Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
kwalba gwangwani ko roba basu dameshi ba,yafison abun sha irin namu da gargajiya da za'a hada a gida,kamar kunun aya zobo da sauransu,daga qarshe ya dauki wani matstsen ruwan lemon zaqi hade da cup ya dawo falon.
Bai jima da fara aikin ba jabir ya iso,daga sallamar sa daya amsa bai sake bi ta kansa ba,shima jabirun sai ya shareshi,saboda ha fuskanci abun sai 'yar tursasawa kadan ta shigo ciki,dole sai an ma ja'afar haka idan anaso rayuwarsa ta dai daita nan kusa,don haka shima sai ya wuce daki abinsa.
Sai da yayo wanka ya canza kaya sannan ya dawo falon,saman hannun kujerar dake daura da ja'afar din ya zauna yana fadin
"Ka gama yajin kenan kayo bikon kanka da kanka" maimakon ya amsa masa,sai kawai ya ciro passport dinsa ya cillawa jabir din.
Bin passport din yayi da kallo,kafin ya sanya hannu ya dauka ya soma budewa yana dubawa. Idanu jabir ya fidda waje sannan ya dorasu saman ja'afar din
"Over stay?" Kamar bazai amsa shi ba,sai kuma yace
"Yes" a daqile yana ci gaba da concentrating kan aikinsa,ajiyar zuciya jabir ya fitar yana daga passport din daga fuskarsa
"Ya Allah,why ja'afar?,kasan visa dinka ya qare amma kaci gaba da zama musu a qasa baka biya anyi expanding maka ita ba?ka sani turkey ba kamar kowacce irin qasa bace, you know how people suffer before they get the visa....shine ka samu suna baka whenever you need zakayi wasa da damarka?"
"I don't like noises please,idan zakayi abinda ya dace kayi,if not ka ajjiyemin passport dina ka qara gaba ka barni naci gaba da zama,dama ban shirya tafiyar ba" gimtse dariyarsa jabir yayi,ya gano shi sarai,neman duk hanyar da zaya kubucewa komawa yakeyi
"Alright,sai kamin transfer abinda za'a kashe ta account dina,kasa dole sai na nema baaba ambassador" ya fada yana bata rai shima hadi da miqewa
"Bani dako sisi" ya fada kansa tsaye
"Kut!" Jabir ya fada yana fito da ido waje,dariya kuma na masa yawo can qasan ransa,lallai ja'afar din mugun dan rainin wayo ne,recently yaga amount din dake qaramin account dinsa ma,wanda shine baya ajiya kudi mai yawa a ciki,the amount is very huge,kamar yasan me yake tunani,sai ya daga kyawawan idanun nan nashi dake dauke da wani irin sinadari mi qarfi ya zubewa jabir su
"I mean bani dako sisin da zan batar don komawata gida,bcoz ban shirya ba" dole dariya ta subucewa jabir,cikin ransa yace
"Kayi ka gama,komawa gida dole,mu lafiyarka da hankalinka mukeso,tafi mana kuma komai"
"Okay,.....duk naji,but bani zan maka komai ba,you know,dole kaje da kanka,tunda kai mai laifi ne a wajensu yanzu" kamar bazai amsa ba kafin yace
"Naji" ciki ciki,kada kai jabir din kawai yayi yana nufar kitchen,cikin ransa yana fadin
"Allah ya shirya ja'afar,mai zama dashi sai ya shirya,zuma ga zaqi ga harbi ga kuma ba tsoro" .
Abinci ya shiryo musu,ya kuma kawo har nan inda ja'afar din yake,yanata wani ciccijewa da basarwa amma jabir yayi kamar bai gane me yake nufi ba,ya gama daagiyar duka ya sauko suka fara cin abincin.
Yadda jabir din yaga yana ci ya tabbatar masa a kwanakin da ya qauracewa gidan bai cin wani abincin kirki,dama can shi din irin mutanen nan ne da ba abincin kowa suke iya ci ba,sau tari sun gwammace su haqura da abincin,sai yaji tausayinsa ya darsar masa a rai,yaji har cikin zuciyarsa yana fatan wannan auren ya zame ma rayuwar ja'afar din wani babban sauyi da kuma ci gaba,suna gamawa kiran amaryarsa ya shigo,don haka ya miqe yabar wajen,jaafar ya bishi da tsaki da kuma harara,ganin yadda yaketa zumudin amsa kiran nata.
