Advertisements
Chapter 111 Reading Kundin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kundin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Complete Novels

Chapter   111 / 120

330K to 333K   out of 359.7K words

shine tara su take,ba abinda take da su,shi kansa yasan babu wani anu qwaya daya da na kusa da shi bama iyalinshi ba da zasuyi kukan basu da shi ko yafi qarfinsu,shi a ganinsa babban abun kunya ne ma ace kai din wani je,ko Allah ya maka rufin asiri,ana maka kallon mai rufim asiri,a ganka cikin kama kai kyau amma iyalinka a wahale ko cikin mummunar kama,wannan shine babban abin kunyar da magidanci zai aikata wanda zai jawo masa tur da ala wadai a bakunan al'umma.

       "Abu abdallah" ta furta a nutse,tunda yaji sunan yasan itace,amma hakan bai sanyashi ya waiwayo ba,sai ya nutsu yana jin yadda take takowa zuwa inda yake tsaye,bata dakata ba sai data sha gabanshi,ta tsaya tana dubanshi idanunta cikin nashi kaman yadda nashi yake,duk da cewa a cikin hijabi take,duk da cewa daga bacci ta tashi batai wanka ba,duk da cewa ba ko digon kwalli cikin idanunta amma bata fasa yin kyau ba cikin idanunshi,kyanta cikarta da kamalarta sun fito muraran,ta jima tana kallonshi wanda sannu a hankali dumin da zuciyarsa tayi ya soma sauka,da wannan damar tayi amfani ta soma cewa
"Ina ganin bata haka ya kamata ka bullowa anty ba....bazaiyiwu dare daya kace sai ta maka girki ba bayan can bata saba ba,a mata haquri a bata dama ta koya tukunna...."
"Wacce damar?,wacce dama za'a bata ne sumayya?" Ya furta cikin sanyi,saidai daga yanayin yadda yake maganar kawai kasan ranshi akwai sauran damuwa a ciki
"Akwai damar data wuce na sai mata rana guda cikin ranakun makaranta catering school?,ta koya ita kadai?,cikin gida ko a can duk wanda take so?......daga yau bana son ki sake sanya baki cikin wannan matsalar...ki barmu" ya fada cikin salon dakatarwa,yawu ta hadiye kafin ta sake lanqwasa murya
"Kayi haquri idan hakan ya bata maka,banyi ba da niyyar shishshige...rayuwarka rayuwata ce,haka nan rayuwarka rayuwar su'ad ce,hakan na nuni da cewa dukkaninmu abu guda ne...kwanciyar hankali nutsuwa da zaman lafiyar dayanmu yana da amfani a garemu baki daya,bazanso ace kullum kai da ita ba kwanciyar hankali ba....hakan zai iya shafata zai iya shafar iyalin da muke son samarwa nan gaba,tunda dai muna tare da ku"idanu ya zuba mata yana karantar tsantsar gaskiyar dake cikin zuciyarta da takeson fadi,hankali nutsuwa da karamci ne zallah cikin kalamanta,don me yasa ta samu dama irin wannan maimakon tayi qoqarin tarwatsa zamansu da su'ad ta mallakeshi ita daya saima take qoqarin gyarawa?,kyakkyawar zuciya ce itace amsa,wadda ba kowanne bawa Allah yake wa baiwarta ba,sai 'yan baiwa daga cikin bayin nasa,maimakon ya bata amsa kawai sai ji tayi ya janyota cikin jikinsa ya juyata da hanzari ya rungumeta ta baya yana shinshinarta,duk da cewa batayi wanka ba amma hakan bai hana wannan qamshin nata mai sanyi fita daga jikinta ba,dumin fatarta ya dinga ratsawa cikin tashi,hannunshi ya dora saman cikinta yana yawo da shi,wani farinciki na maye gurbin bacin ranshi,duk sanda ya farka da shi yaje farkawa cikin ranshi,kullum yana lissafe da ranar da zaya iso cikin duniya
"Wannan ne abu mafi muhimmanci da ya kamata ace kinyi zaki tsaya kina wani tsarani" dariya ce ta kubce mata ta soma qoqarin boyeta
"Au tsara ka ma nake yaya?"
"Waye yayan naki,yau kuma yaya na zama?" Girarta ta dage sanda yake leqo fuskarta
"Eh....ko nayi laifi?"
"A'ah....bakiyi ba" ya fada yana cikata tare da durqusawa gabanta,tasan me zayayi tunda ya fara kware mata hijabi,ba dama su tsaya inuwa daya sai ya fara lalubar cikinta,baya ta ja tana ware ido tare da kada masa yatsa alamar a'ah,sosai idanun nata suka fito sun sake wani fari tas da su,hakan yaso shagaltar da shi
"Sulhu nazo nema ba gaidaka muka zo yi ba" sai ya miqe daga durquson da yayi yana ci gaba da kallonta tare da nuna kanshi da yatsa
"Ni kuka yiwa haka?,zamu hadu,awa ashirin cif suka rage" dariya ta saki ganin yadda yake kwatantawa da hannunshi,ta juya taba niyyar ficewa,duk da yadda tayi kewar lafiyayyar fatarsa amma hakan bazaisa ta bashi dama suyi wani anu sq zai sosa ran su'a din ba,abinda ko ita aka yiwa ba zata taba jin dadi ba
"Amma kaman zazzabi naji jikinki ko?" Waiwayowa tayi tana dubanshi
"Ina jin hakan idan na tashi da safe,amma da nayi wanka shikenan bana sake ji"
"Ko nazo na dubaki?" Ta gane sarai wayo yake son yi mata sai ta saki qaramar dariya sannan ta juya ta fice tana cewa
"Mun yafe".

