Advertisements
Chapter 9 Reading Auren Huce Haushi Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Auren Huce Haushi Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 22

24K to 27K   out of 63.3K words

Asia wallahi ba Wanda ya kawo zaka zauna a 9ja".
Girarsa Daya ta gefen dama ya Dan dage Yana yiwa Faruq wani kallo.
"Au kunyi zaton Ina waje kenan ko? To Ina gida Bauchi state, cikin garin Azare katagum local government, nasan ba sai nayi maka bayanin komai akan Zahra ba, an fada maka wacece ita tunda Wanda na ganku yasan komai a Kanta watakila Abu Daya ze bashi mamaki ganin mu tare a Nan tunda ya sanni ko ba sosai ba a can tunda time to time Yana shiga gurin malamina suna gaisawa idan ya shiga garin, sai albishir Daya Zan maka itace yarinyar da nake fada maka mun taba haduwa da ita a cikin jirgi ita da Babanta wadda na tura Sameer ya bisu Zuwa Jordan,ai ka gane bayanin ko?"
Kai Faruq din ya jinjina Yana fadin "Yes". Ya fada yana mamakin abun sosai wato shi Mahmud komai ya sake a gaba saiya cimma burinsa. "Sai yanzu ya gane ka har hotunan daurin auren ya nuna min a phone dinsa, Shima ya Dade Yana tunanin a Ina yasan fuskar ka tunda ba farin sani yayi maka ba sai dai a hoto, shi yasa Sam be ganeka ba tunda ta Ina za'ayi tunanin zakayi irin wannan rayuwar, Dan Allah fada min ta Yaya hakan ya faru harda Auren irin wannan yarinyar haka wato ribar kafa kenan ko?"
"To abubuwan da yawa Dan Ni dai nasan na baro gidan Hajiya Inna cikin fushi kofa takalmana ban iya tsayawa na saka ba kawai dai nasan duk phones dina suna jikina na kamo hanya a kafata Amma Abu Daya nayi noticing kamar jama'ar da nake wucewa basa ganina sam, nayi tafiyar da bansan iyakarta ba daga Nan Kuma ban Kara sanin abubuwan da suka faru ba na dai tsinceni ne a gadon Asbiti bana magana ko kadan amma Ina Jin abinda ake fada mayarwar ce Bana iyawa, Wanda suka shinceni wani babban malami ne da marikin zahra da d'an Kanwar Malam din, shifa Malam din ya dage min da Addu'oi a kaina Dan har Taraba Saida yaje akan matsalata gurin wani tsoho malaminsa, a haka har Allah ya bani lafiya, sai Kuma nayi arba da Zahra a garin duk da Daman a bincken Sameer ya gano mazauna Bauchi state ne, sai naji Naga gurin Zama na dage da Addu'a da sadaka amma fa ban fadawa kowa ba ko Sameer saboda a lokacin maganar aurenta akeyi na shiga wani Hali a lokacin sai dai nayi Alkawari sai halarci daurin aurenta Kuma sai nayi Mata kyauta ta ban mamaki kafin nabar garin, sai kuma ubangijin da yake amsa addu'ar bayinsa ya juya lamarin cikin kankanin lokaci, aka bani aurenta lokacin Dana yanke kauna da samunta a matsayin matar aure uwar 'ya'yana".
Ba karamin mamaki Faruq yayi ba ya Kuma Kara jinjinawa girman Allah swa, wato duk gwagwarmayar da aka Sha Rabon wannan yarinyar ne ya rantse Kuma ya kaddaro shine ze taka da kafarsa ya karbi aurensa ba tare da wakilcin iyayensa ba sai iyayen Amana.
"Wato Ni duk lamarin ya juye min wallahi".
Dan murmushi Mahmud yayi Yana fadin.
"Kaima kenan da ba a kanka hakan ya faru ba, sometimes idan na zauna sai naga kamar Almara wasu abubuwan da suka faru, kasan abinda zakayi min".
Kai Faruq ya girgiza alamar "A'a.
Fuska ya hade Sosai Yana kallonsa Ido cikin ido.
"Kada naji labarin ka hadu Dani a Sokoto Koda wasa, Nina fita da kafata Kuma ida kafata Zan koma Amma ba yanzu ba, Kuma kada naji labarin nayi aure a gurin kowa koda nazo da Zahra kada ka nuna kasanta ko a fuska, Nina taro match din ni zanji da kayana".
Kai kuwai Faruq ke gyadawa tunda ya Fara maganar yasan ba Wasa a cikinta.
"In sha Allah hakan bazata faru ba".
Sun Kai kusan karfe uku suna tattaunawa akan abubuwan da suka ringa faruwa bayan bayanan, kafin kowa ya nufi NASA gurin kafin lokacin sallar asuba. Ba karamin mamaki Faruq yakeyi ba idan yaji Mahmud Yana fada masa wani abun Dan shi sai gurinsa yaji wasu abubuwan duk da Yana cikin gidan.