πππππ
*_SHIN KINA YIWA KANKI DA JIKINKI TANADIN SABULAN WANKA MASU KYAU MAI DA TSOHUWA YARINYA KO KEMA HAR YANZU DANGWALI YABA KIKE SAWA JIKINKI?_*
*_SABULUN DAKE GYARA JIKI DA FUSKA YA MAIDA FATA TAMKAR TA JARIRI SABUWAR HAIHUWA?_*
*_SABULUN DA DUK INDA KIKA SHIGA FATARKI ZAKI FITA DABAN DATA SAURAN MATA?,YA MAIDAKI TAMKAR WATA DAN DAREN SHA HUDU?_*
*NASAN ZAKIYI TUNANIN A INA ZAKI SAMU WANNAN INGANTACCEN SABULUN?AMSAR ITACE_*
*_J-SKIN CARE PRODUCTS (JANNAT SKIN CARE PRODUCTS)_*
_SUKE SAMAR DA KALOLIN SABULAI NA KECE RAINI KAMAR HAKA_
Black soap
Kiddies Black soap
Sugar body scrub
Body butter
Kojic acid soap
Turmeric soap
Goat milk soap
Honey soap
Carrot soap
Face and body cream
Hair growth oil
*_dukka wadan nan kalolin sabulai J-SKIN CARE PRODUCTS sun samar muku dasu bisa farashi dai dai da aljihun kowa_*
*_Baya ga haka kuma,wani abun qayatarwar,suna karbar kwangilar yin sabulun cold process ga masu yin biki ko suna_*
*Zaku iya dubasu a shafukansu na sada zumunta*
*Instgram*:J-skincare products
*Tiktok*:jannatskincare
*Ko ki tuntubesu kai tsaye ta wannan number wayar*
0813 801 1240
*J-skin care products,DUNIYAR SABULAI MAI DA TSOHUWA YARINYA*
27
*********Sosai maimunatu takejin dadin zama gidan bappa sule,saboda tana samun kulawa qwarai da gaske,ga kuma 'yammatan 'ya'yansa da suke kusan sa'anni da ita,hanne da hauwa,sun fita wayo da kuma gogewa,don inda suke din ba za'a kirashi da karkara ba,maraya ce,jininsu ya hadu sosai saboda kirkinsu da yadda suke nuna mata qauna da janta a jiki,nan da nan shaquwa ta shiga tsakaninsu,abun na yiwa maimunatu dadi,ashe dangi dadi garesu,koda ace batasan dangin mahaifinta ba,amma a qalla samun wadan nan a kusa na dauke mata kewa da fargabar rasa dangin mahaifi da kaso hamsin cikin dari.
A lokacin maimunatu ta sake tabbatarwa kanta lallai inna furera shigo shigo babu zurfi tayi musu,a duk sanda tazo gembu ashe nuna musu take komai lafiya lau,sannan maimunatu najin dadin can shi yasa taqi biyota nan ganin dangi,abunda yayi matuqar baiwa maimunatu mamaki,kasancewarta miskila ba kasafai takan buda baki tacewa inna furera zata bita b,saidai ita kanta takan karanci tsantsar yadda maimunatun ke son biyotan,don tasha gwaba mata baqar magana kan cewa duk ta gama nacin da qwallafa ran,wataqila ita da gembu sai idan taje yawon arba'in idan ta haihu gidan buderi,wani lokacin saidai ta sakaye taci kukanta,wani lokacin kuma har hanya take bin inna furera cike da fata da kuma burin zataji tausayinta ta tafi da ita,saidai ko sau daya bata taba sauyawa ba,daga bisani data qara wayo sai ta tattara ta qyale,ta sanyawa ranta dangana da haquri.
A sannan maimunatu taga kara ta dangin mahaifiyarta da zumunci,kowa da abinda zai kawo bisa al'adar auren fulani,basu duba cewa DR yace abar komai zai mata ba,cikin qaramin lokaci aka tara mata kayan amfanin kitchen irin nasu kala kala,wanda ba lallai a sameshi a can ba.
**********Biki ya rage saura sati guda kacal,tun a lokacin hidima ta balle daga kowanne bangare,gidan dr da kuma gidan minister harda gidansu amarya ga jabir wato fatima,saidai hidimar da ake gidan minister zata baka mamaki,kai kace bikin yara shida za'ayi ba yarinya daya ba,tun a kwanaki bakwai din da sukayi saura gidan ya fara karbar baki.
