Advertisements
Chapter 107 Reading Kundin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Kundin Kaddarata Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Complete Novels

Chapter   107 / 120

318K to 321K   out of 359.7K words

Tana tsaka da bude robar taga fitowar eesha ta haura sama,da alama wajen ummi zata,kamar tace mata ummin na sashen baba sai kuma ta fasa tunda ba shirginta take shiga ba,ta kammala shan ruwan ta ta maida robar ta rufe ta kama matattakalar benen ta soma haurawa saman,tana tsakiya eeshan ta fara saukowa,bata dubeta taci gaba da hawa abinta,tana step din qarshe eeshan ta iso inda take,wata wawuyar bangaza da bata zata ba bare tsammata eeshan tayi mata,wanda hakan ya sanya sumayyan yin taga taga baki daya tayi baya,ta gama saddaqarwa ta gama yawo,saboda step.ne ya kusa ashirin wanda ba shakka idan har ta samu nasarar komawa da baya sai ta gangara ta kan kowanne,cikim azama tare da kiran sunan Allah taji kamar an turata gaba,singalin qafarta ya daki qasa ya bafa wata qara,ta sanya hannayenta ta dafe qasa sanda take faduwa,wanda banda hakan da saman cikinta zata fada,suma hannayen qarar suka bayar ta zube ta gefen hannunta na dama daidai sanda taji muryar ummi cikin qaraji tana fadin
"Hasbunallahu wani'imal wakil,innalillahi wa inna ilaihi raji'un aisha!!" Ta qarashe fadi tana haurowa saman cikin wata iriyar sassarfa da gaggawa,idanu eesha ta soma fiddawa gabanta na wata matsananciyar faduwa,tasan tata ta qare,ya akayi har ummi ta iso wajen bata lura ba?.


Tuni ummi ta isa inda sumayya ke yashe,azaba da radadin da hannunta da qafarta daga buge kadai sun isheta,ambaton sunan Allah akwai take tana jin yadda qashin qafarta ke zugi da tsuko,a rude ummin ke tambayarta da qyar ta bata amsar qafafunta,ta matsa qafar sai ta sanya qara sabida azaba,cikin matsanancin bacin rai ummi ta waiwaya ta dubi eesha
"Ashe baki da hankali eesha?"
"Wallahi ummi....." Ta soma fada cikin rawar jikibda rawar murya,tsawa ta daka mata wadda ta sanya hantar cikinta kadawa tana gaya mata ta bace da wajen,sai da taga saukarta sannan ta maida hankalinta ga sumayya taba mata sannu,tausayinta na kamata,taimaka mata tayi sai data jinginata da kujera sannan ta dauki waya ta kira baba da anty maamaa.


Kusan lokaci daya suka shigo,salati anty maamaa ta dinga yi,shi kanshi baban shiru yayi ranshi na sosuwa,ba bata lokaci ya kira driver yasa ya fito da mota suka sanya sumayyan ciki
"Inaga ba asibiti ya kamata aje ba,wajen masu gyara za'aje a duba mata qafan da hannun,tunda Allah yasa bata fadi kan cikin ba" inji ummi,hakan ya sanya baba ya kira mutumin dake musu irin wannan aikin,basu da nisa sosai shi yasa bai bata wani lokaci ba ya iso.


Sai daya duddubata sannan ya tabbatar musu qafarta gocewar qashi ce,hannun kuma targade ne,zaiyi mata gyara,dui wanda ke wajen sai daya tausaya mata,tasha wuya sosai wajen gyaran,haka ta dinga hada gumi taba kiran sunan Allah kaman zata suma,murqususu take ga ciki a gaba daya fara tasawa,kafin a gama ta hada gumi sharkaf,ya gama ya baiwa ummi maganin da za'a ringa shafa mata da kuma yadda za'a kula da wajen,yace duk bayan kwana bibbiyu zaizo ya dinga dubawa,godiya baba yayi mishi sannan ya sallameshi.


Kusan kasa runtsawa sukayi baki daya,sai daga bisani baba ya fara tafiya,anty maamaa kam bata iya tafiya ba ita kanta sai wajen biyu na dare,ummi kuwa kwanan zaune tayi tare da sumayyan,sajida ma da qyar tayi bacci,duk tausayin sumayyan ya cikata,eesha kuwa tunda ta shige ba'a sake jin motsinta ba,ita so tayi cikin ya zube idan yaso ayi mata hukunci baki daya,ran ummin ya kai maqura wajen baci,tausayin sumayya kawai ya isheta,ta riga ta gama yanke hukunci a gobe aysha zata bar gidan,kome mamanta zata fada saidai ta fada,don ba zata yarda tana jibtana gani a bata amana ba kuma ta kasa riqewa,me zata cewa almustapha idan wani abu ya samu cikinsa?


