Advertisements
Chapter 53 Reading Gurbin Ido Complete Hausa Novel BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Gurbin Ido Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Complete Novels

Chapter   53 / 67

156K to 159K   out of 200.8K words

ba zata yarda tayi hakan ba.



Alwala ya shiga ya daura da ruwa me dumi,abun sallah ya shinfida,ya tsaya sosai akai yana fuskantar ubangijinsa,ya masa baiwa a rayuwa har karo biyu,a cikin wannan rintsin rayuwar da mata na gari ke tsada da wahala,duk kuwa da cewa duniya cike take da tarin mata birjik,amma ta aure wahala take,saidia shi din ya kebanceshi da baiwa ta musamman.



°°°°°°°°°sai data yi kusan minti biyar da farkawa amma bata motsa ba,a hankali take shaqar tattausan qamshin dake fita daga jikinta jacket din nashi da har yanzu itace a jikinta,qamshin da babu abinda yake tuna mata sai daren jiya,abubuwan da suka faru suka runga dawo mata,sai ta dinga jin komai kamar a mafarki,kwanyarta ta dinga tuno kalaman da bakinsa suka dinga furta mata,sai ta sauke ajiyar zuciya me nauyi,ta kasa kunnenta taji ko zataji motsinsa ta koma ta sake lafewa?,jin shuru ya tabbatar mata da baya dakin kwata kwata,don haka ta miqe ta zauna sosai tana kallon lokaci,qarfe kusan sha daya da rabi na rana,tun asuba data yi wuf a daddafe tayi sallarta ta koma bata sake farkawa ba sai yanzu.



Zaune tayi tana qiyasta da yadda zata miqe,ko ina ciwo yake mata a jikinta,cinyoyinta kamar anyi ajiyar dutse,duk da ya ragu ba kamar daren jiya ba,sai ta yanke shawarar ta sake shiga bandakin ta hada ruwan zafi ta yiwa kanta yadda yayi mata jiya,tana zuro qafarta qafa taqi bata hadin kai,sai ta narke gaba daya zuciyarta ta karye,kada dai ace ya illatata gaba daya ba zata sake moruwa ba?,idan haka ya tabbata da wanne ido zata yima mutane bayani?,take qwalla ta cika mata idanuwa,ba dadewa kuma suka fara bin kuncinta,dai dai lokacin da ya turo qofar ya shigo.



Fes fararen idanuwansa da suka sake wani haske suka sauka a kanta,yana sanye da wata hoodie jacket wine color da baqin wando,ya sauke hular a bayansa,sai tattausan baqin gashinsa sake sheqi cike a kansa,ya sake wani fresh dashi,jikinsa na fidda rikitaccen qamshin nan nasa.



K'as tayi da kanta tana jin inama bata farka ba,yayin da murmushi ya subucewa fuskarsa,cikin zuciyarsa ya furta



"Yanzun ne ya kamata kiyi tsoro me dalili yarinya ba tsoron baya ba na sakalci da shagwaba" takowa yaci gaba dayi zuwa gabanta,yana ayyana yadda zai dasa zazzafar soyayyarsa a ranta,tunda ya fahimci ya ribatu da samun empty heart da bata taba daukan soyayya me zafi irin wadda yake buri ba,so yake tayi masa soyayyar da ba'a taba masa kwatankwacinta ba,yana buqatar ya samu qauna data ninka wadda shaheeda tayi masa,soyayyar da zata zama abar kwatance,ya riga da ya gama sallama mata rayuwarsa,saboda haka bayajin akwai wani abu da zai musu shamaki a tsakaninsu shi da ita.



