar ta sanar da ni na matuk'ar girgiza da jin zancen tun lokacin nike kokarin kiran ki amman bata shiga daga baya ne na kira kawu Amadu ya fad'i man komae, na matuk'ar tausaya maki Fatuu wllh Allah ne shaida har kuka nayi sosae nace Ashe ba rabon dae kiyi karatu kuma ki auri wanda kike so" kuka sosae Fatuu ta fashe dashi tasa hijab d'in jikinta ta rufe bakinta don kar sautin ya fita itama Haulat kwallan ta fara yi ta shiga rarrashinta tana cewa tayi hakuri kowa a rayuwa da kalar kaddarar shi ita kuma wannan ce tata, cikin kuka tace "Haulat za'a man Aure ba tare da gwaggo ta zo ba Saboda tana fushi dani don na amince aman auren, nima don banda yadda zan yi ne amman wllh ban son Auren nan....." sosae taci gaba da yin kuka suna haka yadikko ta shigo a rud'e ta shiga tambayar ko lafiya Haulat tace ba komae Saboda gwaggo bata zo bane nan itama tasa baki suka cigaba da rarrashin ta tare suna ce mata dole gwaggo zatai fushi yanzu amman zata saukko ko ba yanzu ba, sai da aka kira sallar isha suka tashi suka yi Bayan sun gama ne Yadikko ta nuna mata kayan da su Haulat suka zo dasu Manyan bokitan su cin cin da dublan ne dasu zannuwan gado da labulaye harda kayan gara su buhun shinkafa biyu katan d'in Taliya da Macaroni suma bibbiyu jarkar Mai su gishiri Man shanu da sauran su dae bin kayan da ido kawae tay ba tare da ta ce komae ba, tana gama nuna mata tace bari taje wurin Yaya ta d'aukko kayan lefenta da shiru har yanzu ba'a maido su nan ba, lokacin da Yadikkon taje bayan sun gaisa da wad'anda suke d'akin ta sanar ma Yaya ta zo d'aukar kaya ne, wani kallo ta jefa mata cikin harshen fulatanci tace to cinye kayan zasu yi da har sai an biyo sahu d'an murmushi had'i da d'an ta6e baki Yadikko tay tace dama daga gidan su Angon ne ake ta kira ana son aji ko akwae abunda baiyi ba kaman takalma da kuma d'inkakkun kaya anata ce masu bata gwada ba shiyasa tazo ta tafi dasu ta gwada amman bari taje sai a sanar masu har yanzu Amaryar bata ma ga kayan ba, tana fad'in hakan ta fara kokarin juyawa ta tafi Yayar ta tsaidata Fuska a murtuke tace ai sai su yi ta d'auka kuma dole za'a fitar ma da Mutanen gida nasu, ita dae Yadikko bata ce komae ba don tasan yanzu ace tayi rashin kunya kaman yadda aka saba cewa, guda biyu ta fara d'auka duk suna kallonta ba wanda yay yunkurin taimaka mata sai bayan da ta kai su daki ne ta dawo tare da Haulat da Mino suka kwashe sauran, bayan sun maida su can suka zauna don sake kallon kayan dama basu samu sun duba ba sosae da suna can, sosae Haulat ta shiga yaba kayan duk yadda akai da Fatuu tazo taga kayan ta gwada k'iyawa tay tace ai ba sai tasa ba tunda tailor ya gwadata, suna cikin kallo sai ga Kawu Amadu da Kamalu sun shigo yadikko tace yazo shima ya ga lefen sosae shima ya yaba saidae acan k'asan ranshi sam bai farin ciki da Auran ba kamar da Kamalu yay mashi bayani kan wanda za'a aura matan don shima ba so yake ba yafi son tay karatun ta kamar yadda shima yake da burin ya koma Katsina don yay karatu, bayan sun gama gani yadikko ta kawo ma Haulat Abinci da k'yar ta matsa ma Fatuu ta d'an ci suna gamawa Haulat ta shiga bathroom tayo wanka don a mugun gajiye take bayan ta fito tay shirin kwanciya itama Fatun ruwan ta watso bayan ta shirya ta hau gadon lokacin tuni bacci yay awon gaba da Haulat, Sam Fatuu ta kasa bacci sai faman sak'e sak'en mafita take rashin zuwan gwaggo ya dameta sosae ga Auran da shima bata son ayi can wata zuciyar ta ayyana mata ko ta kira Haisam ta fad'a mashi halin da take ciki game da wanda za'a aura matan sai kuma ta ayyana to in ta fad'i mashi shi mai zai iya yi mata tasan ba iya sa Ard'o ya fasa zai yi ba k'arshe ya bata hak'uri kawae dama a k'ule take dashi don kwata kwata ya daina kiran ta, haka taci gaba da yin tufka da warwara ta sak'a wannan ta kwance wannan har dare ya raba ba tare da ta ankare ba, can wuraren Asuba ta mik'e ta saukko daga kan gadon ta nufi inda akwatunan da tazo da su suke ta bisu da ido kaman mai nazarin wani abu kafin ta kai hannu ta d'aukko trolley d'in a hankali don kar ya saki sauti, k'asa ta aje shi ta bud'e ta sake d'aukko babban shima ta bud'e ta fiddo wasu kaya ta saka acikin trolley d'in ta d'aukko wasu takalma daga can gefe suma ta saka ciki duk wani abu da tasan zata buk'ata ta saka sannan ta rufe babban Akwatin ta maida shi inda yake ta d'aukko wata Handbag d'inta dake rataye ta bude kud'in da Khalid ya bata ne a ciki dama bata ta6a ko yar biyar ba ta curo su ta nufi akwatunan lefenta ta d'an bud'e d'aya daga ciki ta cusa kud'in kafin ta rufe ta dawo wurin trolley d'in ta rufe shi ta kai hannu ta d'aukko Hijab d'inta dake sagale jikin gadon ta saka har ta d'auki trolley d'in ta nufi hanyar fita sai kuma ta dakata ta juya tana kallon Haulat dake kwance