Author : Huguma Category : Complete Novels
can danginsu ba masu riqe zumunci bane,hakan ya sanya ko sanda iyayensu suka mutu ita taci gaba da riqon mukhtar,sosai taji ba dadi,ta dauki nauyin kayan gadonsu jamilan da fatima,kunya da nauyinta suka ishesu,godiya suka dinga mata,itakam bata kula ba,iyalan mukhtar sunfi qarfin komai a wajenta,ko banza abdallah ya hada haduwar da babu rabuwa cikinta,data koma gida sukayi shawara da ya abbakar da malam,ta barwa yaya yahansu gidansu wanda suka zauna a qarshe ita da mukhtar kyauta,tunda yanzu dukiyar abdallah ba komai bane don su barwa yayan gidan,kuka kam haka ta dinga yinshi,har sai data saka sumayya qwalla,tace mata babu komai haka rayuwa dama take,nan yayan ta fara shiryen shiryen komawa,tunda fes yake akan shiha lokaci lokaci ayi gyara yaya abbakar bai barshi haka ha don kafa ya lalace,gidan da suke ciki kuma zasu saka 'yan haya,sumayya tace ta dinga amsar kudin tana buqatunta na yau da kullum da su.
Suna suka sha hankali kwance,tayi kyau sumayyan sosai,duk wanda ya santa idan ya kalleta sai ya sake dubanta,kana kallon nata zaka san cewa nutsuwa da kwanciyar hankali sun samu muhalli cikin rayuwarta,a nan ta barsu drivanta ya dauketa ya maidata gida wajen mama,tafison ta ganta kusa da ita.
******** ****** ********
Da safe suna zaune falon mama ita da abdallah,yusra da yusufa da maman suna karyawa,yaran na gabanta baki daya kowa na karyawa tana fama da su,gyarawa wancan kofi gyarawa wancan zama,kayan bacci je jikinta ko wanka bata yi ba,yunwar data ke ji ta sanyata zama karyawa,ya abbakar dake shirin fita shi ya shigo yana fadin
"Mama...ga surukinki zai shigo ki gaisa...da alama sauri yake halan ka wucewa zasuyi" sam bata gane wa ya abbakar din yake nufi ba,kafin ta farga har mama ta masa izini,sai muryarshi taji a bakin falon yana niyyar shigowa.
Almustapha ne sanye cikin shadda dinkin tazarce,riga da wando,kanshi babu hula sai sumarshi dake kwance tana zuba qyalli,yayi kyau maqura har taji gabanta na faduwa sanda suka hada ido,ko yaya suka danyi kesa da juna na kwanaki sai taji ya sake zame mata sabo,ta soma tattare kofunan yayin da ya shigo ya tsugunna gaban maman yana gaidata,cikin jin kunya irin na surukuta suka gaisa,yana yi yana satar kallonta,ta kasa daga kai ta dubeshi kaman ta nutse,su yusra suka gaidashi yayin da abdallah ya isa gabanshi ya durqusa yana murmushi ya gaidashi,hannu ya miqa masa sukayi musabaha shina fuskanshi dauke da murmushi,yana son yaron sosai cikin zuciyarshi,saidai tarihin sumayyan da yaji yasan bazasu bashi shi ba,saidai yana kan bakanshi ko nan gaba sai ya dauke yaron,yadda yaron ua sake nutsuwa da girma sai yaji dama danshi ne,dama jininshi ne,saidai ko a yanzun yana jinsa cikin jikinsa tunda akwai jinin sumayya tattare da shi
"Tashi kije mana sumayya" mama ta bata umarni sanda almustaphan ya gama gaisheta ua fita zuwa dakin saukar baqi,a kunyace ta amsa,ta koma daki ta zura hijabi ya sake feffesa turare,dui da cewa qamshi ya kama jikinta,ko daga bacci ta tashi baka rasa jin qamshi a jikinta,don sai ta shafe loko da saqo na jikinta da turare ko ba kwananta bane kuwa,ko da basu tare.
Yana tare da abdallah hannunshi cikin nashi,da alama tambayoyi yake masa kan karatunshi,yana bashi amsa,kuma yana bashi amsa yadda ya kamata don akwai alamun gamsuwa tattare da shi,shigowarta ya sanya abdallan zame hannunshi ya fita ya basu waje,tsaye tayi suna duban juna,ya miqe ya isa gareta ya hadata da jikinsa
"Meye haka?,salon horo ne ko kuwa?,ni zakiyiwa qwalele?,kinsam bazan juri kallonki haka ba ko?" Murmushi ta saka tana ajiye boyayyar ajiyar zuciya,dududud satinsu guda basu ha juna ba amma tana jin kaman sun yi wasu watanni masu dama
"Tsoro nake ji ne?" Ta furta a hankali
"Tsoron me?"
