Author : Maman Teddy Category : Complete Novels
ta juma'a wallahi"
Ita dai Zahra borin kunya ta Fara "Allah ya Baki hakuri nifa na fada Miki kawai dai yawan mutane ya Hana ki gane waye yake Miki magana, Amma yaushe zanyi Miki haka Allah naji maganar ki kinga yanzu ma Zan Sha maganin fa".
Mahmud ne ya taso Yana fadin "Hajiyar mu ki shigo ciki ki fada min abinda ba'a so na sani Zan Baki abinda yafi kazar ma".
"Yauwa nasan kafi da haka, kanaji jiya ne wata daukakkiya ta tadawa yarinyar Nan hankali Wai kome gareta a mahaifa bansan dai sunansa ba da yaren Nasara Amma dai da hausa muna ce Masa tsiron mahaifa Wai sai tayi Mata tiyata,haka kawai ta ragewa zukekiyar 'yar Nan kwaliti yo an yanka mutum tun baiyi haihuwar fari ba Ina labari, shine nace baza'a yanka ta ba ga magani Nan Tasha na wata Daya in Sha Allah ze narke, ai sai daga baya Rakiya ke fada min ita waccan din ta Dade tana sonka tun Kuna turai koba haka bane? Ja'ira taga yarinya danya Sharab zata zauce tayi Mata illah to Banda abunka yaushe zaka ce buduwarka ta duba matarka ai wauta ce babba, wallahi kada a Kara kwatantawa, shine fa yarinyar nan tayi Mana batan dabo tun azzahar muka nemi 'yar Nan muka rasa nayi kuka kamar Zan yada idona to me zamu fada maka daga kawo yarinya ace ta Bata a gidana wallahi in takaice maka labari sai goma Sha biyun dare aka ganota ta Janbulo gidansu kawarta, itama uwar da yake ta kirki ce sai tayi tunani ta Nemo uwarta a waya take tambayarta duk da tana gurinta ta haka akasan guduwa tayi daga gurina cikin dare suka daukota to kaji yanda magana dai take".
Wani kallo ya yiwa Zahra Mai ma'anoni da yawa, sannan ya juya Yana kallon Sameer Wanda tunda Hajiyar makwarari ta Fara zuba ya sadda kansa kasa yayi Dana sanin kawota tafi cikin cikin masaki.
"To shike Nan in Sha Allah za'a kiyaye yanzu kiyi hakuri bata kyauta ba za'a duba korafin, nima ita ta tasoni na dawo ba Shiri wallahi hajiya yarinyar nan rikicinta yayi yawa".
"To ai tayi mini dai-dai ashe jikar tawa tasan kanta zo Nan Yar albarka".
Gurinta tazo ta zauna a kasa kusa da kafarata tana fadin "Hajiya Ina kwana?".
"Lafiya kalau ya jikin naki?"
"Nifa yanzu lafiya ta kalau ba damuwar komai".
Shima Muhmud Zama yayi kusa da ita da gani da shakuwa Mai yawa a tsakaninsu.
"Hajiyarmu kwana biyu Shiru ko nemana bakyayi ko?".
"Kaji kinibibi ta Ina Zan nemeka bayan kayi gudun hijira".
Dariya ya kamayi har ya bawa Zahra mamaki Daman Yana dariya haka.
Tashi tayi duk da Batasan Kan gurin ba Amma tana tunanin kitchen ne a cikin corridor din dake jikin dining area.
Babban tray ta dauko ta sako ruwa da lemo da Madara da plates ta dauko warmer din da aka zuba pepper soup din turkey din ta nufo parlourn ta dire cener table dake gaban Hajiyar tana fadin gashi Hajiyata ki Sha ruwa kafin nayi Miki girki yau fa a Nan Zaki wuni tunda oga ya dauke min Aunty Rukayya ko sallama bamuyi ba".
Inda Sameer din yake Hajiyar ta kalla "baka kyauta ba ai sai suyi sallama Mana kaga bataji Dadi ba".
"Ai zata dawo tunda zamuje Azare Nan da jibi".
Zahra na son taji ba'asin za'a tafi a barta Amma ba hali Dan tunda suka shigo ta kasa had'a Ido da Sameer da gaske ba karamar kunyarsa takeji ba.
Fita sukayi dare suka bar hajiya da zahrar.