"Gudmorning moon" ya fada da wata murya dake cike da shauqi,shauqin da tunda ya tashi har ya fita ya dawo shine taf a zuciyarsa,wani irin memorable night da bazai taba shafewa a rayuwarsa ba muddin yana da rai



"Ina kwana?" Ta fada cikin girmamawa,bai amsa mata ba,sai ya duqa a gabanta,wata kima da daraja ta samu farat daya a wajensa,ba ita kadai ba,hatta anni a yanzun yana jinta fiye da yadda take a wajensa a baya,bare kuma ita maimunatun,hannayensa ya zura ta qasan fuskarta,sannan a hankali in a low sound yace



"Kwana na yana gurinki.....get up dear" fuskarta a narke ta tabe baki irin na mutumin dake shirin sakin kuka,sannan ta langabar da kanta gefe guda,ha fahimci tana son ce masa ba zata iya ba,amma baki ya gaza fada,sai kawai ya miqe a hankali,yasa hannu kamar daren jiyan dai a tausashe ya dauketa ya nufi toilet din da ita,yana tafe yana kallonta duk da ta cusa fuskarta a qirjinsa,da zata iya da tace masa ya sauketa,yanzun ma da ranar Allah sake kalleta zaiyi haihuwar daadarta?.



Bai sanyata dole kan cire kayanta ba,amma ya tsaya ya gasata kamar daxun,mai ciwo yaji dadin jikinta,sai ta fara son qwacewa,sai ya kamata suka antaya ciki gaba daya shi da ita,dole tayi luf,tun tana jin zafi har ruwan ya fara mata dadi,ya sake tara mata wani sannan ya fito ya barta don ta qarasa.



Manyan towel guda biyu tayi amfani dasu,daya tayi daurin qirji dashi,dayan ta lullube kanta ruf,baka ganin komai sai kwantacciyar sumar gaban kanta mai salki,yana tsaye gaba mirror yana kurbar coffee din da ya hado a hankali,ya bude idanuwansa a kan fuskarta.



Sosai yaga fuskartan itama tayi fresh,farinta kamar ya qaru ya kuma sirkuwa da jaja jaja,tsigar jikinsa ta zuba gaba daya,ya hadiye sauran ruwan coffee din daya kurba,sai ya dora cup din saman morrow din,ya nufota a inda take tsaye daga gefan qofar toilet din,tana ta karatun ta yadda zata shirya yana cikin dakin,da kuma kayan da zata saka wadanda ba zasu fidda tsiraicinta ba sosai.



Idanuwanta a kansa kamar yadda nashi yake a kanta,wani abu mai qarfi yaji yana fusgarsa zuwa gareta,wani abu mai nauyi da tasiri da bai taba jinsa a ransa ba.



Tsoro ya hanata motsawa daga inda take,gani take kamar wani abun zai sakeyi mata,ya karanci tsoronta tsaf,sai ya saki murmushin gefen baki har ya isa dab da ita,a hankali ya sauke zip din jacket din nasa qasa,ya kuma balle botiran gaban shirt dinsa me kauri,sai ya qara matsawa taqi gaba kadan ya manneta zuwa cikin qirjinsa,a tare suka sako ajiyar zuciya,yayin da yaci gaba da sauraren bugun zuciyarta yadda yake gudu fat fat,da alama akwai tsoro tattare da ita.



A hankali ya zura hannayenta ya zagaya dasu zuwa bayansa ta yadda zata rungumeshi sosai,shima haka din yayi ,ya zagaye hannuwansa ta bayanta abinda ya qara musu kusanci sosai,ta shige sosai cikin rigarsa,wani irin dumi da unique qamshin nan nasa ya sauka a hancinta,sanyin data soma ji bayan fitowarta yayi qaura,sai ya dora kansa saman kafadarsa,bakinsa saitin kunnenta cikin fusgar kalaman bakinsa sakamakon yadda tudun qirjinta ya fara rikita masa lissafi



"Relax, don't scare,am not going to do anything angel" wata ajiyar zuciyar ta kuma saki,a hankali yaci gaba da shafan bayanta kamar yadda akema qaramin yaro duk sanda yake rigima,tsahon wasu mintuna sannan ya jata a hankali,suka dinga takawa kamar me koyon tafiya,saboda yasan akwai mikin ciwo a jikinta.



