Advertisements
Chapter 4 Reading Auren Huce Haushi Book 2 Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Auren Huce Haushi Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Maman Teddy Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 22

9K to 12K   out of 63.3K words

din na saka yafi sau goma Amma yaki budewa".
Tsaki yayi "Waike Dan Allah Ruky yaushe Zaki girma ne? to oga ne ya shigo cikin dare Nima da asuba naga text message dinsa Dan haka ki Zama ready idan na shigo saimu wuce tare Amma yanzu kada kuyi komai za'a kawo abinci".
"To ai su Iya Rahane har sun kusa gamawa baka fada min ba tun dazu".
Ok, ba komai sai a hada tunda gidan da jama'a, yauwa zuwa an Jima ki bude musu part din Nan na kusa da parking lot sai su zauna a nan tunda shima ogan Bai san ze shigo kanon ba harsu Gama su koma to matsalar madam din ce inaga ta caza Masa Kai Wai cewa fa yayi daina amsa Masa waya tayi".
"Kamar ya Bata amsa masa waya? Batasan kowaye bane da zata ringa yi masa haka?"
"Eh kusan hakan ne gaskiya"
"Allah ya rufa asiri" ta fada.
Sukayi sallama ta kashe Kiran tana dariya "su oga anzo hannu ana walagigi da rayuwar 'yan Mata gashi kaima kazo hannun yarinya tana juyaka son ranta, nasan bana raba Daya biyu saboda shi ta rufe wayarta jiya, taki magana dashi a wayar Ya Sameer karshe ma ta sakata jirgi, yes! Haka nake son irin matansu su kasance, idan suka samu wadda ta mace a kansu ta Zama sorry Amma wannan ta shuka mulkinta yanda takeso tunda Batasan waye shi ba".
Ya juya ta koma kitchen inda tabar su zilai suna aiki, tana shiga zilan tace Wai ni lafiya yarinyar Nan? naji shirun yayi yawa ko dai rakani zakiyi na gano lafiyarta kada na Zama babbar kwabo an hadoni da yarinya nayi wasarere da lamarinta".
'yar dariya. Rukayya tayi "gaskiya kinaji da matar big bro irin wannan shiga damuwa jiya fa ko barcin kirki bakiyi ba kina zaman jiranmu yau ma tun Asuba kike ta nemanta, ki kwantar da hankalin ki Aunty sirikinki ne ya taho ba Shirin wannan 'yar taki tsaye ce taki saurarensa ko a waya dole ya tsallake hidimominsa ya nufo Nigeria".
Iya Rahane ce ta aje Wukar hannunta tana duban Rukayya "kikace uban gidan mu ya shigo garin?"
"Kwarai kuwa iya jiya cikin dare ya shigo Kinga kuwa sai ki fadawa Aunty ta kauda Kai kawai gurin son ganin 'yarta ba yanzu ba gaskiya, Dan haka da an gama aikin Nan zamu bar Nan Bangaren mu koma wancan".
"Wannan gaskiya ne inba tayi dalili ba yaushe zamu shigo wannan guri harda kwana a cikinsa, Amma dalilin uwar dakinmu mun dangwali arziki ai wannan ba komai bane akan gidan da aka sauke mu a sokoto, Kai Naga inda arziki ya amsa sunansa wannan yaro uwarsa tayi farar haihuwa wallahi Nan kusa Banga mutane masu karamcin su ba, uwarsa yarinya karama sai halin girma".
Ita dai zilai sai ta rasa Wai wannan maganar dawa ake ne waye suke zance a kansa ne ita fa maganar Zahra take musu su Kuma sun kamo wata tashar Ina hadin zahra ba Wanda suke magana a kansa ko dai Mai gidan ne ya dawo Basu gane me take nufi ba, ita Zahra matar Almajirin Malam Bukar Wanda gidan zaman ma na Baba Malam ne mutanen da yaje yiwa aiki turawa suka gyara Masa shi, to Ina shi Ina wannan Aljqnnar duniyar suda aka kawosu zaman 'yan kwanaki na ganin likita.
Cikin nuna mamaki zilan tace "ikon Allah ai ban sani ba kice da anyi uwar banza gara da Kika fada min kada naje nakai kaina girma ta Fadi".
"Ai Koda kin shiga basa Nan ba a nan suka kwana ba".
Wayar Rukayya ce tayi qara ta dauka ta fice daga kitchen din shine abinda ya Hana zilai fadar abinda tayi niyyar tambayarki Rukayyar.
Hira iya rahane taci gaba da yiwa zilai a Kan Mahmud amma ko Daya zilan Bata gano ainishin waye take magana a kansa ba.

