Author : Maman Teddy Category : Complete Novels
kuwa ya Mahmud ai jiya nayi kuka kamar ba gobe tashin hankalina Daya idan ta B'ata me za'a fada maka idan ka dawo Ashe kana hanya".
Baki zahra ta zubura tana kiftawa Rukayya Ido.
Kafin yayi magana sukaji magana daga bayansu.
"Waye nake gani kamar DANGEN SHUNI!?"
Da sauri Mahmud ya juya itama zahra juyawar tayi Jin kamar muryar data sani ce take Fadin hakan.
"Lah! Lah! Lah! Wa nake gani haka? Zakariyya Daman ana ganinku, rabon da mu hadu tun zuwana na karshen kontagora".
Zahra ce ta Matso tana Fadin Lah Ya Abba, Kaine ina yini?"
"Lafiya kalau ya kukaje gida? ai da safe na Kira Rukayya take fada min bakwa tare ta dawo gida".
"Eh wallahi, yasu Umma?"
"Suna lafiya daga Ina haka?"
Dan kallon Mahmud tayi kafin tace Masa "daga gida muke Mommy mukazo gaishewa".
Kusa da Mahmud ya matso Yana Fadin "DANGEN SHUNI! Allah ya taimaki manyan kasa. Daman ana ganinku haka available? Gaskiya na zama lucky. Daman wallahi neman number ka nakeyi nayi interview da kamfanin ku na Nan Kano last two weeks Amma har yau ban samu number ba, kasan lamarin kasar Saida wakasani,to ya akaji da jama'a?"
.
"Lafiya kalau Alhamdulillahi, Rukayya ki bashi number ta zamuyi maganar later, ko kana Shirin Zama sirikina ne?".
'yar dariya yayi "Hakan nake fata ai zuwan zahra jiya Ni Alkhairi ya zamar min".
Dan Jim Mahmud yayi, me kenan zakariyya kenan brother din sajida ne?
"Anyway we'll talk later in Sha Allah, madam let's go".
Sukayi sallama da Ya Abba suka nufi ciki zuciyar zahra fal murna wato duk abinda Allah yayi akwai hikima a cikinsa, wannan dalilin ne yasa ta tattara ta nufi Janbulo Ashe ita zata Zama dalilin haduwarsu.
Saida suka gulewa ganinsu sannan Ya Abba ya kalli Rukayya, "Daman Kuna da relation da DANGE?".
"Eh aminin Ya Sameer ne tun suna secondary School, yanzu haka shine P.A dinsa ai jiya zahra da muka dauko daga can wife dinsa ce an samu wani incidence ne tayi tafiyar ta can Janbulo din".
Baki sake yake kallon Rukayya abin jinsa yake kamar Almara badan ya gansu tare ba baze taba gaskata zance Rukayya ba, gaskiya he's surprised to ai shi ba haka maganar tazo Masa ba daga bakin sajida.
"Wai kina nufin DANGE ne mijin zahra?"
"Eh Mana shine, Wai Daman Kasan Ya Mahmud din ne?"
"So sai kuwa farin sani, muna haduwa da a kwantagora a unguwa Daya ma kuwa, ai kakarsa ta wurin Babansa 'yar can ce Nima kakata 'yar can ce Ummar mu kadai ta Haifa a Rimin sumaila Aurenta ya mutu ta koma gida, duk 'yan uwan Umma suna can kwantagoran na Niger state da Abuja, kinsa meya daure min Kai kuwa?"
Girgiza Masa Kai tayi alamar A'a.
"Cewa fa akayi ita zahrar an aura Mata Almajirin wani malami da yake a unguwarsu saboda duk Wanda yazo ze aureta sai an fasa Auren"
"Nima naji kadan daga labarinta gurin ya Sameer to ga dai mijinta Nan sauran bayanin Kuma ban San yanda akayi ya faru ba, tunda ya Sameer ba fada mana zeyi ba".
A parlour suka Sami mommy da kannan Rukayya Mata Bilkisu da Husna sai karamar yarinya 'yar Auntyn su Sameer Afra.
Tunda suka shigo zahra ke sadda Kai kasa da gaske nauyin mommy take ji, gaisuwar yaran suka ringa amsawa da gudu Afta ta nufo zahra tana Fadin "welcome Aunty" ta shige jikinta tana tattabata.
