Author : Maman Teddy Category : Complete Novels
uncle Mustapha ya riko hannunsa.
"Ina zaka tafi?".
Idunu jajur ya kalli uncle din, yana girgiza masa Kai, wallahi bazan zauna dashi ba idan ka matsa min za'ayi Dana sani, yanzu babu abinda ze hanani nayi abinda banyi a wancan lokacin ba, uncle kana da daraja da qima a idanuna to ka fada masa ya fita faga sabgata idan Yana so ya tsira da Dan sauran mutumcin Daya yage Mana to ya kiyaye shiga duk abinda ya shafeni, mu hadu a Sokoto two thirty flight dina ze tashi duk abin bukata a kwai shi a nan, idan ka shiga asibiti Faisal ze rakaka gurin malamina ka duba shi anyi Masa aikin spinal cord ne"..
Ya kada ya fice abinsa.
"Yanzu irin wannan Ina ranar ta ka zubarwa da kanka qima da girma saboda sakawa Rai hassada a banza, shima ya juya ya fice daga gurin zuciyarsa babu Dadi Dan ko kadan baiga laifin yaron ba an Bata Masa fiye da kima. ya bar uncle saminu ya kasa ko kwakwjwaran motsi.
[19/02, 11:46 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHI*
AISHAT ISAH MUSAH.
(Maman Fateemah)
Bismillahir Rahamanir Rahim.
P. 73
........... Tunda Zahra ta farka daga barci taji Sam Bata Jin Dadi jikinta ita ba Mai zazzabi ba duk jijinta ciwo yake Mata, ta Kuma kasa fita Dan Bata son su hadu da Dan gidanta kada ya Kara Bata kunya Dan taga alama tasa tayi kaura daga idanunsa sai ya iya yi Mata abinda yafi hugging ma ga Kuma uwa uba tana Jin bala'in nauyi Ya Abbas tunda ko banza yayan mijinta ne ya wani kwakumeta ko kunya babu, agogon waya ta duba karfe Tara saura kwata na agogon kasar, tattaunawrsu da Aunty Aisha ta ringa dawo Mata tiryan-tiryan. Tasha mamakin halin da aka saka mahmud Ciki yaga masifa da tashin hankali ace kowa yayi maka naqi, kuma dadin dadawa kowa ya kasa fashimtarsa, ta yarda kamar yanda Aunty Aishat din ta fada abun an Dade ana shirya shi Saida aka Sha Kan kowa sannan aka fasa maganar, kuma tayi wani irin tasiri Banda taimakon Allah da wani labarin akeyi ba wannan ba.
Yunkurawa tayi ta tashi sai taji tana bukatar kasancewa kusa dashi ta lallashe shi, abin tausayi be kuma abunda ya fada gaskiya ne, sai yanzu ta gane gundarin me maganarsa take nufi duk da na gari dole yabi iyayensa, kawai shedan ne ya tunzura ta ta hau dokin zuciya Mai mmakon ta Zuba Ido taga yanda abun ze kasance sai ta kasa ta hau fushin fari, ai dole ma hakan ce zata kasance tunda Yana da magabatansa, idan sun amince da auren da akayi Masa laba'asa idan Basu amince ba shikenan.
Tana zuwa wannan gab'ar taji wata irin faduwar gaba, kada fa iyayensa Suki yarda da ita a matsayin mararsa.
"No!!!. In Sha Allah mutu ka raba takalmin kaza.".
Ta sauko daga gadon gara ta fita ko tayi arba dashi tayi yanda tayi ta Shawo Kan kayanta.
Wanka ta shiga shaf-shaf ta fito ta shirya ta saka rigar cotton lace marar nauyi tana baza kamshinta, bata daura dankwalin lace din ba karamin gyale ta Dan rufe gashinta dashi ta sako plat shoes ta fito zata shiga kitchen tayi musu abin break fast kada ta Zama cima zaune sai dai ayi a Bata.
Parlourn ba kowa shiru sai karar a/c kakeji kawai sai Kuma sansanyan kamshin turarukan daki tunda gidansu akazo, kitchen ta nufa Kai tsaye saboda tana da yakinin masu gidan Basu tashi ba, da sauri tayo baya ganin mutum tsaye Cikin kitchen din daga shi sai boxer short da singlet, shima Jin motsi daga bayansa ga wani scent Mai shegen Dadi ya bakunci hancinsa yasa shi juyowa babu shiri.
"Ya subhanallahi!".