Hira Hajiya ke Mata sosai tamkar sun shekara da sanin juna, taci Naman sosai Tasha madarar tana fadin "irinta muke Sha a makka laban kuke cewa ko tunda Sameer yace min mamarki balarabiyar Jordan ce ko?"
"Eh 'yar can ce".
"Ikon Allah ke Kuma Allah ya kaddaro naki mahaifin a wannan nashiya tamu, ai Sameer ya bani labarinki batun yanzu ba tun lokacin da mijinki ya kaini jidda akayi min aikin Ido da yaga wata yarinya diyar larabawa yake bani labarin ya ganki a jirgi keda wani mutum ko mahaifin ne ko Kuma dai mariki ne basu ba, Saida za'a daura Aurenki yazo yake dauko min tsohon zancen harna gane nace nasa a Ina suka laluboki yace min ikon Allah ne ya hada ku, daga Nan ban Kara ce masa komai ba, Fadima ki rik'e mijinki da kyau Yana sonki yanda Baki zato tun Baki San meye so ba yake Miki shi, kingan shi nan tun suna makarantar sakandire suke tare da Sameer Bai yadda shi ba, da Allah ya daukaka shi saiya Kara janyo shi jikin shi duk inda ya saka kafa Sameer yake aje tashi, duk abinda Sameer ya mallaka mijinki ne sila komu iyayensa da kakanni muna cikin cin arzikin".
Zahra abin jinsa take wani bai-bai me hakan yake nufi ne wai? Ana nufin Mahmud ne ubangidan Sameer ko me ake nufi? Lallai biri yayi kama da mutum duba da yanda suke rayuwa a Nan daga lokacin da sukazo garin zuwa yanzu kusan umarni ne oga Sameer yake karba kawai kasa hakuri tayi Saida ta tofa tata tambayar.
"Wai ni Hajiya waye Mai gidan nan ne? na Ya Sameer ne? ko kuma na wani abokin nasu ne? Naga ya sakar musu ragamar ko Ina na gidan Baya tsoron abinda zeje yazo,nifa tsoro ma yake bani kamar baza'a mutu ba gaskiya ya mayar Dani gida inda nafi wayo, anan mutum saiya shagala da duniya wallahi".
Baki Hajiyar ta rike tana yiwa zahra wani kallo.
"Amma yarinyar nan lamarin ki da sauran gyara, gidanwa ze daukoki ya kawo idan ba gidansa ba, yo wannan ai Bai kama kafar gidajensa na sokoto da Abuja ba, ni duk naje Kinga na Abujan,? ganin likita naje lokacin Ina ciwon kafa, na sokoton Kuma bikin kanwarsa wadda take a can Germany mukaje, wannan mutane da karamci suke, gashi kinyi sa'ar suruka Hajiya zainab Bata da damuwa ko kankani" .
Tsai Zahra tayi da ranta Kenan da gaske shi Dan Sokoto ne kamar yanda ya fada Mata sannan da gaske sunan Babar tasa zainab din Kennan lokacin da take fadar iya Abu yace ta daina fada gatsal sunan surukarta ne ta dauka Wasa yake Mata wallahi kenan duk abinda ya fada ba joking a ciki.
"To ai shike nan nayi zaton ko gidan na wani ne muka Mike kafa a cikinsa"..
'Ko alama ranar dasu Hajiya Inna sukazo ai nayi zaton fa a Nan zasu kwana gurinki sai Kuma suka juya surukar Taki ce Bata samu zuwa ba sai ita kakarsa da matar kanin mahaifinsa, ki yiwa Allah ki taushi zuciyarsa yayi hakuri ya koma gida tunda Naga alamar kece Zaki iya wannan jahadin, wani irin fushi yayi da kowa har Amminsa abin ya shafa ranar da nace Miki su Hajiya innar sunzo Saida Tasha kukanta a dakina, wallahi Banda idan na Fadi ga inda yake abin ze iya shafar tarensu da Sameer da saina fada musu kodan samun kwanciyar hankalin Ammin tasa tafi kwanan watanni Bata gidan ubansa saboda rikicin da akayi a gidan yanda mijinki ya fice yabar gidan itama ta fice ta bar musu gidan, abunfa Babu dadi kiyi wannan aikin ladan Dan Allah ko an samu kwanciyar hankali a zuri'ar su.