"Ina tsoron ko kazo tafiya da nine ba tare da na shirya ba,in sake tafiya in bar mama" murmushi mai sauti ya subuce masa,sannan ya soma rada mata
"Hakan naso matata,saboda mi kadai nasan yadda nayi kewarki,saidai idan hakan bai miki ba...zan iya zama na jiraki har tsahon sanda zaki gama abinda kike yi,ba abinda bazan miki ba,kinsan saboda me?" Kai ta girgiza alamar a'ah,sai ya juyo da ita suna fuskantar juna idanunshi cikin nata
"Ke din macace ta musamman,mai fifita farincikin mijinta akan nata,mai fifita buqatarta akan tasa,ina sane da cewa,sau tari kikan dauki zabina ki bar naki,kikan gabatar da komai nawa gaban naki,kin maida kanki tamkar baiwa a gareni" sai ya saketa ya durqusa gabanta kan gwiwarsa
"Don me nima bazan zama bawa a wajenki ba?,wannan shine qarshen adalcin da zan miki,Allah ya halicci zuciya da son mai kyautata mata da qi da kuma gudun duk abinda zai munana mata" bata ankara ba qwallar zallar farinciki ta subuce mata cakude da murmushi,jin kanta take tana shawagi a sama,cikin wata duniya wadda take mata kwatankwanci da duniyar SARAUTAR MATA,sai ya miqe da hanzari ya rungumeta ta baya saboda cikinta ya masa shamaki ta gaba,sun jima a haka sannan ya janye yana dauke mata hawayen da yatsansa
"Ko a yanzun ma ka buqaci mu tafi ni mai biyayya ce a gareka" kai yake girgizawa cikin farinciki
"A'ah....kije ki gama shirinki a nutse" kai itama ta girgiza
"Um...um,bazan barka kana jira ba haka noor,kaje ka dawo"
"Na yadda,amma zaki rakani asibiti?,zanje na duba bayin Allah"
"Sam'an wa d'a atan noor" murmushi ya saki kalman ta masa dadi,kissing dinta yayi sosai,sannan yace mata zaya dawo da yammar su je.
A nutse ta fara shirinta,tana yi lokaci lokaci murmushi na qwace mata,lallai kam gaskiyar masu magana da suke cewa namiji tamkar yaro yake,sannan idan kika maida kanki baiwa shima zai zamto bawa a wajenki musamman idan yasan suka haqqoqinki da Allah ya dora masa.
Da la'asar sakaliya ya iso kuwa,ya dauketa suka tafi,a nan yake tambayarta abdallah,tace babanshi yazo ua dauke abinsa,tana dariya tace shikam ko yauahe gani yake kaman zan daukeshi ne
"Akwai kam lokaci,lokacin da zamu daukeshin kuma babu yadda zaiyi" murmushi tayi don bata data cewa,kaman kowanne lokaci sunji dadin zuwanshi,suka dinga gaidasu cikin girmamawa,kan ya wuce office sai da ya bincika,komai yana tafiya kan tsari da kulawa tamkar yana nan,daga bisani suka wuce office din yana maqale da ita.