Ya fada lokacin daya Dora idanunsa Kan fuskar Zahra, da wani mahaukacin sauri ta juya fit ta fice daga Cikin kitchen din, shima sayyid da sauri ya aje cup din Daya dauko ze Zuba coffee din daya dafa.
Ko duriyarta sayyid Bai gani ba sai dai kamshin da tabar Masa.
Zahra na shiga daki ta Danna Masa key tana maida numfashi.
"Waye wannan Kuma da yake da irin wannan freedom din a cikin gidan matar aure irin haka? Gaskiya wannan rayuwar da sake, dole meu amor yazo su bar shi ai da matsala sosai gidan musulmi Kuma matar gidan Matashiyar mace Mai jini a jika, shaidan ake gudu gaskiya.
Wayarta ta dauka tana neman Aunty Hassana su gaisa.
______
Mahmud yana fita kofar baya ya koma ya shiga bedroom dinsa ya dauko abokiyar tafiyarsa jakar laptop ya shiga mota sai tashin motar uncle Mustapha yaji Dan ya fita har waje baiga mahmud din ba Bai Kuma kawo Yana Cikin gidan ba.
Da sallama ya shiga dakina da aka kwantar da Baba Malam din Yana zaune shi kadai Yana lazimi ga kayan break fast Nan an kawo Masa Bai Kai ga cinsa ba.
Sallamar Baba malam ya amsa Yana fadin.
"Sannu da zuwa mahmudu, Amma yau kayi sakko, ya Naga ran naka babu Dadi lafiya dai ko?"
Dan murmushi yayi duk da iyakarsa fuska.
"Babu komai kawai dai bana Jin dadin jikina ne".
Ya fada Yana karasawa kusa dashi ya gaishe shi ya Kara duba Jikin nasa, abinci ya dauko ya hada Masa yaci sosai sannan ya fada masa Yana son yaje Nigeria a yau in Sha Allah, addu'a yayi Masa sosai tare da Kara bashi Baki yayi hakuri ta koma ga iyayensa, sadda Kai kasa yayi kafin yace.
"A karayi Mana addu'a can na nufa idan Allah ya amince Mana".
"Kai! Masha Allah kazo min da abinda ya faranta min Raina mahmudu ubangiji yayi maka albarka ya Kara Kare ka daga dukkan sharri abin halitta Dan isar Manzon Allah s a w.w, kaje babu abinda ze faru da yardar ubangiji,Ina Kuma Fadimar ko ba tare zaku tafi ba?".
"Eh su sai jibi zasu taho da Hasanata wadda Dan uwana da mukazo dashi ya dawo ya kawota ta duba ka".
"Ikon Allah ai Bai min bayani ba yace dai ga iyalinsa tazo ta gaisheni, yanzu mahmudu daman takwayene Kai? Koda Wai ban taba sani ba, ko danma Kai ai saidai hamdala Amma me kake fada".
Murmushi yayi Yana Dan shafa sumar Kansa wadda Tasha gyara.
"Ayi hakuri yanayin ne yazo a haka".
"Babu komai hakan shine dai dai Allah yayi yagora ya Kara arziki Mai dorewa".
"Allahumma Amin".
Nurses ne Wanda suke bada maganj suka shigo, suka gaisa da malam Cikin harshen turanci sannan suka gaisa da mahmud da yarensu, magunguna suka bashi ya Sha sannan suka fice,Hira sukaci gaba dayi inda Baba malam ya dinga bawa mahmud Addu'oi masu karfi na tsarin jiki sanan ya Kara bashi wata yace ya dunga karantawa duk bayan sallar farilla in Sha Allah badai sihirin Dan mutum ba.
BISMILLAHI WA BILLAHI BISMILLAHI MASHA ALLAHU BISMILLAHI WALA HAULA WALAQUWWATA ILLABILLAH ÷ QALA MUSA MAJI'ITUM BIHISSIHIR INNALLAHA SAYUBDULUHU INNALLAHA LAYUSLUHU AMALAL MUBSIDIN FAWAQA'QAL HAQQU WA BADALA MA KANU YA'AMALUN FAGULIBU HUNALIKA WQNQALQBU AAGIRIN.
Godiya sosai mahmud ya yiwa Malam yace masa ze tafi Amma baze wuce sati daya ba ko biyu ze dawo tunda ya fadawa doctor kada a sallamar masa patient sai tafiyarsa ta nuna kukunna.
Yana fita ya Kira Mr salahuddeen yace su hadu a Airport ze dauko mota.
Karfe biyu da mintuna flights din su Mahmud ya dago Nigeria text kawai ya turawa Ya Abbas, itama Aishar ya tura Mata nata da bayanin komai.
