Author : Mamuhgee Category : Complete Novels
ta saki kukanta sosai tana kifa kanta a table din.
Da sauri afrah taja kujera dab da ita ta zauna tana fadin
"Innalillahi,wai menene yake damunki maimoon?,meye matsalar?" Bata bata amsa ba,sai kawai tasa hannu ta zare wayarta dake gefe,tasan me zatayi mata.
Contact ta shiga ta fara laluben sunayen soyayya data sama wata contact,saidai babu ko daya a ciki data gani,haka ta haqura,ta sanya ainihin sunansa saiga number din ta fito,kallon maimunatu da batasan ma tanayi ba tayi taja qaramin tsaki,wai itakam yaushe zata bude zuciyarta ta yarda soyayya takeyi?,ta kuma gane ita ke wahalar da ita?,kawai saita canza sunan dake kan number zuwa honey bee,sannan kanta tsaye ta danna masa kira.
Dai dai lokacin yana kwance a wajen hutawa daya ware cikin office dinsa,tunda yazo yake zaune a wajen,ya gaza hassala komai,baisan me yake damunsa ba,gaba daya tunda ta tafi ta tafi da walwalarsa,hannunsa daya bisa fuskarsa,sai yaji shigowar kira wayarsa.
Har tayi ringing dinta ta katse bai dauka ba,ta sake shigowa ta kuma katsewa,ya shareta yana ci gaba da kwanciyarsa,har sai da yaji qishirwa,sannan ya miqe zaune ya jawo wayar yana son duba lokaci,don da wuri zai fita daga company din yau,saboda ya lura bazai iya aikata wani abun kirki ba.
Ganin miscall da number ta yasa ya tashi ya zauna sosai,bai zaci wayarsu na amfani ba a school,daga sama kuna tex ne
_ka kira pls yaa ja'afar,qawar maimoon ce_
Bai gama karantawa ba ya fita a saqon ya kira number din,yana jin yadda zuciyarsa ta tafi gaba daya ta kuma afu gason jin muryarta.
Da sauri afra ta duba kiran sannan ta dan matsa gefe kadan daga inda maimunatu ke zaune ta daga
"What's happening?" Ya tambaya kai tsaye,jin ba muryar maimunatun bace
"Kuka dai takeyi,na tambayeta taqi magana"
"Bata wayar" ya fada cikin jin wani tashin hankali yana shigarsa,meye ya sameta?,itace tambayar daya fara yiwa kansa.
"Yaa ja'afar ne" ta rada mata a hankali,kafin ta gama fuskantarta har ta nana mata wayar a kunne
"Angel" ya furta cikin wani irin taushi,da zuzzurfar muryarsa data aike mata da wasu saqonni lungu da saqo na jikinta karo daya,wani nauyi taji zuciyarta tayi,hawayenta kuma ya dauke cak,ta zuqi numfashi sosai tanason fesarwa amma kamar ya riqe
"Hello.....angel,my moon" ya sake fada very softly,wannan karon fidda numfashin tayi gaba daya,wanda ya zame mata kamar ajiyar zuciya mai sauti,batasan sanda tasa hannu ta dafe wayar sosai a kunnenta ba,har yanzu idanuwanta suna rufe tana sauraren saukar numfashin sa daga cikin wayar,da alama shima ta taba zuciyarsa sosai
"Say something mana angel,bazan iya jurewa ba,meye ya faru?"
"Zazzabi" ta fada muryarta a mugun narke,kuka mara sauti me dauke da hawaye yana kubce mata
"Ya salam......jirani gani nan zuwa" ya fada yana katse wayar gaba daya.
A gaggauce ya maida takalminsa ya kira PA yayi cigiyar key din motarsa,ya karba ya fice ba tare daya tsaya sauraren kowa ko kuma meeting dake gabansa awa daya mai zuwa ba.