Itama zahra Bata kwanta ba sai kusan biyu da rabi bayan ta gama karatun Alqur'ani ta Fara nafifili sannan ta kwanta, harta gama addu'ar kwanciyar barci sai Kuma ta canza Shawara ta tashi ta dauko Jakarta tana fadin "Bari na kunna wayar nan ba turawa Ammah text na ban hakuri tayi breakfast dashi sai Kuma da Dan hantsi na kirata nasan zata huce ta saurareni lokacin, sannan na Kira bestie musha hurar yau she gamo".
Jakar ta dauko ta koma saman gadon Tana gyara Zama, duk iya binciken ta tayi Babu duk wani Abu Mai mahimmanci data saka a ciki, zazzage jakar tayi wayam kamar ba'a taba ajewa a cikinta ba.
Tagumi ta buga tana tunanin, to a Ina suka zube wadannan kayan? Kuma me yasa sauran Basu zube ba? ko jiya lokacin da suka fito daga gidan mommy komai Yana ciki Kuma ai ko daga motar Bata fito ba lokacin da sukaje sahad din.
Jiki ba kwari ta matsa tsakiyar gadon ta kwanta ita duk lamarin ya tsinke Mata wa zata tambaya Ina kayanta na jaka suke da wannan tunanin barci yayi gaba da ita.
Hudu da rabi Mahmud ya tashi as usual, duk da Daren da suka raba da Faruq besa shi ya makara ba, nafila yayi sannan yayi raka'atanul fajri ya fito Jin an Fara Kiran sallar na biyu, harya nufi Hanyar fita daga corridorn sai ya dawo baya ya tura kofar dakin da take, a kwace ya ganta tsakiyar gadon hular data saka ta cire gefe guda Ribom din shima yayi nasa gurin blanket din ya sauka har saman cikinta ga rigar ita da Babu duk Daya, a hankali yake shigowa cikin dakin kamar Mai tsoron kada ya tasheta, Yana Kare Mata kallo yanda tayi wani mahaukacin kyau a cikin dinligh din dakin, har ze tasheta saiya tuna condition din da take ciki ya juya ta fice daga dakin, yaso ya gyara Mata gashin Amma yasan matukar ya tabata sai ya sake alwalasa, a waya ya Kira Faruq ya fito su wuce masallaci.

A cikin barci taji kamar an bude kofa dakin, fargigit ta tashi tana addu'ar tashi daga barci, kamshin turarensa da taji ya hade dakin shiya tabbatar Mata daya shigo cikin dakin. A gurguje ta nufi toilet jin har an Fara sallah a masallatai, fatan ta Allah yasa har ta Idar Bai dawo daga masallacin ba Dan ita fa wallahi tsoronsa takeji Bata shuryawa abinda yake muradi ba...
[2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: AUREN HUCE HAUSHI.


MAMAN FATEEMAH.


Page 50.