Hannunta zahra ta riqe suka karasa gurin da mommy ke zaune yayin da su Husna suka koma dayan parlourn.
A kasa Kan carpet suka zauna, a tare suka gaishe da mommy din, ta yiwa Mahmud sannu da dawowa sannan ta Dora da godiya, hidima da akeyi da Sameer. Zahra ta kalla ganin sai sadda Kai tajeyi yasa tace.
" 'ya ta ko jikin ne Naga bakya walwala sosai?".
Yana ji yayi fuska Bai tankaba ba dai iya shegen da tayi ba kenan jiyan saita magantu da bakinta.
Bata yarda sun hada Ido ba tace.
"A'a ba komai mommy lafiya ta kalau".
"To Masha Allah haka nake son ji, kina jina ki saki jikinki Dani ki daina Jin nauyi na kinji, ni uwace idan kina da damuwa duk da bama fatan hakan ki sameni ki fada min ki daina yanke hukunci da kanki".
"To in Sha Allah bazan qara ba na gode". Ta fada tana Wasa kitson Afra kanana Yar dasu.
Tashi mommy tayi tana fadin "Bari na fadawa Alhaji kunzo sai ku shuga ki gaisa yaga 'yar tasa wadda bai sani ba".
Ta nufi nufi wani corridor dake hannun dama.
Bata dade ba ta dawo tana fad'in "Mahmud kuje Yana parlourn kasa". Saida aka yiwa Afra wayo da chocolates sannan ta yards tabi mommy dakinta ita Kuma zahra suka nufi bangaren Abban su Sameer din.
A Nan suka same shi a parlourn Wanda yaji kayan more rayuwa dai-dai da shekarunsa, babban mutum mai cikar Kamala, fari sosai kamar irin buzayen nan, a Nan zahra ta gano inda Aunty Rukayya ta samo farin ta dan mommy dai irin wankan tarwada din nan ce shi yasa tayi mamakin Jin Rukayya kanwarsa ce uwa Daya uba Daya.
Da madaukakiyar fara'a ta taresu Yana fadin "Masha Allah sannunku da zuwa, ka kyauta Mahmud daka kawo min yarinyar nan kaga na Riga Alhaji Muhammad ganinta ko? masha Allah ku zauna".
Ya fada Yana nuna musu seat din Zama, basu zauna ba a kasa suka zauna suna gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska, da gani shi mutun ne Mai yawan fara'a.
"Allah yayi muku Albarka ya kade fitina a tsakaninku naji Dadi kwarai daka kawo min ita, yarinya ayi hakuri da juna kinji, mijinki na jama'a ne Saida hakuri kiyi Masa biyayya gwargwadon iyawarki, Kai Kuma ka kula da lamarin ta kada ka yarda wani ya wulakanta maka ita amana ce suka baka, a yanda kaje musu ba kowa ne ze dauki yarinya kamar wannan ya baka ba, to ka kula da ita sosai ka Bata dukkan farin ciki tayi rawar gani, daga karshe Ina rokonka abinda ban taba saka Baki a cikin duk kwaramniyar da akayi a baya ba sai yau, kayi hakuri ka koma gida ba girmanka da mutuncinka bane haka ai ba'a fushi da iyaye duk rintsi albarkarsu ake nema kome ka Zama indai kana da iyaye yaro ne Kai, nasan an bata maka Amma idan ka duba ko tukwicin wannan yarinyar da Allah yayi Maka ai sai ka huce ka nuna godiyarka ga Allah Daya baka ita, Kai ba karamin mutum bane a kasar Nan Koda kuwa a shekaru kake da karancin girma, kaje gida ka hada hankalin ka guri daya, Allah yayi Albarka ya Kara daukaka numa ganin sakonni mun gode kwarai da gaske, idan Kuma naji Shiru baka koma ba da kaina zanyi abinda baka so ayi din, Dan ko shekaranjiya Saida Hajiya Inna Tasha kukanta a dakin Nan Ina amfanin irin haka ai musulmin kwarai da yafiya aka San Shi kaji Mahmud ayi hakuri ayi afuwa Allah yasa son masu yafiya".
Tunda Alhajin ya Fara magana jikin Mahmud yayi sanyi da gaske duk badak'alar da akayi ko uffan Bai tofa ba sai yanzu Kuma yasan baya raba Daya biyu damuwar da yaga hajiya Inna a ciki ta Dame shi.