       Kacaniya sosai ke tashi a kitchen din kamar wadda zata dafa abincin baqi dari,ta rasa inda zata tsomala kanta,gefanta sumayyan ta nufa da niyyar dafa ko couse couse ne sharp sharp tunda tana da miyar hanta a fridge,har ta dauko tukunya taji su'ad ta fasa ihu,da sauri ta waiwayo kana ta nufeta,tukunya ta soma dorawa bayan ta kunna gas din,sai da tukunyar ta dauki zafi sannan ta taro ruwa ta soma zubawa,tururin da taga ya taso ya nufo hannunta shi ya sata sakin qara ta yarda cup din ruwan nan ua tarwatse a wajen har ya kashe wutar gas din gas ya soma fita,da hanzari sumayya ta qarasa tana ambatar subhanallah ta kashe gas din,sannan ta dubi su'ad data janye gefe
"Amma dai bakiji ciwo ba?" Harara ta watsa mata,dukkan komai itace ummul aba'isin data tsiri yi masa girki da ya sashi cewa itama sai tayi,da can ai basu san dora tukunya gidan ba idan ba kuku ne yake nan ba,ganin bata amsa mata ba ya sanyata nufar wajen ta sauke tukunyar daga saman gas din ta zubda ruwan ta zuba sabo sannan ta sake kunnawa ta dora,inda suke ajiyan kayan tea ta nufa ta hada ganyayyaki masu dandanon da tasan almustapha naso ta dinga gwadawa tana zubawa ta gama ta sanya ganyan shayin ahmad tea ciki sannan ta maida murfi ta rufe,su'ad na gefe haka kawai taji kishi ya rufeta yadda taga sumayyan nayi,itakam bata lura ba tace da ita ne kawai
"Idan ya dahu zakiji yana qamshi sai ki juye a flask" tsaki ta bita da shi
"Nima na iya ai basai an nunan iyawa ba" bata bi ta kanta ba tayi ne dama kawai saboda mijinsu,tunda ta sani tunda ya kafe tofa sai tayi kuma sai ya dandana ko baici ba,idan bai masa ba dandanon baci zaiyi ba haka zaya fita da yunwar cikinsa.

       Tana tsaka da bare plaitain ta soma jiyo qamshin dahuwar shayin,cikin flask din tea na alfarma dake kitchen din su'ad ta zabi daya ta fiddoshi ta bude ta ajjiye cikin sink,tukunyar ta tsurawa ido,yadda take tururi kawai ya sanya ta tsorata,ta yaya ake juyewa kawai take tunani,haka tayi qundunbala ta janyo towel hand socks dake maqale a hanger da suke ajiye towels na kitchen ta zura a hannunta,murfin ta fara budewa tayi wancakali da shi nan ma tayi gefe tana haki,ta dauki a qalla minti biyar ta rasa ya zata sauke,murmushin mamaki ya qwacewa sumayya,ashe da gaske akwai irinsu su'ad a duniya?,wannan mece a cikin mata,sai kawai ta miqe ta isa bakin tukunyar ta ciri safa daya ta sauke tea din tana juyeshi a flsk din,tana tsaka da juyewa ta matso kuda da ita
"Waike wa ya sakaki,ce miki akayi bazab iya ba?" Sai data gama juyewa ta daga kai ta kalleta
"Na san zaki iya ai,kawai taimako ne kuma ba laifi hakan ko a musulunci" shiru tayi tana daure fuska tare dq zare idanu har ta gama ta kulle flask din bayan ta daurayeshi ta wuce gurin nata sabgar.

