Author : Huguma Category : Complete Novels
amsawa....kin tafi kin bar wayarki gida wancan sarkin kiran ya kira ya kusa sau hamsin" cewar ummi,sai tayi murmushi tana miqewa,don itama wuni daya kawai amma tayi kewarshi,sajida ce ta gaida eesha ta amsa tana tambayarta mamanta
"Au eesha bakiga sumayya bane?sumayya ga eesha zata mana hutu kan ta wuce school"sai data daga kai ta dubeta sanda take shirin wucewa,wani kishinta na sukarta fiye da yadda take kishin su'ad,kyau da hutun daya ratsata ya tsaya mata awuya,komai nata yaji yadda akeso,itama sumayyan juyowa tayi,ta dan saki fuska saboda maganan da ummin tayi
"na ganta...mun wuni lpy?" Ta fada adake
"Lafiya ya mutan gidan..." Tafada tana yin gaba,qasa qasa ta amsa mata bata sake juyowa ba tayi wucewarta,ta rasa me ya tsarewa eesha a rayuwa,taqamaimai batasan me tayi mata ba,ta san dai kawai rashin jituwarsu tun fara ganin eeshan data yi,sanda amira ta biyota kani satin bikinta,abinda kawai ta sanyawa ranta eeshan nada raina talaka,wanda idan har haka ne ita kuwa ba zata bari ta taka ta ba,tunda itama ta mutuntata ta karramata.
Bata sake saukowa ba tana can suna soyewarsu da almustapha kaman su hadiye juna,wanka kawai tayi ta kirashi ya katse ya biyota,ya jima kwance dama ya kasa tsinana komai,muryar tata kawai yake sonji,sun jima suna hirar sannan yace da ita
"Af....naso na manta....kaman dazun naji ummi na cewa aisha tazo ko?" Dan jim sumayya tayi sannan ta amsa
"Eh haka ne"
"Well....,ban so ki shiga shirginta,ki tuna ko yaushe akwai banbanci tsakanin ki da ita" kai ta kada tana mamakin me yasa sam ba jituwa tsakaninsu,ya washi ganinya,bata manta randa ya sake nanuqeta ba a bayan gida bayan ya hango tahowar eeshan,ba shakka ruwa baya tsami banza imma dai ta taba masa wani laifi irin wanda baya so ayi masa ko kuma wani abu makamancin haka
"An gama yallabai"
"Ba yallabai ba....wancan sunan nake so" dariya ta qyalqyale da ita
"To my.....happinesssssss...." Ta fada a rarrabe tare da jan S din wanda sautinta ya ratsa dodon kunnenshi
"Ohhhh....babe....ki shiga hankali fa...so kike ki tsokaneni ko?" Dariya ta kuma saki
"Ni na isa...kaga ma Allah ya bamu alkhairi sai da safe"
"Kina kashen waya gobe zan sa a satoki a kawo min ke,bar wayar a haka ki gama shirin baccinki kizo na saki bacci" idanu ta zaro,tasan me zaiyi mata
"Kudin wayanka fa na tafiya"
"And so what?" Ya tambayeta a tausashe
"Ok...am sorry,amma fa zan iya minti arba'in kamin na gama shirina"
"Ba damu bane" ya furta yana kwance rub da ciki saman sofa
"Okeyyyy,sai na dawo"
"Take care..." Yace mata kaman ya hanata tafiyan.
*to ga eesha tazo?ko me zai faru?,ku biyoni muje*
Assalamu alaikum fans,ya haquri da ni,sabgogi ne ba yadda bawa ya iya,kana naka Allah na nashi,wani lokaci suyita zuwa maka ajajjere kuma dole ka aiwatar da su,haka zamuyita haquri har mu kammala labarin,ina gaisuwa gareku baki daya,Allah yasa mu dace.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
9⃣8⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*Allah S W T yana cewa annabin rahama sanda ya shiga damuwa kan rashin musuluntar kafirai*
*haqiqa kai(annabi muhammad S A W)baka shiryar da wanda kake so,saidai Allah yana shiryar da wanda yaga dama*
Saboda haka 'yan uwa kayi qoqarin nusasheshe da bawan dake kan bata,shiriya ka barwa Allah tashi ce.
______________________________________
Washe gari qarfe tara na safiya ta farka da wata iriyar yunwa,kasancewar jiya suna tsaka da waya da almustapha bacci ya dauketa ba tare data ci abinci ba,sajida na gefe tana ta baccinta ta shiga toilet ta wanke bakinta sannan ta dawo ta daura zani kan rigar baccinta ta zura hijabi ta fice.