*********Katafaren beauty parlor ne,wanda aka tanadeshi musamman saboda gyaran jiki,turara jiki,fidda duk wata dauda,tada komada da maida tsohuwa yarinya a zamanance,waje ne na wane da wane,waje ne na idan ka isa ka shiga.
Daga cikin wajen fira ce ke tashi,da alama mata an hadu,kuma an samu abunda ake buqata,qawayen amarya samha ne,kowacce da abinda ake mata a wajen,wasu gyaran manicure and pedicure,wasu gyaran gashi,wasu kuma lalle ake zana musu,yayin da wasu kuma ake musu gyaran fuskarsu don su sake kyan gani a wajen bikin.
Gefe guda amarya unaisa ce cikin wata irin riga data lullube jikinta da ita,sai kanta kawai ake gani,hayaqi dake cike da qamshi ne yake futowa daga wuyanta,magana suke qasa qasa ita da wata matashiya kamarta dake gefanta,wanda hayaniyar da sauran keyi yasa ba zaka iya jin me suke fada din sosai ba saika matsa kusa dasu
"Na samu information.....jibi zai dawo nigeria"
"Na rasa wanne irin so kike masa samiha,ta ya zaki auri mutumin dako zance bai taba zuwa wajenki ba bare ayi maganar so?" Murmushi ta saki tana girgiza kai
"Ba zaki gane ba husna,ja'afar na daban ne,irinsa ba'a jiran sai sunzo zance kafin su cancanta a auresu,na musamman ne shi,sabodashi naqi aure har sai da na samu cikar burina ta hanyar daddy,na nace duk da yayi aure,har Allah ya qaddara rabona ne,matarsa da yake matuqar so ta rasu,saboda shi naqi auren unais naqi auren ahmad naqi auren hanif ke da duk wanda kika sani" kai husna ta jinjina
"Amma wanne qwarin gwiwa kk dashi na cewa zai soki?,da har zaki auri mijin matacciya wanda yake cikin halin SO BAYAN RAI?" Murmushi ta sake saki
"Karkiji komai,duk abinda kk so baka gajiya dashi,soyayyar da nake masa ita zata ja mana ragama,i will do all my best naga ya soni,kada ki manta,ni ba qaramar mace bace,na hada komai da kowanne namiji zaiyi sha'awa ya kuma burgeshi"
"But kin manta kina da kishiya kenan" murmushin dake nuna hankalinta a kwance yake ta saki
"Kusan hakan gaskiya,yarinya ce qarama wadda ta fito daga ruga,kinga yaushe zata tsoratani?,beside ma kuma itama hadi ne,rigima ce irin ta kakanni kawai,abun ma dariya yake ban idan na tuna,namiji irin ja'afar da wannan a matsayin mata idan banda rigimar tsofaffi?very classy guy,har na fara imagining yadda zai fatattaketa wlh a kurkusa duk sanda suka fara haduwa da ita" ta qarashe fada tana sakin dariya,don ta tabbata abinda zai biyo baya kenan,wannan shine yaqini bisa hasashenta.
Ita kanta husna data hasaso ja'afar din,ta kuma san wayeshi da yadda yake,sai taji hasashen unaisan haka yake,'yar ruga?,ba shakka kam bazai iya zama da ita ba,kamar yadda tayi amanna ba zata iya goga kishi da kyakkyawa kuma me aji irin qawarta unaisa diyar minister ba.
_ba'asan maci tuwo ba sai miya ta qare,muje zuwa_
**********Ζarfe hudu na rana agogon turkey,biyu na rana agogon nigeria jirgin Turkish airline ya sauka a filin sauka da tashin jirage na malam aminu kano,dauke da tarin passengers,ciki harda jabir usma khalid akko da ja'afar marwan khalid akko.
Dukkansu sanye suke da wasu lafiyayyun Italian suit,kalolin da suka dace da gayu aji da kuma kyansu,duk wanda ya kallesu sai ya maida kansa ya dada kallonsu,zaratan fulanin samari guda biyu,wadanda ilimi hutu da kuma kudi ya ratsa kowannensu,jikoki kuma jinin khalidu akko.
