Advertisements
Chapter 65 Reading Gurbin Ido Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Gurbin Ido Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   65 / 67

192K to 195K   out of 200.8K words

suka dauko daga uwa da uba suka cakude,duka duka basu haura awa guda da zuwansu duniya ba,saidai soyayyar dake kewaye dasu mai tarin yawa ce.

A hankali qofar toilet din ta bude, maimunatu ce tare da umma sa'adah,gefe kuma afrah ce,suna riqe da ita a hannu tana takawa a hankali,sai kuma duka hankula sukayi kansu,kowa yana zabga mata sannu

"Anya maimunatu ba zaki bar kukan nan haka ba?,ko babies dinne bakiso?" Hajja ta fada tana kama baki,dubanta umma sa'adah tayi

"Daadarta take tunawa,wai dama haka tasha wahala ta haifeta?,ta sake shan wahala.bata haifa abinda ke cikinta ba ta rasu?" Kowa saida jikinsa yayi sanyi,suka fara bata baki cikin nuna kulawa.

A mugun sukwane motocin guda biyu suka dira farfajiyar asibitin,motar farko bata ko kai ga kammala tsaiwa ba aka bude murfinta aka sauko da wani irin kuzari hanzari da kuma sassarfa.

Captain ja'afar ne,sanye da wani farin kaftan da aka qawata shi da dimki na musamman,tamkar yana da masaniyar yau din rana ce ta musamman a rayuwarsa,biye dashi kuwa manyan ma'aikatansa ne,don ya baro company ne babu shiri.

Dukka baya suka rufa masa,jabir ya qara hanzari ya cimmasa

"Relax mana captain,ance lafiya qalau fa ta sauka"

"I know dude,na qagu na ganta ne" ya fada yana sake qara hanzarinsa harda sassarfa.

Daga baya dukka suka tsaya,banda jabir da yaci gaba da binsa har suka isa bakin qofar, ja'afar dinne a gaba,don haka yana bude qofar hankalin kowa yayi kanshi,yayin da shi kuma idanunsa gaba daya suke kan maimunatunshi dake zaune saman gado,umma sa'adah na qoqarin bata tea tasha ko za'a samu ruwan nono ya samu,don yaran sun fara qananun rigingimu.

Suna hada idanu sabbin qwalla suka cika mata idanu,abubuwa ne mabanbanta cikin zuciyarta,farinciki takeji mara misaltuwa da a yau ta bawa ja'afar din muradin ransa wato 'ya'ya,tunda cikinta ya girma baya cikakken bacci,don ta fishi samun barci me kyau ma,kullum cikin addu'a yake ba dare ba rana,hidima yake mata da jikinsa da aljihunsa,ya qwallafa rai matuqa akan cikin,har ta dinga jin anya ba mutuwa zasuyi ita da yaran ba?,anya itama ba wucewa zatayi yadda daadarta ta rasu ba?,sai gashi komai yazo ya wuce kamar ba'ayi ba.

Abu na biyu zallar shagwaba ne da kuma tuna irin wahalar data sha,yazo yanzu zaa sauke masa nasa rabon da bai samu ba a dazun d tana labor.

Dukka gaidashi suke,yayin da manyan ke masa barka,yana amsa musu amma hankalinsa ya karkata gaba daya a kanta,miqewa sukayi suka fara basu waje,afra da laila suka isa gefan gadon suka ajjiye yaran suma sukabi bayansu.

Shuru dakin ya dauka bayan ficewarsu, hannayensa saye a aljihun rigarsa yana qare musu kallo daga nesa,yana jin komai tamkar a mafarki,idan ya kalleta sai ya maida dubansa ga yaran,duk da baya iya ganin fuskarsu sosai

"Angel" ya kirayi sunanta a tausashe,yana jin wata sabuwar soyayyarta tana ratsa qashi bargo da kuma jijiyar jikinsa,kasa daga kai tayi ta kalleshi,sai ya haqura da kiran saboda yadda yakeji kamar ana fusgarshi zuwa gareta ya soma takawa a hankali,har ya isa bakin gadon,jikinta na gogar gwiwoyinta data zubo qafafunta qasa ta jingina da bangon.