Ita dai zahra Banda gyada Kai babu abinda takeyi, Dan ji tayi abin yafi karfin dan karamin tunaninta.
[2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH
Page 46.
_______Sun Jima a gurin suna hira da Hajiyar tana Kara Bata labarin taren Sameer da Mahmud, anan tasan mamansa 'yar Niger ce Kuma cewa shi din da gaske twins ne su kamar na Ammah mace da namiji.
Suna nan suna hira har aka Kira sallah, da sauri Zahra ta tashi tana fadar "Hajiya Kinga guri Yana neman kurewa ban Dora miki abinci ba ko".
"Kinga dawo ki kaini inda zanyi alwala nayi sallah Banda kinibibi ki wani ce Zaki dafa min abinci, to Wanda Rahane da wannan yarinyar Dana gani akace tare kuka taho da ita Wanda suke faman aikinsa kuma ayi iri dashi? Ina fada Miki ki nutsu mijinki yawa ke garesu Kuma duk cikinsu mijinki daban ne sai kin koyi kamewa da gaske sannan Zaki fuskanci yanayin kowa Ina ke Ina wani dorawa Baki abinci banqiba dai in mijinki Zaki ringa yiwa wannan ba laifi,amma ba kowanne karabiti ba kice Zaki wani kama rawar jikin yi Masa, mujeni ki nuna min nayi dahara kafin a shiga sallah".
'yar Jakarta ta hannu ta daukar Mata suka nufi bedroom din da suka kwana.
Saida ta rakata har cikin toilet din ta nuna Mata duk abinda ya kamata sannan ta fito, sallaya ta shimfida Mata sannan ta karasa gyaran gadon da Bata Ida ba dazu ta saka freshner ta Daki ta rage karfin A/C din dakin. Hajiyar ce ta fito tana fadin "Ina dalili komai ya Zama na tab'e tab'e sai mutum yasha wahala kafin ya tantance yanda za'ayi"
Dan murmushi Zahra tayi "Haba Hajiya me yake da wahala saboda Allah?"
"Babu Miko min gyalena nayi sallah naji kamar an tada sallar"
Hijabin ta Mika Mata tana fadin "Bari naje na dawo ta nufi kofa ta fice.
Gaba Daya ta fice daga part din, ta cikin barandar Nan tabi ta shiga babban part din, ko Ina tadal sai sanyi da sansanyan kamshi ke tashi Nan ma wani bangaren ne daban da gyar ta gano inda ta kwana saboda duk gurin shine parlourn da yafi kankanta Amma yafi sauran tsaruwa, a hankali ta bude dakin ta shiga yana nan yanda tabar Shi direct bedside din ta janyo wayar na Nan yanda ta ajeta Saida kudin America dollars data gani a ciki shiya Bata mamaki Daman dasu a ciki ta saka ko Kuma daga baya aka aje Dan tab'e Baki tayi tunda ba matsalarta bace, gurin mirror taje ta dauko kayan da Aunty Rukayya ta saya Mata ta dauko luggage dinta ta zuba kayan ta duka ta fito daga ciki, a nan parlourn ta aje luggage din ta wuce ta ratsa duk parlours din Shiru ba motsin kowa, ta nufi inda su Aunty zilai suke Nan ma shiru, ta dawo kitchen Nan ma shiru abin ya Bata mamaki to suna Ina ne? Hanyar fita ta nufa sai Kara jinjina maganganun da sukayi da Hajiya takeyi abin yayi matukar daure Mata Kai shin abinda Hajiyar makwarari ta fada haka yake ko Kuma rudun tsufa ne kawai.
Cikin sa'a tana fitowa ta hango iya Rahane ta bullo ta bayan wani gini da wani babban basket a hannunta, ganin zahra yasa ya tsaya tana fadin "ai Daga can nake nayi zaton ko tare kuka fita Maida Hajiyar makwarari da shiga naji Shiru a gurin naku".
"A'a Iya Ina nan Hajiyar ma tana nan sallah takeyi Ina wuni? Wallahi tun dazu naso fitowa to saiga Hajiya ita ta zaunar dani sai data shiga sallah na fito".
'yar dariya Iya Rahanen tayi "Lafiya kalau ya jikin naki? Sai Kuma ga Uban gidan mu yayi Mana zuwan bazata ko? Masha Allah, ai Hajiyar sai ku kai almuru Bata gaji ba kin Sha labari dai Kam".