.[2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨

AUREN HUCE HAUSHI.


✨✨


MAMAN FATEEMAH.


Page 45.




________Sai kusa karfe Sha Daya da rabi Mahmud ya farka shima yunwa ce ta tashe shi, ido ya tsura Mata barcinta take hankali kwance tayi pillow da gefen kafadarsa, hannu yasa ya shafi gefen fuskarta da gashi ya kwanta lambam, hancinta ya dan ja kadan, dan yamutsa fuska tayi tana bude idanunta a hankali, Ido cikin ido sukayi dashi da sauri ta Maida nata ta rufe.
"Ki tashi muyi wanka ki bani abinci Naga alama ke barci baya isarki".
Zare jikinta tayi still dai idanun a rufe, tana Jan bargon zuwa kirjinta.
"Kaje ka Fara Yi sai nayi nima".
Ta fada tana juya Masa baya, Dan murmushi yayi ya Dan rankwafa dai dai fuskarta.
"Ok, ba damuwa jeki hada min ruwan saina Farayi kafin na fito, saiki hada min abinda zanci".
Yunkurawa tayi ta tashi zaune, tana mutsumutsun yanda zata tashi haka a gabansa.
"Ka Miko min Riga na saka saina shiga na hada maka".
Ba musu ya dauko Mata Rigar ta Karba ta saka ta Mike ta nufi toilet din.
Saida ya tabbatar da ta shagala gurin abinda takeyi ya tashi ya nufi toilet din, tana zuba turaren wanka cikin ruwan data hada ya shigo ciki ba zato ba tsammani sai ganin mutum tayi ya shigo daga shi sai boxer a jikinsa, gurin da take tsaye ya nufo, da sauri ta matsa gefe kanta a kasa Bata yarda sun sake hada Ido ba tace Masa.
"An Gama hadawa".
Tana aje robar dake hannunta ta juya da zummar barin gurin. Taku biyu tayi taji anyi sama da ita cak sai cikin ruwan daga ita har kayan jikinta, wata ajiyar zuciya ta sauke tana fadin "Dan Allah ka Bari wallahi nayi wanka fa".
"I know, tayani zakiyi Dan rashin kirki ai ni bakonki ne ya kamata ki tarairayeni har wankan ma kiyi min tunda kin hanani sukuni Saida Kika gargadoni na dawo gurinki Kinga kuwa ai duk lokacinki yanzu nawa ne".
Har ta bude Baki zatayi magana ya Dora Dan yatsansa a Kan lips dinta "kin manta ba'a magana a cikinki toilet? Muyi wankan later munyi maganar".
Janyota yayi jikinsa ya Fara cire Mata jikakkun kayan jikinta, a tsorace da Kuma wata azababbiyar kunyarsa da takeji ta Kara ninkuwa, dan wani Abu ne da be taba faruwa da ita ba a tarihin rayuwarta irin wannan kebewar da namiji baligi da uwar tana irin wannan Bata taba yiba shi yasa Daya hade jikinsu ta shiga tsuma kamar wadda Zazzabi ya rufe, wankan sukayi tare duk da shi dai kadai yake sha'aninsa Dan ita dai kam sai hankali.
Saida ya Gama son ransa sannan ya karasa wankan ya fito ya barta a ciki,Saida ta kimtsa kanta sannan ta fito, lokacin har ya shirya cikin wasu kananan Kaya Yana daura agogo, tsaye tayi a kofar toilet din ita Bata koma ba ita Bata karaso inda yake ba, kallon kasa kasa take masa gani tayi gaba Daya ya canza Mata kamar anyi musanyarsa da wani ya Kara zaman wani handsome dashi jikinsa ya Kara Zama fresh dashi.
Inda take tsayen ya nufa "pls ki shirya Ina son fita ne wurin after zuhur".
