Author : Huguma Category : Complete Novels
karbesu ya sanya qafa ya fito abinsa ya koma sashen nasu,ranan kuwa can suka kwana,bai karbosu ba itama ummin bata aiko musu da su ba,da yake yaran sun riga da sun saba,ba kuma su fiye shan nono ba,hakan duka bai masa ba,ji yake gidan yayi kadan ya dauki soyayyarsu,da safe ko karuawa basuyi ba ya sata ta shirya suka fice zuwa gidanshin nan,wanda anan kadai yake gani zasu baje kolinsu,ya kuwa baje kolin sin ranshi,ya yiwa soyayyarsa cikin zuciyarta service ta sake dawowa sabuwa fil,ya kuma sake dasa mata yadda zata soshin,irin soyayyar mai zafi mai tsayawa a rai,wanda bata barin zuciya ta huta bare gangar jiki,yayi qara'i iya son ranshi ita kuna ta durqusa ta tallafi dukkan nau'in abinda yazo mata da shi,na hadda ta haddace,na karba ta karbeshi yadda ya kamata.
Kwana daya da wunu taji bai zancan su koma gida,dukan kararta da alkunyarta taci tura,yaranta na cikin ranta abinka da uwa,tana zaune tana miqa masa kayanshi da dai dai yana shiryawa tace
"Allah yasa su amatu zaka dauko min"kai ya girgiza
"Wa?a'ah,ai kisaka rai kin yayesu kawai,tunda ummi ta gayamin babu abinda basu ci....ke infact ma zaki soma rainon ciki ne" gira ta dan ya mutsa a shagwabe
"Wake da cikin,ni?,ni ban gaya maka ba" bai kulata ba har sai da ya gama fesa turarenshi sannan ya fincikota jikinsa ba tare data tsammaci hakan ba,haka ne ya sanyata fadawa jikin nashi gaba daya
"Ke kike da ciki,tsakamin kwanakin dawowata ni na tabbatar da cewa nayi ajiya,kuma ni na gaya miki,kema kuma zaki ga alama nan da four to five weeks....am telling you" dariya tayi kawai tana maida abun wasa,dariyar shima yayi sannan yace
"Zamu ga wanda dariyarsa zata kasance ta nasara"
"Allah ya nuna mana" ta fada cikin basar da zancan,wasa wasa sai ga 'yan biyu shiru har sati guda,suma kuma suna gidan basu komai ba,randa suka cika sati biyu saiga ummi da yaran,cikin girmamawa da kunya ta tarbeta,ummun tace ga 'yan yaye ta dawo da su sunzo kuma ganin gida da Allah ya sanya alkhairi,mamaki ya cikata,wato almustapha yace musu sun dawo nan ne sannan ta yaye yaran,kusan awar ummin biyu sannan ta musu sallama ta tafi ta sanar musu anty maamaa da baba suna nan zuwa.
Abun kaman wasa saiga zancan almustapha ya tabbata,da kanta tayi gwaji da PT strip,kuka ta saki cike da tsoro da fargaba,tayi firgai firgai da ita tana jiran dawowar almustapha,ina zata iya da twince wata bakwai ga wani sabon cikin,sanda ya dawo takw gaya masa dariya ya dinga kwasa abinshi hankalinsa kwance
"Sanda nake gaya miki kin dauka da wasa nake?" Takaici ya cikata,wato shi ko a jikinsa ma,sai abinci da ya jawo yanaci yana baiwa su amatullah sunata darunau abinsu,sai ta fashe da kuka ta miqe ta shige daki,cikin mamaki ya bita da kallo din bai zaci haka ba,sai yaji wani abu na susar ranshi,mamaki bai cikashi ba har ya gama bawa yaran abincin,kafin ya kammala abinda zaiyi sun bingire da bacci,hakan ya sanya ya kwashesu suka shiga dakin,tana takure waje daya tana jan hanci da alama taci kukanta sosai,sanyasu yayi cikin gadonsu dake gefe daya,ya tofesu da addu'o'i sannan ya nufeta,ya jima yana kalllnta kafin yayi qas da murya
"Me ya saki kuka sumayya?!" Tun kafin ta bashi amsa wasu sabbin qwallar suka biyo kuncinta
"Yanzu don Allah ya dace ace na sake samun wani cikin?" Kai ya kada
"Eh ya dace mana,tunda har Allah ya baki yasan cewa ya dace ne" sai ta barke da kuka tana fadin ni wallahi bana so,tun yana lallashinta sai ya fahimci da gaske take,ya tunzura sosai,maganganun data dinga yi suka qona ranshi matuqa,kanshi ya dinga lallasa bai tsitstsinka mata mari ba,sai kawai ya miqe ya dauki kayanshi ya fice a dakin,ranar farko da suka taba raba makwanci kenan tun randa ta zama ita kadai.