Cikin ladabi Mahmud ya Fara magana. "Nagode Abba in Sha Allah Zan koma, Nima nayi wannan tunanin ba fushi nayi dasu ba sune dai sukayi fushi dani, Ina son su huce ne tukunna kada na koma a maido hannun agogo baya".
"Kai haba wannan maganar ai babu ita to ai itama zahara'u ta zamar maka garkuwa, ki tashi ku tafi dare ya Farayi ga yanayin sanyi Allah yayi Albarka ayi kokari ayi yanda nace".
"In Sha Allah Abba".
'yar karamar Leda Fara Alhajin ya mikowa Mahmud Yana fadin "ungo rikewa 'yata".
Godiya sukayi Masa Sosai suka nufi kofa Yana saka musu Albarka.
Lokacin da suka fito Rukayya ta shigo suna tare da mommy.
"Aunty Rukayya har Ya Abban ya tafi?". Zahrar ta fada tana nufar inda Rukayyar take.
"Eh ya wuce tun dazu".
"Ok shikenan da sako Zan bashi gurin Ummah Amma na Kirata a waya".
Sallama sukayiwa Mommy Rukayya ta rakosu har gurin mota da ledar da mommy ta bawa zahra kyautar dangin turaren wuta dasu humra.
Da sukazo fita kudi masu yawa taga ya bawa Mai gadin gidan sannan suka wuce, tunda suka fito daga parlourn Alhaji Abban su Sameer Mahmud yayi dif da alamar anyi Masa famin wani Miki a zuciyarsa.
Ganin haka yasa zahra ta Kama kanta itama.
Titin gidan Bashir tofa suka fito gasu can sun fita gidan Buhari, sahad store taga ya shigo ya nemi guri yayi parking sannan ya bude Yana Fadi ki jirani ina zuwa ya wuce ciki.
Bai Dade da shiga ba wata mota tayi parking kusa da tasu, gurin akwai wadatar hasken da yasa kana iya ganin Wanda yake cikin mota.
Ba zato ba tsammani kawai idanun Zahra suka sarke Dana Musbahu Wanda ya fito daga gurin driver suna tare da wani Guy da alamar dayan irin ya'yan hutun Nan ne, da gani Suma sayyayar sukazo, da sauri ya nufo gurinta jikinsa har rawa yakeyi Yana fadin "Zahra!" dai-dai lokacin Kuma Mahmud ya fito tare da ma'aikatan gurin sun dauko Masa Kaya sun nufo motar, shi Kuma wannan gayen Yana ganin Mahmud yayi wata irin zabura ya nufeshi ya rungume shi jikinsa na wata irin tsuma Yana fadin "Ya Mahmud Ina ka shiga ka barmu".
[2/1, 6:08 PM] ASHMAR🤍: ✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
MAMAN FATEEMAH.
Page 48.
___ Rungume juna sukayi sosai, kuka ya saka Masa kamar karamin yaro da gani ba karamin missing dinsa yayi ba , Shima Mahmud Jin wani Abu yake yi a zuciyarsa badan namijin duniya bane da Babu abinda ze hana shi zubda hawayen shima, yayi kewar Faruq sosai saboda sunyi wata irin shaquwa dashi ta ban mamaki,duk da ba uwa daya ta haifesu ba Kuma kusan sa'anni ne Dan baifi wata hudu Mahmud ya bashi ba, Amma Yana bashi girma sosai,duk abinda yakeyi hankalinsa dari bisa dari Yana Kan musbahu Wanda yayi mutuwar tsaye shi Bai karasa gurin zahrar ba, shi kima bai dawo baya ba, me yake Shirin faruwa ne? wannan din meye dinta yasan dai tayi aure ance wani k'olo aka aura mata, to Ina auren kada dai gudowa tayi ta shigo yawon duniya?.
Ita ma zahrar ji tayi komai ya tsaya mata, har wata zufa taji tana tsatstsafo Mata a jikinta abun kamar a mafarki, gurin da su Mahmud suke ta kara kallo still suna yanda suke Saidai gaba Daya hankalinsa Yana gurinsu fuskarsa ba annuri ko misqala zarratin kamar dade duniya be taba dariya ba, sadda Kai zahra tayi dan ji tayi wani irin tsoronsa na shigarta tuna karonsu tayi wanda ya kusan cinye mata lebe, kasa tayi da kanta jiran taji ya zata kaya.