Gaban mudubi ya tsaidata,sannan yaja mata kujera ya kuma zareta daga jikinsa yace



"Seat here" a hankali ta zauna tana rintse idanunta saboda yadda wajen har yanzu yake mata ciwo,ya lura da hakan,sai ya saki boyayyen murmushi,wani sashe na zuciyarsa kuma na jin tausayinsa kan barnar da yayi mata.



Man shafawarsa ya dauko,ya bude ya dora saman mirror din,ya lakato ya daga tattausan tafukan hannunta da kallo da suke jazur, saboda tsaban fari har wani kwanciyar jini sukayi,ya lakata mata man sannan yace



"Lemme help you" sai ya koma daga bayanta ya fara shafa mata a baya.



Idanunta ta lumshe kawai,zallan mamakinsa suna sake shigarta,kamar ba ja'afar ba,ja'afar din anni da amma,gaba daya kamar wani ja'afar na daban aka sauya mata,dukka ya kwance gaba daya.



Wasu abubuwa taji suna mata yawo dukka jikinta,in a romantic way yake mata shafan man,tana iya kallonsa ta cikin madubin yadda gaba daya yanayinsa ya canza, tsoro ya sake cikata,ta riqe kukanta da kyau wanda ke shirin qwace mata,idan yace zai sake wani abu da ita ta tabbatar mutuwa zatayi,ba zata iya sake dauka ba.



Sosai ya dinga qoqarin controlling kansa,bayan ya gama shafa mata zuwa inda yasan ba zata iya ba sai ya dauko hand drayer, already ya iya wannan,shike gyara ma su amna da amra kai sanda suna raye,harma shaheeda,tunda dukansu suna da yawan suma,mamarsu ce kawai bata kaisu ba,don su shi sukayo wajen yawan sumar,don baya sati baiyi gyaran fuska ba,tunda ba kasafai yake rage sumar kansa ba.



Tsaiwa yayi shi da kansa yana kallon innocent face nata ta madubi bayan ya gama gyara mata gashin ya kuma kame mata shi da band,fuskarta ta fito fayau kuma tayi wani irin fes,idanunta sun sake girma da haske,hakanan siraren labbanta kamar an sake qawatasu,sai ya sunkuya yayi kissing tsakiyar kanta yana lumshe idanunsa.



Dukka kayanta noqewa tayi taqi sakawa,daya fita ya bata option na ta saka kayan da taga sun mata a dakin,har nashi luggage din ya bude mata yace ta zaba.



Wata farar turtle neck shirt nashi ta dauko,tana da dan kauri,sannan itama dogon hannu ne da ita,a sake take,don ba size dinta bane,ita ta saka,ta tsaya tana duban kanta a madubi,rigar tayi mata kuma tayi mata kyau sosai,saidai kuma tana kunyar ya ganta da kayanshi a jikinta,ta lumshe idanu tana shaqar daddan qamshin dake fita daga jikin tattausar rigar,batasan me yasa qamshinsa yake kashe mata jiki ba,bata gama wannan tunanin ba ya buda qofa ya sake shigowa dauke data leda mai kauri,sai ta bude fararen idanuwanta da sauri.



Kamar wani sakarai ko kuma yau ya fara ganinta haka ya saki baki yana kallonta,bai taba ganin kyan rigar ba sai yau data sanyata a jikinta,kallon kallo sukaima juna kafin ta janye kallonta daga kansa,ya tako a hankali zuwa ciki yana ajjiye ledar,zuciyarsa nason ya qarasa gareta amma kuma wani sashen yana masa burki,yana kuma gaya masa



"Dole ka bita a hankali,sai ka rage tsoronka daka dasa mata tukunna, ayanzun a tsorace take dakai,dole kadan nisanceta kadan" da wannan shawarar ya samu waje ya zauna,ya fidda komai dake cikin ledar,breakfast ne da qamshinsa ya cika dakin,da alama wadanda suka tsarashi sun san sirrin girki



"Oya,come and take your breakfast" yayi maganar da mayen kallon nan nasa,qas tayi da kanta,sannan ta fara takowa a hankali,yabi qafafunta da kallo,yadda take tafiyar kawai ya isa ya shaida maka lallai wani abu me girma ya faru da ita.