_______Tun idar da sallar Zahra ta shiga kakkabe gadon Tana dubawa ko Allah zesa tayi arba da tarkacen ta na cikin jaka amma ko alamarsu Babu dole ta hakura ta linke sallayar da hijabin Adana saboda tsaro.
Bata koma barci ba gyara dakin tayi duk da ba wani datti Dan da gani sabon guri ne da alama ma kamar a jiyan aka Fara amfani dashi Dan ko toilet din shima haka ne, Bata dauki dogon lokaci ba ta gama komai ta bazawa dakin kamshi Dan ga Room freshners Nan kamar anyi gorinsu, wanka ta shige, ta Jima tana gasa jikinta da ruwan dumi sannan tayi wanka ta fito haka nan taji tana son tayi kwalliya Sosai.
Zama tayi ta tsara light makeup tabi jikinta ta Sanya turaren gabobi Dana bayan kunne duk ta saka tunda gasu nan kamar ba da kudi ake sayensu ba, ita dai ta zubawa sarautar Allah Ido taga inda wasan ze Kare, clothset din ta nufa ta bude dayan bangaren, English wears ta saka riga da siket blue black masu ratsin fari a jikin coat din,rolling tayi da farin veil ta fito Shar da ita gefe gadon ta zauna tana karanta addu'ar Azkar din safe.
Su Mahmud Basu shigo gidan ba sai wurin bakwai tun bayan idar da sallar sukayi zaman karatun alqur'ani da Azkar din Suma a masallacin. Faruq yaso ya wuce gida amma Mahmud ya Hana shi yace yayi zamansa a Nan ze fiye Masa shi yau ze koma Nasarawa Daman akwai abinda yazo yi Nan din zuwa anjima Idan ya gama zasu wuce Kuma ma Basu gaisa da madam ba, part din Daya kwana ya wuce shi kumq Mahmud ya nufi sabon part din har ya Fara hawan steps din ya dawo Yana Kiran Faruq.
Shima gangarowa yayi Yana nufo Mahmud din Saida ya Karaso yace masa.
"Ina key din waccen car din akwai Kaya a baya za'a fito dasu".
"Oh! Sorry, wallahi na manta Yana ciki trouser din Dana sake jiya, harna na fito dashi na manta ban baka ba, daman ni ka barwa ita Naga tayi maka kadan motar five millions ai sai mu Kuma ma motar Mata ce"
"Nima ba tawa bace ta madam ce idan kana so ka tafi da ita kawai".
Baki ya rike alamar mamaki Yana 'yar dariya.
"Haba dai yaushe za'ayi haka da Wasa nake gani nayi dai tayi kankanta a gurinka harma ita din gaskiya".
"To Yaya kake son ayi kenan?kaga dai bani na Bata ita ba Babanta ya saya Mata Kuma saina ce batayi ba, Ina laifi da ake bani aro da ita fa nazo airport lokacin da zanyi tafiya,Kuma anan na aje ta harna dawo sannan na dauko Mata abarta, Kuma kawai saina ce Mata tayi kadan to ina wadda tafitan da Zan bata?".
Ya fada Yana kallonsa, shima kallon nasa yake yi, shi wani zance yake masa me Kama da zaurance me yake nufi da hakan Yana nufin a baibai ya ninketa kenan kome?.
"Pls jeka dauko min we will discuss later". Da sauri ya nufi ciki ya dauko key din suka nufi gurin da motar take.
Kayan ciki suka dauko, da gudu malam ya taho ya karbe kayan hannun Mahmud Yana fadin "Haba yallabai meye amfanin na a gidan da har zaka dauki kaya". Ya karba yayi gaba da sauri Faruq ba biye dashi suka nufi parlourn kowa da dauke da ledojin a hannau.
Har gurin dining table ya Kai kayan ya Dora kayan Faruq ma a Nan ya dora na hannunsa, Malam musa ne ya koma ya dauko sauran da suka rage a cikin motar.
Maimakon Mahmud ya shigo saiya Koma dayan part din bai jima ba ya fito rike da laptop da wayoyi tablet guda biyu.
A parlourn ya iske Faruq Yana tsaye kusa da wani freme Mai hoton wani tsibiri a tsakiyar teku gurin yayi matukar kyau sosai.
Jin shigowar Mahmud yasa ya baro gurin Yana fadin "gaskiya tsarin gurin Nan yayi kyau sosai banyi zaton ze kai haka ba kafin a gama".
Wani kallo Mahmud din yayi masa Yana aje abubuwan dake hannuwansa.
"Amma Faruq ka fiye gulma, Ina cewa Kaine ka zana ginin Nan da hannunka zakazo kana wani zance daban a Kai Kuma, ni zonan ka shigar min da wasu sakonni cikin laptop din nan jiya naso yin aikin ka hanani".
Ya fada Yana kokarin kunna wayoyin dake hannuwansa.
Saida ya nuna masa komai sannan ya nufi upstairs.