"Lallai kam nasha hira, Wai Kuna Ina ne? Na duba banganku ba a can".
Rike Baki tayi kamar yarinya " ke! 'yar Nan ki rufa Mana asiri, Banda dalilin wadalilatan Ina mu Ina kwana a bangaren yallabai, tun sassafe muka dawo nan kafin Rukayya ta tafi, Bari na yiwa zilan magana ko?".
"A'a mu shiga kawai".
Tare suka karasa shiga cikin bangaren. Masha Allah guri ne Mai kyau tamkar gidansu na Azare abinda ya banbanta su kalilan ne tunda wancan Renovation ne,wannan Kuma haka aka tsara shi sai banbancin furnitures kawai, nan ma question mark tayiwa abun.
Jin sallamar zahra yasa zilai fitowa daga kitchen din tana fadin "Masha Allah, wallahi jiya ban samu kwanciyar hankali ba Saida Rukayya ta shigo tace min kin wuce Daki kin kwanta har Ammah na Kira na fada Mata Baku dawo ba, tace min na kwantar da hankalina ba komai tunda bake kadai Kika fita ba, Kuma sai muka wayi gari da zuwan yallabai? Ai ya shigo shida oga Sameer mun gaisa".
"Eh wallahi muna cikin gari gidan Hajiyar makwarari kakar oga har dare, kunyi waya da Ammah kuwa yau?"
Saita share zancen Mahmud din.
"Eh mun gaisa tun wurin karfe shida na safe har take tambayar ya jikin naki tunda wayarki Bata shiga, nace mata da sauki amma dai kun wuni a Asibiti Dan sai wurin Sha biyun dare kuka dawo".
"Ok.ba damuwa Bari na bude wayar na kirata sai yanzu na dauko wayar, Bari na koma na baro Hajiya tana sallah inaga yanzu ta Gama kada ta jini Shiru amma dai Zaki zo can din ko?".
Ta fada tana mik'ewa tsaye.
Zaro Ido tayi Kamar wadda taga abin tsoro.
"A'a wannan fa Daya ai jiya ba yau ba, sai dai In da abinda za'ayi Miki ki fada min ta waya sai nazo nayi Miki".
Sallama ta yiwa Iya Rahane suka fito tare da Zilan, Saida sukayi nisa sannan zahra ta tsaya itama Zilan tsayawa tayi.
"Aunty zilai me Kika fashimta daga lokacin da mukazo zuwa yanzu?"
Zahra ta jefa Mata tambaya.
"To abin ne da yawa gaskiya, Dan ni lissafina ya kwance gaba daya wallahi na rasa tudun dafawa Amma dai komai rintsin mijinki shine ke Jan ragamar gidan nan Dan dazu lokacin da oga Sameer ya kawo Hajiya naji suna magana da wasu ma'aikatan gidan Nan akan oga yayi zuwan bazata, sai Kuma lokacin Daya fito a can gurin Naga ya Tara su yana magana dasu oga Sameer Yana gefe harya gama oga Sameer ya rarraba musu kudi muma har ya aiki wani Wanda Naga ya shigo da waccen babbar motar ya kawo Mana dubu ashirin ashirin nida iya Rahane".
Ajiyar zuciya zahra tayi tana duban bangaren motocin hango motarta tayi a cikin parking lot din, kenan a Nan ya ajeta ko kuma jiyan yazo da ita Nan Dan kamar Bata ganta ba jiya, rausayar da Kai tayi tana wani tunani kafin tace.
"Muje kawai Aunty zilai mu zuba idanu a hankali gaskiya zatayi halinta, nifa duk hankalina ya koma gida Amma naji yana fadin zasuje Azare jibi za'a dawo min da Aunty Rukayya, Kinga ba zancen komawar mu kenan, ni Kuma abinda bazan yarda ba kenan ya ajeni a wannan gjdan da bansan asalinsa ba gashi Nan Kashi-kashi kamar gidan marasa gaskiya".
"A'a kada kiyi haka ki Bari kiga iya gudun ruwansa Mana nasan dai baze cutar dake ba, to kiyi Masa biyayya a duk abina ze umarceki matukar Bai sabawa shari'a ba,kiyi hakuri wata rana ma garinsu ze koma sai kice bazaki bishi ba? ai shi aure ba inda baya Kai mace, ki duba Maman Akwanga kin taba cewa tayi rayuwar Azare".