Hannayensa ya sanya ya daga fuskarta da kyau yana kallonta,sai itama ta zube masa idanuwanta da sukayi wani tarwai, tausayinta ya kamashi,yaso ace dukka gwagwarmayar naqudar data sha yana tare da ita,sai gashi ya qunsa mata ciki ya barta da wahala ita kadai

85


"Angel ya kika yimin haka?,kinajin naquda kika bari na tafi na barki?,bayan alqawari ne muka yiwa juna,dadi ko wuya zamu rabasu tare?" Kyakkyawan murmushi ta sauke masa duk da har yanzu da qwalla a idanuwanta

"Banason raba maka hankali ne ko na tashi hankalinka,kayimin dukka wani abu daya dace kayi din"

"Duk da haka angel,ki yafeni" ya fada yana sanyata cikin jikinsa yana kuma shafa bayanta a hankali.

Yadda taji zuciyarsa na bugawa ya alamta mata zuciyarsa ta motsu da soyayyarta,hanya mafi sauqi kenan da take gane hakan

"Ka cancanci dukka yabo da kuma jinjina" ta fada masa murya can qasa,sai kuma ta zare jikinta a hankali,da kallo ya bita

"Banyi wanka bafa,jikina duka warin asibiti yakeyi"

"Yafimin qamshin dukka turaren dake duniya" ya amsa mata yana narkar da idanunsa cikin nata,yana sake jin ta zama mallakinsa.

Motsawar da daya daga cikin yaran sukayi shi ya tuna musu da wanzuwar yaran a wajen,ya saki wani qawataccen murmushi yana juyawa zuwa inda suke,yasa hannu ya fara dauko wanda yafi kusa dashi ya dorashi saman cinyarta,sannan ya sake dauko dayan shima ya jerashi da dan uwansa,yasa hannu a hankali ya bude fuskokinsu da kyau.

Idanu ya zuba musu kamar yadda itama taketa kallonsu,cike da mamakin yanzun wadan nan yaranta ne?,mallakinta ne?,ita da ja'afar dinta?.

Gani yake kamar sun masa nesa duk da kusa dashi suke,kamar zasu kubcewa idanuwansa,kawai sai ya ranqwafo dab da fuskokinsu yana sake qare musu kallo,dai dai sanda dayan shima ya motsa ya tura hannunsa a baki ya fara tsotsa.

Dago kansa yayi sai suka hada ido,ta tabe baki gami da yamutse fuska

"Kaga kura da shan bugu ko?" Wata qawatacciyar dariya ce ta subuce masa

"Wonderful,na dauka idanuna kemin gizo,ashe da gaske ne photocopy na na baki, alhamdulillah,kinga tun yanzu suna alamta miki da daddynsu sukeyi ba dake ba" rigimar ganga ta saka masa shi kuma ya lalace wajen lallashi,kamar ba mutane ke jiransa a waje ba

"Kin manta yanzun kin girma ne?,maman twins ce ke fa?" Ya rada mata a kunne,saita sunne kanta a kafadarsa tana dariya

"Karki damu,next year photocopy dinki zamu ajjiye,kinga shikenan rigima ta qare" ido ta fidda tana dubansa

"Mutuwa kakeso nayi hubby?"

"Ba zaki mutu ba,saikin haifan kamar haka kamar haka sau shida,suma sun bani jikoki kamar hakan" ya qarasa maganar yana debesu ya maida su gadonsu dake kusa da nata,sannan ya dauko tea din da umma sa'adah ta ajjiye ya dawo kusa da ita ya zauna sosai cinyoyinsu na gogar na juna,har sannan binsa take da kallo,idan suka kebe ya sake mata kamar hakan nan saika rantse da Allah ba shine ja'afar marwan akko ba