Kasa motsawa tayi daga wajen,sai kunnuwanta suka shiga maimaito mata abinda yace
"Ta jirashi gashinan?,da gaske zuwan zaiyi??" Zuciyarta dai ta cika da wasi wasi,amma duk da haka sai tayi likimo taci gaba da kwanciya a wajen,har zuwa sanda ta tsinci muryar afra na kiranta irin kiran gaggawa,idanuwa kawai ta bude tana jiran isowarta
"Ana kiranki office din principal,yaa ja'afar ne yazo" batasan ta miqe da hanzari ba sai data ji kanta ya saara,ta dafe kanta da hannunta sannan ta dubi afra
"Muje ki rakani please" hannunta ta riqe tana murmushi,tanason tsokanarta amma kuma yanayinta yana nuna seriousness dinta kan condition din duk da take ciki,don haka shuru tayi tana taka mata zuwa office din.
A nutse tayi sallama a office din,idanuwanta na kallon qasa,don ta tabbatar indai idanunta a dage suke kuma yana cikin office din,tofa lallai idanunsa suna kanta ne,ita kuma a yanzun batajin zata iya dauke idanunsa akanta,bata jin zata iya jurema wannan kallon nasa,qamshinsa kawai ya isa ya bata tabbacin yana cikin office din,taci gaba da takawa a hankali,sai zuciyarta ta gaza jurema rashin kallon fuskarsa,ta yanke shawarar ko satar kallonsa ne tayi.
Ta kuwa aikata hakan,saidai kuma ya kamata,don caraf idanuwansu suka hadu waje daya,yana binta da wani irin mayen kallon da shi kadai yasan fassararsa,gaba daya yaga kamar an sake canza masa ita,ta sake kyau ta sake fresh,saidai tadan faada kadan
"Zaki bishi zakuje ku dawo" principal din ya fada kansa tsaye,tunda yasan waye ja'afar din a wajenta
"Okay sir" ta fada kanta a qasa,sannan ta miqe ta soma takawa a hankali tana ficewa a office din da zummar zuwa dakinsu ta gani idan akwai abinda zata dauko.
A hankali taji an riqo hannunta ta baya a tausashe tana hanyar komawa hostel,da sauri ta waiwayo,tadan razana saboda hanyace da babu masu wucewa sosai a kanta,sannan kuma batasan ana biye da ita ba.
Idanuwansu suka sarqe waje guda,kowanne ya jefi dan uwansa da wani abu mai matuqar tasiri a ruhi da gangar jiki,suka shiga jin kamar zasu narke a wajen saboda abinda ke zagaya zugata da gangar jikinsu,sukaci gaba kuma da kallon junansu kamar an manne idanuwan nasu cikin na juna ne,bata ankara ba ba zato taji ya fusgeta zuwa cikin jikinsa da wani irin zafi,har takalmin qafarta yana zamewa daga qafartata.
Sosai ya riqeta a jikinsa saidai kuma cikin taushi,baiyi wata wata ba ya kama fuskarta da kyau ya riqe gam,ya fara sauke mata kisses,tare da lashe labbanta da yayi matuqar missing dinsu kamar hauka.
Gaba daya ya kunce mata noti,jikinta ya dauki rawa,tanata qoqarin tureshi amma yafi qarfinta nesa ba kusa ba,sai da dabara tazo mata,ta kama labbansa ta ciza da dan qarfi,sannan ya saketa ya d'an ja da baya yana fadin
"Wash Allah na amma na" a wahalce kamar wanda aka yiwa duka aka galabaitar dashi.
Da rinannu idanuwansa yake kallonta,yayi da ita kuma dariya taso kubce mata jin kiran sunan amma da yayi kamar wani qaramin yaro,amma saita danne,ya rigata magantuwa
"Wannan fa mugunta ce,so kike ki.kasheni ko?,tunda kika shigo kinqi kallona,sannan kuma kin fito kin barni ni daya irin baki damu dani ba ko?,kuma yanzun ina welcoming naki saiki cijemin labba?" Ya fada yana taba leban nasa da zara zaran yatsunsa guda biyu.
Bakinta tadan rufe tana fidda fararen idanuwanta waje,wanda hakan ya qara fidda girmansu
"Bafa haka bane,ban wani cijeka sosai ba,nan din hanya ce,wani yana iya zuwa wucewa" sauke yatsun nasa yayi yana ci gaba da jifanta da mayataccen kallonsa,sai ya fara takowa yana fadi a hankali
"I don't care ni ko waye zai ganmu,ni ke kadai nake gani idanuwana da zuciyata gaba daya,kuma zakisan kin cijeni,you will pay" ya qarasa maganar yana riskarta gami da surarta gaba daya cikin hannuwansa.