Kofa ya nufa ita Kuma ta nufi gurin mirror tana goge jikinta, hand dryer data gani a gefen mirror ta dauka ta jona ta busar da kanta, cikin kankanin lokaci ta shirya gurin kayan ta nufa tsaye tayi tana kallonsu. To Wai ita Nan din Ina ne gidan waye taga ya shigo ya barrarraje Yana tsula sha'aninsa ga kayan Mata birjik Kuma ance mamallakinsa ko aure beyi ba to Ina ba"asin kayan nan na can part din Aunty Rukayya tace nata ne to wannan fa na waye su kuma? Qundunbala tayi ta dauko wasu English wears, ta saka masu kalar brown dark sai veil milk colour tayi rolling ta fesa turarenta dake cikin handbag dinta sai lokacin taga maganin da Hajiyar makwarari ta bata, Dan murmushi tayi a zuciyarta ta ayyana "zanzo na Baki hakuri Hajiya nasan ban kyauta Miki ba dole ce tasa na aikata hakan".
Dakin ta Fara gyarawa ta cire bedsheet din ta duba gurin da take tunanin zata iya ganinsu ta duba.
Very luckily ta gansu ta Ciro Daya ta baza zata Fara shimfidawa ke Nan ya shigo dakin Yana waya, da hannu ya nuna Mata ta taso, ba musu ta taso ya nufo inda yake hannunta ya kama ya nufi kofa wani Abu kawai ya taba daga can kasa kofar ta bude, da kallo ta bishi tana mamakinsa gaba Daya ya canza Mata Kuma yanda yake mu'amala da gidan Yana Bata mamaki, har suka fito parlour na biyu Yana ta wayarsa wadda ta fuskanci kamar suna maganar kasuwanci ne sabo da aka Riga aka fara, direct dining ya nufa da ita Saida ya zaunar da ita sannan ya zauna.
Wani Dan guri ya danna jikin table din, ba'a Jima ba saiga wani saurayi ya shigo ta wata kofa.
Baiyi magana ba tun bayan sallamar da yayi Zahra ta amsa masa, wayar ya kashe ya juyo Yana duban Wanda ya shigo din.
" Safwan Kada naji labarin Ina garin nan a bakin kowa, kaje inda na turaka jiya?"
"Naje oga komai ya Zama normal, harma sun Fara aiki saidai Zayyan yace wannan Matar tana yawan zuwa kusa da gidan amma dai Bata karasowa take komawa".
"Ok ba damuwa kaje kawai idan ka dawo ka taho da fresh milk da fruits a saka a kitchen din nan".
"Ok sir, na gode ya juya ya nufi inda ya fito har ya danyi nisa yaji maganar Mahmud.
"Safwan banji ka gaishe da madam ba, bahaushiya ce ba wani yaren zatayi makaba, Naga alama saina miqaka makarantar koyon turanci tunda Naga shi kadai ne kake da matsalarsa".
Dan Sosa Kai yayi yana dawowa baya.
"Afuwan Auntyn mu wallahi na dauka bakijin yaren mu, Ina kwana?"
"Lafiya kalau ya aiki?".
"Alhamdulillahi Auntyn mu, Allah ya Kara sutura ya bar Mana ke a gidan oga Dan isar Annabin Rahama".
"Amin ya Hayyu Ya Qayyum".
Muhmud ya fada.
Hanya ya nuna Masa alamar ya wuce bai Kara tofa wata maganar ba ya juya yabar gurin.
Ita Zahra kallon ikon Allah takeyi wallahi wannan ba Wanda suka zauna a Azare bane da banbanci nesa ba kusa ba.
Iskar Bakinsa ya hura Mata a fuska saitin idanunta, "kallon na menene Kona canza Miki ne? Kika tsareni da wadannan eyes din naki masu hanani sakat idan Ina kallonsu Dan Allah ki barni naci abinci kome kike bukata saina Baki badai kin hanani zaman can ba, to aini gaba ta Kaini gobarar Titi a jos, haka ake fada ko?" Ya tambaya Yana bude abincin.
Dan kwabe fuska tayi tana Dan turza kafa a kasa.
"Ni wallahi bani nace ka dawo ba kawai Kaine kayi niyya da kanka ka dawo Ni ba ruwana to na kiraki nayi maka me?".
"Au haka Zaki ce shike Nan yanzu dai bani abinci daga baya sai kiyi min bayanin yanda aka haihu a ragaya".
Bata gane hausar tasa ba tayi Shiru dai kawai.
Abinci ne kusan kala biyar Banda pepper soup na turkey.
Kasa hakuri zahra yayi Wai daga Ina wannan abincin irin haka?"