"Haaa.... bude bakin ki karba" hankali kwance ya zauna yana bata tea din,tana sha yana mata tambayoyi game da haihuwar tata tana bashi amsa,gab da zata shanye dr noor ta turo dakin ta shigo,kanta tsaye bata wani koma da baya ba,don itama wayayyar 'yar boko ce,wannan din ba baqon abu bane a wajenta,sai suka gaisa tayi masa barka sannan ta wuce wajen yaran kai tsaye tana sake kallonsu,yaran sun bata sha'awa matuqa,bama itaba,duk wanda yaji labarin an haifa twins yaran captain ja'afar akko sai ya leqo ganinsu,ya kuma tafi da kyansu da girmansu a baki,wannan yasa tuntuni hajja ta tofesu da addu'o'in tsari

"Bakin dan adam bashi da kyau,wasu jariran da yawa tun a nan ake nakastasu,wasu suke rasa rayuwarsu,wani ma zai tanka abu baisan yana da kambun bakan ba,sai musiba ta fadawa abu yayita lalacewa a rasa dalili"(haka zancan hajja yake,don Allah komai zamu gani ya burgemu bama akan mutum kawai ba mu dinga shuru da bakinmu koda zuciyarmu ta yaba,idan ma ya zama dole sai.munyi magana mu hada da tubarkalla.ma sha Allah,wasunmu da yawa basusan suna da kambun baka ba,da yawa qila sun zama silar lalacewa ko mutuwar wasu amma basu sani ba,mu kula,kambun baka daban maita daban,a musulunci babu maita,amma akwai kambun baka,mu zama masu yawan fadin ma sha Allah,kome muka gani ya burgemu,ko uwa baason ki fiya yaba kyan danki ko wani abu nashi,zai iya yiwuwa kina da kambun bakan ke a karan kanki amma bakisan kina dashi ba,sannan mu iyaye mu dinga kula da yawaita yiwa yaranmu addu'a,musamamn idan zamu fita wani waje,musamman kuma idan Allah ya musu baiwar kyau ko wani abu,ga masu zuwa kasuwa su dinga haquri suna aje yaran a gida,mu rage yabon yaranmu da rage yawan fadin baiwarsu,kamar baiwar wayo ko basirar karatu,wani da ya tanka shikenan,sai kiga karatun yaro nata komawa baya a rasa daga inda matsalar take,karmu manta da addu'ar da annabi kewa jikokinsa sayyadina hassan da hussain,Allah ya kare mana su daga mugun ido da mugun baki ameen summa ameen).

"Allah ya raya su,ya albarkacesu captain, congratulations" ta fada tana duba maimunatu

"Thank you dr noor" ya fada shima yana jin dadin kulawar da take bawa familyn nashi.

"Yauwa komai lafiya lau,zaku iya tafiya nan da awa biyu,amma ya kamata su fara shan nono yanzu,saboda wannan yellow din nonon kada lokacin samuwarsa ya wuce,yana da amfani sosai a jikinsu".

Cikin awanni biyun suka gama shirya komai sai tafiya gida,a nan fa aka fara dambarwa,anni na cewa gidan dr zaa wuce da ita,hajja na cewa gidan wajenta zata je,yayin da umma sa'ada ma ke ganin ita yafi cancanta ta karbeta,saidai shi ogan ba wanda ya cewa komai,sai tsintarsu sukayi a sabon gida,ainihin gidan da shaheeda ta zauna,wanda aka sake gyarawa aka kuma sake canza masa fasali,tuni ya gama aikinsa an zuba komai,suturun sawar maimunatu kawai zaa dauko,don twins dakinsu ya dade da kammala,an sanya komai da yara zasu buqata,da gadajensu na kwanciya kowa nashi daban.

"Shikenan dan uwana ya raba magana" anty maama ta fada tana dariya,don ita kanta yadda yaran suka shiga ranta,inda zaa bata maimunatu karba zatayi da gudu,shuru tayi dai kawai ganin masu son karbar nasu nada yawa,kuma duka sun fita cancanta.

Cikin kwanaki shidan da suka biyo baya kusan kullum gidan cike yake da 'yan barka,masu wuni da masu zuwa su tafi,yaran sunzo da wani albarka da kuma farinjini na musamman,ba daga dangin maimunatu ba daga dangin ja'afar ba,ga 'yan uwan amma suma da baa barsu a baya ba,don wadan nan sune jikokin fari a wajenta.