Kitchen ta shiga tana yin sallama,mai aikin ummi uwani na tsaye gaba gas tana fere dankalin turawa ita juyo cikin sakin fuska ta amsa,hakanan take son sumayyan,ta yaba hankalinta sosai,sam basu taba jin dadin zama da abokiyar zamanta ba shi yasa suke mamakin halayyarta,hasalima umarni ne kawai tsakaninsu,ka saba kuma taci mutuncinka ko gaban waye,kaman bayi take daukansu,gefe daya eesha ce sanye da kayan bacci tana jingine da freezer,hannunta daya riqe da cup,daya hannun kuma waya ce tana amsawa,uwani duka ta girme musu don ta kusa sa'ar ummi,mai aikinta ce da suka jima tare,amanarta da hankali yasa tasu tazo daya da ummi,tunda sumayya ta dawo wajen ummin ita kewa sumayya komi duk abinda take da buqata,fuskar sumayya qunshe da murmushi ta qarasa kusa da uwanin sanda take yunqurin gaida sumayyan tayi maza cikin girmamawa ta soma gaidata,ta amsa tana fadin
"Halan wani abun kike da buqata uwar dakinmu?" Murmushi sumayyan tayi
"Ai naga ma kaman aiki kike ko?"
"Ba matsala fadi abinda kike so sai ayi miki ai......"
"Ba aikin wanda zakiyi har sai kin gama min nawa" eesha ta fada tana sauke waya daga kunnenta idanunta a akansu
"Ai duka zan iya hajiya aisha....nata aiki yafi mu....."
"Bakiji me nace bane?,ko sai na sake maimaita wa?" Ta kuma fadi a gadarance,murmushi sumayya ta yiwa uwani
"Kada ki damu baba uwani...ci gaba da aikinki" ta fada tana matsawa gaba,ta samu tukunya ta dauraye ta zuba ruwa da duka kayan qamshin da take buqata ta dora saman daya gas din,sannan ta bude freezer ta fitar da nama ta zuba masa ruwa don ya narke ta janyo kujera ta dawo gefan baban ta zauna suna hira jefi jefi,wannan dabi'a ta sumayyan na daya daga cikin abubuwan da ya sanya baki daya ma'aikatan ke qaunarta,bata dauki rayuwa da zafi ba,komai nata a sauqaqe yake,idanuwan eesha na kanta,baqinciki ya cikata,so tayi taja zancan da tsaho ta yayyaba mata magana ta qona mata rai,saidai anyi katari sumayyan bata bi ta kanta ba,wani wawan tsaki ta ja sannan tace da baba
"Saura bayan fitata ki kama aikin wasu,zan shiga wanka kafin ma fito a shirya min saman dining"
"To" kawai baban tace da ita,sai ta juya ta fice tana wani taku tana jin kanta dai dai da kowa,da kallon takaici sumayya ta bita sai data fita ta dauke kai,batasan me ta dauki rayuwa ba,yanzu kaman baba data yi sa'a da uwarka idan ba dole ba ma yaushe zaka sanyasu wani aiki
"Kiyi haquri baba don Allah" sumayyan ta fada cikin rashin jim dadi,dariya baban tayi
"Banda abinki uwar daki ai babu komai,tana cin albarkacin hajiya ne da alhaji,dukkansu su da yaransu an shaida mutanen arziqi ne,don wannan tayi ai ba komai na lokaci ne zata koma inda ta fito" kai ta jinjina kawai suka ci gaba da hirarsu,kusan tare suka gama,wanda hakan yayi dai dai da shigowar sauran ma'aikatan,suka gaisa baki daya sannan ta fice ta basu waje,bayan an kai kayan karin dining saboda harda ummi tayi,gasashshen nama ne da kayan lambu,sai breadin inibi da ruwan shayi,na eesha kuwa chips ne da qwai sai nata ruwan shayin.