Sayyid ya Jima a tsaye a parlour ko zaga ta inda Zahra zata bullo Amma yaga Shiru dole ya koma ya dauko coffee dinsa ya wuce dakinsa.
Bai Jima da barin parlourn ba Aunty Aishar ta sakko Cikin gayunta kitchen ta shiga ta Fara aiki tana tunanin irin yanda Hussein ya gindaya Mata dokoki akan matarsa tana ganin soyayya Amma sai take ganin Dan uwan nata yayi zurfi da yawa.
Tana Cikin aiki Sayyid ya shigo yayi Shirin fita school.
"Aunty Ina kwanq?" Ya fada Yana shigowa ciki.
"Lafiya kalau Sayyid har an fito yau da wuri haka? Gashi ko break ban Gama hadawa ba".
"No Aunty I am ok, Nasha coffee tun dazu, Wai Ni Aunty bakuwa kikayi a gidan Nan ne ko Kuma gamo nayi da safiyar Allah wata"Ala?".
Dariya tambayar ta bawa Aunty Aishar,duk yanda akayi yaga Zahra kenan, Amma sai tace masa.
"Meta faru Kuma kake wata magana irin haka?"
"Wallahi Aunty ba maganar jocking Naga yarinyar India ko larabawa a gidan Nan har fa Cikin kitchen din nan ta shigo muna had a Ido ta fice kamar walkiya ko dana fita ko Mai kama da ita bangani ba wallahi".
"Eh bakuwa ce nayi Baku San juna bane shi yasa ita ma Bata San da zamanka a gidan bane shi yasa inaga itama tsorata tayi gaskiya".
"Wow! Amma daga Ina Kika samo irin wannan Mai zafin haka? Gaskiya za'a da ita Dan Allah Ina kamu wallahi daga wannan Kuma kallo ya Kare ki Fara min campaign Dan Allah".
Ya fada Yana hade hannu irin ba 'yan kabilar Hindi na nan Indian din🙏🙏.
Anzo gurin tab Allah kiyaye da mijinta baya nan da a gabansa zeyi wannan kwabar da kuwa sun kwashi 'yan kallo.
"Wai kana nufi sonta jakeyi kenan?"
"Kwarai kuwa".
Ya fada da tabbatarwa.
"To ai matar Aure ce".
Dafe Kai yayi Yana fadin.
"Oh my God! Waye wannan Mai sa'ar da yayi min shigar sauri Dan Allah?".
"Wanda ya fika sonta ne ya dauke abarsa".
Langabar da Kai yayi Yana fadin.
"Shikenan na wuce school, Amma fa I really loved her".
"Matar Auren?"
Baice komai ba ya saka Kai ya fice daga kitchen din ransa babu Dadi. "Allah ya kyauta, wato mahmud ya yiwa Sayyid wani irin farin sani kenan, yasan matukar zeyi arba da ita sai an samu matsala gashi kuwa ya kasa ba marad'a kunya".
Sai da ta Gama komai ta dauko abincin data Zuba musu ita da zahrar a wani guri ta aje basket din ta koma ta dauko wani Abu kaman story mat da table mat ya shinfida sannan ta koma sama lokacin sweet heart din ya fito daga wanka, taimaka Masa tayi ya shirya tunda shi azumin litinin da alhamis yakeyi itama Aishar lalurar mu ta Mata ta hanata dauka, fita zeyi Yana da wasu ayyuka da Mahmud ya turo Masa Wanda zeyi masa su, tare suka gangaro Aishar ke fadar .
"Bari na kirawo Zahra ki gaisa tunda ba lallai yau ku hadu ba naji kace sai dare sosai zaka dawo aikin da yawa".
Dan janyota yayi jikinsa.
"Kyaleta ai Dan uwanki ya dasa Mana 'yar kunya a tsakaninmu tunda yayi mata irin wannan wawar rungumar a gabana kamar ze bude aiki kinji yanda jikinsa yake tsuma kuwa a lokacin?"
"Kai sweet heart Banda fa... Dan kaga baya kusa, shida abarsa har zakace Wai jikinsa Yana tsuma Kamar wani sabon shiga".
"Ni dai abinda naji nake fada Miki bawai Qage nayi masa ba, Kika sani ko farin shigar ne koma Bai shigan ba".
Ya fada yana dage Mata girar idonsa Daya.