Wasa wasa sai qaramin abu ya soma zama babba,dan abu qalilan saita sanya kuka,ta daina kulashi sam,iyakarta da shi gaisuwa sai ko girko,shima sai ya daina ci kota dafa din,yadda ta dafa haka zata zo ta dauke,hakan na bala'in qona mata rai,sam bata jin dadin zaman gidan,amma gani taje itace da gaskiya ita ya kamata a bawa haquri ai,bini bini kuka,ko su amatu ke fada ko rigima yanzu zata sanya kuka,wani lokaci yazo ya kwashe abinsa ta qaracu hamcininta ita kadaj,wani lokaci su kwana ma wajensa,tana can ta kasa bacci saboda rashinsh amma ba zata nuna ko ta sauko ba,abinda ya bata masa fiye sa zato,a hankali ta soma rama,ga laulayi tana fama da shi,cikin haka Allah ya kawo halima abujan sunzo wani seminar ita da abdur rahman ta leqo ta wunan musu,baki kawai halima ga sake tana duban sumayya,yo aiko ita ba zata tafka wannan shirmen ba,shi yasa data shigo tana yabon gida sai uhmm kawai take cewa,abin ma haushi ua bata ta kasa ce mata komai ba harta tafi,dadin abun ma su 'yan biyu babu abinda sukayi,sai girma da suka dada da qiba kaman ana jansu,ashe mama ra zayyanewa komai,ranan raga tashinnhankalin da bata taba gani ba,jin muryar maman ta sauya ya daga hankalinya,ta mata fada kaman ta cinyeta,ta kuma tabbatar mata matuqar bata sauya ba to kaman a kunnen malam,ta kuma sani gamonau bazai mata kyau ba,a rannan ta zauna ta yuwa kanta bita daya bayan daya,istigfari ta dinga yi sanda ta dawo hayyacinta,ta tuna girman zunubin data dauka a wannan tsakanin abinda ta yiwa almustaphan,a ranan ta duk abinda ta danja baya da yi duka ta miqe tayi,tayiwa 'yan biyu kwalliyarsu duk da dama bata fasa ba,amma ta yau din ta musamman ce,ta barau falo cikin kekunansu ta shiga nata wankan,tunda ya shigo ya fahimci sauyi a falon,bai ce komai ba ya kwashe yaransa daketa bangala masa dariya da daga masa hannu kowa na son ya soma daukarta,dariya ta saki ya kwashesu baki daya ta haura sama da su,sannan ya kwashi kekunansun ya kai dakinsa,koda ta fito taga bata gansu ba tasan ya shigo kenan,duk sai taji ba dadi,tabbas bata kyauta ba,ada bai shiga ko fita sai da saninta,amma yanzu duka ta bata wadan nan lamuran,sai data gama shiryawa tsaf cikin wasu sabbanin qananun kaya data taba siya a dubai,bata taba amfani da su ba sai ranar,tayi masifar kyau kai kace sumayyar nan ce 'yar sha takwas,kaman bata haifi yara har uku ba,ta koma saman dining ta kwashe abincin ta jera kan wani kwando mai kyau ta haura saman da su.
Sanda ta tura qofar dakin yana zaune saman gado da su abinsa,ko ina birjik da kayan wasansu kala kala,daya na saman qirjinsa daya na saman cinyarsa yana dan kada qafar a hankali,yana dan bubbuga bayan amatur rahman dake saman qirjinsa,da alama bacci suke ji kuma daf yake daukarsu,don ya saba musu idan zasuyi bacci hakan yake musu,da zarar kuwa ya musun baccin zai daukesu ba wuya,abin sai ya burgeta duk da cewa ba karon farko taka hakan ba
"Yanzu mahaifi uba irin wannan shi zaki hanawa samun yara?" Zuciyarta ta tuhumeta,sai ta sake jin rashin kyautawar tata sosai
"Sannu da zuwa" ta fada a sanyaue,daga kai yayi ya dubeta sai kuma ya kauda idanun nashi,ta masa kyau ba kadan ba,ji yake kaman yaje ya rungumota,saidai miskilancin ya motsa,ga bacin ranta dake sakadar zuciyarsa
"Yauws" ya amsa can qasa wanda da qyar ta jiyo amsar,sai data kammala shirya komai baice mata qala ba,ta matso kusa da shi ta sunkuya tana fadin
"Sannu da zuwa.....barin dauke maka su kazo kaci abinci"
"Dakata,barmin su ai kaya na ne ko?" Ya dakatar da ita ba alamun zafi tattare da shi,amma sigar da yayi maganar kawai kasan akwai fushi cikin maganar tasa
"Wai naga ga abinci..."