A dakin ummin ta kwana,nan ummi ta kawo mata ruwa da roba ta daura alwala saboda yadda qafar tayi mata tsami,a hankali ta waiwayo tana gaida ummin bayan ta idar da sallar,amsawa tayi tana tambayarta jiki ta amsa mata alhmdlh,sannu ta sake mata tare da bata baki kan abinda eeshan tayi,ita kunya ce ma ta kamata,sai kace ummin ce ta aikata?.


Qarfe biyun rana ummi ta isa dakin eeshan ta taddata kwance,zumbur ta miqe tana gaidata,a tsautsaye ta amsa tana ajjiye mata kudi
"Ki tashi maza ki shirya ki wuce gida,koda wasa kada kice zaki sake dawowa gidan nan a yanzu,tunda ba yau ashe kika soma qoqarin aikata mata hakan ba,idan banda tsabaar rashin mutunci eesha bata ci darajata ba a wajenki?,ko duka bata ci darajar wannan ba ai taci darajar dan tayin dake cikinta ko?,to ki tashi ki shirya ki wuce gida" kuja eesha ta saki,abinda take bege wato so yake yayi mata nisa,garin neman gira zata rasa idanu
"Yanzu ummi sabida ita zaki raba zumuncin dake tsakaninmu?" Cikin mamaki ummin ta waiwayo tana dubanta
"Van raba ba,amma a yanzu dai na raba har sanda zata bar gidan nan,na riga na gama magana da mamanki" ta juya tana ficewa,abun takaicin ma sam bata ga nadama tattare da ita ba,don ko qafar benen bata taka da niyyar zuwa dubata kan abinda tayi mata ba.


Wunin ranar yini tayi tana tofa fatiha a wajen,haka ya kawo mata sauqi sosai kan radadin dake damunta.


****** ***** *******


Ranar da abin ya faru baki daya bai samu zama sosai ba,ayyuka sunyi musu yawa can company,sau uku yana kira yaji a kashe.


A gajiye ya dawo,a falo ya sami su'ad din,tana kwance dai dai saman kujera,sanye da gajeran wando da qaramar vest iya ciki,ko ina baja baja da kwalayen data gama ciye ciye,yayin da bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,tsallaketa yayi ya nufi bedroom dinshi kai tsaye ya rage kayan jikinsa,duk abinda yake tunanunta na mqale a ranshi,yau daya tak da baiji muryarta ba jinsa yake kaman maraya,yayi tsammanin zai iya share mata kaman yadda ta shareshi amma sai yake ji abun ba mai yiwuwa bane a wajenshi,towel ya dauka ya wuce bathroom yayi wanka.


Ko mai bai iya shafawa ba bare ya ya sanya kaya ya janyo wayarshi ya soma lalubar wayarta,a kashe aka sake ce masa take,sai yaji hankalinsa bai kwanta,lambar ummi ya soma laluba cikin sa'a ta shiga,fitowar ummin daga dakin kenan taga shigowar kiran
"Ummi an yini lpy?"
"Lpy lau almustapha ya aiki?"
"Alhamdulillah" sai kuma yayi shiru,halin nashi ya motsa,itakam da zaiyu shirun da yafi mata,tasan wal'alla sumayyan yake nema,ita kuma batasan zancan yaje kunnenshi,tafiso matarshi ta warke saidai yazo ya tadda labari kaman ma ba'a yi ba
"Ummi.....sumayya" ya fada kaman mai tsoron fadin
"Uhmmmm,wani abu ne?"
"Tun jiya bamuyi magana ba,ko zan samu jinta?" Kaman ta hanashi saidai ba yadda zata hanashi magana da matarshi
"Kashe zan kai mata"
"Ummi batta a haka zan jira" dariya ma yaso bata har sai data ce
"Almustapha?,kaman wanda network din zai gudu?" Kunya ta kamashi amma sai ya dake yayi shiru yana sauraron tafiyar ummin.