Zaman jiran jirgin da zai tashi zuwa gombe sukayi,wanda duka duka bai wuce awa guda ba suka daga zuwa gomben.
Ta gefan idanu jabir yaketa karantar ja'afar tunda suka sauka a qasar,fuskarsa kadaran kadaham take,babu walwala hakanan ba wata fara'a bace saman fuskar tasa ba,hannunaa guda daya yana soke a aljihunsa,har zuwa sanda suke nufar motar da tazo daga gidan Dr marwan domin kaisu gida.
Muslimu driver din abbi shine yazo daukansu,cikin wata baqar range Rover,ko ba'a gaya maka kasan cewa sabuwa ce,sai qyalli take da daukan idanu,jabir yayi tsammanin samun masu tarbarsu bayan muslimun da zai tuqa su,saidai babu kowa saishi din,sai ya alaqanta hakan da shakkar ja'afar da sukeyi,don ba kasafai ko a baya zasuyi tafiya tare a samu masu tarbarsu ba.
Cikin matuqar girmamawa da jin dadin dawowarsu muslimu ya gaidasu,sannan ya sanya jakankunansu a mota,ya shiga ya tada motar suka dauki hanya.
Tunda suka hau hanyar idanunsa na bisa titunansu,yana qiyasta watanni da ya share bashi qasarsa,watanni ne masu dan dama,dashi kansa baisan gudun da suke ba sai yanzu.
Tazarar dake tsakanin gidan dr marwan akko da airport din ba mai yawa bace,dalilin da yasa basu dauki wani lokaci mai tsaho ba suka isa gidan.
Bin ginin gidan nasu yake da kallo kamar wanda a yau yafara arba dashi,ba komai yake kallo ba sai sabon fenti da yaga anbi gidan dashi duk da girma da fadinsa,cikin qanqanin lokaci yaji zuciyarsa na masa qunci,da gaske shirin bikin suke kenan,sai ya dauke kansa daga inda yake kallo din,ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fito ya biyo bayan jabir.
Tun a harabar gidan tarin ma'aikata dake aiki a qarqashin gidan suka fara musu maraba,kusan da jabir ya barsu,dama shike da wannan juriyar,ya sanya kansa zuwa cikin gidan,a yau din da yake a cikin gidan,sai yaji wani irin kewa da zumudi mai yawan gaske nason ganin mahaifiyarsa ita da gudan jininsa amna,baisan yayi kewarsu kamar hauka ba sai yanzu da yake a kusa dasu.
Da tattausar muryarsa mai zurfin nan yayi sallama cikin falon nasa,haj aishatu dake nutse saman kujerun alfarma da aka yiwa falon nata qawanya dasu ta daga kanta daga duban farar takardar dake dauke da rubutu a hannunta tana amsa sallamar tasa,idanunsu suka gauraya da juna,ta saki boyayyar ajiyar zuciya mai nauyi
"Alhmadlh ya rabb" ta fada can qasan zuciyarta,sai ta dubi matar da suke tare
"Ki shiga ciki kice ina samra?,ta baki waje kici abinci,zan kiraki mintuna kadan" miqewa tayi tana godiya,sannan tabi hanyar da zata sadata da farfajiyar sassan haj aishatun da take kamae qaramin tsakar gida mai siffar garden da aka wadata da wasu fararen duwatsu na wuta.
Ci gaba yayi da takowa cikin falon,yayin da amma wannan karon tayi qoqarin ajjiye kunyar dake tsakaninsu
"Maraba lale,ashe kuna gab da isowa?" Wani dan qaramin miskilin murmushi ya subuce masa,ya qaraso gabanta ya zube ya soma gaisheta,tana amsa masa itama cikin kulawa tare da karantar yanayinsa.
Baiyi wata qiba ba sam,saidai jikinsa a murje yake kadan,sai kuma fatarsa data sakw fresh da kuma haske,alamin weather din qasar data karbeshi,akwai maganganu masu tarin yawa dake ran amma,saidai a yanzun kamar yayi wuri tace komai,don haka ta barwa lokaci na gaba idan suka gama warwarewa daga gajiyar tafiya.
Yadda ja'afar ya zube mata haka jabir,don marabarsa da ja'afar din daukan cikinsa ne na tsahon wata tara ne kawai batayi ba.