      Kusan dai har ta gama bata san me su'ad ke ciki ba,tana gamawa ta juye plaitain dinta ta dumama liver souce dinta ta fice ta bata kitchen din.

       Tun daga lokacin matuqar tana kitchen din zata mata iya gyaran da ya dace,bata damu da duk abinda zata fada ba,tana yine kawai saboda almustaphan,tun tana masifa har ta dawo saidai harara,sau tari dariya take baiwa sumayyan,saboda ta lura da cewa tsabar girman kai ne kawai ke dawainiya da su'ad din,wani lokaci qunshe dariyarta take kawai idan tana girki,abin sai wanda ya gani,taka hau yanar gizo ne ta dubo yadda ake yi,wani abun bai ciyuwa hatta gurin wanda ya takura din sai ta dinga yi,idan har ya ciyu to ranan sumayya na kusa ta sanya hannu,cikin qanqanin lokaci su'ad din ta fara gane shayi ruwa ne,tayi roqon tayi magiyar ya samo mata mai aiki yayi funfurus da ita,har kukan takaici da wuya duka sai da tayi ,ya share tamakar baisan tana yi ba,don wannan ce kadai hanyar da zai hora ta kan iskancin da take ji saman kanta,har sumayya a wani dare take roqarshi ua samo matan wadda zata kama mata,saboda tana ganin yadda ake gwagwagwa wajen dafa shayi ma kawai,har yau ta kasa dauke yadda ake,ita dinma shiru ya nata kaman baiji me tace ba,ganin hakan ya sanya taja bakinta ta tsuke,tasan tunda yayi hakan baison zancen ne,sai da ya tabbatar ta dahu sannan ya samo wadda zata dinga taimaka mata,da sharadin tare zasu dinga yi tana ganin yadda akeyi.

      Abu na gaba daya soma jan hankalinta shine yadda ta fuskanci maan din na nuna tsantsar kulawa da riritawa ga cikin dake jikin sumayyan,da fari ta dauki abun duka wasa,sannu sannu ta soma fahimtar soyayyar da bata taba gani yana yiwa wani abu ba ita yake gwadawa abinda ke cikin dako duniya bai iso ba,bata tabbatar da haka ba sai a wani yammaci wanda ranar sumayya zata karbi girki.

       Tun da yamma tana zaune babban falonsu,bata faye zama cikinsa ba sai jifa jifa amma yau ta kasa ta tsare,sam sumayyan bata damu da zamanta ba,sabgoginta take hankali kwance,zuwa qarfe biyar ta gama shirya masa dining tsaf da kalar abincin da yace yana so,bayan itama ta hada wanda ranta ke so,shinkafa ta dafa ta zuba wake a kai ta bare kifin gwangwani a kai,sannan ta soya manja ta yanka salad tumatir albasa da cocumber,tana da yajinta tun daga gida wanda kusan shi ya tada mata kwadayin cin fara da man ma,salad dinne kawai bata gyara ba don haka ta barshi ta shiga wanka,ta shirya tsaf cikin wani wando ya lafe a jikinta kamar a jikin nata aka dinka shi,da kadan ya zarta gwiwa,wandon baqi ne hakan ya sanya ta saka shirt fara,ta gyara gashinta ta daureshi da baqin ribbom ya sauka har saman kafadunta,fashion tayi amfani da su baqaqe masu adon farin stone ajiki,lite make up ce a fuskarta wadda tasan tafi burge almustaphan,feshe jikinta tayi da turare sannan ta laluba cikin kayanta ta zaro abaya,har ta zura sai kuma ta cire,sam yau sai taji bata sha'awar saka ta,bata bari su'ad ra ganta cikin irin wannan shigar,yawanci tafi zama haka sanda suke falonshi ko nata falon su biyu,wasu slippers masu kyau baqaqe da suka bayyana kyan farar qafarta ta zura sannan ta tako a hankali ta fito.