Baaba tabawa ke zaune a gidan,sai wata mai aikin yasira da anty sa'adah ta kawo mata,gefe daya ga afrah da take wuni sai dare take tafiya,kullum akwai driver da zai daukota ya kuma dawo da ita permanent wannan umarnin captain ja'afar ne.

Tun afra na iya irga kayan barka da abinda maimunatu da yaranta suka samu har ta bacewa lissafi,saidai ta karba takai dakin yaran ta ajjiye kawai,ita kanta batasan adadin mutanen da sukazo mata ba suka mata alkhairi,bata taba sanin ja'afar mai mutane bane har haka sai data haifa 'yan biyu,tarin tururuwar mutane,wasunsu shi kansa bai sansu ba,duk da haka ba'a hana kowa shiga gidan, saboda anni tace albarka ce,kuma lokaci ne.

Hatta abbu da abbi baa barsu a baya ba,kowanne sai daya tako qafa da qafa yaga jikokinsa,kuma kowannensu sai daya ajjiye musu barka mai nauyi,bama kamar abbuun da yakejin su kamar 'ya'yansa,yana ji kamar shi aka yiwa haihuwar shi da yake da qarancin zuri'a.

Kayan lefen da aka ranta masa kudi aka masa aka sanyashi biya su ya maimaitawa maimunatu wannan karon,akwatina yayi mata sosai kamar yadda kowanne yaro a cikinsu aka masa nasa,duk da komai nasu iri daya ne,kasa cewa komai maimunatu tayi,saboda gatan da ja'afar din ke gwada mata har gani takeyi yayi yawa

"Kadan daga aikin manya,indai zuciyarsa naso....to babu algus a soyayyarsa,da dukka zuciya ruhi da gangar jikinsa yakeyi a aikace" baba tabawa ta fada,jinjina kai kawai maimunatu tayi,don ita din ganau ce ba jiyau ba.

Hankulan abbuu hajja da umma sa'adah ya kwanta sosai,iya soyayyar da ja'afar ke nuna mata da danginsa kadai ya tabbatar musu koda babu su maimunatu ba zata wulaqanta ba.

Ranar suna tun asuba abbi da abbu kowa yayi radin suna a masallacin unguwarsu,akayi rabon goro da alawa aka fadin sunan yaran,marwan abbinda abubakar saddiq abbu,a nan gida afrah ta zaba musu nickname da (sa'ad da as'ad).

Gidan dr kuwa suna sukayi sosai,yayin da gidan captain ja'afar sukayi nasu sunan,fadin irin kyan da maimunatun tayi bata baki ne,don kusan sau hudu ja'afar yana dawowa gidan ta boyayyar qofar baya,don kawai yazo ya sake ganinta ita da yaran nashi masu zubin diyan larabawa kamar yadda baaba tabawa kan fada idan ta gama musu wanka ta shiryasu tana dan musu rawa.

Dukka danginta sun amsa kira,abinka da mai dashi,tun daga gembu har adamawa,abun farincikin tron suna ya watse lafiya,gift data samu kuwa tattarasu tayi tace ba zata iya budasu ba sai ta huta sosai.

Kwanaki biyu rak gidan ya zamana iya na masu shi,sai baaba tabawa da kuma yasira,saidai duk da haka lokaci lokaci daga can gidan abbunta ko gidan dr marwan suna shigowa dubata tare da ganin yara.

Cikin wani irin gata da kuma kulawa ta shiga rainon yaranta,gefe daya kuma hajja tana tsumata da gyara na musamman,dukka wata kulawa ta buri ta dorawa jikokin nata biyu afrah da maimoon,kasancewar bikin afra ya matso,sai ya zamana duk wani gyara da za'a yi mata tare da maimunatun take hadawanata gyaran har yafi na maimunatun,sosai hajja ya bude tsohuwar ajiyarta na tsohuwar babarbariya,ta shiga gyaran jikarta da kyau,duk wani gata daya dace tayi mata lokacin biki da bata sameshi ba yanzun take zubeshi,daga ita har abbun,shi kansa garar da yayi mata mai uban yawa abar kallo ce,duk da ja'afar din yace baya buqatar komai amma kuma abbun yace ya sani yayi haquri,aladace,kuma alada mai kyau ce wadda musulunci baiyi suka ba.