Haka zilai ta dunga tausar zahra har suka shiga part din da suka zauna Zahra ta dauki luggage dinta Zilan ta karba suka shiga ta ciki suka fito barandar nan zilai sai mamakin abin take Bata taba tunanin da wani ginin a bayan wannan ba, Bata Gama sarewa da lamarin ba Saida suka shiga ciki, a parlourn farko suka tarar da Hajiya ta rabsa uban tagumi ta zubawa kofa idon suna shigowa ta sauke ajiyar zuciya tana fadin "Haba 'yar Nan daga Bari na dawo Kika nemi gurin Zama Kika manta Dani saboda Allah kin kyauta min kenan? duk sanyi ya game min jiki har attishawa na Fara nasan mura Kuma sai abinda hali yayi kawai".
Da sauri zahra ta karasa kusa da Hajiyar tana fadin "Ayya wallahi nayi tunanin ko zakiyi nafilfili ne fa shi yasa na fita dauko wayata da kayana Dana Bari a wancen dakin, taso muje kici abinci kinji Hajiyarmu insha Allah bazakiyi mura ba, Aunty zilai Naga da kaji a can bangaren inda muka fito kiyi Mata irin pepper soup din da Naga kin yiwa Inna maimuna lokacin tana mura, ko a soya Mata ta tafi gida dashi".
"To in Sha Allah Bari naje ai kayan dazu wani mutum ya debesu ya mayar kitchen din part din da muka koma harma an karo wasu kayan masu yawa mun shafa'a mu nuna Miki su".
Ta fada tana mik'ewa ta nufi kofa ita Kuma zahra ta nufi dining ta daukowa Hajiyar abinci.
*** *** ***
Tunda garin Allah ya waye Mama ke faman Kai kawo a cikin Daki ta Kai gwaro ta Kai mari, tun bayan wayar da sukayi da Aunty larai hankalinta Bai kwanta ba sai yarfe gumi takeyi baji ba gani, ta Kira wayar Asabe yafi Shurin masaki amsar Daya ce switch off.
Wannan wane irin Abu ne Kullum tana tubkar gaba baya na warwarewa, Wai ita wannan Matar meta taka ne, duk abinda takeyi ya tashi a banza Kenan?
Tun bayan kaiwa Mai gadi sakon Nan Basu Kara samun damar shiga gidan Nan ba ko kofar ma tafi karfin zuwansu gashi yanzu Kuma aunty larai tazo Mata da wani Abun d'aga hankalin ga sako Amma isar dashi shine aiki ga wayar Asabe Bata shiga da sai ta Kai ko ta bayan gidan ne ta jefa abin bukatar dai ya shiga gidan ga sakon ya taho daga Jos din Kuma ance ba'a son ya kwana ba'a aiwatar dashi ba, akwai matsala Dan ze iya warware duk ayyukan baya, kuma wani aikin ze iya yin kome a Kanta ko 'ya'yan ta shine ta tada hankalin ta, tunda tasan idan tayi sake kwabarta ce zatayi ruwa, tayi tunanin ko sahura zata aika Tasha ta karbo sakon idan yaso sai tayi Mata bayanin yanda zatayi da sakon idan ta Kai can gidan zahrar, tayi tunanin ko zilai zata Kira tace Mata ta fadawa Zahra sahura zata je tayi musu share-share kafin su dawo, Nan ma taga abun ba lallai ya yuwu ba. Kara Kiran Asaben ta gwada still dai a rufe, dangwarar da wayar tayi duk abin duniya ya taru yayi Mata yawa.
Duk iya tunanin ta ya Kare ta rasa Ina ne mafita dole ta tashi ta fice daga dakin tana tunanin dole ta tura sahura taje ta Kirawo Mata Asaben in ba haka ba tasan watan Jin kunya ne yake neman Kama Mata.
Wannan kenan.
Tunda Ammah ta fita daga bangaren Abban take kokarin neman zahra Amma Shiru har bayan Azzahar inda taji Dadi da zilai tace Mata zahrar a gidan ta kwana Kuma Mai gidan ma yazo, tasan kome ne ne zezo da sauki.