Author : Maman Teddy Category : Complete Novels
Banda kada yaron Nan Sameer yaga Kamar ta raina abinda yakeyi da yanzu ta tsufa a Kano, sakon text ta turawa zahrar ta tashi ya nufi bedroom dinta.
**** **** ****
Tun bayan fitar zilai zahra ta wuce bedroom tabar Hajiya nacin abincin ta, a gurguje ta sake wanka ta gyara jikinta Bata wani Bata lokaci ba ta shirya cikin wata doguwar Rigar lace cotton Mai kalar blue black, anyi touching dinsa da silver ash yayi Mata kyau sosai.Bata daura dankwalin ba rolling tayi da ash din gyalen ta feshe jikinta da turenta ita abin har mamaki yake bata, ta rasa yanda akayi duk inda take sai taga turaren da take amfani dashi a gurin. Dan watsa hannu tayi irin baka gane Abu ba din nan.
Parlourn ta koma gurin Hajiya dai dai lokacin da su Sameer da Mahmud suka shigo.
"Bakin Hajiya ne yaki rufuwa data hango zahra ta nufo ta Fadi take "Masha Allah! Haka ake so wwnnan 'ya naga alama bazakiyi saken da za'a karbe miki miji ba, ki Kama abinki ki rike wallahi sonsa akeyi kamar goron hannun sarki ki matse kayanki tunda Allah kadai yasan gwagwarmayar da yasha kafin ki shigo hannunsa..."
Sameer ne ta katse Mata hanzarin zancen data dauko ya Fara fadin "ki tashi na mayar dake gida garin Zan Bari yanzu Banda kina Nan da nayi nisa a Hanya".
Shi kuwa Mahmud Banda kallon zahra ba abinda yakeyi gani yayi ta Kare Masa wani sanyin kyau a idanunsa, Kuma fir Taki yarda su hada Ido dasu duk kowa da kalar kunyar da takeji tasa.
"Hajiyarmu ya zaman guri Daya nasan kin gaji sosai ko".
"Mahmud din ta kalla Wanda ya nufo ta.
"A'a ban gaji ba ai wannan yarinyar da Abun gari take, jiya ma dai an Bata Mata Rai ne yasa na ganta Kamar marar wayo Amma yau ai ka gani sai Ina taka saka Dani takeyi".
"Dan Allah ki taso bana son nayi dare a hanya ke Kuma kin tsaya sai maimaita zance kikeyi, abinda ya wuce ai ya wuce".
Da sauri Zahra ta juya ta koma ciki ta barsu Sameer nata yiwa Hajiyar Dan zance, turarika da sabulai ta daukowa Hajiyar ta fito, lokacin Hajiyar na gyara lullubin gyalenta tana fadin "ai Zan dawo ne tunda ban karbo Mata dawa'in Dana saka ayi Mata ba a sanka, Kasan duk wannan jidaliyar ta jiya Bata Hana da almuru Saida Tofeek ya kaini Sanka naje na fadawa Malam karami ya taimawa jikata da maganin tsarin jiki Dana Baki, yo anyi sake Baki ya Kamata dubi fa yanda take tubarkalla, yo tunda ya fito da ita Nan ai magana kuma ta gare haka ze dunga reto da ita,to kasan wani idon da bakin ba masu kyau bane, shi yasa gara a dafata daga Nan" shi dai mahmud ban kunshe dariya ba abinda yakeyi yasan kadan da aikin Hajjaju ne hakan, shi Kuwa Sameer ya cika yayi fam shi yayi Dana sanin kawota gidan nan Dan Allah kadai yasan abinda ta fada Mata tunda kanwa Bata jiqa a bakinta.
"Wallahi Zan tafi na barki a gidan nan haba saboda Allah kin kama zance kamar an saka Miki batir".
Dakuwa tayi Masa ungo Nan. Dan nema kake wani zaro min Ido to tsoron ka zanji kome? wato gaskiyar ce baza'a fada ba".
Juyawa yayi ya nufi kofa da hanzari Hajiyar tabi bayansa itama zahrar da sauri tabi bayan Hajiyar, ji tayi an riko ledar da hannunta gaba daya ya dawo da ita jikinsa.