Tana zaune ta gama shirin baccinta tana karanta wani qaramin littafin labarai na larbci,qafarta na saman matashi mai laushi,hannunta daya na ajjiye saman cinyarta,wayar ummi ta miqa mata tana cewa
"Almustapha" littafin ta ajjiye ta karba gabanta na faduwa ta kara kunnenta sanda ummin ke juyawa ta fice,shiru yayi kawai yana saurarenta tamkar baya kan layin yana hadiye wani abu,fitar numfashinta kawai ya soma samar masa da nutsuwa,sallama tayi masa sai da ya bada tazarar wasu sakannni sannan ya amsa
"Why sumayya why?,wato idan ban nemeki ba ba zaki neme ni ba?"
"Ba haka bane.....wayarce bansan inda ta fada ba"
"Kaman yaya?" Ya tambayeta,da sauri ta gyara zancanta
"Amm...ina nufin ta dauna daukan chargy ne" tsaki ya ja sannan yace
"Kamanni ace wayar matata ta har takai matsayin da don kanta zata daina daukan chargy?,ki cire layukanki ki bar amfani da ita,gobe da safe za'a kawo miki wasu,daya ni kadai zan dinga kiranki da ita always ta zama akunne kusa da ke,dayan kuma ki kira duk wanda kika ga dama"
"Na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara arziqi"
"Amin.....nifa gaskiya na fara gajiya,haquri na ya kusa qarewa fa....a qa'ida ai cikinki ya shiga wata uku...am a doctor nasan yadda zan kula da mata ta" gabanta ya fadi,yau bisa dukkan alamu rigima yake ji tunda taji muryanshi ta fuskanci haka,tayi qas da murya
"Habba mana.....duka saura sati nawa lokacin da suka ce ya cika,ka qara haquri mana please kaji?" Shiru kawai yayi yana sauraren muryarta yana nazari
"Me ya sameki?" Taji ya furta kai tsaye,sai ta hau fiddo da idanu tana kalle kalle,ta daga wayar ta duba voice call ne ba vedio call ba bare tace yana ganinta
"Ni?...ba bau komai me ka gani"
"Akwai wani sauyi tattare da muryarki,kuma jikina ya bani haka"murmushi tayi duk don ta dauke hankalinsa
"wrong doctor,baka canka dai dai ba,am fine,ina shirin yin bacci ma ummi ta shigo"
"Ban yarda ba,but....tunda kince haka ne is ok,ki kunna wayarki kafin a kawo wata"
"An gama yallabai" murmushi yayi,yanajin kaman tana lallabashi ne kawai ya sauka daga kan layin,sai kawai ua datse kiran yana jin wayar kawai bata yi masa ba,jikinsa bai bashi ba,sam ma ba irin wannan hirar yakeso suyi ba,hankalinsa baki daya yayo nijeria.


Ajiyar zuciya ta saki da taga ya datae layin,da alama halin ne yau ya motsa,dole ta tashi sajida ta sanyata ta dauko wayar ta jona a chargy sannan ta kunnata kafin ta kwanta.


****** ****** *******



Washegari misalin sha daya na safiyar ranan yana tsaye gaban mudubi yana shiryawa,kominshi a nutse a tsare,ya gama komai tsaf yana taje sumarshi ya janyi wayoyinshi dake gefe,tun jiya da ita ya kwana cikin ranshi,yana jin mawuyacine idan baiyi rashin ta ido ba yaje kawai ya daukota,yana jin kaman sun shekara goma ne basu ga juna ba,number baba ya soma don ya gaidashi kaman kowacce safiya,idanunshi suka sauka kan takardar dake gefanshi,ya saka hannu ya dauko ya bude ta,ranshi ya baci sosai ba wai don kudin da ya kashe kawai kan takardar ba,sai na yanda su'ad tayi burus da maganarshi.