"Daga jama'ar Annabi, kinsan mu 'ya'yan malamai ko Ina muka sauka gida ne".
Shiru tayi ta zuba Masa abincin zata Zuba nata ya dauke plate din.
"Kin manta ai ba raba Abinci a tsakaninmu muci kawai".
Tare sukaci abincin suka Gama, tana Dan kallonsa lokaci-lokaci, da gaske yazo Mata da abubuwan mamaki da yawa Amma azarbabi ba nata bane. Dole tabi kamai a hankali saida ya tabbatar ta koshi sannan ya saurara mata, Nan cikin parlourn suka dawo suka zauna ya dorata a cinyarsa yasa hannunsa ya zagayo cikinta yana ta faman
amsa wayayoyi, sai ya amsa way kamar uku, sannan ya aje ya fuskance ta. Wasu irin wayoyine guda uku Wanda ita dai sai a T.V take ganinsu amma sai gasu a hannunsa kuma ya wani ci magani Dan kada ta Tama Fara masa wasu tambayoyi.
'
"Bani labari ya akayi ciwo Bai tashi kamaki ba Saida nayi Nissan Zango, naji doctor tace Wai rashin samun biyan bukata ne yake kawo miki yawan ciwon marar saboda sha'awarki tana motsawa Baki samun biyan bukata".
Waro Idanu tayi Baki bude tana Masa wani kallo.."Ni kuma? Wane irin magana ce wannan bayan fibroid din Kuma harda bita da kullin sharri? ta Nan Kuma ta bullo? To ai sai tazo ta ta cire min sha'awar tunda ita ta ganta, kawai ta Fadi gaskiya tanaso tayi amfani da aikinta ta cuceni,tunda da hadin bakinka Ashe ni aka mayar sakarya aka tasoni tunda daga kauyen mu aka kawoni gurin budurwaka ta dubani,ta ganeni ciki da bai kaga ko idan ta aureka bani da wata fuffuka da zanyi Mata, wata Kila da Allah baisa ta fito da maitarta fili ba da Allah kadai yasan illar da zatayi min.Da Jin saita cire min mahaifa gaba daya, ka fada Mata wallahi da gatana Ina da gatan da wallahi ta cutar da lafiyata Saida ta kare rayuwarta a life in prison, kuma indai Kaine nabar Mata taje ta hadiyeka kada wata ta Kara ganinka tace tana so, an fada Mata Ni Ina da damuwa ne da zata ringa wulakantani in dai saina Kara zuwa ta dubani ciwon yayi min abinda Zeyi min Kuma yau in Sha Allah gida Zan koma bazan iya Zama a Nan ba Ni duk kanon ma ta fice min daga Rai, ka mayar Dani inda nafi wayo".
Ta karasa fada tana juyar da fuskar ta gefe.
Kwanto da kansa yayi gefen wuyanta. "Cewa fa nayi ki bani labari ba cewa nayi meye damuwar ki ba, Ni meye laifina daga na turoki a duba min lafiyarki".
Ai fadar hakan saiya tunzurata nan da nan sai hawaye.
"Oh! My God!, Mena fada Kuma? pls tell me".
"Kwace Kanta ta shiga yi tana fadin.
Daman nasan ba Sona kakeyi ba tunda Ni matar shige ce Bata da daraja kuma wallahi duk Wanda ya Zama sanadin da wannan gararin rayuwar ya sameni ban yafe Masa ba, da qimata da mutuncina an mayar Dani wata shakatafi kowa saiya takani yanda yaso bani da wata qima".
Ta sunkuyar da kanta tana wani kuka Mai cin zuciya.
Iya dagula lissafi tayi Masa Dan kasa cewa komai yayi sai sakata da yayi a jikinsa ya kwantar da ita shi kadai yasan abinda yakeji, suna haka yaji wayar Daya Bari a kunne wadda yake amfanin yau da gobe ta dauki kida Mai Dadi.
A hankali ya Kai duba gurin wayar, Sameer ne.