"Bazam ci ba,a qoshe nake...." Sai kuka ya qwace mata,idanunsa ya lumshe yana saurarenta,baiso baison yaji kuka ko kadan,sai yaja qaramin tsaki wanda ya sake karya zuciyar sumayyan,miqewa yayi ya janyo gadajen 'yan biyu ya sakasu a ciki,ya tofa musu addu'a,sannan ya dawo saman gadon ya tattare dukkan kayan wasan nasu da kofunansu da ya hafa musu abinci da feeders ya kammale su waje daya,ya sake dawowa ya miqe bayansa jikin fuskar gadon tare da miqe qafafunaa,har yanzun kukan take bata tsagaita ba,yana jin kamar ana jan ranshi ne,qarasowa tayi gabanshi kanta a qasa ta durqusa
"Kayi haquri don Allah ka yafemin,nasan cewa ni mai laifi ce a gareka"
"Laifi?,na mefa?,bayan kina jin kinyi daidai sai kuma daidanki ta koma laifi" hawayenta suka sake qaruwa ta sake qas da kai
"Na sani,na cancanci duk wani hukunci,amma kayi haquri ka yafemin don girman Allah" har cikin zuciyarsa kalaman suka kai ziyara,sai sun sake taso masa da bacin ranshi,maganganun data dinga gaya masa a sannan
"Ke zan bawa haquri ai,tunda ba'a miki dai dai ba ko?" Kai ta kada
"Ba haka bane"
"To yaya ne?,sumayya ki gayamin,me na rage ki da shi da kike tantamar haihuwa da ni?,mene da ake buqata wanda bakya samu?,meye aibuna?dame na gaza miki?,ci sha sutura ko muhalli?,ki gayan daya daga ciki?,me kike so nayi ina kike so na saka raina,meye laifina?,akan me zanqi na haihu?,meye Allah baiyimin ba,ina da arziqin da ko 'ya'ya million za'a haifa min zan iya daukar nauyinsu,zan iya kula da su,to me yayi saura?,me ya rage min?,so kike ki tunzari ni?,ki tunzurani nayi abinda banyi niyya ba?,kinsan mata nawa ke kawomin kansu na auresu?,duba nan" ya fada yana bude wayoyinshi a zafafe kamar yadda yake maganar cikin zafi ya shiga fannin saqonni ya bude kana ya tura mata dukkan wayoyin gabanta
"Su'af bata yi arba'in ba baban yarinyar da na yiwa aiki ambassadorn nijer yake min tallan 'yarshi,duba qasa bayan shi ga saura nan,mutane iri daban daban,ba wadda idan nace ina so za'a hanani,so kike na dauko wata cikinsu dolen dole na kawo rayuwarmu?" Kuka ta fashe da shi qwarai fiye dana dazu,tausayinsa da tausayin kanta ya kamata,tabbas gashinan har da hotunan wasunsu
"Kayi haquri don Allah man kayi haquri,wallahi na daina,ina son cikina ina son abuna,kuskure ne" sai tausayinta ya kamashi ganin yadda yake take kuka haiqan,hade hannayensa yayi waje guda yana dubanta
"Yanzu ya kike so ayi,a cire miki cikin?" Wata harara da batasan da ita ba ta watsa masa
"Wallahi banaso ina son abuna ba wanda zai cire min" a zahiri da ranshi ba'a bace yake ba tabbas dariya ce zata zo mishi,amma da yake yana cikin bacin rai sai harar tata ta saukar masa da sanyi cikin zuciyarsa,ya lumshe idanu sannan ya ware mata hannayenshi,tamkar jira take sai kuwa ta taso da hanzari ta fada ya rufeta ruf ta sake narkewa da wani salon kukam
"Relax baby...relax" ya fada yana shafan sumar kanta dake fake waje guda,a hankali kukan ya ragu ta soma sauke ajiyar zuciya
"Kace musu kana so?" Ra furta a hankali
"Suwa?" Ya tambayeta yana dan tunani
"Au" ya fadi bayan ya tuna,sai ya sanya dariya har sautinta na fitowa,wato wani kishi da da can bata da shi a yanzu zata koya
"Bance musu ba,amma indai kika sake cewa bakison baby na dake jikinki to ki tabbatar zan auro saliha tayi ta haifo min yara iya yadda nakeso..." Bai qarasa ba ta cika masa kunne da kukan shagwaba
"Sorry sorry....bazan sake fadi ba indai kema baki sake ba" ya fada yana dariya tare da sake gayyatota zuwa cikin jikinsa tayi lamo tana dariya ciki ciki,kusan tare suka sauke ajiyar zuciya kowa najin wani nauyi na sauka daga qirjinsa,saboda ba qaramin kewar juna sukayi ba,ba wanda bai jigata ba cikinsu dauriya kawai sukayi,a ranan an biya bashin soyayya qwarai,dama ance fushin masoya hutu ne.