Kusan shi ya fara fita yabar jabiru da amma,wanda dama koda a baya abun kusan haka yake,hirarsu da amman bata qarewa,zaka sauka jabir ya haifa ba ja'afar ba.
Yana fitowa sukayi kacibus da ammi,kana kallonta kasan an fara shiga hidima,daga boys quarters na gidan take,taje ta duba yadda aka gyara gami da tsara wajen saboda saukar baqi 'yan biki.
"Oyoyo,saukar yaushe?,ina ta ciki ban jiku ba?" Murmushin gefan baki yayi,ya gaidata itama a girmame kamar yadda suka saba
"Me zakuci?,don gidan gaba daya a hargitse yake,banjin zaku samu kalar abincin da kuke so"
"Ki turo mana hisham kawai ammi" muryar jabir dake tahowa daga baya ta bata amsa,don yasan halim ja'afar din sarai,tsaf zai iya cewa
"We are okay" bayan shi magana ta gaskiya yunwa yakeji
"Banajin zaku samu hisham cikin gidan nan jabir,gidan yau kusan babu kowa sai baqi,yana can hidimar saukar nasu baqin"
"Ba damuwa zan kirashi" jabir ya fada suka soma gaisawa sannan shima yabi bayan ja'afar wanda ya wuce sassan anni,ammi tayi gaba tana tunanin abinda zata sa a samar musu me dan sauqi da zasu iya ci.
Sanda ya sanya kai falon har yayi kamar zai koma saboda muryoyin baqi da yaji sai kuma yaci gaba da cusa kai,sai daya shiga din sannan ya fuskanci su waye a falon,anty maama ce,sai ummi badi'a matar uncle abbas.
Qaramin tsaki yaja qasan ransa,su kadai amma sun cika falon da hayaniya kamar mutum dubu,dukkansu maraba suke masa banda anni da taja bakinta ta tsuke,ya qaraso ya zauna saman hannun kujera yana amsa marabarsu,kafin dukansu su biyun su miqe anty maama tana cewa
"Anni bari muje,nan da awa biyu idan bamu dawo ba don Allah hayatu ko muslimu suje su debomin yaran nan"
"Zan gaya musu,amma kada kuje ku zauna kuma"
"Muna samo abinda mukeso zamu dawo"
"Allah ya tsare" suka amsa suna ficewa,sai falon ya rage saura shi da annin.
"Barka da warhaka" ya fada cikin rusunawa
"Barkan ka" ta bashi amsa a taqaice tana bata fuska,saidai a yau din baiji bata fuskarta ya dameshi ba kamar yadda suke da ita a baya,yana jin a wannan bigiren shi yafi cancanta ya bata fuska akan kowa
"Ina wuni?"
"Daban wuni ba zaka ganni?,ai da zamanka kayi a sassanka,ni yafi cancanta nazo na gaisheka ai,tunda yanzu ka zama uban kowa,sai abinda kakeso ka tsara zamu dinga bi,tunda kaika haifi kanka" kyawawan idanunsa ya lumshe kana ya budesu,ita tsohuwar batasan abinda yakeji bane?,batasan irin qunci da ciwon data haddasa masa ba haka siddan yana zaman zamansa yana lallaba rayuwarsa?
Muryoyin sallamarsu ta katse anni daga ruwan tijarar data debo ta shirya sauke masa su tas yau a kansa,duka 'yammatan gidan ne suka shigo,wansa dawowarsu kenan daga gyaran gashi.
Da hayaniya suka shigo saboda yadda sabgogin bikin suka fara musu dadi,amma suna hada idanu kowacce sai tayi turus,ta kuma saita bakinta,kudin goro ya yiwa gaisuwarsu ya amsa su gaba daya,babu wadda tayi gigin zama dukka suka juya suna barin sashen,daidai lokacin da amna wadda aka yiwa kanta gyara na musamman take rugowa cikin falon riqe da leda a hannunta cike da kayan qwalam tana qwalawa anni kira gami da cewa tazo suci.
Cak ta tsaya sanda tayi idanu hudu da mahaifin nata,sai kuma ta watsar da ledar hannun nata,ta take da gudu tayo wajensa tana kiran
"Dadddyyyyy...." Qasa ya sauko ya tanqwashe qafafunsa,ya kuma bude mata hannayensa gaba daya,yana jin wata irin qauna da qarfin jini dake tsakanin uba da