"Precious ba irin huge din Nan na welcome saiki wani shareni"
Ya fada Yana Dan goga Mata sajensa a gefen kumatunta cikin wani irin low voice.
Wani yar taji a jikinta.
Cikin shagwaba tace "Dan Allah ya Bari na rakata kada su tafi ban Bata komai ba, Kuma na saka Aunty zilai ta dafa Mata nama".
Juyota yayi suna facing din juna. "Baze tafi ba kawai ya gaji da surutun Hajiya ne itafa Bata gajiya da magana, kawo na gani dame-dame za'a bawa kakar tamu?"
Ya fada Yana duba cikin ledar.
"Inye ashe dai da wayonki irin wannan Abu haka? jazakumullahu khairan. Bari na Kara gyara Miki kudi ya Ciro daga aljihun wandonsa ya saka a ledar Yana fadin sai kice ta sayi man shafawa ko kice ta sayi goro, bari mu dawo ki bani abida ya samu, Kuma idan anjima Zaki rakani gidan su Sameer na gaishe da mommy sannan muje muga Mai sunana"
.
Bai saki hannun nata ba, a haka suka nufi kofar fita.
Taso ta zame hannunsa daga cikin nata tasan ba Karamin aikinsa bane su fita harabar a haka, kuma taga alama gidan da mutane da yawa ga kuma Hqjiya da Sameer.
Ganin kada ya Bata kunya yasa ya saki hannun ya rike ledar kawai kafin taje gurin motar ta shiga gurin su Aunty zilai ta gani ko angama.
Cikin ikon Allah ta samu an Gama soya Mata cikin roba, Ashe Daman tun safe suka dafa aka saka a fridge yanzu soyawa kawai sukayi, a ciki babban warmer aka zuba zilai ce ta dauko suka fito suka nufi gurin da suke tsaye suna jiran zuwansu.
Saida Motar tabar harabar gidan sannan suka juya suka koma, Saida suka wuce idanun jama'a ya janyota jikinsa Yana shagar kamshin jikinta, a haka suka shige ciki zame jikinta tayi tana Dan dubansa. "ga abinci Nan na kawo maka nan ko can table Amuje".
Dan bakinta ya shafa kadan ka Yana kwaikwayon maganarta..
"Bari nayi wanka sai muzo muci abincin nasan kema bakici ba ko?".
"Kai ta gyada masa.
Gurin da Hajiyar taci abincin ta gyara sannan ta dauko wata table mat da shimfida a kasa ta jera abincin, gurin kayan kallo taje da gani ko hadasu ba'ayi ba, ta tsuguna tana hadawa ya shigo, yayi wanka ya saka Riga armless da wando three quarter blue black na kamfanin Adidas sai fitar da wannan kanshin nashi yakeyi wanda har ya Zama constant a jikinsa, direct inda take ya nufa dago ta yayi "oya taso kibar wannan ba aikin ki bane akwai Wanda zaya hadasu".
Kai ta gyada masa ta bishi suka koma, abincin ta zuba musu sukaci Saida suka koshi, sannan ta tattara gurin ta dauke komai ta dawo ta zauna a gefensa.
Jikinta ya Dan kwanto Yana Dan matsa kafadar ta.
"Precious".
Ya Kira sunan sunanta.
"Na'am".
"Fada min me Haseenar ta fada Miki Kika yi yaji Zaki Kira min Ruwa? Banda Allah yasa Ammah tana yina da kin tayar min da zaune tsaye, ni na taho Ina mararin ki ke kuma kina gudun Zama dani ko?".
Sakin kafadar yayi ya kwantar da ita a cinyarsa suna facing na juna.
"Nifa na fada maka ba guduwa nayi ba to a cikinsu ai ba Wanda yayi min laifin da zanyi yaji? Kuma Dan lalacewa na tsaya Ina yiwa wannan Mai saffar mazan yaji,kawai dai Naga bazan iya tolerating na nonsense dinta ba,wato zatayi amfani da damarta tayi min illah tunda Nina hanata cikar muradinta ki? Ai naji ance tare kukayi karatu ba a UK? Dan Allah ka fada min waye Kai wallahi zuciyarta taki samun nutsuwa, abubuwan da nake gani a Nan sun girmewa tunanina, pls tell me, Me amor".