Bugun zuciyarta ya qaru,tsoro ya cikata,kada a ganta fa mutuncinta ya zube,tunda ba kowa bane yasan alaqarsu ba,shi bayajin kunya ne
"Don Allah......don Allah,ja saukeni,akwai abinda zan dauko a daki"
"Bana buqatar komai,ke kadai nake buqata"
"To zan iya qarasa mota da kaina"
"Banaso shima,jikinki akwai dan dumi amma ba mai yawa ba" runtse idanunta kawai tayi sosai,ta buda suit dinsa ta saman ta cusa kanta a ciki tana jin tsoro da fargabar wanda zai iya ganinsu a haka,cikin taimakon Allah har suka kai bakin motar basu gamu da kowa ba,dama yammace,kuma hanyar bata jama'a bace.
"Sauka to madam karki hadiyeni,irin wannan riqon haka?" Ya fada yana duban fuskarta murmushi na qwacewa miskilar fuskarsa,wani zillo.tayi ta sauka jin fassarar da yayi mata,gefe guda kuma zuciyarta ta cika da mamakin dama.yana raha da tsokana irin haka?.
Da kansa ya bude mata motar ta shiga,ya tattara mata hijab dinta daya fito zuwa ciki ya rufe mata,sannan ya zagaya seat dinsa yana jin zuciyarsa wasai,duk wani nauyi da tayi ya nemeshi ya rasa cikin qanqanin lokaci,yayin da itama ta langabar da kanta a kafada tana kallonsa sanda yake zagayowa ta gaban motar zuwa seat dinsa
"Ya Allah,yashe ta fara sonsa har haka ne?" Saita lumshe idanunta itama sirritaccen murmushi yana kubce mata.
77
Tunda suka shiga motar ko sau daya bai sani hannunsa daga cikin nata ba,yana riqe dashi gam yana murzawa a hankali,ya dameta kan ta fada masa me yasa tadan rame ba kamar yadda ya dawo da ita ba?,ko akwai mai matsa mata?,ko makarantar babu dadi?" Tsaf ta boye idanunta cikin hijab,taqi kuma cewa komai dashi,sai ya sakar mata lallausan murmushi
"Ni bari na gaya miki....tunda ke kina boyemin,kada nace kina sona ko?" Curewa ta sakeyi waje daya dariya mai dan siririn sauti tana qwace mata,abinda ya sake jan hankalinsa a kanta kenan,ya saki murmushi shima me sautin
"Bana iya baccin,bana iya cin abinci,Allah kinji nace miki Allah,tunda kika tafi kika tafi da dukka farinciki da walwalata,har na dinga jina kamar marayan da babu uwa babu uba" kanta ta daga a hankali,bakinta ya subuce tace
"Kamar ni kenan?" Idamunta na nuna alamun rauninta,tausayinta ya tsarga masa sosai, cikin ransa yace
"Kin kusa yin dariya in sha Allah" amma a fili saiya riqe hannunta dakyau,ya jashi zuwa qirjinsa saitin zuciyarsa
"Ki daukeni kamar uwa da uba a wajenki,nayi alqawari zan cike miki dukka wani gurbi da gibi da kike dashi a rayuwarki" idanunta ta maida ta lumshe,tana jin kewarsu,maganarsa ta ta katse mata tunani
"Wannan zafin jikin tun yaushe kika fara shi?"
"Last week ne"
"Ya kamata kiga likita kenan,don kada yaci gaba" ya fada tana sanya signal a motarsa,kanta ta girgiza tana bin titin da zai kaisu gidana abbi da kallo
"Yana sauka.....amna nakeson ka daukomin,tunda na dawo ban ganta ba" fuska yadan kwabe kamar yaro qarami
"Noooo......so nake mu shiga duniyar da zata bamu nutsuwa,wadda babu kowa a cikinta daga ni sai ke" yadda yayi maganar yana rage gudun motar ya kuma sanya idanunsa cikin nata sai wani nauyin ya kamata,ta maida kanta baya ta jinginar tana rufe idanuwanta.