Suna cikin yin break din wayarsa tayi qara,sai ya duba me kiran,jabir ne kamar yadda ya zata,daga wayar yayi,amma sai ya sanyata a hands free ya dorata saman cinyarsa,idanuwansa akan fuskarta yayi masa sallama



"Yallabai,wai anya kuwa lafiya?"



"Me ka gani?" Ya tambayeshi kai tsaye



"Jiya nayita bugu na baku dinner dinku,yauma da safe haka zamu wuce strolling da fa'eema zata dan ga gari shima shuru" sai da yayi sipping coffee dinsa sannan yace



"To sai akayi yaaya?" Dariyar da yaketa riqewa ce taso fitowa,ya sake danneta



"A'ah wai kada ka mace ma mutane a daki ne,shi yasa nake cigiyarka,kuma jiya da dare naji dakin kamar ba lafiya ba,har zan kawo dauki fa'eema ta hanani" tsaki yaja yana saurin kashe wayar daga hands free din da ya sakata ya karata a kunnensa



"Amma qur'ani cewa yayi idan baku samu kowa cikin gida ba kada ku shigesu har sai an muku izini,idan ma akace ku koma to ku koma,na meye wannan bin qwaqwafin?,ni bazan huta ba?,ko kai kadai ne me iyali?"



"Allah ya baka haquri,daga abun arziqi?" Yayi maganar yana tuntsirewa da dariya,fatima nata mintsininsa da yi masa sign na ya daina don Allah,don shike maganar amma ita kejin kunyar, batasan yadda zasu hada ido da ja'afar ba,tana matuqar girmamashi



"Inda kazo min daki a jiyan ma saina farfashe maka kai,banyi laifi ba"



"Sai ogaaaaa,tuba nake" ya fada dariyarsa na fita gaba daya



"Da anni fa zan kira.....wallahi nace mata ba lafiya ba" ya sake fada cikin wani karsashi tare da son sake tunzuro ja'afar din



"Sai ka bada himma" daga haka ya yanke wayar kit,wani murmushi da baisan daga inda yake ba na fita a fuskarsa, jabir jabir?,dan uwan da babu kamarsa,yasan ya fahimci komai,don yaga gilmawarsa a fitar da yayi,ya kirashi ne kawai ya zolayeshi,kuma sai yayi din sannan hankalinsa zai kwanta,jabir ya masa haka ina ga anni,gardin case kenan,ya fada a ransa.

69

Ya tabbatar anni ba zata qyaleshi ba ba zata daga masa qafa ba,ko a yanzun ma baisan wanne kalar tijara zata masa ba idan ta fahimci abinda yake faruwa.

"Gaskiya kana sakani jin kunya wallahi" fatima ta fada tana jifan jabir da harara,ga mamakinta murmushi ne kwance saman fuskarsa,amma kuma hawaye ne ke shirin sauko masa,sosai hankalinta ya tashi

"Sweetheart.....menene?" Hannunta ya kama ya riqe gam yana duban fuskarta

"Real version na ja'afar dina ne ya dawo, alhamdulillah.......bansan wanne kalar godiya zan wa Allah ba,bansan wanne kalar godiya zan yima maimoon ba......jikina ya bani,sannan yanayinsa ya nuna tun daga yadda yake amsa wayata,my ja'afar has back" Sai siraran hawaye suka biyo gefan hancinsa,ajiyar Zuciya ta sauke,ta kuma riqe tafukan hannuwan nasa da kyau