Tsuru yayi da Ido Yana kallonta Dan kalmar ta bashi mamaki data fito daga bakinta.
"A ina Kika iya yaren Portuguese?".
Ai Yana fadar haka ta bude Baki alamar mamaki da sauri ta yunkura zata fece ya mayar da ita jikinsa.
"Ya haka Zaki gudu daga tambaya".
"Nima bansan ko wane yare bane na fada sunan ne naji yayi min Dadi shi yasa na fada maka Ni ko ma'anarsa ban sani ba".
Ta fada tana Kara sunne Kai a kirjinsa.
"A'a idan ba Rami meya kawo zancen Rami? Meye na Jin kunya tinda kince Baki San ma'nar sunan ba duk da haka yau ranar Nan special ce a gurina badan da dutse tsakanin mu ba da Saina bada special gift Nima".
.
[2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
✨✨✨
MAMAN FATEEMAH.
Page. 47
📖🖋️
________Duk yanda Mahmud yaso zahra ta bashi amsa abun yaci tura da gaske take kunyarsa Bata taba zaton Yana Jin yaren ba, shima kyaleta yayi dan bashi da amsar tambayarta a yanzu dai sai hakan yayi Masa dadi, wata hirar ya dauko Mata ta tafiyar da yayi da ire-iren cigaban da yake ganin makarantun mu zasu samu, har aka Kira sallar la'asar suna gurin tashi yayi suka shiga ciki yayi Shirin masallaci.
Misalin karfe takwas da kwata suka fito zuwa unguwar da zata raka shi, sunyi wata irin dacewa dole idan ka kallesu ka Kara, Dan kallonsa tayi "Zan leka na yiwa su Aunty zilai sallama".
Daka ya amsa Mata saboda Yana amsa waya.
A parlour ta iskesu suna Hira, a gurguje suka gaisa ta fada musu zasu fita, a dawo lafiya sukayi Mata ta juya ta nufi kofa har ta kusa fita ta ji maganar Aunty zilai bayanta.
"Uwar dakina Ammah tace a fada Miki ki bude wayarki tana son magana dake, yanzu ba dadewa ta kirani tace na Kai Miki tawa, na fada Mata Mai gidan Yana Nan shine tace to idan kin fito na fada Miki lallai ki bude zakuyi magana".
Dan rausayar da Kai zahra tayi da alamun damuwa a fuskarta.
"Ni wallahi na kasa bude wayar ne laifi nayi Mata fa".
"Laifi Kuma kina Nan tana can akayi laifin?"
Kai ta gyada Mata alamar Eh.
"Dan Allah ki bude wayar kuyi magana ko hankalinta ya kwanta,Allah a cikin damuwa take".
"To shikenan sai mun dawo din".
Ta fice tana amsa a dawo lafiyar Aunty zilan.
Motarta daya kawo ta gani, Wanda ya Kira da safwan dazu ya fito daga ciki da alamar shiya kawota nan seat din kusa da driver Mahmud ya budewa Zahra Yana fadin "Bismillah"
Saida ta zauna sannan ya nufo gurin safwan din yayi Masa magana sannan ya shigo ya tayar da motar suka nufi gate din fita, a dawo lafiya masu gadin sakayi musu Dan ba mutum Daya zahra ta gani ba.
Sunyi tafiya Mai Dan nisa kafin ya riko hannunta Bai kalleta ba gabansa yake kallo yace.
"Kina tambaya ta wannan gidan na wanene ko?"
Ya Dan juyo Yana kallonta.
"Eh" ta fada a takaice.
"Gidan a hannuna yake, kusan Kuma ni aka wakilta a Kan ma'aikatan cikinsa to Yana yin rayuwa ne yasa nayi nesa dashi Amma yanzu bani da sabgogi da yawa Ina ga ma anan zamu Dan Zauna na wani lokacin kafin muga yanda za'ayi akan matsalarki ta fibroid din nan dan tunda aka fada min hankalina kasa kwanciya yayi Saida na Kira likitan dana fada Miki, shine yace ya kamata muje suyi nasu binciken su tabbar da abinda Nan din suka fada".
Dan marairaice Masa tayi.