"Wallahi Kai dai Yaya Babba ne, Banda irin haka da gani kasan ai Yana shanawa dubi fa yanda ya damu daga Dan turza shi da tayi yanzu ma kaji yanda yake jaddada min na kular masa da ita kamar wata jaririya".
"Ke dai mubar maganar lokaci ne ze nuna".
Har gurin mota tayi masa Rakiya tana fada Masa zasu fita fa.
Sama ta koma ta dauko Afnan wadda ta koma barci tun da akayi Mata wanka Dan kada ta tashi suna can bazajiyo kukanta ba.
Dakin Zahra ta Dan buga kadan tana fadin.
"Pls open the door" .
Jim muryar Aunty Aishar yasa Zahra tasowa da sauri ta bude kofar tana sakin murmushinta Mai kayatarwa.
"Ina kwana Aunty?"
Ta fada tana karbar Afnan dake barci, can tsakiyar gado Zahra ta kaita ta kwantar.
" Ki fito muyi break fast tun dazu na kawo na koma na sallami sweet heart ne shi yasa".
Tare suka jera zuwa gurin da tayi musu shinfida, abincin gargajiyar ba bahaushe tayi musu kunun tsamiya ne da kosai sai pepper soup din cow legs.
Suna gamawa Zahra ta kwashe kayan ta mayar kitchen ta wanke su ta aje komai a muhallinsa, taso ta yiwa Aunty Aishar magamar guy dai data gani sai wata Zuciyar ta kwabeta, Bata sani ba ko kaninta ne shaqiqi muharraminta.
A gurin ta dawo ta Sami Aunty Aishar tana amsa waya daga ganin yanda take amsawa kasan ba wayar sawa bace Mai wayar Yana da girma da kima a idanunta.
Zahra Bata zauna ba ciki ta shige tana shiga taga Afnan tana daddaga kafa tana Wasa ta tashi, daukarta tayi tana fadin.
"My Afee Babyyy.."
Yarinyar na ganinta ta Fara dariya shaidar ta ganeta kenan.
Saida Aunty Aishar ta Gama wayar ta shigo tana fadin.
"Au Kice mutuniyar ce ta tashi? Sai ki shirya fita zamuyi yanzu guri ya kure sosai kinsan Hussein shi komai nasa baya fada sai guri ya kure, sosai jibi fa zamu wuce Nigeria shine yace muje kasuwa kiyi tsaraba shi ya wuce Nigeria".
Da madaukakin mamaki Zahra ta dago ta kalli Aunty.
"Ya wuce Nigeria?"
Sai idonta yayi kwal-kwal ta tabbata abinda ya fada gaskiya ne, shikenan ita Kuma haka tata kaddarar take.
Girgiza Mata Kai Aunty Aishar tayi.
"Haba Banda shagwaba Mana, keda kike fushi dashi, yasan ko yazo bazaki saurarasa ba shi yasa ya tafi tunda baisan laifin da yayi Miki ba kike dafa shi da naki salon, Dan Allah a rangwanta Masa shi bako ne a cikin soyayya Bai taba yinta ba ke Kuma Naga taki da zafi ta kamashi batayi Masa da Wasa ba".
Da kyar ta iya mayar da hawayen, da suka so zubowa ta rasa dalili itama tata zuciyar Bata da wani karfi a Kan lamarinsa.
"Shike nan Aunty inda sabo na Saba yayi tafiyarsa Bai fada min ba".
Aunty Aishat ji tayi yarinyar ta Bata tausayi, kenan shima Yana gwada Mata halin miskilancin nasa, nata ne baya iya jurewa.
"Ki rabu dashi tafiyar ce tazo masa ba zato kiyi hakuri dole zamu zauna ya daina Miki irin haka tunda ke ba sanin halin yawonsa kikayi ba, inaga duk duniya Amminsa kadai yake bude Baki ya fada Mata duk inda zaya a cikin duniyar nan kafin yayi fushi kenan".
A hanya ma sosai Aunty Aishar ta dinga bawa Zahra Baki harta Dan ware, sun shiaga manayan shagununan kayan sakawa Ganin Zahra taki daukar komai yasa Aunty Aishar lodar kayan da take ganin sun dace, sunje bangaren jewelry's ma ta dauka Kamar me shoes and bags ta dauka kamar Gori ita Zahra Abu har tsoro ya Fara Bata kashe kudi ake kamar yayi daurin cargo aka yiwa kayan Aunty Aishar ta cike komai sannan suka bar gurin, sun shiga kasuwa nan ma ba kananun kudi ta kashe ba suma awon cargo din tayi musu daga karshe suka nufi gurin gyaran gashi da jiki Aunty Aishat ta saki kudi ba kadan ba anyi Mata gyara iya gyara, suna Cikin Yi Mata gyaran jiki matar Mai gurin tazo tana tambayar Aunty Aishar cikin yaren indianci, tunda su dai basa Jin turanci duk da India suma suna English.