"Alhamdulillah,ita zaka yita maimaitawa,sai kuma ka yawaita yima annabi salati saboda nuna zallar godiyarka ga ubangiji" kai ya jinjina yana sake qaunar matarsa,ko yaushe kalamanta akwai Allah a ciki

"In sha Allah,bansan da waa zan raba wannan farincikin ba bayan ke.....kinsan inda daa ne,ko uffan bazaice min ba,har nayi na gaji na gama,abinda bamu saba dashi ba kenan,duk miskilancin sa babu ni a cikinsa" kai ta jinjina,ita kanta taji dadin hakan sosai.

Wuni sur a dakin sukayishi shi da ita,shima kuma jabir bai sake namansa ba,sosai ta dinga dari dari dashi da kuma jin kunyarsa,don da daddare bayan ya sake sanyata ta gasa kanta,tana tsaye bayan ta fito amma taqi kallonsa,sai ya qaraso gabanta,ya dora hannunsa saman nata sannan ya dagasu ya dora kan kumatunsa na hagu da dama

"Me yasa bakison kallo na?,har yanzu tsoro na kike?,irin tsoron da nake gani a idanunki yanzu,irinsa na gani sanda hannuwana sukayi kuskuren marinki......na baki dama,ki rama marinki adadin yadda kikeso" zame hannunta tayi da sauri tana girgiza kai,ta kuma kasa ce masa komai

"Just do it....kar kiji komai" sake girgiza kanta tayi,bakinta yana rawa

"N......na yafe" shuru yayi yana sake zuba mata idanu,hannayensa zube a aljihun wandonsa yana kallonta,baya gajiya da kallonta kwata kwata,sai ya taka a hankali ya rungumeta ta baya,cikin wani sauti da yafi kama da rada ya soma magana

"Tun randa hannuwana suka kai kan fuskarki na gaza mantawa da abinda nayi mikin,nakeji ban kyauta ba,ban sani ba.....ko tun a sannan ubangiji ya zuba dukkan abinda zai zuba a tsakaninmu?,a lokacin da nake jin duk duniya ba wanda ya kaini rashi,na mareki ne a lokacin da nake cikin tsananin damuwa na rasa shaheeda da amra ta,bisa dukkan alamu Allah ya bani wata shaheedan......zaki samar min new amra?" Karon farko da murmushi mai cike da kunya ya qwace mata,sai ta juyo ta cusa kanta a qirjinsa tana murmushi,kafin kuma ta zare jikinsa a nata,binta yayi da kallo,baiso hakan ba,yaso ne su dan jima a tsaye ko hakan zai rage masa zafi.

°°°°°°°°°dukka kwanakin ukun da suka biyo bayansu kusan biqinta ya dinga yi,bai sake neman komai daga gareta ba,saboda ya tabbatar ta jigata a hannunsa,duk kuwa da cewa kawaici kawai yakeyi da kuma qoqarin kame kansa,amma yana ji a jikinsa,har yanzu bata sake masa jiki yadda yakeso ba,yanata qoqarin ganin yabi kowacce hanya data kamata da zai dasa mata soyayyarsa a ranta mai zafi,amma baiga alamun komai ba daga gareta,saidai shi din ya yadda da kansa,ya kuma tabbatar babu.macen da zata iya tsallake tarkonsa.

Shirinsa bai kammala ba,don haka sanya jabir ya gabatar masa da batun komawa sai ya dubeshi

"Wai nikam duka kwana nawa mukayi?" Cikin mamaki da dariyar yadda lissafi ya bacewa ja'afar din nasa yace

"Iya kwanakin da na gaya maka mana,har ka manta?"