Bayansa ya Mahmud ya ringa Dan bubbugawa da tafin hannunsa Yana fadin.
"Haba Faruq meye na kuka da girmanka da komai Kai ba mace ba, ka nutsu ka share wannan hawayen, akwai mace fa a kusa damu tana kallonka, wallahi wata Rana sai tayi maka gorin ragon maza"
Ya fada Yana sakinsa da sauri yama duban masu rike da kayan daya saya a hannu "sorry na barku da Kaya kuyi hakuri Dan Allah mu karasa ku saka a mota"
Yayi gaba yana yiwa Mushahu wani shegen kallo, Faruq na rike dashi ram Kamar Yana gudun ya bace Masa.
Back seat Faruq ya bude suka zuba kayan,Faruq din ne ya curo kudin da baisan yawansu ba ya Mika musu sukayi godiya suka wuce bakin aikinsu.
Jikin motar Mahmud ya tsaya Yana facing din musbahu da fuskar shanu.
"Dan Allah Ya Mahmud kana Ina ne duk tsawon wannan lokacin? Kuma wacece wannan da kuke tare?"
Fuska Babu annuri Kona sisin kwabo ya Maida dubansa Kan Faruq din "Idan ka Gama abinda kazoyi ka sameni a Bawo road komai dare Ina jiranka". Ganin yanda mahmud ya daure fuska yasa yaja bakinsa yayi shiru be kara tambayarsa komai ba.
"Ok. Zan shigo yanzu ma in Sha Allah, Nima yau na shigo around four thirty, yanzu ma uncle mushahu na rako, dan yayar Mamee ne gashi nan,bari nayi masa magana ku gaisa be ganeka bane".
Da hanzari Mahmud ya daga masa hannu "pls Faruq no need". Ya fada yana dhugewa motar, abinda ya daurewa Faruq kai kenan, wai Ya Mahmud ne yake driving da kansa, sai yake ganin kamar an canza masa Ya Mahmud dinsa da wani.
Saida ya fice daga harabar gurin sannan Faruq ya karaso gurin Uncle dinsa yana fadar "Yanzu fa a hanya muke maganar Ya mahmud da kai ashe yana kusa damu wallahi ba wanda ya zaci yana kasar nan, abinda ya bani mamaki wannan Babyn da suke tare a sanina da Ya Mahmud baya harkar mata gaskiya, sai dai ban sani ba ko bacin rai ya saka shi yin hulda irin wannan dasu".
Faruq be ankare da shi kadai yake zubarsa ba sai da ya kai aya yaji Musbahu be tofa masa ko A ba sannan ya dan taba shi.
Firgigit yayi alamun yayi zurfi a cikin dogon tunani.
Dogon numfashi yaja yana yiwa Faruq duban tsanaki, kafin yace.
"Faruq waye wannan nake gani kamar Mahmud?".
"Shine mana baka ganeshi bane?".
Wani gumi yaji nan da nan ya rufe shi tabbas Shiya gani a cikin hotunan da Najib ya turo masa na daurin Auren zahra, ya dade yana hasaso inda yasan face din amma ya kasa tantancewa ke nan DANGE shine mijin da aka aurawa zahra a matsayin Almajirin Alaramma? take a nan yaji wata irin karaya ta mamaye masa zuciya yasan ya rasa zahra har abada, shi dinwa da ze iya ja da wannan dan tahaliki, ko manyan manajojinsa bai isa yayi takara dasu ba kafin ma a kai ga P.A dinsa.
Cikin nuna tsantsar karaya ya cewa Faruq.
"Ban gane shi ba sai bayan ya wuce, ina labarin dana baka dazu akan fasa aurena da akayi?" Kai Faruq ya gyada masa yana fadin "Na gane bana yarinar nan 'yar Azare ba?.
"Eh to ai wannan ta cikin motar itace yarinyar da nake fada maka kuma tabbas shine aka aura mata a matsayin Almajiri kolo, bari na nuna maka hotunan daurin auren, dan wani yaro nasa ya turo min hotunan na dade ina tunanin inda nasan fuskar Amma ban taba ko hasashen shine ba, tunda nasan meze kawo shi Azare harda zaman Almajiranci".
"What!!! Almajiranci kuma?