Yana tsaka da duban takardar ta fito daga wanka tana tsane jikinta da towel
"Yanzu wai har ka shirya zaka fita,nifa gaskiya na gaki da wuni a gida ni kadai kaman mayya,bayan nasan wuraren shan iska birjik amma ka hanani zuwa ko guri daya"
"Mene wannan?" Ya tambayeta yana nuna mata takardar,daga kai tayi ta kalleta sai kuma ta basar tana hade rai
"Nifa gaskiya banda interest shi yasa na ajjiyeta" ranshi ya kuma baci,ya gyara tsaiwarshi yana kafeta da idanunshi masu sanya mutum yin laushi
"Kinsan nawa na biya miki?,kudin mutum nawa na biya ake kadai don kije ki koya ke kadai din?"
"Sai na biyaka kudinka kamin total,amma bazan iya zuwa ba gsky,ai ba ajina bane ba aganni wani ina koyon girki,haka kawai Allah ya maka arziqin da zamu iya daukan kowanne irin cook kawai sai na bata wa kaina lokacin koyon dafe dafe?" Ta amsa mishi ba tare data dubeshi ba ta soma shafa mai,kai ya gyada yana qoqarin hadiye bacin ranshi,ya maida takardar saman madubin ya ajjiye,shi kadai yasan hukuncin da zaya yanke mata,sai ya janyo jakarshi ya riqe a hannunshi,daya hannun kuma yana riqe da wayoyinshi ya soma takawa zai fice
"Ka mance yau zani siyayya?" Ta furta cikin harshen nasara,banza yayi da ita yaci gaba da takawa har ya fice.


A falo ya tadda mai musu girki ta kammala shirya abinci,cikin girmamawa ta rusuna da harshen larabci ta gaidashi ya amsa yana tsaidara,jakarsa ya bude ya fidda rafar kudi irin na qasar dubai masu azabar kauri da yawa ya miqa mata,shaida mata yayi ya sallameta a aiki ga wannan taje na nemi sana'a tayi,cikin rawar jiki ta sanya hannu biyu ta amsa,ita kanta tasan kudin ba qananun kudi bane,zasu isheta yin duk sana'ar da takeso,tabbas ba qaramin taimakonta yayi ba,ta duqa tayi masa godiya mai yawa sannan ta fice.


Yana kurbar tea yake lalubar lambarta,muryarta kawai yake so ya soma ji a wannan safiyar kafin ya fice,daidai lokacin da a wancan bangaren sumayya take takawa a hankali har ta fice daga dakin saboda mai gyaran ya gaya mata ta dinga takawa ko yaya ne.


Sajida na tsaka da mopping tsakar dakin ta jiyo ringing din wayar sumayyan,ajjiye mop stick din tayi ta nufi inda wayar take,sai taga sunan man,tasan halinshi sarai,idan ya kira mamarsu kiran ya zama miscal yayita fada kenan,hakan ya sanya ta daga ta sanar masa yanzu zata kaima sumayyan kada ta zama misscall,gaidashi ta soma yi sannan tace
"Antyn ta fita tattaka qafarta,amman bari na kai mata" jikinshi ya sake bashi irin yanayin jiya,sai ya ajjiye cup din hannunshi yana tattara hankalinshi gareta
"Tattaka qafarta?,me ya samu qafan?" Ya tambayeta yana addu'an kada dai ace cikin ne ya soma sanya mata kunburin qafa har yanzu
"Faduwa tayi" gabanshi yayi wani mummunan faduwa,a rude yace
"Subhanallah?,garin yaya?"
"Anty aysha ce ta turota daga upstair" bai san sanda ya miqe tsaye zumbur ba,cikin matsanancin tashin hankali da qaraji yace
"Upstairs?,mahaukaciya ce ita?,me ya sami qwaqwalwarta?"tsoro ya kama sajida kaman ita tayi laifin,cikin rawar murya
"ban sani ba uncle"ganin yarinyar ta tsorace ya sanyashi qoqarin sanyaya ranshi saidai bakan ya gagara,sai ua rage sautin muryarshi yana tambayarta yadda akai abun ya faru,bata boye masa komai ba ta kwashe duka ta gaya masa,harda nata wanda ta zuba ruwan klien ta fadi,ranshi ya kai qololuwar baci
" kada ki gayawa kowa munyi waya kin gayan me ya faru,ok?"
"Yes uncle" ta fada tana addu'a cikin ranta Allah yasa unclr man yaci uban anty aysha,dama taji haushi sosai abinda ta yiwa anty amira,har kuka tayi,kullum kuma sai ta tausaya mata idan taga tana dingisa qafarta.