Tunda ya doso saman yaji wani kanshin Dadi Wanda ya kasa tantance Kona menene, direct dakin Daya kwana ya shige Yana son ya sake wanka yana son ya fita wasu sabgogin nasa wanda yaken son yayi da Kansa.
Ya shiga ciki ba dadewa Zahra ta fito ta nufi kasa tana ayyana bari ta duba Koda kayan amfanin kitchen Dana abinci tasan abinda ya kamata tayi kada ta Zama sakarya wadda ta rako Mata. Plat shoes ta saka fari tas dashi ta nufo down stairs din cikin takunta mai daukar hankali, Bata ankara da mutum a zaune ba Saida ta ahigo tsakiyar falon taja ta tsaya tana rarraba idanu tana son tantance ya fasalin ginin yake da inda ya Kamata ta dosa,.
Carab suka hada Ido dashi ya aje abinda yakeyi ya Zuba Mata idanu irin kallon Nan na wuce shari'a Yana tsarkake ubangijin da ya yi wannan halittar da take gabansa.
Dan zabura zahrar tayi ganin mutum ba zato ba tsammani.
Aje abinda yakeyi yayi ya taso har lokacin Yana kallonta Dan ja baya tayi ganin ya nufo ta.
"Ina Zaki Kuma nida na taso na gaishe da Aunty na".
Ya fada Yana murmushi, saida ya matso ta Dan gane shi, shine jiya ya rungume Mahmud a kofar store din da yayi sayayya.
Sai lokacin ta Dan nutsu amma da tana tunanin ta Ina zata fece ta Koma saman tasan ko banza tana da mafaka a can.
Dan murmushi tayi itama tana fadin "Yaya sunan bakon da babu sallama? Kawai na wayi gari da ganin mutun ai dole na rasana".
Dariya yayi Yana fadin "Good morning Aunty".
"Morning".
Ta amsa masa a dan darare din nan ba wani sakewa, tana kallonsa.
"I am Faruq Dange".
Ya fada Yana juyawa zuwa inda yake aikinsa.
A hankali ta bude bakinta tace Masa.
"Sunana Fatima Zahra Muhammad Sani, Ina maka.barka da zuwa".
Tana Gama fada ta wuce can inda ta hango Kaya akan dining table.
Sakato yayi Yana kallonta Bai taba tunanin tana Jin yaren ba, Kai kawai ya girgiza Yana dan murmushi Yana fadin "wato Ya Mahmud sai a barshi kawai sannin inda ya dosa sai Allah, shi yasa kenan duk yayi d'iban Karan mahaukaciya da matan daketa rashin hankali a Kansa yayi tafiyarsa ya kyale kowa da nata salon rashin hankalin".