Ta tadda sajida ta farka harta gama gyara dakin tayi wanka abinta,sam yarinyar anty farida bata yi mata rainon yaran masu kudi ba,ta iya qananun aikace aikace dai dai da ita,ta iya shata tsaf da gyaran gado,ta gaida sumayyan sannan ta shige toilet tayi nata wankan,ta shirya sannan suka sauko,sun tadda ummi itama ma saukowa a dining suka hade baki daya harda eesha,a ladabce sumayya ta gaida ummi ta amsa fuska sake tana tambayarta ya jiki tace alhmdlh
"Amma dai ai zuwa yanzu amai ya tsaya ko?" Kai eesha ta dago tana duban sumayyan,tunda tazi take zargin hakan dangane da sumayyan saidai bata da tabbas sai yanzu,kanta a qasa cikin jin nauyi ta amsa mata da eh
"Alhmdlh haka ake so Allah ya qara afuwa"
"Amin" tace da ita,kafin ta sake cewa wani abu yaron gidan da ummi ta aika ya soma danna qararrawa daga bakin qofar falon,sumayya zata miqr ummin ta dakatar da ita,ta miqe da kanta ta tafi amsowa,jawo kwanukan data yi abincin tayi ta soma budewa tana zubawa cikin plates uku,nata ummi da sajida,yayin da eesha ke gefe daya tana jefa chips bakinta,gaba daya abincin yayi mata,hakan ya sanya sumayya na gama zubawa ta kai hannu ta bude ta janyi wani plates din
"Ci zakiyi ne?" Sumayya ta tambaya,don tana so ya kai mata ne har wajem sha biyu zuwa daya kafin nan an gama girkin rana,din bata fiya son wahalar da masu aikin ba tayi ta sasu dafa mata abinci kamar kanta aka soma ciki,banza tayi da ita kaman ba da ita take magana ba,sai ma fara yunqurin diba da tayi,hakan ya qona ran sumayya,hakan ya sanya ta sake maimaitawa
"Magana nake dake" sai a sannan ta daga kai ta dubeta
"Tunda ba abincinki bane saiki sauraramin ko?"
"Gaskiya kika fada,amma kiba nawa bane ni na dafa saboda haka sai wanda naga dama sannan zaici" ta fada tana janye flask din ta maida murfin ta rufe shi ruf,sajida ta miqawa tace ta kai mata daki,ta amsa kuwa tana murna ta haye saka da shi,din jiya itama eeshan sai data zalunceta don kawai ta takata bata sani ba,hakan ya bata ran eeshan matuqa,tana ganin kamar ita zata sumayyan zata yiwa haka?,idan ma da tasan cewa ita tayi da ba zata nuna kwadayinta a kai ba,amma tunda har hakan ta faru dole ta taka mata birki ko don gaba
"Kece matsiyaciya,ba sabanba,duk inda dan talaka yake sai ya nuna hali?" Idanunta ta watsa mata,a fuska zaka rantse bata damu da maganar data watsa mata ba,a nutse tace da ita
"Ko 'yar qaruna?" Isowad ummi wajen yasa sumayya ta ja abincinta ta soma ci,cikin murmushi ummi ta dubi nata plate din ba tare data lura da sauyin yanayin fuskar sumayya ba
"Wannnnan dai ba girkin uwani bane....sumayya ya aka haihu a ragaya?" Ta fahimci sarai me take nufi,tuni ta hanata yin komai,itakam bata iyawa ta wuni sur ba tare data tsinana komai ba,murmushi tayi kanta a qasa
"Ummi na gaji da kwanciya ne,sai naje ja tayata muka yi"
"Ki dai dinga kula,don wannan mijin naki wallahi yazo yaga ba dai dai ba sai ya daga hankalin kowa" ta warashe tana dariya,ta ja plate dim gabanta ta soma ci cikin zuciyarta taba yaba qwarewar girkin sumayya,gefe daya na zuciyarta kuma yana tausayawa almustapha,tasan ko ba'a fada ba yayi kewar abinci mai kyau dadi da tsafta.
Eesha na gefe ta cika tayi bam,gani take maganar ummin na qarshe ma kamar da ita take,wato ciki ne da ita shine take wannan iskancin?,jan kujerarta tayi baya sannan ta miqe,binta da kallo ummi tayi sannan tace
"A'ah,ya haka"
"Na qoshi ne ummi,zan koma bacci" ta fada tan zare jikinya daga wajen
"Aikin kenan fa,sam baku gajiya da bacci,kudai rago ko don saboda aure"
"Uhmmm....." Kawai ta fada tana nufar daki.
Ko data shiga kasa zaune tayi bare tsaye,ta kai ta kawo ta rasa sakat,zuciyarta kaman ta fashe,batasan kishin sh'ad da takeyi salama bane akan na sumayya sai yanzu,wayarta ta cilla saman gado sannan tabi lafiyar gadon tana tunanin ina mafita?,tilas ta samawa kanta qofar shiga gidab mustapha koda tsiya koda tsiyatsiya.
Itakam bayan sun gama wucewarta tayi wajen anty maamaa,dawowarta kenan daga sashen mai gidan wanda yanzun ya fita
"Uwar biyun mu" anty maama ke tsokanarta,dariya ta saka,tana jin kunyar antyn ita kanta
"Baki gajiya kullum sai kinzo gaidani?,da kinyi zamanki ma" ta fada suna gaisawa da sajida data rakota,hira sukayi sosai abinsu,anty maama babu ruwanta,tana da sauqin kai da dadin zama tun asali,abinda yasa zamansu yayi qarko kenan da ummi.