A parking lot na gidansa dake government road ya tsaya,sannan ya kirayi me gadin,ya gaya masa ya rufe masa gidan,idan anzo nemansa yace he's not available😂,kasaqe mai gadin yayi yana maimaita kalmar
"Yallabai kamar wani layin waya?" Ya fada a ransa
"Jeka" ja'afar din ya fada yana sallamarsa,sai ya amsa da to yana komawa bakin aikinsa.
Yanxun ma daukar abarsa cak yayi har zuwa sassansa,tare sukayi alwala sukayi sallar la'asar data kubce musu su duka,ya waiwayo yana dubanta a hankali bayan sun isar,sai ya zame ya kashingida yana tokare jikinsa da jikinta,idanunsa a qasa
"Me zakaci?" Ta tambayeshi saboda tunawan da tayi yace bai iyacin abinci
"Anything angel,indai daga gareki ne zanci,amma for now dai barci nakeji" ya fada yana zamewa a hankali,ya aza kansa saman cinyarta kwanciyar rigingine yadda yake ganin fuskarta fes,yana kafeta da wani irin kallo,idanuwansa suna lullumshewa.
Hannunsa ya sanya ya zare tafin hannunta data rufe fuskarta dasu,muryarsa da matuqar rauni yace
"Noooo.....don Allah please ki barni na more,don Allah,badon ni ba" sai ya maida hannuwansa ya harde a qijinsa yana ci gaba da kallonta,idanuwansa na masa nauyi,wani irin barci na rinjayar idanuwan nasa,a hankali yana kallonta suna rufewa,har suka rufe gaba daya,wani daddadan baccin da ya manta rabonsa dashi yayi awon gaba dashi.
Saukar numfashin sa cikin nutsuwa ya tabbatar mata baccin yakeyi da gaske,a hankali ta sauke idanuwanta kan fuskarsa
"Ma sha Allah,fatabarakallahu ahsanul khaliqin" ya fita a bakinta,asalin kyau ta gani dab da ita cakude cikin fata chocolate color.
A hankali take qare masa kallo,kwantacciyar sumar fuskarsa mai santsi baqa sidik data sake qwawata fuskarsa,wani irin gyaran fuska yakeyi,kamar na jaruman fina finan qasar hindu,koma waye yake masa aski tabbas expert ne,ya kuma san aikinsa,bata taba damuwa da aski ko sanin me askin maza ke ciki ba,amma a yanzun askin ya burgeta sosai.
Yatsanta guda daya ta sanya tsakanin gashin girarsa masu laushi tana zagaya girar,caraf taji ya kama hannunta,ya riqe da kyau cikin tattausan tafin hannunsa,cikin murya dake cike da mayen bacci yace
"Am sorry angel,hannunkin nan mai laushi da yawa zaya hanani yin bacci,har gwara kici gaba da kallona,na baki dama,ina jinsa kamar garkuwa ne a tattare dani" yana gama fadin hakan ya sanya hannuwan nasa qasan kuncinsa yayi filo da tafin hannun nata,yana kuma sake gyara kwanciyarsa sosai cikin jikinta,kamar qaramin yaron dake jin rigima ya samu mamarsa ta dorashi kan cinyarta.
Kunya da mamakin yadda baccinsa ya katse,ya kuma fahimci kallonsa takeyi ya kamata,sai tayi shuru kawai tana murmusawa kadan kadan,har zuwa sanda itama nata baccin ya iso,ya rinjayeta,sai gashi a hankali ta kifa fuskarta a tasa,sannu a hankali suka fara musayar numfashin juna.
Shi ya fara farkawa,amma sai ya gaza motsawa saboda yadda tayi masa rumfa,cikin jikinsa ya dinga jin wani abu yana shigarsa yana ratsashi,ya dinga sauke murmushi shi kadai,zaiso su tabbata a haka,saidai kuma yana dan motsawa kadan itama ta farka,ta kuma tashi da sauri cikin kunya da mamakin yadda gaba daya tayi male male a jikinsa,daga kanta zuwa qirjinta.