Rayuwa mai cike da tsafta da ingantacciyar soyayya ke gudana cikin gidan,gida ne da suka ginashi cikin so qauna da aminci,kowanne farincikin dan uwansa shine nasa,dukkansu kowa ya qoqarin ganin ya kyautatawa dan uwanshi,sai da cikinta yayi wata biyu cif sannan suka daga dubai da kyawawan 'yan biyunsu,sun tafi sun bar mutane da kewarsu,a can dinma gida ya saiya musu mai dauke da falo daya kitchen mai girma da corridor biyu,daya dakunan baccinsu shi da sumayyan,daya kuma na yaran da spare din wani guda,a nan dinma ingantacciyar rayuwa suka shimfida,duk abinda yakeso shi take masa,kaman yadda duk abinda takeso shi yake mata matuqar bai saba dokar shari'a ba.
***** ***** ****** *****
******* ****** *******
Qatuwar harabar gidan dattijon tsohon professor muhammad mukhtar wanda aka sake sauyawa ginin gidan fasali qawace yake da nau'o'in ado kama daga yadiddika balan balan da launin qwayaye iri iri,kujerun zama da tebura ma alfarma,carfet carfet da ka qawata wajen,iya ganinka yara ne ke sha'aninsu wadanda ba zasu gaza shekara biyar zuwa qasa ba,sai kuma manya jifa jifa wadanda 'yan uwa ne na jimi,daga qofar iya wajen da aka tanada saboda sha'anin makeken hotone na amataullah da amatur rahman,yan biyu kyautar Allah,'ya'ya ga doctor muhammad mukhtar,hamshaqin attajirin nan wanda ya mallaki kamfanoni na sarrafa abaya da mayafai a qasashen duniya daban daban,babban mai noma auduga afadin nijeria,mutum da ya mallaki manya manyan gidan marayu da gajiyayyu wanda babu irinsa a fadin africa dake taimkao ga wadan nan mutane,mijin macen data zama haske wa al'ummar nigeria bama yankinta arewa kawai ba,matar data mallami centers na koyawa mata sana'o'i,centers na horar da yara 'yammata matasa,macen data shahara wajem gina makarantu da masallatai,matar data yi fice wajen samar da maqabartu,tallafawa tsofaffi da masu rangwamen gata wato hajiya sumayya sulaiman abdu,sannan jikoki wajen dattijo mai cike da dattako da karamci,tsohon ambassador muhammad mukhtar gwambe,yau rana ce ta musamman wanda ilajirin jikoki da 'ya'ya wanda suka fito daga barin familyn mukhtar na uwa da uba,da kuma na abokai,da duk wanda ya hada alaqa da sumayya dukkansu suna gidan,rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar amatullah da amatur rahman,wanda suke cika shekara uku da haihuwa,duk yara matan dake wajen suna sanye cikin dogayen riguna fara qal da aka yiwa don baqi wanda kyauta doctor almustapha ya bada a rabawa suk wanda ya halacci wajen,mazan ma jallabiya ce ta maza fara qal da baqin hirami a kansu,wajen yayi kyau matuqa da irin adon da aka masa na fari da baqi,shewa yaran suka sanya sanda aka iso da qaton cake din 'yan biyun cikin kwali aka sanyashi a muhallinsa aka budeshi jiran fitowarasu kawai ake.