Suna tsaka da hira mahmoud ya shigo,ya sake wata qiba da haske,ta jima rabon data ganshi,fuskarshi qunshe da murmushi yake fadin
"Antynmu matar yayanmu"
"Ka fadi haka mana tunda kayi wuyar gani kai da mus'ab,amaren ma rowarsu ake mana har yau ba'a kawo mana su ba" ta fada cikin sigar tsokana,anty maama na gefe tana dariya
"Habba anty,sashen naku ne kaman wani tsaro naga yaa man ya qara masa,tunda ya fahimci alqasim abokina ne shikenan naga ya soma nima ciccije min,kinsan halin mutumin sai a hankali,dama yaya lafiyar kura" ya fada bayan ya zauna daura da anty maama yana dariya
"Kaci gidanku,yayanka ne,sannan banda tsaurin ido a gaban mace ka dinga sille mata miji ha'an?" Dariya suka sa baki dayansu sannan suka fara gaisawa ya dora da cewa
"Amare gobe zasu zo dukansu,sun so zuwa dubaki ance bakiji dadi ba,to sai naji ya man ya koma dubai na tsammaci tare kuka koma"
"Kace gobe muna da manyan baqi,to Allah ya nuna mana"
"Ke tsohuwa,yaiushe sirutunki ya ragu ne?" Ya tsokani sakida dake zaune gefe,dariya ta saki
"Yana nan bai ragu ba"
"Au to,na fasa tayaki murnar da nayi niyya" dariya sunayya tayi,akwai wasa tsakaninsu,shikam mahmoud ba ruwanshi,wani lokaci akwai ban dariya sumayya ta fada tana dariya,hira sukayi abinsu sosai kafin daga bisani ta musu sallama ta koma wajen ummi.
Data koma eesha ce kawai a falon,itama bata zauna ba daki ta koma ta nade kan gado,saboda lokacin yin wayarsu da almustapha ya kusa.
******** ***** *********
Washegari akayi rasuea maqotan gidan baba prof,hakan ya sanya duka ummi da anty maama basa nan suna gidan rasuwar,gidan daga ma'aikata sai ita sai eesha,sajida ma ta bisu,ga baqi da zasu zo matan mus'ab da mahmoud,hakan ya sanya bayan sun gana wayarsu da mama,zainab,halima,abdallah da yaya yahansu,kowa sai data kirashi suka sha waya sosai,credit mai yawa ta qarar,sannan ta tashi ta shiga wanka kasancewar bata yi wanka da wuri ba tana fitowa a wankan ta shirya cikin wani yadi mai azabar kyau cikin lefanta,ta dubi kanta a madubi,ta zama wata classy sumayya,ita kanta tasan ta sake kyau da sauyawa sosai,hannunta ta dora saman cikinta data fara jin alamun dagawarsa,murmushi ta saki har cikin ranta tana jin farinciki,tana qissima yaya almustapha zaiyi duk randa yazo yaga cikin nan ya fito?,turare ta fesa ta yane kanta da siririn mayafi medium size ta fito daga dakin.
A falo ta samu eesha saman kujera qafa daya kan daya anata sana'ar danna waya,daga kai tayi ta dubi sumayya,duk da batayi makeup ba amma ba qaramin kyau tayi ba,ta dan zubawa material din jikinta ido,tana da irinshi,daga dubai mamarta ta kawo mata shi,yana daga daga cikin kayan ta da take ji da su,wani kishi ya cika kata ido,dinkin doguwar riga ne wanda ya fitar da sigarta,ta zuba saitin cikinta ido,baiyi fitowar da kowa zai iya ganewa ba,amma matuqar ka qware wajen gulma sa ido da iya munafunci kallo daya zaka yi masa ka gane tana dauke da yaron ciki,wani abu ya tsaya mata a wuya,cikin da bai isa zama mutum ba ya tsone mata ido,saboda ta fuskanci kowa maraba yake da shi,faranta ran kowa yake banda ita,land line dake falon ta dauka tayi kira sashen ma'aikata,tayi sa'a kuwa baba uwanin ce ta dauka ta buqaci ganinta
"Gani nan uwar daki" ta ambata,bata tsaya falon ba tayi shigewarta kitchen taba jiranta,qwararan mintuna biyar saiga baban
"Baba....yaufa zamuyi baqi me za'a tana darmusu ne?,amarensu mahmoud?"