Juyowa yayi sosai yana fuskantarta kamar dazun da idanuwansa da suka dan kada kadan sabida baccin daya tashi a shi
"Yunwa nakeji,please ayimin taimakon gaggawa" kai ta gyada masa tana murmushi dake nuna zallar kunya
"Uhmm madam,a taimakeni,tsohuwar yunwa ta tashi" da ido tayi masa nuni kan ya dagata,bai dagata ba ya tsareta da ido amma girki yakeso,mirginawa gefe yayi da sauri yana cewa
"Ya salam.....afwan" abinda ya bata damar tashi kenan,ta dauki ribbon dinta daya zame yayi nasa waje ta tattare sumarta mau santsi waje daya sannan ta tashi,yana kwancen har yanzu cikin mutuwar jiki yana qare mata kallo,idanuwansa suna lullumshewa,shi daya yana sake tsumuwa da ganin surarta,kasancewar yanzu babu hijabi a jikinta.
Har takai qofa taji yace cikin wata irin murya daya cika taushi da yawa
"Angel moon" sai ta tsaya cak ta waiwayo,murmushinsa shine abu na farko data fara gani sannan ya motsa bakinsa,cikin wani slow ya furta
"I love you"....." Wani kunya ya bata yadda ya furta mata maganar,da kuma yadda ya kafeta da idanu,sai ta juya da dan sassarfa ta fita a dakin,bata tsaya ba sai datakai kitchen,sai ra jingina da freezer din cikin kitchen din tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya gami da murmushi mai taushi,ko wanne second da zaizo ya wuce mamaki J yake bata,completely ya canza,wai dama haka yake?,sai ta tuna wani hira da suka taba yi da afra,a sannan ta dauka sharrinta ne,bata gasgatata ba sai yanzu
"Hmmm,rabu da miskilallun na masu jin izza da isa,da yawansu idan kikaga yadda suku sukurkucewa akan soyayya sai sun baki tausayi,Allah saiki rainasu inda xaki gansu gaban macen da suka matowa,amma suna fitowa waje sai suyita wani izza suna muzurai" saita sauke wani sabon murmushin,ta taka zuwa tsakiyar kitchen din,kwanyarta na mata searching,cikin abubuwan data karanta a dairy din shaheeda a favourite food nashi,wanne ne mai sauqi da zata dafa masa.
Rub da ciki yayi bayan ta fita,ya jima a haka yana hasashen yadda yakeji a jikinsa akan maimunatu,da yadda soyayyarta tayi masa wani irin kamu,yana jin buqatuwa sosai zuwa gareta,saidai yanason ya bata space,kada ta dauka jikinta kawai.shine abinda yake buqata.
Toilet ya shiga yayi aswaki da miswak na Aarak,wanda indai yayi bacci irin hakan yakeyinsa,ya fesa mouth fresh a bakin nasa bayan ya daura alwala sannan ya fito,yanason ya qarar da dukka lokacinsa tare da ita.
Sam sam bataji shigowarsa ba,sai tsintar kanta tayi jingine a qirjinsa,ya zagaye ta ta qugunta,ya sanya hannuwansa saman plate tummy dinta,ya kuma dora kansa saman kafadarta yana leqen abinda take dafawa,da muryar dake wanzar da soyayya a zukata ya fara magana
"Shine kika gudu?,bayan ko kwatar abinda yake raina ban gaya miki ba?,lemme tell you one to two reasons that make me love you" sai ya sake mannata cikin jikinsa sosai kamar xai maidasu abu daya,ya sake qas da muryarsa
"I love you because you make me feel again that am worth something.....i love you because you make me smile when I almost forgotten how to.....i love you angel for so many reasons" gaba daya kalamansa sun kashe mata jiki,kawai saita kasa ci gaba da yanka dankalin da takeyi akan chopping board,tana riqe dai da wuqar kawai a hannunta.
Sakinta yayi daya lura da haka,sai ya zame ya dawo gabanta,ya karba wuqar ya fara yayyanka mata da sauri da sauri,har yadda ya iya ya bata mamaki,yana yankan yana daga kai yana kallonta kamar zata bace masa,hakan ya sanya saura kadan ya datse hannunsa,don haka ta karba aikinta tace ta gode
"Ko kin koreni ba inda zani" narai narai tayi da fuska,zuciyarta cike fal da saqonni amma kuma nauyi da kunya hadi da rashin sabon da har yanzu basuyi ba ya hanata furtawa,ya gama karantar qwayar idanunta da kyau,don haka murmushi kawai ya saki
"A juri zuwa rafi da tulu diban ruwa" ya