"Gani nayi kamar bamu qarasa ba ko?" Yayi tambayar kamar yana kokwanto,dariya dai sai data zowa jabir

"Akramakallah mr ja'afar,kace kawai honeymoon yayi dadi" cikin basarwa ya dauke kai ya kuma sake hade fuska ganin jabir din yanason ramfoshi

"Mtsweew,matsalata dakai kenan,kawai akwai wasu ayyuka ne da ban kammalasu ba,banason kuma su zame min kwantai"

"Gaskiya ne yallabai.....saika bada himma,zaka iya kammalasu nan da yammacin gobe kafin tashin jirginmu ai,musamman idan ka samu network me kyau" kai tsaye ya fahimci inda jabir yasa gaba,sai ya shareshi kawai bai tanka masa ba.

Gyaran murya jabir din yayi

"Munata waya da anni ne,tana complain na an koma makaranta bamu dawo ba,maimoon din anata kira daga makarantarsu,har sunci satin farko".

A sukwane ya waiwayo yana duban jabir din,sai da yaji zuciyarsa ta tsinke,tabdijan,ai shi gaba daya ma ya ma manta da wani batun makarantarta,ci gaba yayi da duban jabir din kamar wanda ke neman mafita daga garesa

"Yaya dai?" Ya tambayeshi yana dubansa,kansa ya dauke

"Nothing,kawai babu yiwuwar ta koma din"

"Banjin anni zata bari gaskiya,don tanata maganar kada a katseta"

"Eh,tunda ita ke aurenmu ba ni da ita?" Baki jabir ya bude dariya na matuqar cinsa

"Annin?"

"Eh maryam farouq kumo ba" idanu jabir ya fidda gaba daya sannan ya miqe shima kamar yadda ja'afar ya miqe

"Ah wallahi ka sha kaina,kafi qarfina,an tashi a wasan,zaka maimaita kuma a gaban wadda ka kama sunanta"

"And so what?" Ya fada cikin rashin damuwa,tunaninsa a yanzu shine kawai yadda zai fuskanci anni da maganar qin maidata makaranta,musamman idan ya tuna yadda kwashe dashi sanda take shirin hanashi kaita,hannunsa ya sanya ya shafi sumar kansa tare da furzar da iska daga bakinsa.

°°°°°°°°°°°tun saura awa guda jirginsu ya tashi zuwa nigeria suka isa OR tambo international airport din,don haka dole suka zauna a gates zaman jiran cikar lokaci.

Jabir da ja'afar gaba daya suna waje basu shigo ba,sai ita da fatima,jifa jifa suna taba hira da ita,saidai hankalinta gaba daya ya kasu kashi biyu.

Kashin farko yana ga qofa,tana duban ta inda ja'afar din xai bullo,yau kawai da suka dauki mintuna ba kusa da juna ba sai takejin kamar tayi missing wani muhimmin abu,daya kuma gefen hankalinta yana ya daukuwa ne ga wasu matasan yara su biyu,dayar a qalla zatayi shekara goma,yayin da dayar kuma takai kusan shekara sha biyar,tunda suka zauna a wajen take kallonsu,fuskarsu taketa kalla,sai take ji cikin jikinta da ruhinta kamar ta sansu,kamar ta taba rayuwa da ita,abu na biyu kuma mamarsu da tunda suka shigo wajen fuskarta na kallon babban glass dake wajen,wanda ta nan kana iya hango farfajiyar airport din da jiragen dake girke a wajen,shuru ita daya,bata magana da kowa,saidai lokaci bayan lokaci takan waiwayo tayi ma yaran dake amfani sa wata tab da alama game suke,ta musu magana ta sake maida kanta ga wajen,kamar wadda ke cikin wani zuzzurfan tunani.

A duk sanda tayi magana sai maimunatun taji gabanta yayi mummunar faduwa,saboda sautin muryar irin tata sak,kuma irin ta daadarta,saidai sautin yafi nata nuna shekaru,batasan mene yaketa fusgar hankalinta akanta ba,ta kuma gaza ganin fuskarta,sannan kuma ta gaza dauke idanuwanta daga kan

53 / 67