"Eh gaskiya ya kamata,me kike buqatar ayi musu?,ai saiki fada ki samu waje ki zauna" dariya tayi
"Baba,wai haka zanta kwanciya kamar ruwa?,kema kin sani motsa jikin ai yana da muhimmanci ko?,yanzu bari kiga" nan ta tsara ma baban abinda za'ayi,baba na tsaye ita tana daga zaune suka soma aikinsu,suna yi baba na bata labaruka suna hirarsu abinsu,kafin su kammala kusan shigowar eesha hudu,tazo ta bude freezer ta fice,ko waiwayowa sumayya bata yiba bare ta nuna taga shigowarta,ita dai abun na daure mata kai,ta rasa meke tsakaninsu?,bayan da suka kammala sumayya ta dora tuwan semo wanda duja baifu malmala shida ba,tayi miyar kuka wadda taji nama da tantaqwashi,ita take sha'awa,tana dab da barin kitchen din amira ta fado,daga gidan mutuwar take,saboda suna da alaqa da familyn saifullahi
"Uwar biyu" ta soma fadi sannan ta bude freezer ta dauki ruwan sanyi ta sha sosai saboda ranar da ake yi,sumayyan na tsaye tana dubanta
"Ya na ganki haka afujajan" kai ta kada
"Ke dai bari kawai,wallahi bacci kazo nayi kafin yamma na wuce gida,drivan ma na sallameshi na karbi key din na koma da kaina" dariya ta danyi
"Wannan bacci wannan bacci amira anya qalau kike,jiya fa ina jiyo ummi na miki fada kin dora girki kinje ki kwanta kin barshi ya soma qonewa,vanda Allah ya sanya mai aikinki bata tafi gida ba gobara zaki hada"
"Shaye shaye na fara" ta fada cikin sigar tsokana
"Ko kuma da kin riga kin sha din ba" itama ta maida mata cikin tsokanar suka soma takawa don ficewa daga kitchen din suna dariya
"Allah amiran yaya musty(da yake taa sauya mata suna)bansan meke damuna ba,yanzun fa ko saif bana iya jira ya dawo kan ya dawo na jima duniyar bacci"
"Tabdi....kije kiga likita kam,Allah yasa kema kin biyo sahu?"
"Allah ko?,kaddau bakin saif ya kamani?" Ta fada tana fiddo ido
"Ke dalla,meye ne kika wani waremin idanunkin nan irin na yayanki kamar ni nayi abun" ta fada sanda sukaqaraso cikin falon eesha na zaune,dariya amira ta saki har da d'an ihunta
"Kice kawai yayana rikitaki yake da idanunshin nan,kinsan Allah sunfi nawa kyau,ni kaina lokacin ina qarama cewa nake muyi musanye,Allah yasa ki haifo mana mai kama da shi"murmushi kawai tayi tana tuna yanayin kallonshi,yadda ya iya hukunci da ido,yana rikita ta ba qarya ba a duk sanda ya ritsata da kallonshi,murmushi ya subuce mata a sarari ba tare data sani ba
"yar is,kinzo ko ki nemi hanyar gidan ko?,wallahi kada kiyi aure ki tsammaci zan dinga jelan zuwa gidanki" sumayya ta tsinci amira na gayawa eesha,dariya eeshan tayi
"Ke kuwa zuwa ya kama,idan akayi 'yar gida ai kinga ko bako qaunar Allah dole kizo,ko banza na zama yayarki"ta fada da biyu,tabbas maganan ta samu shiga zuciyar sumayya,ta kuma fahimci sarai inda zancan eesha ya dosa,saidai batasan ka wa take maganan ba,mahmoud da mus'ab har yau basu cika wata biyu da aure ba,ya adam bai garin ma baki daya matanshi biyu ga yara kusan hudu,ya girme mata ma sosai,almustapha fa?,wani sashe na zuciyarta ya gaya mata,sai ta soma juya zancan a hankali cikin ranta
"Ah lallai fa,ga mai yawan rai kenan.....kinga bacci zanje nayi na wasu awannai,bari naje na dawo sai mu qarasa zancan....wai nikam me ya samu number salama bata shiga?" Ta tambayi eeshan tana yin gaba
"Salama?,bakisan muhsin ya sauya mata layi ba,bikinta bai wuce one month ba yace bai sonta da tsohon layinta,but dazun ma tace na tura mata num dinki ba mamaki kiji ta kiraki"
"Kice akwai shagali....saura ku sai ku bada himma" ta fada tana dariya
"Me kike ci na baka na zuba" eeshan