Murmushi yaga taba saki sanda suka shiga office din,ya tambayeta mai ya fari?,sai ta kada kai tace mishi ba komai,kamota yayi ya matseta,ta saki qara a shagwabe,ya sake tambayarta,cikin muryarta mai sanyi tace
"Kawai ina tuna last zuwanmu office din nan,abinda ya faru" shima ya tuna sai ya saki murmushi ya lumshe idanunsa ya bude sannan ya kashe mata ido
"Na tuna babe....amma kada ki soma cewa zaki tsokaneni....kinsan me?,wani kwarjini kikamin wanda ban taba jin wata diya mace duk fadin duniya tun tasowata tamin ba a sannan na kasa miki scan,sannan ga wani shock da naji sanda naga skin dinki....kai babe,you are unique wlh" dariya ta saki ta dora kanta kan qirjinsa,daga gefe idanunta suka sauka kan hotunan mukhtar dake saman table dinsa,ta qurawa hotunan idanu,a hankali ya maida kansa inda yaga ta maida hankalinta,sai ya jata zuwa wajen,ya sanya hannu ya daga hoton yana kalla kafin ya dubeta
"Mukhtar?" Ya fada cikin sigar tambaya,idanu kawai ta zubawa almustaphan
"Am sorry" ya fada sannan ya hadesu waje guda ya yagasu qananu ya ajjiye saman teburin sannan ya waiwayo ya dubeta
"Ina da kishi a kanki babe.....am sorry if i hurt you" ya fadi yana duban idanunta da son karantar yanayinta,saidai taqi bashi dama,hannunta ya kama yana ci gaba da kallonta bayan ya matso da ita dab da shi har suna musayar numfashi
"Na yarje miki ki masa addu'a,ki sashi a addu'o'inki,amma banda nan" ya dora hannunshi saitin zuciyarta
"Nan din mallakata ce ni daya har ABADAN"knocking din da aka yi shi ya qwaceta,don ya soma dora mata wani nauyi,tamkar yana jiran amsar da zata bashi,daya daga cikin nurses din ne ta shigo dauke da file na mutanen da zai gani,cikin harshen turanci ya tambayeta na mutum nawa ne?,tace masa talatin,yace mata ta rage guda goman qarshe ta maida musu ashirin zai iya gani
"Sir....suna son ganinka da gaske ne goman da kace a cire din...."da hannu ya dakatar da ita kana ya mata nuni da idanu kan ta rage kaman yadda yace mata,qarasawa tayi ta irga ta debe din,sumayya ta matso kusa da shi murya can qasa
"sorry sir,ayi haquri a gansu" hararar wasa ya jefa mata
"Ke zaki tayani?,da wuya fa?"
"Na maka alqawarin ba zaka gaji ba,ina gefanka fa?"
"Really?" Ya fada yana dage mata girarsa guda daya,idanunta ta juya kafin tace
"Yes sir" tana sakin murmushi,kiranta yayi ta dawo da su din sannan ya sa mata kujera daura da shi ta zauna,da dai dai da dai dai patient ke shigowa yana dubasu,wani abun wanda yasan zata iya ya sanyata ta tayashi,wanda ba zata iya ba kuma yayi abinshi tana kallo,suna tsaka da haka wata budurwa ta shigo,kana kallonta kasan tana ji da kanta,cikin yauqi ta zauna kan kujerar da marasa lafiyan ke zama suyi bayani,sai fama take tana wani basarwa,sam bai daga kai ba bare yasan wanda ya shigo,hankalinshi na kan sumayya dake cike takardar wadda ta fita take shigar da wasu abubuwa da yace ta shigar,akwai fikira tattare da ita da basira mai dimbin yawa,komai tayi sai kaga hikima a ciki,tamkar likita haka ta tsara komai yana kallonta murmushi irin na gefen baki na fita kadan kadan,hakan ya sake sanyawa ya tafi da patient din data shigo
"Me kika karanta ne?" Ya tambayi sumayya fa kanta ke duqe tana rubuta kwanan wata,dubanshi tazo yi sai suka hada idanu da ita tana dubansu,hakan ya sanya maimakon ta bashi amsa sai ta masa alama da idanu na ana jiranshi,sai a sannan ya dauke kai ya dubi patient din,murmushi ta sakar masa,ya dauke kai yana bude file din nata
"Me sunanki?" Ya tambaya saboda yaga kaman ba suna kan file din da alama sabo ne
"Meela" ta bashi amsa tana yauqi
"Meye ne meela?" Ya tambaya a akausashe don ya soma jin haushin yadda take wani gwalangwaso
"Eh da shi ake kira ne amma real name din ja...."
"go straight to the point,akwai masu jira,meke damunki?" Ya tambaya yana rubuce rubucensa,sumayya na gefe dariya na son qwace mata,ya koma sak doctor almustaphan dan gidan baba prof data sani a baya,nuqu nuqu ta soma yi saboda ganin sumayya a wajen,tsaf ya karanceta,sai kawai ya rufe file din nata ya tura mata gabanta
"Zaki iya tafiya" ya fada yana kafeta da mayun idanunshi
"Ai..ai sirri ne" ta fada cikin in ina,juyawa yayi ya dubi sumayya da dariya ke ci,amma sai ka zata batasan meke faruwa ba
"I said the door is opened ko?" Ganin cewa da gaske yake ya sanya ta samawa kanta nutsuwa ta soma masa bayani,magunguna ya rubuta mata yace taje ta karba ya sallameta ta miqe ta fice.