      Qarar bude qofar falon nata da rufewa ita ta soma jan hankalin su'ad din,idanu ta zuba mata baki daya,sannu a hankali wani kishi ya soma sokarta na ganin yadda sumayyan tayi kyau kamar 'yar tsana,kai kace drowing ne na girly,cikin da take tsammani zai batata sai gashi ya zame wani ado a jikinta,ya shiga wata na biyar ya zauna daras a jikinta abin sha'awa,ko daya bai tafi  da hips da boobs da take da su ba saima qara fito da su da yayi,karon farko data soma ganinta cikin yanayin shigar,a hankali ta janye idanunta daga kanta kishi na nuqurqusarta,da ciki ma kenan ina ga tana ita kadai?,ta yiwa kanta wannan tambayar,da qyar ta iya hadiye yawu ta maida idanunta kan t.v taci gaba da kallo ba don tana fahimta ba,itakam dukkan abin nan da take batasan tana yi ba,kanta tsaye ta shige kitchen tana daga tsaye ta soma gyaran salad dinta.

        Tunda ya shigo baki daya tayi gaba da dukkanin imaninsa,ruwa ya shigo sha amma baki daya ya nemi qishirwar ya rasa,sai kawai ya harde hannunshi a qirji ya jingina da qofa yana kallonta,baiso ma tasan ya shigo bare ya ta daina kaikawonta,ilahirin jikinta yake bi da kallo,wani sanyi da farinciki na saukar masa,godiya yakewa Allah cikin zuciyarsa,ba shakka duk yadda yaso ga son dai daita matsayinta cikin zuciyarshi da sauran mata yasan yayiwa kanshi qarya,abune ba mai yiwuwa ba,koda ciwon makanta da ciwon bacewar tunani zai kamashi yana da tabbacin zai iya gane randa yake ranar girkinta,tun daga harabar gidan da yake iya ajje motarsa kama da duk wani lungu da saqo na gidan sauyawa yake,ba'a magana qamshi tsafta da sauransu,sai yake jin kamar harda iskar gidan ma sauyata ake,babu mamaki ko don tsananin soyayyarta da kullum kwanan duniya ake linka masa ne?.

        Sai data gama yankawa ta isa gaban famfo ta tara shi cikin ruwa,da hanzari taji an jawota,ko da daga bacci ta tashi tasan waye,mannata yayi da jikinsa ya zagaye hannayensa saman cikinta,sannan ya dora kanshi kan kafadarta
"Barka da dawowa....barka da dawowa sanyin idaniya hasken cikin gidansa....tun dazu naji yanayin gidan ya sauya ashe yariman maza ne ya iso" baisan sanda ta juyi da ita suna fuskantar juna ba,idanunta cikin nashi tana masa wani irin kallo,shi dinma kallon yake jifarta da shi,ya gaza cewa komai,ko yaushe furucinta na musamman ne a gurinsa,duk abinda zata furta ya isa kunnenshi mai dadi ne,mai laushi ne,mai taushi ne mau faranta zuciya tare da zare mata gajiya da baqinciki,kasa cewa komai yayi sai kallon kallo tsakaninsu tare da jifan juna da murmushi,bakinsu kawai ya hade waje daya yana aijata mata da wasu kisses masu zafin gaske,ganin yana neman wuce gona da iri a muhallin da bai dace ba ya sanyata tureshi suna maida numfashi,ya matsa din amma bai bar jikinta ba,dubanta yake da rikitattun idanunshi da suka sauya lokaci daya,cike da shauqi yake dubantan nata
"A kitchen muke fa" ta fada a shagwabe,hancinta ya kama ya dan jaa
"To waye ya jawo?,irin wannan shigar ko gaban wa na ganki hakan na iya faruwa" ya fada da qyar cikin muryarshi dara fara jirkicewa
"Bamu gaisa da baby ba" murmushi ta saki
"Wannan baby......wanne irin qauna ne haka my maan" kada kai kawai yayi yana murmushi,qugunta ya riqo baki daya da hannayenshi
"Qauna?,indai wannan ce qauna to kam bakiga komai ba,babu abinda kika gani babe....banajin zan iya bayyana qaunar da nake mishi ko mata,daga cikin dalilan da ya sanya kenan ban damu da duba me zaki haifa min ba,ko me kika haifamin ina so ina maraba da shi,gudan jin muhammad almustapha ne da summyn malam" murmushi ta saki sosai saboda sunan da ya kirata da shi har fararen haqoranta na bayyana,dubanta yake shima yana murmushi wani farinciki na shigarshi,da kanta ta yaye masa t.shirt din dake jikinta zuwa saman cikinta,ya durqusa a hankali hannunshi saman cikin.