Daga daya bangaren yaran suka fito,sanye da gown golden mai adon baqi,ta cikin tsahonta ya kai gwiwa mai gajeran hannu,sai ta saman mai dogon hannu,kallo daya zaka muau idan bakasan au wayw iyayensu ba kace daga jinsin karabawa aka dauko su,sun kwashi kyau ta kowanne bangare,sunyi kyau matuqa da gaske,takalmin qafarau kawai abun kallo ne,kana dubansu kasan sunji gata iya gata,daga bayansu kuma hajiya sumayyace dauke sa wani yaro wanda saika rantse usainin sumayya ne saboda kama,sanye yake cikin wando na yara three quater da baqin takalmi hightop na yara,sai farar shirt a jikinsa mai gajeran hannu,kan yaron na kwance saman kafadarta,kar kaso kaga sumayyan a lokacin tayi kyau na qin qarawa,sanye take da wani lafiyayyen lace wanda kyawunsa da tsarywarsa kadai ya isa ya gaya maka shi din mai tsada ne,peach ne mai dan turuwa,wanda aka yiwa ado d'ai d'ai da mint green,komai nata ya dace da shigarta,ita dinma kana dubanta kasan cewa Allah yayi halittar mace a wajen,wadda kyau da nutsuwa suka hadu suka nuna hutu da tsantsar nin dadin da take ciki,murmushi kawai take sakewa sanda taga yawan yaran da wajen ya tara,ciki kuwa harda yaran yaya abbakar,yaran halima da kuma yaran zainab,yaran farida huda da uwar gayya amira wadda ke cikinsu tana ta qoqarin saita wajen,sai yaran mahmoud da mus'ab mace da namiji,ga kuma yaran lamin da usman,musaddiq da huzaifa ne basa qasar banda nasu yaran saidai ayi hotuna a tura musu,baki daya wajen ya rude da hargowar yara badon komai ba sai hango boss dinsu amatur rahman,yarinyace mai tsokana rawar kai da surutu,itace usaina saidai tafi 'yar uwarta iya komai,saika rantse itace babba,kusan duk yaran dake wajen dan team dinta ne,dai dai ne suke sabga da amatullah,itakam zamu iya cewa tayo gado ne,gadon miskilanci rashin son magana da shiru shiru,hakan ya sanya amatur rahman ta rainata qwarai,don ma maibi musu ,a hakan ma sumayya tayi tsaiwar daka a kansu,wani lokaci MUKHTAR wanda shike bi musu wanda yaci sunayen mutane biyu shike shigarwa amatullah din,suna kiranshi da qarami yayin da almustapha ke kiransa da aboki,amatullah da amatur rahman kuma daughters,idan daya zai kira zaya ce daughter,qaramin dake hannun sumayya kuma shine MUHAMMAD mai sunan baban professor suna kiranshi amir.
Cikin lokaci qanqani aka soma gabatar da bikin birthday din,wanda yayi masifar qayatarwa,yara sun wala sunyi farinciki qwarai da gaske,a qalla sai magariba sannan suka soma haramar tashi,masu tafiya aka fara zuwa daukansu,masu kwana cikin gidan kuma kowa ya shiga ciki.
Bayan amira wadda kwana zatayi ra saka duka yaran mata sunyi wanka sai ta fice zata wajen ummi ta bawa qaramin yaronta nono,wanda yaranta biyu,babbar itace farha sai qaramin hadim,sumayya ta bari da su tana tsakiyarsu tana fama da su kan kowanne ya nutsu,mai cin abinci yaci mai kwanciya ya kwanta,wahalar da ita suke sosai don amatur rahman ta hada gang sunata tayi,miqewa tsaye tayi kawai tana kallonsu
"Wannan yarinya halan fitinar amira ta dauko ne?" Ta raya haka cikin zuciyarta,qaramar dariya taji an saki a bayanta,hakan ya sanyata waiwayowa a hankali,almustapha ne tsaye ya jingina da qofa,hannayenshi harde a qirjinsa yana murmushi da alama ita yakewa dariya,sauke hannyen nashi yayi ya fitota da hannu,don tabbas idan ya sake ya shigo cikin dakin yaran ba zasu barshi ya fita da wuri ba,ta gane sarai me yake nufi,sau ta dubi jikinta,don tunda aka tashi daga wajen batayi wanka ba,abinda take ta sauri tayi kenan kada yazo ya sameta a hakan,sai gashi bata cimma nasara ba,kafadarshi ya dage hadi da girarahi ya watsa hannayenshi yana murmushi alamun babu ruwanshi,ta nuna kanta da yatsa alamar niko?,ya kada mata kai yana nufin eh din,sai kawai ta juya ta dubi su amatallah tace
"Amatu.....ga abul_aulad" take kowa hankalinsa yayo kan qofar,kafin kace meye sun moqe aun dunguma kanshi,wayyo sumayyan ta gama masa tsiya,yau yasan ciwon kai babu fashi,idan ba'ayi da gaske ba ma duk yadda ya ciwa yau din buri bazai iya aikata komai ba,tana masa dariyan mugunta ta zame ta barshi da su,hakan ya bata damar yin wanka ta shirya