Dauka yayi baice komai ba "Ina kofar part din Nan kana da bakuwa".
"Dude ka shigo sai muyi maganar".
Ya kashe ya aje wayar, Jin ya ambaci Sameer ya shigo yasa zahra yayi kokarin zare jikinta amma Dan bawan Allah nan kememe yaki sakinta saiya gyara Mata Zama kawai.
Dago Kai tayi da niyyar yi Masa magiyar ta saketa ta tashi dai dai lokacin Sameer ya karaso gurin, be taba tunanin tana jikinsa ba tunda shi kadai ake hangowa Saida ya kure musu yanda ba yanda za'ayi ya koma, tsaye yayi shi Bai Kona ba shi Kuma be karasa gurinsu ba ita kuma Zahra kunya kamar ta nutse wallahi Bata taba tunanin rashin ta idonsa ta Kai har haka ba.
"Have a seat, kazo ka tsaya Wai kuka take min na kawota an Mata wulakanci na Maida ta gida ita ko sunan Kano Bata sonji".
Sameer 'yar dariya yayi "Ni ba ruwana a ciki Dan aikene ni kasan Mata Dan Abu kadan saiya tada musu hankali, Daman bakuwar tata ce Hajiyar makwarari ce ta kirani bayan nabar Nan Ina gidan mommy na mayar da Rukayya saiga kiranta Wai lallai saina daukota tazo taga madam shine mommy tace na kawo ta indan ba haka ba zata iya rikita lissafin kasan halinta dai".
"Ok ba damuwa ku shigo tare ai Hajiyarmu ce ba inda bazata shiga ba".
"Ok sir".
Ya juya ya fice daga parlourn da sauri,mamakin Mahmud ne ya kamashi sosai ya rasa wane irin so yake yiwa yarinyar Nan ne haka? Yana tare da wannan mezeyci da wata Haseena ai saidai tayi hakuri da can Bata you tasiri ba gurinsa ba bare yanzu daya Sami abinda ya kwallafa rain a kansa.
Zahra Jin Sameer ya fice yasa ta dago da kanta daga kijinsa tana ajiyar zuciya, Dan just tayi kukan ta Kama nasa guri sai mamakin furucin oga Sameer daya cika Mata zuciya wai sir to me hakan ke nufi itafa kada su manna Mata Dan karamin hauka gaskiya.
Dan Allah ka barni na tashi kaji fa Hajiya ce yace fa
Zata shigo, Kuma Dan Allah bakaji kunya ba ka wani sakani a jikinta salon yace bani da tarbiyya".
Wani kallo ya watsa Mata "ai yau ko waye ze shigo gurin Nan a haka ze samemu gara asan Ina sonki tunda kina ganin ba sonki nake ba har kina kallona kina fadin Wai matar shige ce ke idan aka sameni rungume da kayana Ina lallashi kuwa koya saiya sheda ina son abuna, nine dai ba Sona ake ba anfi son wannan Mai jan kamar karas tunda saboda shi aka yarfeni da bakaken maganganu".
Har ta bude Baki zata bashi amasa taji rangada sallamar Hajiyar makwarari, ai ita kanta Bata San yanda akayi ba ta tsinci kanta a tsaye ballentana shi da ake zaune a jikinsa, shi dai Sameer Bai San lokacin da dariya ta kubce Masa ba ganin yanda Zahra tayi wani wuk'i-wuk'i da ita shima gogan dariyar yake Amma a ciki.

Da sauri ta nufi Hajiyar tana fadin. Oyoyo -oyoyo ga Hajiyata ga Hajiyata".
"Ke tafi can Ashe duk abinda na fada Miki ta bayan kunnenki ya wuce Saida Kika fice Kika barmu da tashin hankali, jiya kukan da nayi rabona da yin irinsa tun rasuwar mijina. Amma Kika sakani maimaitwa Dan Allah ke kuwa 'yar Nan Ina Kika tafi jiya".
"Haba Hajiya Dan Allah haka mukayi da ke a gida kafin mu taho wato kin karya Alkawarin kenan? To a kazarki

4 / 22