"Nifa wallahi na warke na fada maka ba wani ciwo fa yanzu Dan Allah ka hakura, kaga su Ammah Basu San zamu Dade ba, kaga harda Mai aikinta ta bani aro fa Kuma kusan itace ma'aminciyarta a fannin abincin bangaren ta".
"Kin warke kamar Yaya? Ai abinda ze Hana a duba min lafiyarki sai ikon Allah kinaji fa Yana Hana Mata haihuwa Ni Kuma da nake son duk shekara ki aje Mana baby koma babies, idan Allah yasa nafi ki karfin jini ki dinga bamu twins, kawai lokaci kadan ki ciki gidan da 'ya'yan mu".
Ya fada Yana Kai hannunsa akan cikinta Yana kashe Mata Ido daya.
"Oya talk Mana kinyi shiru".
"To me kakeso nace ai ka Gama Yanke hukunci".
Saita share maganarsa ta biyu.
Gidan Sameer suka Fara nufa Sam Sameer din besan da zuwansu ba Saida ya kusa da shiga kuntau din sannan ya kirashi ya fada Masa gasu Nan zuwa.
"Masha Allah gida ne shima Babba Mai kyau sosai Amma baiko Kama kafar inda sukayi masauki ba, da fara'a sosai Fateeha ta tarbi zahra wannan shine haduwarsu ta farko face to face ba karamin mamaki Fateeha tayi ba, duk da Sameer ya nuna Mata wani hoton zahra amma sai taga hoton Wasa ne akan zahirin gaskiya ba karya oga Mahmud yayi mace dai dai da level dinsa Dole 'yan bani na iya su dauki na wuta Dana gashi da ita, me wannan mezeci da irinsu Haseena.
Da sauri ta garasa gurin zahrar tana fadin "maraba da babbar bakuwa irin wannan zuwan bazata?
Ta mika Mata yaron da yake hannunta tana murmushi, itama zahrar murmushin ta mayar Mata.
Cikin parlourn suka shiga gaba daya, gaishe da Muhmud din Fateeha tayi, yayi Mata barka, sannan zahrar ma suka Kara gaisawa da oga Sameer, taje ta Mikawa Mahmud Babyn.
"Ki rikeshi a haka na ganshi, wallahi bana iya daukar Yara a haka tausayi suke bani, Sai naga kamar Zan karya su ne idan na dauke su".Ya fada Yana jifanta da wani kallo.
Itama kallon nasa Zahra tayi da yi Masa alamar zakayi bayani da hausar garinku, tana Dan kada Masa sexy eyes dinta. A haka yayi masa addu'a ya shafa kansa, cheque ya Dora Masa a jikinsa abinda ta gani jikin cheque din ba Karamin mamaki ya Bata ba, shi Kuma Dan gogan Saiya fuske yayi kamar baiga kallon tuhumar data bishi dashi ba.
Godiya sosai Fateeha tayiwa Mahmud ta dauki cheque din ta kaiwa Sameer, ba karamin mamaki yayi ba yana Kara duba cheque din Yana kallon Mahmud. Kai ya girgiza Masa "don't say anything pls shi yasa ban baka ba na madam ne wadda tayi nakudar haifar min takwara"
Shiru yayi kawai Dan wata kyautar tafi gaban godiyar fatar Baki, a haka Fateeha ta wuce ta barsu tana kakabin abun a zuciyarta Wai shi wane irin kudi wannan bawan Allah ya mallaka Wanda baya Jin ciwon kashe da kyautar su irin haka?.
Abubuwa motsa Baki Fateehar ta kawowa Mahmud, sannan taja zahra suka shige bedroom dinta.
Kan sofa zahra tayi masauki tana rike da Ayyan sunan da ake fadawa yaron kenan, Fateeha na fadin " Masha Allah, Amarya kin Sha kamshi sai yau Allah yayi haduwarmu?".
"Wallahi kuwa Aunty, barka Allah ya Raya Mana".
"Amin ya Rabbi, nifa na dauka da Rana zakizo mu yini muna hira Amma sai naji sweetheart Yana fadar Wai gaku Nan a harya".
Da gyarawa Ayyan riko tayi tana zame rolling din kanta. "nima bansan da fitar ba sai dazu da yamma yace zamuzo nifa naso ya barni nazo suna lokacin Amma yace a'a saiya dawo zamuzo".