Dariya sosai sumayya ta saki kafin nxt patient ta shigo
"Me?" Ya tambayeta yana kallonta,da kanshi kuma ya saki fuskar yana dariya,ya gane me takema dariyan,sai ya cafko yatsunta ya soma lanqwasa mata,ga dariya ga zafin lanqwasa matan da yake,da qyar ta qwaci kanta
"Ku kam mata wlh i dont know.....kai...kai" ya fadi ba tare da ya gama fadan me zaice din ba
"Duka ke kika jawomin,da tuni na gama mun tafi ina gida ina hutawa,ko baby bamu gaisa da shi ba" ya fada yana shafa cikinta,turo qofan da akayi ya sanyashi janye hannun nashi,a nutse yaci gaba da dubasun har ya gama sannan suka tattara suka nufi gida.
Cikin falon nashi dake dauke da dakin bacci biyu suka sameta kwance tana kallo,sanye da riga shimi doguwa zuwa gwiwa,gajeran hannu ne da ita hannun vest,ciki ciki ta amsa sallamar tasu sannan ta daga ido ta bisu da kallo.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖
*~NA~*
*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*
*WATTPAD:HUGUMA*
*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)
1⃣0⃣5⃣
*Bismillahir rahmanir rahim*
*Allah S W T yana bayyana kansa cikin qur'ani mai girma da*
*FA'AALIL LIMA YURID(mai aikata abinda yakeso*
*ya Allah muna gareka kayi mana jagoranci*
_____________________________________
*Wannan shafi sadaukarwa ne ga*
*HAUWA'U AG tare da diyanta AHMAD*
Ba wanda ta amsa sallamarsa a cikinsu,hakan ya sanya sumayya tayi wucewarta ba tare data sake cewa komai ba.
Satinsu biyu dai dai a kano suka koma dubai,bayan sun ziyarci gidan maimmartaba sarkin rano,mahaifin ummi,tsoho mai ran qarfe,karon farko kenan da sumayya ta kai ziyara,tsantsar soyayyar da tsohon kewa almustaphan ta shafi sumayya,kowa haba haba yake da su yana neman wajen ajjiuesu,taga kara taga karamci,ba qaramin dadi zuwan yayi mata ba,duk da bata samu zuwa gidajen sauran 'yan uwa ba,amma tayi alqawarin duk sanda tazo kano toba shakka zata sake zuwa musu,kyautar girma tsohon yayi musu shida matanshi,duk da mahaifiyar ummi ta rasu,amma matan baban nata sun daukeata tamkar diyarsu,suna farinciki da juna suka rabu,tun a sannan ummi taso riqe sumayya har sai ta haihu amma almustapha ya shafawa idonshi kwalli yace ba yanzu ba zai kawota idan lokacin yayi,yayin da cikin zuciyarshi ma sam ba haka bane,don baida niyyar kawota din,yana ganin meye amfaninsa a matsayinsa na likita kenan.
A hankali kwanaki suka ci gaba da wucewa,ba abinda ta daga qafa ko ta sauya game da kyautatawar da takewa almustaphan,dukkan wani abu data sani cewa yana so takan sanyashi gaba da komai nata,lamarin su'ad kam sam baya damunta,duk wani iskancinta da tambotsanta basa gabanta,sai taga dama ma zata ganta bare wani sabga ya hadasu,abu daya take qoqari a kai shine tausar almustapha a duk sanda ta kunnoshi,sam bazata so ace su'ad din tabar gidan na,kullum fatanta shine Allah ya shiryata ta gane illar abinda take yi,ta tabbatar da cewa duk duniya bata da wata mafita matsawar almustapha ya sawwaqewa su'ad tofa za'a ce itace sila,bayan duk wanda zaiyi alqalancin baisan meke wakana game da zamantakewar auren su'ad din cikin gidan ba,saidai hasashe dai kawai.
A haka cikinta ya shiga watanni tara har ya soma yunqirin shiga na goma,kallo daya zaka mata ba zaka so sake dubanta ba sabida tausayi,sosai cikin yayi wani girma har wani lokaci sai ta tallafeshi idan tana tafiya saboda girmansa da yadda ya sauko qasa,ta sauya kamanni sosai kamar ba sumayyan ba,munin da tayi a da nafila ne,har bata son kallon kanta a mudubi,sau tari idan taga almustapha na kallonta sai ta kau da kai tana tunanin munin da tayi yake kallp,saidai shi sam ba haka bane cikin zuciyarshi,tsananin tausayinta ke damunshi,ba don kada yayi riga malam masallaci ba da tuni ya yankata ya cire mata cikin ta huta,yakan tallafo fuskarta ya saki murmushi
"Ki daina boyen fuskarki,a hakan kinmin kyan da ban taba ganin kin yimin irinsa ba,kinsan me?" Sai ta kada kai cikin murmushi
"Da zaki sake zama haka nan da wata takwas ma bayan kin haife wannan cikin ina so,da nafi kowa murna"
"Kayimin addu'a Allah ya rabani da wannan ma lafiya"
"Yadda zuqar numfashina ya zamemin dole haka wannan addu'ar ta zamemin dole" ya fada yana karata da jikinsa tare da shafa bayanta a hankali yana ci gaba da yi mata addu'a cikin ranshi.