"Yes of course, bari na nuna maka pictures din ka gani". Ya fada da kyarin gwiwa duk da karfin hali kawai yakeyi hankalinsa idan yayi dubu a tashe take.
Ya ciro wayarsa daga cikin aljihun wando ya shiga gallary ya nemo hotunan, cikin sauri da zaquwa Faruq ya karbi wayar, da Sameer ya fara cin karo a hoton yana kusa da Ya Mahmud sai kuma wadanda be sansu ba, a hankali ya ringa duba hotunan tabbas Ya Mahmud ne tunda ga P.A dinsa nan wato duk tunanin da akeyi yana turai ashe yana Bauchi state saboda tsabar iya bada kafa.
Dago da kai yayi yana kallon Uncle din nasa da mamaki fal fuskarsa.
"Na gani tabbasa wlh shine, to amma ta yaya hakan ta faru? nayi mamakin auren daka fada min yayi, bafa wanda yasan inda yake ya yanke hulda da kowa fa, yanzu na gama fada maka irin badaqalar da aka sha a family din wanda yasa ya tsallake yayi tafiyarsa, uncle sorry bari na bishi hankalina baze kwanta gani nake kamar dabara yayi min ya gudu".
Kai kawai Musbahu ya iya jinjina masa, yayi hanyar ficewa da sauri, yana fita Allah ya kawo adaidaita ba kowa ya tare ya shiga saida suka fara tafiya ya fada masa Hausawa Bawo road.
Tunda Mahmud ya fice daga harabar sahad store ya saki motar yana wani irin tuki, ko iskar data aje zahra be duba ba itama takurewa tayi jikin kofa da gaske shakkarsa takeji dan ya hade gabas da yamma kudu da Arewa, ya doki sitiyari yafi sau shurin masaki.
Ita dai zahra sai addu'a take Allah ya sauke su lafiya, gaban wani gida taga ya tsaya Mai shegen kyau haske ya cika ko Ina da karfi ya danna Horn din kamar ance masa Mai gadin sabon kurma ne, da sauri ya fito ya nufo motar banban mutum ne ba yaro ba, ganin baisan motar ba yasa ya karaso da sauri ganin Wanda yake wannan mahaukacin horn din.
Bazato yayi arba da Mahmud, da sauri ya zube Yana kwasar gaisuwa, hannu kawai ya iya d'aga Masa da sauri ya koma har Yana hadawa da gudu yaje ya bude gate din, da gudun dai ya shige har kofar ya nufi ba parking space ba, kofar da zata sadaka da main parlourn ya tsaya ko motar be tsaya kashewa ba ya zagayo ya bude side din zahrar take zaune yasa hannu ya fisgota waje, be saurari komai ba ya nufi steps din shiga ciki da ita, ganinsa kamar mahaukacin Zaki ya saka zahra cikin tashin hankali, da hannu Daya ya zura katin ya bude kofar, be tsaya a parlourn ba direct upstairs ya nufa da ita tana turjewa tare da fasa masa kuka Dan wani irin riko ya yiwa hannun Kamar ze tsinke Mata tsintsiyar hannu, be saurareta ba Saida ya dangana da inda yayi niyya bedroom din da suke sama guda uku, ya nufi na kusa dashi da karfi ya tura kofar da suka shiga yasa kafa ya Maida kofar,Kan wani lafiyayyan Turkish bed yayi musu masauki, yana zuwa Bai bi takan kukan da takeyi ba ya saka hannu ya fisge Rolling din da tayi yana huci.Dan magana ma ya kasayi saboda wani Abu da yake taso Masa, baya tayi da sauri ganin Yana neman cakumo rigarta, Kan gadon ya hauro Shima ko takalmin kafarsa be cire ba, Rigar jikinsa ya cire yayi jifa da ita, ya kamota tata Rigar ms yasa hannunsa ya karketa tun daga sama har kasa, take jikinta ya bayyana, ya kasance daga ita sai farar bra tas da farin pant a jikinta,jikin Nan sai wani glowing yake kamar kifi tarwad'a, cikin tashin hankali da matsananciyar kunya ga kuka take fadar "Dan Allah kayi hakuri me nayi maka wallahi bani na kirasa ba, shine ya ganoni ya taho ko magana banyi Masa ba,ai kana kallon mu, wallahi bansa zasuzo ba ba Kaine ka kaini gurin ba?".
Ta fada tana kankame jikinta.
Duk abinda ke jikinsa ya