Sosai itama ta hada hankalinta da kyau wajen kula da jikinta yaranta dama mijinta,a yanzun take jinta a matsayin cikakkiyar macen aure kamar kowacce diya mace,tayi kwance kwance tana debe tsaffin dabarun kama miji ba boka ba malam daga bakin hajja sa baaba tabawa,sannan tana samun sabbabi daga wajen afreen dinta da kuma fatiman jabir wadda tuni ta haife nata boy din don har ya fara wayo.

Kafin tayi arba'in gaba daya ja'afar din ya sukurkuce mata,kulawar da take bashi kamar wani fami da kuma qwalele take masa,tako ina ta cika sosai,ta qara kyau da haske,ga wasu fitinannun turaruka da take amfani dasu,randa ya ritsata a daki akaso yin aika aika Allah ya qwaceta da qyar,tun daga ranar take takatsantsan,don so take itama saita cika kwanakinta sannan ta rikeshi yadda zata ida rikitashi da kyau.

_sai muce Allah ya qara danqon qauna moon din captain🥰😊😊,muje zuwa ga page din qarshe in sha Allah_

86


*BAYAN WASU SHEKARU*


Babban dakin taro ne wanda ya cika maqil da zallar mata,manya mata masu ji da aji da kuma jin sun kai wani matsayi sun kuma taka mataki na rayuwa.

Daga can step inda mai gabatarwa take,ta qarashe bayaninta da fadin

"We will call our star that we have gathered here to honor her......maimoon abubakar muhammad" ta qarashe kiran da madaukakin sauti.

Shuru dakin taron ya dauka,kowa ya tattara hankalinsa gami da zuba idanuwansa yana jiran ganin bullowarta,wasu sun santa,amma kuma ako da yaushe basu gajiya da ganinta,ita din ta dabance,tun daga yanayin halitta zuwa suttura da kuma yadda tasan mutuncin dressing,idan akace dressing to dressing mai nuna zallar kamala da kuma aji a rayuwa,dai dai da qamshinta na musamman ne,baa maganar sauran abubuwa,wadanda kuma basu santa din ba,zumudi suke suyi tozali da kyakkyawar fuskar da labarinta ya cika kunnuwansu kafin zuwan wannan rana,fuskar data zama ta alkhairi kuma jirgin fito ga duk wani mabuqaci mai neman taimako,fuskar data hadu da qalubale da gagwarmayar rayuwa iri daban daban,amma tayi hobbosa ta tabbatar bata koma baya ba.

Cikin nutsuwa sautun takalman qafarta dake da tsinin dunduniya maras tsaho suka ratsowa ta cikin mutane,sai ta dauki hankulan mutane da dama nima na juya don ganin tahowar tata.

Kyakkyawar farar bafulatanar usul,mai wani irin haske daya cakude da surkin jaja jaja,tamkar jini zai diga a jikinta saman lallausar fatarta mai santsi da sheqi,wadda ke nuni da zallar hutu wadata da kuma jin dadi,ma'abociyar wani irin kyau mai fusgar hankali da wani irin kwarjini daya cakude da zallar kirki da son jama'a dake saya mata soyayyar mutane duk inda ta tsoma qafarta.

Sanye take da dark blue din wani yadi na mata,wanda aka yiwa ado da light blue da kuma yarfin gold din zare,kalar data sake fitar da kyanta,wani lafiyayyen mayafi ne a jikinta da bashi da shara shara ko kadan mahadin lafiyayyan takalmin qafarta mai madauri,hannayenta kana iya hangen warwaraye masu fashion masu tsadar gaske,wanda zaka tsammaci gold ne,amma ba shi bane,kasancewar sam bata da sha'awar amfani da gold din.

Ci gaba tayi da takowa har ta iso wajen,ta karba abun maganar tana duban fuskar mc din,tata fuskarta dauke da murmushi,sanna ta maida dubanta ga matan dake gabanta,gyara zaman fararen eye glasses din data sanya don qawata adonta tayi,sannan tayi bismillah ta fara magana cikin tataccen turancinta daya cakuda da

65 / 67