Semina ce ta kamashi ta sati guda wadda za'a yi a china ta 'yan kasuwa,sam yace ba zashi ba,ita ta tausashi da qyar tace ba'a jiran haihuwa sai sanda Allah ya kawota,ko kadan baison tafiya don ko fita ya rage,tausayi take bashi matuqa,hatta tashi sai tayi da gaske take iya yinsa ko shi ya dagata,ita ta tayashi hada kayanshi tana yi tana tsokanarshi wai ya zama rago,jawota yayi jikinsa yana dan mintsinarta yadda ba zata ji zafi ba yana murmushi
"Laifin wa?uhmmm babe,bake kika maidani haka ba?" Dariya ta saki,ta jawo hannunsa ta dora saman cikinta
"Laifin wannan ne ba nawa ba"sake matseta yayi a jikinsa yana sakin murmushi,tasan duka hanyar da zata sashi nishadi.
Sai da ya hadata da babban asibitin dake qasar wanda anan yake musu aiki lokaci lokaci,ya basu lambarta lambar gidan da adress,sannan itama ya bata number dinsu,sannan ya karba mata nurse guda daya wanda suka tanada saboda jinyar marasa lafiya wadda zata dinga zuwa tana kwana da ita,sam bai fadawa ummi ba don ya tabbatar cewa zatayi ya turota nigeria,shikuwa baison ko daya abinda zai rabashi da ita dai dai da minti daya
Tattaki ta masa har zuwa cikin falonta,kasancewar ranar girkinta ne,ya jawota kusa da shi ya riqe dukkanin hannayenta cikin nashi yana duban qwayar idanunta
"Kimin alqawari zaki kulamin da kanki har na dawo,ba tunani ba damuwa,kinyi alqawari?" Murmushi ta sakar masa mai kwantar da zuciya ta gyada kai
"Nayi maka noor,Allah ya tsaremin kai ya dawo min da kai lafiya"
"Amiiin baby na" ya furta yana lumshe idanunsa sannan ya matso da ita gab da shi yayi kissing goshinta zuwa wuyanta.
Tare da su'ad suka rakoshi har bakin mota,sai da driver ya ja suka fice sannan kowacce ta juya zuwa ciki,wani kallon banza take jifar sumayyan da shi gami da jan dogon tsaki,bata kulata ba don idan da sabo ta saba,tayi wucewarta ciki abinta.
******* **** ********
Bayan kwanaki biyar da tafiyarshi ne inda suke saka ran dawowarshi jibi,tun safe take jin ciwon mara kadan kadan,saidai bata gayawa ko nurse dinta ba saboda tunda cikinta ya shiga wata na goma take fama da irin hakan kadan kadan lokaci zuwa lokaci,yanzun ma fitsari ne ya tasheta,sai data dauki a qalla minti biyar ta iya yunqurawa ta miqe,mararta ta amsa sai data ce wash sannan ta iya miqewa a daddafe ta qarasa bandakin mararta na ciwo sosai,koda taje fitsarin kadan tayi sai ciwon da ya dadu,dawowa tayi cikin dakin ta soma kai kawo a tsakar dakin,a jikinta take ji tabbas naquda take,bata da maraba da abinda take ji lokacin haihuwar abdallah.
Tsahon awa daya tana gumurzu babu sassauci,hakan ya sanya ta fito falo a daddafe,ta dauki waya ta kira lambar nurse din,cikin sakanni kadan ta iso ta dubata ta tabbatar haihuwa ce,saidai akwai saura,asibitin ta sanarwa,babu jimawa saiga mota sun aiko da ita suka daukesu suka wuce,su'ad taji motsinsu,ta dauka wasu ne ta leqo da taga sune ta koma tayi kwanciyarta abinta.
Daki ne na musamman suka bata,dauke da na'urori kala daban daban bayan ta sauya riga zuwa ta asibiti,tun tana daure ciwon har abun ya soma wuce