Zaru Aishat din tayi domin ta rasa yanda zata tunkari Zahra da tambayar domin wani Abu matar ta sakawa Zahra a hannu taga yaki Zama kuma a ka'idarsa na matan aure ne kuma an fada Mata matar Auren ce gyara kawai za'a Kara yi mata, magana matar tayi Mata akan taje ta tambayar Mata ita saboda tasan wane iri abubuwan zata yi Mata.
Aunty Aishar ji tayi abun yayi Mata nauyi gaskiya, ai da kunya taje tana titsiye yarinya da irin wannan tambayar,cewa tayi suyi Mata na 'yan matan kawai mantawa tayi tace musu haka ashe Bata tare ba.
Zahra har Saida ta gaji da Shan abubuwa, Miko Mata ake tana shanyewa Saida taji tana neman yin amansu sannan aka saurara Mata aka dosa tureren jiki, kunshi ne tace bata son irin nasu Mai yawan Nan sai akayi Mata Dan kadan Mai azabar kyau, lokacin da aka Gama Mata komai ta fito Saida Aunty Aishar ta shiga wani shock Dan yes matar bros ta wanku iya wankuwa Ina ma Yana Nan da yau dai saiya maida yawu kenan maganar sweet heart da kamshin gaskiya kenan tunda idan ba Rami meya kawo zancen Rami ance an saka Mata abun matan aure yaqi Zama kenan budurwa ce, ita kwamacalarsu nema take tafi karfin tunaninta.
Sun dauki hanya sosai Afnan na jikin Zahra duk tayi laushi da gani ta gaji, sai 'yar mita take Auntyn ce da Dan kallo inda suka tana ci gaba da driving din ta, tamabaya ta jefowa Zahra Wai dazu kun hadu da Sayyid ne da safe?".
Dan Jim Zahra tayi sai Kuma tace "ko wani Dana gani a kitchen daga shi sai boxer short da singlet Yana tsaye a gurin coffee maker?"
"Eh shi nake nufi".
"Na ganshi lokacin Dana fito da zummar na Dora abin break sai na gashi ba yanda ya kamata ba tunda baligi ne shi Kuma ba gidansa bane, Kinga ai Bai kamata Yana fitowa a haka ba,ko Dan bansan ya kuke dashi ba ko mamanku daya".
Wata kwana ta shiga kafin ta danyi tsaki..
"Wallahi kanin sweet heart ne, ni kaina bana son zamansa a gidan tunda idan Yana nan bana sakewa nayi duk irin shigar da nakeso tunda Allah yasa shi Mutum ne Mai shegen son Mata dan haka yau a sama Zaki kwana bana son samun matsala Daman abunda yasa na baki daki a kasa Ina muku wani zato ne ashae hasashena gaskiya ne, yanzu kuwa da baya kasar saina shige dake ciki gudun samun matsalar da yaketa jamin kunne a kanta".
Nisawa Zahra tayi tana fadin Allah ya kyauta.
Koda suka shigo Basu huta ba abin bude Baki suka yiwa masa.
A tsakanin kwana biyun nan Zahra ta gaji iya gajiya
Kuma Basu Kara haduwa da Sayyid ba,dan duk wata kafa Aishat din ta toshe ta yayi nacin har yayi zuciya Dan ko kasa Bata saukowa.
Ranar da zasu tafi Mr salahuddeen yazo ya daukesu da kayansu sai a ranar Abulkhairi ya dawo gida, har dashi za'ayi tafiyar.
[23/02, 12:00 pm] Abu Saleh: * AUREN HUCE HAUSHIN*
. AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah.
09061432330
Or
08055362975.
Page 75
......... Tunda jirgin su zahra ya sauka a filin jirgin sultan saddiq Abubakar dake Sokoto gabanta ke faduwa,tasan a Nan ne komai fa ze iya tabbata ko ayi ko a fasa gata a Sokoto sai Kuma abinda Rabbi Izzati ya hukunta shi ne ze tabbata, Afnan ce a sabe a kafadarta tana takawa a hankali tamkar Bata son taka kasar Dan da gaske ta Gama yin giving up a cikin Lamarinsu da mahmud.
Aunty Aishat ce tsaye a Kan kayan da sukazo dasu