     wani wawan tsaki mai shiga kunnuwa suka ji anja,su'ad ce wadda tun shigowarshi cikin kitchen din ta kasa samun nutsuwa,baki dayan hankalinta ya karkata kitchen ne,ta kasa zama har sai data biyo bayansu,kusan duk rabin maganar tasu cikin kunne da idanunta suja yisu,wanda sam basu san da shigowar tata ba banda yanzun,ko kusa ko alama bata taba sanin cewa haka almustaphan ke qaunar haihuwa ba,tayi tsammanin cewa ra'ayinsu daya a qidarsu daya,saboda ganin ko alama bai taba mata magana kan rashin samun juna biyunta ba,abinda bata sani ba shine yana sawa rashi lokaci ne,idan yayi zata haifa masa,bugu da qari yana tausayim macen da bata haihu ba,hakan ya sanya yake ganin girma da qimar ni'imah har gobe
"Amma dai wannan abun bai dace ba ko?" Ta fada zuciyarta kamar zata fadi qasa,waiwayowa yayi yana dubanta
"Shigowa kai tsaye ba tare da yin sallama bane bai dace ba ko ko meye?" Kasa cewa komai tayi don tasan ita ta kawo kanta,ta sani cewa duk ranan girkinta hatta da zurga zurga sumayyan bata fiya ba,data gama uzurorinta ta masa sallama shikenan sai da safe,mazewa ta sake yi kishi na cinta
"Kitchen wajen kowa ne,na shigo daukar abu sai na fasa saboda ku?"
"Yaushe kika fara labe?,kina tsammamin banga shigowarki ba?,kina tsaye tsohon minti goma?" Mamaki ya cikata,bata yi zaton ya ganta ba,da shigowa daukan abu tayi niyyar fakewa tayi boren qarya,da idanu ya tsatstsareta yana hukuntata da kallonshi,wanda ta san fassarar hakan sarai,duk sai ta daburce,numfasawa yayi ya dauke kanshi daga gareta fuskanshi daure ya maida ga sumayya data soma wanke salad dinta
"Muje ki shiryan ruwa nayi wanka"amsa masa tayi da to,ta rufe salad dinta ta ajjiye gefe sannan ta ratsa ta fice,sai data fice daga kitchen din sannan ya maida kallonsa ga su'ad dake tsaye tana cije baki cikin takaici,a hankali ya tako zuwa gabanta,daf da ita ya tsaya tazarar dake tsakaninsu bata da yawa
"Me yasa ko yaushe baki daukan gyara?,baki gyaran kuskurenki cikin sauqi?,Kada kiyi abinda zai siya miki raini,ki guji yin abinda bai dace ba,abinda duk kikasan ba'a yi miki ki nisanci yiwa wani,umarni na baki ba shawara ba" baya ya danja sannan ya juya shima ya fice,yafi kowa sanin halinta,tafi gane tsauri,daukar sauqi take tamkar wata isa ce tata tasa ake mata hakan.

       Dukkanin maganganunsa ba damunta sukayi ba a yanzu,abu daya tak ke mata yawo cikin kwanya da qwaqwalwa,so qauna kulawa da tsantsar soyayya da ta gani zalla a qwayar idanunshi yana nunawa ga ciki dama wadda ke dauke da cikin,me yake shirin faruwa ne?,shine tambayar da take wa kanta,a hankali qwaqwalwarta ta soma mata tariyar wasu shekaru can baya da suka shude,shekarun da a cikinsu ta fidda mahaifarta,a sanda anty kubra ke zabga mata fada,a lokacin da take gaya mata tayi kuskure,take gaya mata zata iya dana sani a gaba,take shaida mata matakin kama almustapha a hannu da kyau shine ta ajjiye masa iri,ta hada jini da irin gidan baban,shine zata samu dukkan abinda take so,zata zama tasu ta har abada,jinta take kawai a sannan,gani take labarin qanzon kurege ne kawai,tunda bata ga wani damuwa ko alamu tattare da da almustaphan ba,saidai a yanzu jikinta ya soma sanyi,wutar kishi ta soma nuna mata akwai wani abu dake shirin faruwa,tattalin da take gani wajenshi a kanta ya zarce soyayyar da yake mata ita daya face harda ta abinda ke cikinta,indai ko haka ne itace mafi cancanta data samu wannan launin soyayya da qauna mai ratsa gangar jiki da zuciya,saidai zata sanya ido taga shin abinda take hasashen haka ne?.




*gobe ina da uziri,idan kuka jini shiru saidai kuyi haquri,duk da zanso ace na muku,so nake mu kammala littafin nan kusa

111 / 120