Ya jima jingine jikin kujera yana huci shi daya kamar wani mayunwacin zaki,ya rasa wanne hukunci ne ya dace da yarinyar,ba shakka mutum biyu ne rak a duniya zasuyi masa haka ya qyalesu daga ummi sai baba,ya kamata ya nuna mata wa ta tabo,ya kamata ta gane kuskurenta,baiga dalilin ma da zai sanya ya qyale ta ba,data aikata mishi wannan abun data aikata din gwara tayi masa gagarumar sata,gefe guda haushin sumayyan ya kamashi,don me zata boye mishi?,me yasa ba zata gaya mishi ba,yanzun da wani mummunan abu ne ya sameta haka zata yi shiru,batasan muhimmancin lafiyarta a gareshi ba?,kai bama lafiyarta ba,batasan muhimmancin kanta baki daya tattare da tashi rayuwar ba,bazai iya jira har sai ya koma gida sannan ya dauki mataki ba,hakan ya sanya ya soma lalubar lambar CP,bugu uku kacal ya daga,bayan gaisuwa sama sama da kuma ya bayan saduwa ya soma shaida masa abinda yake da buqata,eesha yake so su kamo mishi ita su sanya masa ita bayan kanta,kuma ko waye yazo nemanta kada su sake su bada ita,kai baya so ma su bari asan a station din da suka ajjiyeta,duk da baban eeshan wani ne amma sahun gwiwa ya take na raqumi,hakan ya sanya ba musu suka amsa mishi bayan ya musu bayanin laifin data aikata,ya tambayi mahmoud adress na school dinsu ya aika musu,a yau yaje da buqatar ta kwana bayan cell,wayar ya kashe yana furzar da iska,tabbas sai ta gane shayi ruwa ne.


Yana tsaka da duba number ma'aikacin kamfanin jirgin fly emirate dake yankar masa ticket su'ad ta sauko,cikin taku dai dai kai tsaye ta haye dining,ta soma jawo kayan break din tana duba abinda ma'aikaciyar ta dafa ba tare data lura da sauyawar yanayin almustapha ba,tsaki taja don ita duka abincin bai mata ba,choice din almustapha ne,kenan bata mata nata ba,baki ta bude ta shiga qwala mata kira,saidai har tayi ya gama shiru maqatau ba dalilinta,sai ta miqe da niyyar shiga kitchen nemanta tana zazzaga masifa,banza yayi da ita har taje ta gama bulayinta ta dawi,zuwa sannan ya gama waya da su,saidai dole yayi haquri yabi jirgin gobe da safe shine zai sauka dubai to abuja direct,hakan bai masa ba amma tilas ya karba haka,miqewa yayi ba tare da ya damu da qarasa karyawar ba,sai daya sauka daga step din sannan yace mata
"Na riga dana sallameta,tunda ba tare na auroku ba"
"Wata zaka sauya mana?" Ta tambayeshi ba tare data fuskanci me yake nufi ba
"Ki shirya fara girki da kanki karon farko tunda kika zama matar aure" ya bata amsa yana ficewa,zumbur ta miqe ta sauko da hanzari tabiyo bayanshi tana cewa
"Haba man,ya zamuyi haka da kai?,kaima kasan abinda bazai taba yiwuwa bane"
"Saiki maidashi mai yiwuwar" ya bude motar da kanshi duk da qoqarinbda drivern keyi wajen bude masa motar ya shige abinshi tare da bawa drivern umarnin ya shiga su tafi,binsa tayi da kallo baki daya tunaninta ya koma ga kitchen,gata can gaban tukwane tana fama da gas,kai ta girgiza wlh abinda bata taba yi ba ba zara fara ba yanzu,cikin fushi ta koma ciki kai tsaye ta shiga daki ta dauko wayarta,lambar hajiya khaulat ta soma nema wanda cikin sakanni ta daga,sai ta fashe mata da kuka,daga daya bangaren ta soma fadin
"Yaya?,lafiya?,waye ya taban ke?"
"Mommy man ne,wai kinji ya kori kuka na wai na fara girki da kaina daga yau,don kawai ya siya min foam na catering school nace bana iyawa,kuma na gaya masa ya gayan nawa ya kashe na buyashi,yanzu don Allah mommy nayi kama da wadda zata shiga kitchen zafi da tururi na qonata?" Wani shegen tsaki haj khaulat ta ja
"Shegen yaro tsagera,sai shegen zafin kai da taurin zuciya,to bai isa ba wlh,bamu aura masa ke don ki dafa masa abinci yaci ba,idan ma iya daukan nauyin mai girkin ne bai iyawa ko kuma girkin ne bata iya ba,nan kusa da mu akwai qwararrun masu girki professional zan aiko muku da daya,a aljihuna zan dinga biyanta,cikakkiyar baturiya ce ba abinda bata iya dafawa ba" murmushi su'ad ta saki tare da ihu
"Shi yasa nake sonki mamana wallahi"
"Uhmmm" tace
"Ni

107 / 120