Ledojin ta shiga dubawa taga Dame Dame Nene a ciki, Wanda su Fateeha da mommy ta Bata ta cire ta aje a gefe sai Kuma Wanda ya sawo jiya ta cire na kitchen, kofar data gani a tufe taje tadan tura ga mamakinta a bude ta ganta shiga tayi kitchen ne modern sosai babu abinda babu a cikinsa tsayawa tayi tana nazarinsa kafin ta juya ta koma dauko Kayan.
Saida ta aje komai a muhallinsa sannan ta bude freezer data gani ta kwance, nama ne dasu kifa da kayan miya a Nike cikin manyan bikitin roba, kaji biyu ta Ciro da Zuba a roba ta tarasu a famfo saboda kankarar ta saki.
Filawa ta diba ta kwaba da yeast da barking powder ta rufe ta koma ta gyara Naman ta Dora a wuta.
Wani ruwan ta Dora daban ta dauko Madara ta bude ta diba Mai yawa ta dama Zuba akan ruwa data Dora ta Dan zame murfin sannan ta ciro hollandia custard ta fasa ta dibi yanda take ganin zata ishesu ta dama ta aje a gefe. Plates da cups da duk abinda tasan za'a bukata ta dauko ta wanke ta aje a muhallin Daya dace.
Filawar data kwaba ta dauko taga ya tashi ta ringa murzawa round sai ta Gama ta shafa Mai a frying pan ta rage wuta ta shiga gasawa tanayi tana juyawa.
Biyu ta raba Naman ta dattaka rabi tayi source Rabin Kuma tayi pepper soup dashi ta dama custard din ta dafa coffee Kuma.
Tun daga sama Mahmud ke jiyo wani irin kanshi girki yayi tunanin ko da wani sabon restaurant a Nan kusa dasu, Saida ya fito yana saukowa yaji kamshin ya cika gidan.
Shigar kananun Kaya yayi yayi masifar kyau, yau shigar da yayi ta fito da ainihin ko waye shi Dan ba karya kana kallonsa kasan matashi ne Mai cike da Jin Dadi da wadatar arziki Dan agogon dake hannunsa kadai na millions of naira ne, shigar da ya Jima da daina yinta Nan gida Nigeria rabon da ya fito haka tun kafin ya shiga rubibi.
Hannu Faruq ya shiga tafawa Yana fadin "perfect match, wallahi kun Dace Ashe haka Auntyn tawa take? Haba shi yasa baka sauraren masu yi maka rawar Kai, ya Mahmud Ashe da abinda ka taka shiyasa kayi shuru ka kyale kowa, Mai irin wannan matar mezeci da tarkace irinsu Safna, wallahi na Dade Banga ma'auratan da suka tafi da imanina kamar kai da Aunty na ba, Dan Allah ka tsaya min na auri kanwarta pls🙏".
Ikon Allah Mahmud ya tsaya yana kallo lokaci Daya faruq ya gigice masa wato yaga zahrar kenan tunda ya sauko yaji gidan ya hade da kamshin girki yasa itace a kitchen, ko ba komai yasan Allah yayi Mata baiwar iya abinci a Dan zaman da sukayi ya fashimci hakan.
Shi rasa abin cewa ma yayi a Kan kalaman Faruq, Dan uwansa ne na jini, amma ya gigice da ganin matarsa, tab lallai da matsala Babba.
Bai nuna Masa komai ba sai Dan murmushi da yayi Yana fadin. "Ai mata ta ita kadai ce Bata da Kani ko kanwa, nine wanta nine komai nata Sai dai ka duba ko a Ina ne Zan shige maka gaba in Sha Allah".
"Dan Allah nidai ka taimaka ko cikin family dinta ne ayi min wanna alfarmar ka shige min gaba".
Kyale shi yayi ya nufi kitchen din lokacin ta Gama hada komai ta juyawa kofar baya tana cire jan bayan kwakwa zatayi amfani da ita in anjima.
Kamshinsa ya Fara fada Mata ya shigo gurin a hankali ta juyo, Yana tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa ya zubawa bayanta Ido,yanda ta juyo din nan shi Kansa da take halalinasa Saida yaji wani yarrr a jikinsa Dan gani yayi gaba Daya ta canza Masa ga wani irin cikowa da kirjinta yayi sosai.
Lumshe Ido yayi Yana tunanin lallai dole addinin musuluci da yayi Hani ga mutum baligi ya shiga gurin macen daba muharramarsa gaskiya. Yana can Yana tunani ya tsinkayi muryarta tana fadin "Ina kwana" batare data Kara kallon inda yake ba.
Bai amsa ba ya danyi gyaran murya.
"Meye Kuma Ina kwana? Na fada Miki ki iya tarairaya ta wallahi, kada garin kallon ruwa kwado yayi Miki Qafa, kina da kishiya fa kinsan idan ta fiki iya lafazi da tarairayata can Zan tare a gurinta".
Warrr tayi masa da sexy eyes dinta tana Masa wani kallo.
"Yes ko Baki yarda ba? yanzu na Kira Miki ita ku gaisa".
Kai ta girgiza Masa alamar A'a.
"Come on, zo Nan ki fada min bakya son kishiyar?"
Ya bude Mata hannuwansa alamar ta shigo,

9 / 22