Har Fateeha ta bude Baki zatayi magana ta tuna gargadin Sameer akan sakin bakin magana yace ta iya bakinta akan abida Zata fadawa zahrar.
"Kinsan komai nufin Allah ne sai yau ne ya kaddari mu hadu,munga sako Allah ya saka da Alkhairi yabar zumunci, Kaya irin haka kamar za'a bude Masa Boutique dasu, wasu ai har ya shekara biyar sannan yayi amfani dasu, Kinga wannan material din da Kika sako min me kalar peach wata sister dina da za'a yiwa biki ta kwallafa rai a kansa tana son tasa ranar dinner da taje kasuwa kasa sayensa tayi 350k 4yrd, saita gano na sayar Mata da nawa tunda suna gidan safwan ya kawo kayan".
Ita dai Zahra Shiru tayi Dan ji tayi wani bambarakwai tunda ita dai bataga wasu Kaya ba, amma saita wayance da fadar "lah ba komai ai dan "komai nayiwa d'ana ban fad'i ba, Allah dai ya Raya Mana yayi musu Albarka".
"Allahumma Amin".
Knocking akayi daga waje, umarni Fateeha ta bayar wata yarinya 'yar matashiya ta shigo da babban tray da kayayyakin motsa Baki a Kai ta aje ta gaishe da zahra ta juya ta fice.
Suna cikin hira Sameer ya Kira yace zahra ta fito zasu wuce.
Har gurin mota suka rakosu suna ta godiya, jikin window din da zahra take ta Dan leka tana "Fadin zamu mu shigo in Sha Allah mu yini a gurinki tunda ni bakizo Mana da rana ba".
"To ai ba laifina bane Kinga niba sanin garin naku nayi sosai ba sai a yanda akayi Dani".
Dariya Fateeha tayi "to ai kin Zama 'yar kanon kema tunda gaki a cikinta Baki San ranar barinta ba".
Sameer ne ya yiwa Fateeha magana ta yiwa zahra sallama, ta bude back seat ta saka ledar dake hannunta.
Direct gandun Albasa suka nufa gidan mommy, zahra Bata tashi Jin abinda tayi da Bata kyauta ba Saida suka shigo harabar gidan mommy din.
Dan marairaice Masa tayi da fuska a Karon farko ta riko hannunsa.
"Please me amor ka shiga Kai kadai wallahi kunyar mommy nakeji bazan iya shiga ba".
Ta fada a shagwabe kamar zatayi Masa kuka.
Saida ya gyara parking sannan ya maido hankalinsa gaba Daya gurinta.
Meya hadaki da mommy Kuma da kike Jin kunyar haduwa da ita?".
"Jiya fa harda ita a gidan Hajiyar oga Sameer".
Mai gadi ne ya karaso Yana gaishe da Mahmud tare da jera masa godiya wadda zahra Bata Dan isalinta ba, fitowa Mahmud yayi suka gaisa da Mai gadin,abinda ya tilastawa Zahra fitowa, gaishe da Mai gadin tayi ta Dan Fara tafiya duk da Batasan inda kofar shigar take ba.
Gurin wasu kujeru data gani ta nufa ta zauna da alamar Kamar Baki ne suka tashi daga gurin.
A Nan ya sameta ya Mika Mata hannunsa ta kama ya mikar da ita tsaye, "zo muje ciki dare Yana karayi kin zaunar damu a gurin Fateeha kome kuje fada ma oho Allah yasa dai ba gulma kujeyi ba".
Kafin tayi yunkurin bashi amsa daga bayansu sukaji maganar Rukayya "lah wa nake gani kamar Ya Mahmud da Auntyn mu?"
Da sauri zahra ta zame hannunta ta juya baya tana Fadin "wallahi Aunty Rukayya nayi fushi saboda Allah saiki taho bako sallama".
"Ayya sorry wallahi Nima karfina akafi dole tasa na taho kinsan Ya Sameer ba sauki shine ya tattaroni ko wanka fa sai a gidan Nan nayi".
Ta juya ya Mahmud Ina yini an dawo lafiya?".
"Lafiya kalau Ruky ya kikaji da 'yar rigima Ashe Kuma yaji tayi muku ta gudu".
"Wallahi